Showing 249001 words to 252000 words out of 438336 words
“Amma Baba kana fa jin abinda ya faɗa min, wlhy sai naci uwar yaron nan a gidan nan. Yanzu har lalacewar wannan gidan takai kamar Awwab ya gaya min baƙaƙen magana a gaban Mu'azz amma yay kamar baima ji ba. Ba shi ba hatta uwarsa a gabana aka haifeta.”
Cikin damuwa da ɗan ɓacin rai Paah ya ce, “Amma Adda mi kike so nace muku?. Duk dai mai hankali yaji wannan furucin na Muhammad zai fahimci akwai wani abu a tsakaninku ke da shi. Tabbas Muhammad bashi da ragowa, kuma in ransa ya ɓaci komai yazo bakinsa faɗa yake, amma tunda muke da shi bai taɓa maidama wani murtani ba a cikinmu sai yau. Duk kuwa abinda kiga Muhammad ya magantu a kansa to lallai wannan abun ya kai karen kure. Kuma ni kam gaskiya zuwa yanzu zuciyata ta fara bani akwai abinda yaron nan ke ɓoye mana, inda ace abinda ya faru a farko ne kawai zan iya yarda ƙaddara ta kaisa ga aikatawa. Amma muyi tunani, Muhammad fa duk da tsagerancinsa bazai zauna yana lalata yara ba irin haka a cikin gidan nan, dan duk da mahaifiyarsa na'a halin rashin lafiya bai haɗa mutuntakarta da komai ba. Mudai ƙara bincike gaskiya. Domin mu dukanmu mun san waye Muhammad”.
Da ga haka ya miƙe abinsa ya fice shima. Shiru falon yay babu wanda ya iya motsawa. Sai Hajiya Mammah dake wani irin cika da batsewa da famar jinjina kai. Ta bakin baba prof kowa ke son ji amma babu alamar zai ce wani abu. Sai ma miƙewa da yay shima ya fice a binsa. Ganin haka shima Uncle Abdullahi da Matarsa suka miƙe. Wani irin shegen murmushi Hajiya Ƙarama da ke kallon Hajiya Mammah ta ƙasan ido ta saki, sai kuma ta mike itama batare da tace komai ba ta fita. Dan ta ciki na ciki ne kawai.....
🪴🪴🪴🪴
Watanni huɗu kenan Mamy na gida, babu labarin Mansoor tako ina. Gashi Dad baizo gida ba kuma kowa bai sanar mata ya saketa ba ko bai saketa ba. Gaba ɗaya ta fige ta rame saboda damuwa. Dan har ga ALLAH tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Ta tura masa text message yafi sau dubu. Ta kirashi yafi sau dubu goma. Amma babu amsa babu reply na masseges ɗinta. Ga ciwo ya addabeta a tsaitsaye har dai sai da ta kaita da kwana asibiti ranar. ALLAH sarki Attahiru shine tsaye akan komai. Ganin fa yanda jikin Mamy yay tsamari a wannan karon yaje ga Dad ɗin su ya dinga kuka yana roƙonsa ya yafe mata, sannan ko sau ɗaya yazo ya ganta. Dan sam Mamy bata a cikin hayyacinta. Babu abinda take faɗi sai neman gafarar Dad ɗin. Da farko Dad koran Attahiru yayi, sai da yaga yanda ya riƙe ƙafafun nasa yana rabzar kukan abin tausayi sannan. Dan har ga ALLAH a yanzu tausayin babban ɗan nashi yake yi. Attahir akwai haƙuri, gashi da son ƴan uwansa. Ga biyayya a gare su. Yanzu tunda aka fara abin nan yazo neman ma Mamy afuwa ya masa gargaɗin kada ya sake masa maganar ta bai sake koda kwatantawa ba duk da abin na damunsa. Amma kullum dare yana lura da shi sai yaci kuka. Haka kuma zaita salla yana neman ɗaukin UBANGIJI da yima Mansoor addu'ar ALLAH ya karesa a duk inda yake. Shima sai hakan yaja hankalinsa yake tashi yin ibadar daren.
Yanzu da yake roƙonsa duk sai jikinsa yay sanyi, kamashi yay ya rungume. Sun jima a haka kafin ta ɗagosa yana lallashi. Ya kuma tasashi gaba suka je asibiti suka duba Mamy. Abinda Dad ɗin yayi ya faranta ran kowa. Dan duk wanda yasan Mamy yasan ta horu da horonsa matuƙa. Wannan zuwa na Dad shi ya kawo masalaha ga ciwon Mamy, ta dinga jin sauƙi har al'amura suka fara daidaita. Koda aka sallameta sai suka koma gida. Nan ma ta cigaba da roƙon Dad ɗin gafara yaran suka tayata har sai da yace mata ya yafe mata. Ya kuma kafa mata sharuɗa da dokoki. Ko guda ɗaya kuwa bata musa ba a ciki. Doka ta farko data fara bi shine shiryawa sukaje har gidan Abba suka bashi haƙuri tare da neman gafarar Abban da sauran mutanen Gwarzo da basu wuce ba da su Gwaggo Gudidi. Sun so ganin Yaya Musaddiq aka sanar musu ai ya wuce Chaina yau ne ma ranar tafiyar tasa zai bi ta Lagos. Abin ya basu mamaki. Sun kuma tayashi murna. Sun kuma yi alkawarin zuwa weekend zasu je har gwarzo domin bama su Kawu Musa haƙuri, dan su tunda suka zo aka ɗaura aure da su suka kama gabansu tunda bikin bana ɓangaren su bane ba.
Wannan ban haƙuri da su Mamy suka zo sukayi har gida ga ƙonama Mom rai, dama ga baƙin cikin tafiyar Yaya Musaddiq na cimata zuciya. Har ta kasa haɗiyewa sai da tai ta zabga habaici. Da yake dama Abba a ƙufule yake da ita akan tafiyar Baby basu bari ta masa sallama tama danginsa ba ya ce idan har Mom ta sake cewa ko uff a bakin aurenta. Dan ya tsinke sauran igiyoyin biyu da suka rage. Wannan magana ta matuƙar girgiza Mom da duk danginta. Nan fa suka shiga tausarta da nuna mata kuskurenta. Daga nan akayi zaman sasanci aka sakata bama Abban haƙuri da su Gwaggo Gudidi....
🌜🌜❤️🌛🌛
Tunda ya shigo ɗakin yay tsaye kawai yana kallonta nannaɗe a ƙasa kamar ƴar mage. Barcinta take hankali kwance. Kaɗan ya ɗan jaa idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya buɗe. Durƙusowa yay ya ɗauketa gaba ɗayanta ya maida a saman gado, kafin ya shiga ƙoƙarin zame mata hijjab ɗin. Firgigit ta buɗe idanunta dake jajur duk sun ɗan kumburo alamar anci kuka an gode ALLAH.
Sosai ƙirjina ya shiga bugawa da sauri-sauri ganin yanda ya ranƙwafo kaina, zaram nayi ƙoƙarin tashi jikina na rawa, sai dai zafin daya ratsani ya sani komawa da sauri na kwanta hawaye na ziraro min. Cikin ɗan jujjuya masa kai, lips ɗina da suka sha wahala a wajensa na rawa muryata a ɗashe na ce, “Please Ya Awwab don't do wahala for me again. Wlhy zan iya mutuwa. I'm just 23years only zakai child abuse fa”.
Shiru bashi da alamar cewa uffan, sai idanunsa masu tsananin kaifi da ya zuba min kawai kamar zai cinyeni da su. Cikin kuka sosai na sake buɗe baki zanyi magana ya ɗaura yatsarsa manuniya akan lips ɗin nawa yana mai sake matso da fuskarsa gab da tawa ya ce, “Shiii! Oya sleep”. Ya ƙare maganar can cikin maƙoshi da ɗaura hannunsa ya rufe idanuna. Babu musu na rufe ɗin duk da a cikin tsoro nake. Tun ina ɗari-ɗari har wani barci mai daɗin tsiya yay awan gaba da ni saboda yanda yake shafa kaina a hankali.
Ganin yanda ta fara sauke numfashi a hankali alamar tayi barci ya sashi yin ɗan guntun murmushi. A hankali ya furta, “You are a tiger, Samrh”. Sai kuma ya sake sakin murmushin gefen baki saboda tuno kalmar child abuse data faɗa. Sam yarinyar nan bata jin magana. Ga baki kaman parrot. Vibration ɗin da wayarsa keyi alamar shigowar kira ya katsesa da ga kallon da yake mata. Dan kallon wayar yay dake a kan side drawer. Sai da ta kusan tsinkewa kamar abin dole kafin ya kai hannu ya ɗauka. Ɗagawa yay ya kai kunnensa yana ƙoƙarin barin wajen. Koda Juliet da tai kiran ta gaishesa a taƙaice ya amsa mata. Bata damu ba ta fara masa bayani kan aikin da ya sakata. Ta tabbatar masa ta kammala komai yanzu haka jirgin da zai taho da shi ya ɗakko hanyar Nigeria. Cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara ya lumshe idanunsa dake canja launi. Shi kaɗai ya san mi yake ji a zuciyarsa, amma zai jure in sha ALLAHU. Sunayin sallama kiran Hayatu na shigowa. Gaisawa sukai shima sannan ya bama su Yaya Musaddiq suka gaisa. Kasancewar tafiyar ta Musaddiq sai dare ma ya bama Hayatun umarnin zagayawa da su suga gari zuwa anjima sai ya kawosu nan. Dan yau shi bazai fita ko ina ba zai yini a gida.
Murmushi Hayatu yayi da ga can, amma duk da haka sai da ya tambayesa ko baida lafiya. Dan yasan abinda zai iya hana ogansa kuma yayansa fita ba ƙarami bane. A taƙaice yace masa no kawai ya yanke wayar, Hayatu ya jima shiru yana nazari sai kuma yay ƴar dariya. Anya kuwa! Anya ogan nasa bai faɗa lobayyar pepper ƙanwar tasu ɗin nan ba. Rashin mai bashi amsa ya sashi haɗiye komai ya cigaba da sabgarsa.
Shi kam koda ya kammala wayar shiru yay a cikin kujerar lafe na kusan mintuna ashirin, kafin ya miƙe a hankali ya bi ƙofar dake sadashi da Ummie, ko'ina fes sai ƙamshi yake, ganin kwanikan abinci ya sashi tabbatar da har ta karya. Kusa da ita ya ɗan zauna ya shafa kanta dan barcinta take hankali kwance. Ga wani irin annuri da fuskanta keyi ƙyawunta da dauɗa ya dusashe na sake fitowa. Hawaye ne ya cika masa idanu, amma sai ya haɗiye su dan ƴan mazan maza ne akoda yaushe. Ya ɗan jima a ɗakin har Mama Balki tazo ta samesa duk da yanda kansa ke juya masa da ciwo. Bayan sun gaisa yana ƙoƙarin danne damuwarsa da ciwon da kansa ke masa yay mata bayanin a saka cikin yaran can wasu su gyara sashen Fahad. Yana gama faɗa ya miƙe da sauri ya fice a ɗakin kamar wanda ake tunzurawa. Da kallo Mama da har tsigar jikinta ke tashi da jin wannan batu ta bisa. Sai hawaye sharrr suka shiga ɓulɓulo mata, ga murmushin farin ciki. Wani irin ƙaunar Samraah na ratsa mata zuciya. Yarinyar nan ta cika alƙawarinta kenan. Dan dama ta mata alƙawarin sai ta masa maganar dawowar Fahad ɗin gida. Kasa haƙuri tayi sai da ta koma ta sanarma mijinta. Shima farin cikin ne ya dabaibayesa har murmushi ya gagara barin fuskarsa. Ranar da wannan farin cikin suka yini, tuni kuma an saka masu aiki gyaran sashen Fahad dake manne dana Maash ɗin batare da kowa ya sani a gidan ba. Dan su suna can ma ran kowa ɓace da abinda Maash ɗin ya musu yau........✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 twenty-nine
.......A hankali Maman Malika da tun da suka dawo sashensu ta ɗago ta kalla mijinta. Shima dai zaune yake shiru da alama akwai abinda yake tunani. Agogo ta kalla sannan ta sake kallonsa. Murya a sanyaye ta ce, “Abban Muhseen yau bazaka fita aiki bane wai? Time fa yaja sosai”.
Numfashi ya sauke a hankali, kafin ya kalleta fuskarsa na nuna damuwa sosai. “Zanje Mubeena. Al'amarin gidan nan ne ya fara damuna wlhy. Daga wannan sai wannan. Ga yaron nan sam baya ganin girmanmu. Shi kuma Yaya baya ƙaunar laifinsa sai ma kiga kamar yana tsoron sa.”
“Humm Abban Muhseen ba tsoro bane ba. Sannan wlhy Awwab bawai baida mutunci bane ko kunya. Yaron yana cikin damuwa matuƙa. Ku kuma kun kasa fahimtar hakan. Kowannenku abinda ke gabansa kawai yake yi. Yanzu ko maganar nan daya gayama Adda fa abin a dubace. Dan babu rami miya kawo rami? Tabbas akwai abinda Addar ta sani game da abinda ke faruwa. Idan fa baka manta ba ko waccan ranar ita ta fara fasa zancen yama yarinya fyaɗe, duk da ana cikin tashin hankalin zuwa kamashi ita ba wannan bane damuwarta. Yau kuma itace fa ta tashemu a barci jiya. Ƙarfe sha biyu da wani abu bata kwanta ba mi take yi? A barshi ma batai barcin ba, miya kaita sashen Awwab har tasan yana aikata wani abu? Mufa buɗe zukatanmu mu kalla gaskiya a matsayin gaskiya in ba hakaba ALLAH zamu yi dana sani. Kadai san halin Adda ai da fitinarta, musamman daya kasance burinta a gidan nan Awwab ya auri Azizat. Baka tunanin zata iya shirya komai dan hakan ta kasance tunda an bisa ta lalama, an bisa ta tsiya duk yaƙi. Sannan na fara ji a jikina akwai abinda Awwab ke ɓoyewa a gidan nan. Babu yanda za'ai duk rashin kunyarsa ya dinga lalata yara a cikin gida mudai nemo gaskiya.”
Sosai maganganunta suka shigi Uncle Abdullahi. Yay shiru yana nazarin kowane harafi dalla-dalla da yi masa fashin baƙi....
🪴🌼🪴🌼🪴
Tunda ta iso asibitin ta gagara taɓuka komai. Sosai abinda ya faru a gidan keta mata faman kai kawo a zuciya. Kalaman Awwab sun farkar da ita wasu abubuwa. Tabbas sau biyu tana kama Hajiya Mammah ta fito a sashen Awwab, na farko ranar da ta aiki Yarinyar nan da abinci, na biyu daren ranar da abin ya faru kusan misalin ƙarfe ɗaya ta fito daga ta backyard kamar wacce ke a firgice. Abinda yasa a lokacin bata maida hankalinta a kanta ba itama daga wani waje ta dawo. Abu na uku Hajiya Mammah ta damu akan zancen fyaɗen nan a safiyar ranar, sannan jiya ma itace tazo musu da zancen ga Awwab da wata. Da farko bata damu ba, sai yau da safe data bincika yarinyar nan a sashen masu aiki akace mata bata dawo ba ai. Bata samu damar ƙarasa binciken ba Baba prof ya iso gidan..
Mikewa tai tana mai girgiza kanta, dolene taje ta ƙarasa binciken data fara kafin wankin hula ya kaita dare. Daga nan tana buƙatar yin magana da Yallaɓai a wannan gaɓar. Handbag ɗinta ta ɗauka ta fice a office ɗin. Ko kallon tulin patients ɗin dake zaman jiranta batai ba dan hankalinta ma baya a kansu gaba ɗaya.....
✨💞✨💞✨
Barci sosai nasha. Dan ban tashi farkawa ba sai wajen sha biyu. A hankali na buɗe idanuna bakina na ambaton sunan ALLAH da karanto addu'ar tashi a barci kafin na yunƙura da ƙyar na tashi zaune saboda ciwon da illahirin jikina ke mun. Sam banyi tunanin yana a ɗakin ba, dan haka na miƙe cikin ƙarfin hali saboda wani irin fitsari nake ji sosai. Wani irin motsawa zuciyata tayi sakamakon saukar idanuna a kansa. Zaune yake cikin sofa kamar wani saraki. Laptop ɗin jarabar a saman ƙafarsa sai dai ya saka throw pillow sannan ya ɗaurata. Ta gefensa a saman side table ɗin kujerar bowl ne da chocolate a ciki sai mug alamar ansha coffee ko tea. Ledojin chocolate ɗin da yaci ya zubar a ƙasan na bi da kallo, haka kawai sai naji tausayinsa ya kamani. Dan abinda na fara fahimta da shi kamar bai damu da cin abinci ba sai waɗan nan tarkacen kayan chocolate ɗin. Tabbas koda ace bai son cin abincin akwai ƙarancin gatan mai tsayawa ya bashi ya ɗin.. ganin ya ɗan dakata da danna keyboard ɗin computer ɗin alamar yaji a jikinsa ana kallonsa ya sani saurin kauda idanuna da ƙoƙarin son barin wajen, a ko dai-dai nan ya ɗago manyan idanunsa ya sauke a kaina. Basarwa nayi kamar ban gansa ba na wuce bathroom ɗin. Ina shiga na jingina da ƙofa ina mai sauke ajiyar zuciya mai nauyi da godema ALLAH da ya taimaken bai kamani ina kallonsa ba. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sosai na sake gyara jikina yanda ya kamata, dan har ruwan zafin na shiga. Yau banyin walha ba ina barci, alwala nayi dan naga har sha biyu da kusan rabi yanzu. Hankalina duk yana akan su Yaya Musaddiq shiyyasa ban zauna wani noƙe-noƙe ba na fito sanye cikin bathrobe ɗin sa sky blue. Inda na barsa anan na samesa. Sai da na zo gab da shi ya ɗago kai ya kallan. Murya a sanyaye alamar nasha kuka batare dana kallesa ba na ce, “Ina yini”.
Bai amsa min ba, sai idanunsa masu azabar kaifi daya zuba min. Ji nai duk ina neman daburcewa, dan haka nai ƙoƙarin barin wajen amma sai ya miƙa min hannu alamar nazo. Jinai kawai bazan iya musa masa ba, a hankali na fara takawa zuwa garesa, ɗan nesa kadan da shi na tsaya kaina a ƙasa. Soft hannunsa ya ɗaura akan nawa da nake wasa da su ya matsoni gabansa sosai, a bazata na jini zaune a saman cinyarsa alamar ya ajiye laptop ɗin da pillow ɗin. Sake matsoni yay cikin jikin nasa ya rungume tsam har ina iya jin bugun zuciyarsa kaɗan-kaɗan. Luff nayi wata nutsuwa na ratsani.
“Yaya jikin ya daina zafi?”. Ya faɗa cikin silent muryansa a cikin kunnena. Sosai kunya ya sake ƙamani, maimakon amsa masa sai na sake ƙanƙamesa ina ɓoye fuskana a jikin nasa. Kaɗan naji yunƙurin murmushin sa cikin ƙirjinsa. Shiru kusan mintuna biyu ya sake furta, “Kona duba ne?”.
Kafaɗa na maƙe masa da faɗin, “Uhm-uhm” cikin shagwaɓa ina ƙoƙarin tashi. Amma sai ya hanani yin hakan, hannayena ya kama cikin nashi ya zubama fuskata ido sosai yana kallo. Kasa kallonsa nayi ni dan bazan iya jurewa ba sam. A hakan ma ji nake kamar na gudu. Sake maida muryarsa ƙasan maƙoshi yay da kai hannu a haɓata ya ɗago fuskata da ƙyau ya ce, “Look at me”.
Da ƙyar na iya ɗago idanun na kallesan. Cikin ɗan ɗage gira ya ce, “Shin bakin ƴar mutan Gwarzo ya mutu ne kwana biyu?”.
Bakin na ɗan tura masa kaɗan. Girarsa ya ɗan ƙara ɗagewa da jinjina kai ya ce, “I see, bai mutu ba ashe. Yanzu idan su Ya Musaddiq suka zo mi zaki ce da su ya samu wannan idanun da ya kumbura?”.
Karan farko na ɗago na kallesa. Idanun nawa ya sarƙe cikin nashi, kallon juna muke cikin wani yanayi mai wahalar fassara. Jin yanda tsigar jikina ke tashi jinina na yamutsawa ya sani lumshe nawa a hankali. Murya ƙasa-ƙasa kamar mai koyan magana na ce, “Zan ce kai ne”. Na ƙare maganar in