Showing 174001 words to 177000 words out of 438336 words
korarsu.
“Wannan shine tarihin wannan gida a taƙaice Kandala. Dan na yanke miki abubuwa da yawa ne a cikinsa saboda wasu dalilai. Sannan ina fata ki fahimci wasu da kanki kuma”.
Hawayen da suka kasa tsaya min tun ɗazun na ƙara sharcewa. Cikin rawar murya data gama dasashewa na ce, “Amma mama miyyasa duk kika faɗa min wannan? Bayan baki sanni ba? Baki san koni muguwa bace, ko nama shigo gidan ne dan wata manufa”.
Ɗan murmushi tayi itama tana share hawayenta. Kafin ta kamo hannuna cikin nata. “Nasan ke ba muguwa bace Kandala. Duk da dai da farko haka kawai naji ƙaunarki a cikin zuciyata. Sai kuma wata fuska da nake gani akan fuskarki da bansan dalilin hakan ba. Da ga baya Hayatu ya sanar mana alaƙar dake tsakaninki da Awwab....”
Wani mugun zaro idanu nayi ina zabura gefe da fincike hannayena dake a cikin nata. Magana nake son yi amma na kasa. Sai lips ɗina dake rawa kawai. Murmushi ta saki tare da sake kamo hannun nawa ta ce, “Kwantar fa hankalinki Samraah. Kar kuma ki fasa aikin ladar da kika fara. Daga Ummie har Awwab da ɗan uwansa abin tausayi ne, suna buƙatar mai tallafama rayuwarsu. Mu kuma da muke da damar yin hakan bamu da wani ƙarfin iko. Dama fatan da muke masa yay aure ya samu mace ta gari da zata juya mulki da tsarin wannan gida ta inda kowa baiyi zato ba. Alhamdullah kuma muna fatan an samu, dan ko yanzu Awwab yaso nunama duniya matsayinki a gurinsa dole kowa ya girgiza, duk da ina tsoron kar su cutar dake dan mutanen nan hatsabiban kansu ne suma, dan ma taurin kan Awwab na rage musu tasiri a wasu lokuta. Sai dai duk abinka baka isa gane wanene na kirkin ba idan kika cire Baba prof.. Dan kowa da tasa illar da manufa da kike gani. Amma ke yarinya ce mai wayo da ilimin addini, dan har na zamani na fahimci kina da shi, ɓoyewa kawai kike kamar yadda kika ɓoye mana ainahin kanki da sunanki. Dan ALLAH ki daure ki taimaki waɗan nan bayin ALLAHn. Awwab mutumin kirki ne, yana iya ƙoƙarin sa wajen tsare mutuncin kansa ta hanyoyi da dama da samarin zamanin nan sukan kasa musamman idan kudaɗe na yawo a hannayensu. Kisa a ranki aikin lada kike yi sakamakon ki naga UBANGIJI. Kisa a ranki ceto zakiyi na Uwa da yaƴanta a cikin gobarar da bata da iyaka. Nasan bake zaki bama Ummie lafiya ba, amma zaki zama wani tsanin taimakawa mukai ga samuwar lafiyar tata. Dan in har kina a tare da ita duk maganin da mu kuma zamu nemo mun san zaki bata. Za ki kuma dinga mata addu'a har shi Awwab ɗin dan bana raba ɗayan biyu akwai sihiri mai ƙarfi shima a jikinsa. Fatanmu shima Fahad ya dawo gida su dai-daita da ɗan uwansa. Sannan waɗan nan mutanen da suka cika gidan nan kowa ya koma inda ya fito..”
Karo na farko na saki murmushi mai ciwo. Sai kuma na girgiza kaina. “Mama zan iya tsayawa dai akan samun lafiyar Ummie in sha ALLAHU da kuma batun dawowar ɗan uwansa gida. Amma shi babu abinda ya shafeni da shi ko halin da yake a ciki. Yaje can ya nemo mai taimakonsa. Ai shi ba yaro bane kuma yana cikin hankalinsa. Miyasa bazai dinga ma kansa addu'a ba. Ko sai neman dukiya kawai ya iya. Su kuma dake zaune Mama ai banga amfanin subar gidan ba yanzu, gara suna a cikinsa ta samu lafiya suma su koma kwasar kashinsu a cikin hannayensu. Ai ni baki sani ba. Aduk lokacin da maƙiyi ke tare dani bana son yay nesa da ni, na fison ya cigaba da rayuwa a jikina dan ya cigaba da kallon cigabana da nasarorina zuciyarsa na zafi. Koba komai shi zai ƙare rayuwarsa da lokacinsa ne wajen ganin ya cimmani. A bayyane shike da asara. Bai ƙaru da komai a duniya ba, ya je lahira ya tadda bai ajiye komai a taskarsa ba. Mi yafi wannan daɗi dan ALLAH”.
Murmushi Mama Balki tayi tana mai kai hannu ta shafa fuskata. Sai kuma tace, “ALLAH yayi miki albarka Samraah. Hakan ma Nagode. Amma dan ALLAH ayi haƙuri dai a haɗa da Alhaji Ƙarami. Yaron na cikin jarabawa mai ban tausayi. Karki damu da murɗaɗɗun halayensa abubuwane sukai masa yawa a cikin kai. Sannan da kike ganinsa nan mutum ne mai ibada da tarin ilimin addini. Kawai dai ana gusar masa da kulawa ne saboda kada yay ma kansa addu'ar. Amma a hakan ma azumin Litinin da Alhamis baya taɓa wucesa. Salla a cikin jam'i komi yake. Hayatu ya rantse min ya maya komai girman kasuwanci da abinda zai samu a cikinsa ko muhimmancinsa idan lokacin salla yayi sai ya barsa. Komai girman mai mulki ko wani muƙami ko dukiya dan Awwab na zaman meeting dasu baya hana da an kira salla ya miƙe ya barsu yaje yayi sallarsa. Sam bai haɗa bautama UBANGIJINSA da komai ba. Sadaka da taimakon marasa ƙarfi bazasu musaltu ba. Yasha yin ƙyautar gidajen zama da motoci batare da ya ko damu ba. Ɗaukar nauyin karatun yara da gyara makarantun addini da masallatai da asibitici ba'a magana. Idan zan ta lissafo miki alkairan Awwab zamu kwana nan, hatta samar da ruwa ga masu ƙarancinsa bai gaza ba, sai dai hakan bazai hana kuma ace yana da wasu halaye marasa ƙyau ba. Dan ɗan adam tara yake a komai na rayuwa bai cika goma ba. Ladanki naga UBANGIJIN talikai idan kinyi hakan”.
Ban iya cemata komai ba face duƙar da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma a hankali na furta, “Mama kinada hoton mijinki da ya rasu?”.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_
......Ɗan jimm Mama Balki tayi alamar tunani, kafin ta jinjina kanta. “Za'a samu hotonsa, amma sai dai a wajen Alhaji ƙarami. Dan lokacin da muka dawo rai a ɓace daga garinsu abinda danginsa sukai mana ya sakani a damuwa sosai harna kwanta ciwo. Bani da aiki sai kallon hotonsa ina kuka. Ga kuma halin da Ummie take ciki itama duk na haɗu na ƙara hargitsewa. Shine Ummie ta saka Alhaji Ƙarami ya tattare hotunan duka daga wajena, ni kuma ban sake amsa ba bayan komai ya lafa na samu nutsuwa. Amma ina ganin zan tambayesa yanzu, ko kuma na saka Hayatu ya amso”.
Kai na jinjina mata cikin gamsuwa.
✨❤️✨
Yau kwanaki biyu kenan Mom bata saka Abba a idanunta ba. Dan tun jifar da tai masa a washe garin angwancinsa bai sake shiga inda take ba. Hakama amaryar tasa taƙi fitowa. A tunaninta dana yaƴanta harma da Ummanta ai tsoro ya hana amarya fitowa. Dan haka suka fara jin alfahari a ransu musamman ma Mom. Haka zata fito tsakar gida tana habaici da yada magana. Daga Gwaggo Gudidi har Halime da Gwaggon ce ta kwaɓeta babu mai kulata. Hakama Abba yayi watsin ruwan tsarki da ita shan shagalinsa kawai yake da amaryarsa. Gaba ɗaya ya ajiye shekarun girmansa gefe yana koyama Halime salo-salo da tabbatar mata ita ɗin ma fa mace ce. Itako banda raki da taɓara babu abinda take ɓarar masa. Gaba ɗaya ta susuce bawan ALLAH baya ganin komai da tuna kowa a gabansa sai ita. Hatta kasuwa a kwani biyun nan babu inda yake zuwa a gidan yake yini salla kawai ke fidda shi. Dole kuma akayi abinci Gwaggo Gudidi taje ta ɗiba musu tasa Bibaa na kumbure-kumbure takai musu har falo.
Yau dai zaman ɗaki ya ishi Halime. Tana ganin Abba ya fita sallar la'asar ta fito. Tsaff take cikin kwalliya, duk kwalliyar ba'a yi ta yanda ya kamata ba kaya data saka sun fiddo jikinta tsaff da yi mata ƙyau. Ga uban turare ta bulbula. Tun a gaban mirror ake gwada tafiyar da za'ayi, dan haka koda aka fito taku ake ɗaɗɗaya ana juya jiki su adole amare. Nan ko a cikin ɗaki raki takema Abba😂. Gwaggo Gudidi tai shirin fara gaidawa. Dan haka kai tsaye ɗakin da take ta shiga. Ta samu Gwaggon na haɗa kayan tafiya, dan magana ta gaskiya taɓarar da Abba ke zuba musu a gidan na kasa kimtsa bakinsa ya fara isarta itama. Bata ji na daren farko ba amma jiya da rana da yau gabannin asuba fes a kunnenta. Wannan taɓara da rashin sanin ciwon kai har ina. Gara dai ta gusa taɗan basu waje ai ita uwa ce. Maybe ma idan ta wuce ɗin waccan mahaukaciyar surukar tashi itama tayima kanta faɗa ta shirya ta tafi, dan har yanzu Umma na gidan ta fake da jiyyar Mom duk da itama fa abinda Abban keyi na damunta.
Cike da farin cikin ganin Halime Gwaggo ke faɗin, “Oyoyo oyoyo ɗiyata amarya”.
Kunya ce sosai ta kama Halime. Tai ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. A ran Gwaggo tace (ashe ke da sauranki Imamu bai ida kakkaɓe sauran taki kunyar ba). A fili kam sai ta riƙo hannun Halime cikin nata. Durƙusawa Halimen tayi ƙasa cike da girmamawa da kunya tana gaida Gwaggo. Sai Gwaggo taji hawaye sun ciko mata. Dan abune da bata taɓa gani ga Mom ba. Ko sanda tana amarya fingai-fingai tazo musu babu alamar kunya tattare da ita. Amma ita wannan jiba dai yarinya ƙarama amma Alhamdullah. Bayan sun gaisa Gwaggo taita jan Halime da ƴar hira. Wani ta amsa wani tayi murmushi kawai cikin kunya. Sunfi mintuna ashirin a haka suka fara jin hayaniya na tashi. A tare suka fita, dan muryar Umman Mom suke jiyowa. Cak bakin Mom dake ƙoƙarin yin magana ya maƙale, tun daga bakinta da hanci da idanu duk akan Halime. Kasa haƙuri tayi ta nufo inda suke da sauri. Gaban Halime ta tsaya sai kuma ta nunata da yatsa lips ɗinta na rawa. Amma mi a mamakin kowa sai gani sukai Halimen ta saki murmushi tare da rissinawa a girmame ta ce, “Yaya ina yini? Fatan duk kuna lahiya ke da yara? Ya gajiyar bik.....”
“Wacece ke? Miya dawo dake gidana dan ubanki?”. Mom ta katse Halime jikinta har ɓari yake. Murmushi Halime ta sake saki da ɗan bin Mom da kallo daga sama zuwa ƙasa. Sai kuma ta sake murmusawa da yin fari da ido tana wani watsa hannuwa gaba da baya cikin iyayi ta ce, “Halime mana nasan kin gane ai. Na dawo matsayin da kema kike a gidan, wato MATAR ABBA IMAM”.
Wani shegen tsalle Mom tayi gefe tamkar wadda taci karo da baƙin maciji. Yayinda Gwaggo Gudidi da abin ya bama dariya ta saki murmushi da gyara tsaiwar ta. Wani irin zaburowa Mom tayi kan Halime tana faɗin, “Shegiya munafuka algunguma ƙarya kike wlhy, mi mijina zaiyi da kucaka ƴar aiki irin ki. Dan ubanki faɗa min miya kawo ki?”.
Murmushi Halime ta saki, tare da ja baya kaɗan ta kaucewa cakumar da Mom ke ƙoƙarin kawo mata. Cike da fari da sake yarfar da hannu. Sai kuma ta ɗan duƙo cikin raɗa-raɗa ta furta, “Abinda mijin naki yake yi dake nima shi yake yi dani a cikin ɗaki” ta ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya cike da son sake bata haushi ta gittata ta wuce cikin takun da aka gama kowa a gaban mirror.
Gaba ɗaya Mom tai baya zata zube bakinta a hangane sai da Ummanta da itama tayi sumar tsaye ta tarota....
❤️❤️❤️❤️❤️
Sosai abubuwan da naji a bakin Mama Balki suka sakani a cikin damuwa da ɗimuwa musamman akan mijinta daya rasu, dan gaba ɗaya suffofin data ambacesa dasu kama suke dana Babbanmu. Idan kuma ban manta ba Mom ta taɓa min gugar zana da cewar ai ubanmu har karuwa garesa a Lagos. Lallai tabbas ina buƙatar ganin hoton nan nashi.
Damuwa tamun yawa sai dai ina matuƙar daurewa dan kada kowa ya gane min. Musamman Bahijja sarkin tambaya. Data ganni shiru tata nacin son jin mike damuna. Har cikin rai nima ina ƙaunar yarinyar, sai yanayinta ke ɗauke min kewar Auta. Kwanki biyun nan jikin Ummie da sauƙi sosai, dan na duƙufa addu'a. Yanzu hatta a ruwan wankanta da Mama Balki ke shiga a ɓoye tai mata safe da yamma sai nayi addu'a. Abincin ta da ruwan shanta duka. Dan na daina bata abinci gidan sai wanda nasan ni na girka ko Mama Balki. Damuwa da yawan tunani ya sani ɗan fitowa yau ina zagaya gidan ko zan rage nauyin zuciya da kewar ahalina, dan ina son kiran Yaya Musaddiq akan abinda naji amma na kwaɓi kaina har sai na tabbatar sannan. Wayar Bahijja ce a hannuna na gama magana da Yaya Musaddiq dake sanar min a wajen aikinsu sunce zasu turashi ƙasar waje ya ƙaro karatu. Farin cikin wannan magana ta sani cigaba da tsaiwa a wajen ina kallon kai kawon masu aiki maza dake sabgoginsu a garabar gidan.
A dai-dai nan naga ana ƙoƙarin buɗe ƙaton gate ɗin gidan. Ban kawo komai a raina ba na ɗauke kaina ina cigaba da game a wayar. Har motocin suka gama shigowa ban ɗago ba, dan na ɗauka normal baƙine tunda gidan baya rabo da shiga da fitar motoci. Sai da naji tsaiwar mota a inda nake sannan na ɗago, dan dama a jikin wata motar nake a rumfar ajiyesu. Haka kawai sai da naji ƙirjina ya motsa da ganin wanda banyi tsammani ba. Dan rabonsa da gidan kusan sati ɗaya kenan dama wasu kwanaki.
A hankali ya ziro ƙafafunsa dake cikin takalma boot brown masu laushi da ɗaukar idanu tamkar wani miski, gasu da ɗan tsaho ta sama dan har akan wandonsa sosai suka hau. Ko maƙiyi ya kallesa daga sama har ƙasa yasan yayi ƙyau matuƙa cikin shigar tasa. Ga mayen ƙamshin turarensa da tuni ya mamaye wajen kamar anyi ɓarinsa. Cike da matuƙar girmamawa duk masu aikin suka zube suna gaishesa, cikin lumshe idanu da sake dai-daita nutsuwarsa ya ɗaga musu hannayensa alamar amsawa. Kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan cikin silent voice ɗin nan tasa ya furta, “Kuna lafiya?”.
Cike da jin daɗi da girmamawa duk suka amsa masa. Shima sai bai sake cewa komai ba ya juyo gareni. Kallon cikin ido mukaima juna, na kauda nawa da sauri ina ɗan tura baki. Ganin yanda duk yaransa suka samun ido musamman Hayatu ciki-ciki na ce “Ina yini”.
Bai amsa min ba, bai kuma daina kallona ba. Sai da ya mula dan kansa ya ɗaga ƙafafunsa zai bar wajen. A bazata naji shigar furucinsa cikin kunnena. “Karna sake ganinki a anan wajen”. Da sauri na ɗago, sai dai kafin na iya cewa wani abu yabar wajen yaran nasa na take masa baya. Sai Hayatu ne a hankali ya ce, “Good afternoon maa”. Harara na ɗago na watsa masa. Ya wuce yana murmushi.
Masu aiki dake durƙushe har yanzu kansu a ƙasa duk miƙewa sukayi tare da darewa suka bashi hanya. Shiko ya ratsasu cike da takun nan nasa na mazantaka da tsantsar kamala da nutsuwa. Hayatu da wanda ban san sunansa ba da ƙyamusashiyar baturiyar nan Juliet suka take masa baya. Baki na taɓe tare da raka bayansu da harara. Sai kuma naji duk tsaiwar ta gundireni. Haka na koma ciki ina ƙunƙuni.
Ban sake jin labarinsa ba dan ina sashenmu ina wanke kayan Ummie har yamma. Na kwaso kayan zanje na kai ciki aunty Zakiyya ta kirani a wayar Bahijja. Shine na ajiye na fito domin amsa wayar dan bana son su fahimci komai. Ina fara wayar ƙamshin turarensa ya mamaye wajen. Ɗagowa nai da sauri, sai na hangesa ɗan nesa da ni kaɗan ya nufi gate ɗayan mutumin nan daban san sunansa ba (TJ) biye da shi. Da alama masallaci zasu je dan sanye yake cikin blue jallabiya data fiddo da shi tamkar wani balaraben yankin sudani. Ɗauke idanuna nayi da sauri saboda hararar daya watsomin da ban san ta miye ba. Wayata na cigaba dayi da aunty Zakiyya ina dariya har sai da na kammala sannan na koma na ɗauki kayan Ummie na shiga ciki. Labarin data bani na ɗirkama Halime kayan mata dan ta rikita Abba yasa na kasa daina murmushi. Na samu ummie tana barci, dan yanzu abinda tafi yi kenan. Sai uban ƙamshin turarensa daya tabbatar min daya shigo sashen. Baki na taɓe na ajiye kayan na fita........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*