Showing 138001 words to 141000 words out of 438336 words
ɓanɓare Maash a hannunta bayan sun mata allura mai ƙarfin gaske. Zama yay ƙasa batare da jin ƙyanƙyamin komai ba ya riƙeta a jikinsa ya zubama fiskarta idanunsa da suka rikiɗe gaba ɗaya. Yanda Adams apple ɗin sa ke kai da kawo zai tabbatar maka da kukan zuci yake yi. Yafi mintuna goma zaune a haka shiru, duk maganar da su Hajiya Mammah suke masa bai ko motsa ba. Sai da Paah ya shigo ya kai duƙe kusa da shi, hannu ya fara kaiwa ya riƙo na Ummie dake kwance ka shirɓan allamar barcin nata yay nisa matuƙa, idanu ya zubama hannun cike da tausayawa shima nasa na cika da hawaye, dan har yanzu har gobe yana matuƙar ƙaunar matar tasa rufin asirinsa kuma. Hawayensa ya share kafin ya sauke ajiyar zuciya tare da kiran sunan Maash da bai ko motsa ba.
“Muhammad”.
A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Paah ɗin nasa batare da ya iya cewa komai ba, sai kuma ya ɗauke ya maida kan (Ummi) Hajiya ƙarama da ke tare da sauran masu kula da lafiyarta dan itama likita ce. Sake ɗaukewa yay ya maida kan Samraah dake kwance gefe a sume babu wanda yabi takanta. Yanda ya tsurama wajen ido na tsahon mintina kusan biyu ya saka kowa maida kanhalinsa ga kallon abinda yake kallon. Shima kansa Paah sai a lokacin ya lura da Samraah ɗin.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_
.......Cikin tashin hankali ya miƙe yana ambaton, “Subahanallahi. Ita kuma wannan mike faruwa haka?”.
Idanun Muneef cike da hawaye ya ce, “Paah ai itace ta fara shigowa yima Hajiya Babba shara shine sai....” ya gagara ƙarasawa saboda hararar da Hajiya Mammah ta wurga masa. Duk da kowa ya fahimci Hajiya Mammah ɗin ce ta kwaɓi yaron babu wanda ya iya tankawa. Shi dama Maash kansa a duƙe yake kawai yana duban mahaifiyarsa kamar bai san mi sukeyi ba. Yanda bai kallesu ba bai tanka musu ba ya miƙe ɗauke da Ummiensa. Fita yay daga ɗakin gaba ɗaya da ita. Dole suka shiga darewa suna bashi hanya. Can falon da Samraah ta gyara yaje ya kwantar da ita. Anan ɗin ma sai dai ya tsira mata ido na kusan minti ɗaya kafin ya juya ya koma ɗakin. Yanzu kam ya samu Azizat na ƙoƙarin sheƙa ma Samraah ruwa a jiki cike da mugunta da wulaƙanci, wani irin kallo daya wurga mata ya sakata daburcewa taja da baya tana faman sinne kai. Yanzun ma baice da kowa komai ba ya ƙara da inda Samraah ɗin ke kwance. Sunkuyawa yay gaba ɗayanta ya ɗauka. Dukansu sai da kowa ta waro idanu waje musamman Malika da Azizat da Arwa, yayinda ran Hajiya Mammah ya gama ɓaci amma bata ce komai ba. Kamar ɗazun darewa sukai suka bashi hanya, cike da takun nan nasa na bajinta da ƙarfin jini ya fice ɗauke da Sam-G dake a sume batama san inda kanta yake ba. Kallon kallo aka fara yi, kafin Paah da shi dama komai bai canja ba daga garesa ba sai ma daɗin kulawar da Maash ɗin ya bada akan yarinyar yaji ya bi bayansa. Dan shi dai abinda kawai ya sama ransa dole Maash ya taimaka ma yarinyar, amma yana mamakin ma yaya akai tazo har nan ɗin tunda yasan babu mai shiga sashen Hajiya Mammah ɗin kai tsaye haka sai masu kulawa da ita, tunda kuma waccan ta gudu kusan wata guda kenan ba'a sake kawo wata ba. Ganin Paah ya fita duk suka zabura suma suka bi bayansa. A falon ƙasa suka samu Maash na ƙoƙarin sauke Samraah saman kujerar falon tare da kaiwa zaune shima ya kwantar da kanta a jikinsa. Dai-dai nan Hayatu ya iso gabansa da first eld box. A gabansa ya dire, jikinsa har rawa yake wajen fara fiddo abinda za'a fara buƙata. Maash ɗin ya miƙawa auduga, da farko zubama audigar idanu kawai yayi kamar bazai amsa ba. Sai kuma miya gani oho masa ya kai hannu ya amsa. Jinin goshinta da har lokacin ke fita ya fara ƙoƙarin gogewa, ganin kamar kaɗar bata masa yanda yake so sai kawai ya jawo handkerchief dake jikinsa fari tass ya shiga kwashe jinin da duk ya gama ɓata mata fuska. Sai da ya goge shi tass sannan ya saka ƙaramin bandage dan ciwon ba wani ƙato bane can sosai amma ba laifi da ɗan girmansa. Ganin ya kammala komai Hayatu ya miƙo masa goran ruwa. Karɓa yay ya zuba kaɗan a cikin hannunsa ya shafa mata a fuskar zuwa wuyanta. Numfashi mai nauyi sosai ta kawo, sai kuma ta zabura cikin yanayin firgita ta ƙanƙamesa jikinta na rawa. A hankali ya lumshe idanunsa batare daya ko motsa daga yanda yake ba.. kusan mintuna biyu suna a haka kowa ya zuba musu ido kowai, yayinda zukatan wasu suka gama hasala, wasu ko na tausaya mata...
Shigar ƙamshin turarensa a cikin hancina ya sakani tsayawa cak, wani irin bugawa ƙirjina yayi, ga zuciyata na tafiya da sauri-sauri a cikin ƙirjina, komai daya faru ya shiga dawo min daki-daki. Fara sassauta riƙon da naima koma wanene nayi, sai kuma na sakesa gaba ɗaya na yunƙura zan tashi, sarawar da kaina yayi ya sani kai hannu na dafesa tare da faɗin, “Wash ALLAH na” na koma na kwanta a inda naken. A bazata naji saukar tattausan hannu mai zafi sosai a saman nawa hannun, janye nawan akayi a hankali, hakan ya sani sake buɗe nauyayyun idanuna. Harga ALLAH sai da zuciyata ta harba da ƙarfi Bily saboda saukarsu a cikin na wanda banyi zaton gani ba. Duk kuma yanda naso janyewa hakan ya gagara, kallonsa nake a tsakkiyar ido kamar yanda nima yake kallona. Ga hannunsa riƙe da nawa shi bai sakar min ba, bai kuma ajiye ba....
“Are you okay?!”.
Ya faɗa cikin yanayin motsa lips batare da fitar sautin murya ba, gaba ɗaya naji wata irin kasala ta saukar min, sanyi ya shiga ratsani a cikin ƙashi da ɓargon jikina. A maimakon bashi amsa sai kawai na lumshe nawa idanun a hankali nima, wasu hawaye ne da suka jima maƙale a cikin idanun nawa suka sami damar silalowa batare da nasan dalilin hakan ba...
“Hayat muje hospital”.
Furicin sa cikin sauƙaƙa harshe ya sani buɗesu da sauri. Kaina na girgiza masa da sauri ina ɓata fuska da tura baki, sai kuma na yunƙura zan tashi a jikin nasa ina faɗin, “Ni dai bance ina son zuwa asibiti ba ai”.
Bai tanka min ba, sai maidani da yay a yanda nake ya sake kwantarwa a jikin nasa. Jinai kamar na fasa kuka, amma dole na haƙura dan nasan koma sake yunƙurin tashi bazan iya ba. Saboda wani irin sarawa kaina keyi da juya min.
Azizat ce ta fara jan sirrin tsaki ranta a ɓace tabar wajen duk da bajin abinda suke faɗa sukai ba, sai Maleeka da hawaye suka gama wankema fuska dan tsabar takaici. Dan lokaci ɗaya taji tsanar yarinyar ta gama baibaye rayuwarta. Wata mace kwance a jikin Awwab ɗinta ba ita ba...
Dawowar Hayatu ya katsema kowa zancen zucinsa. Cike da girmamawa ya sanar masa ga Doctor nan a hanyar zuwa. Kamar ko yaushe bai amsa ba. Sai Hajiya Mammah ce cikin ɗan faɗa-faɗa ta furta, “Yanzu ga Hajiya ƙarama a gida matsayin doctor sai an kira wani likita dubata kuma dan ɗigimi?”.
Hayatu rasa abinda zaice mata yay, sai kallon ogan nasa da ya ɗan yi. Da gaske bashi da alamar bama Hajiya Mammah ɗin amsa, dan kansa ma na a ƙasa ne yana faman latsa waya. Sai da Hajiya Ƙarama ta furta, “Ciwon nata ma kamar bamai tsanani bane, magani kawai zata sha in sha ALLAH jikin zai mata sauƙi.” ta ƙare maganar da ƙarasowa ta duba magungunan first eld box dake gefensa. Duk maganin daya kamata nasha ta ware, sannan ta nunama Mama Balki duk yanda zan sha su. Tana kammalawa Hajiya Mammah tace su kamani su tafi dani can sashen masu aiki. Batama rufe baki ba na yunƙura na tashi daga jikinsa hannuna dafe da kaina. Mama Balki da A'i ne suka kamani. Muna ƙoƙarin barin wajen na ɗan ɗago na kallesa, idanu muka haɗa, sai kawai na tura masa baki. Dan luuu yay da idanunsa kamar zai lumshe sai kuma ya ɗauke kansa gaba ɗaya...
❤️★❤️★❤️
Kwanaki huɗu kenan da ɗaura auren Abba da Halime. Har zuwa yanzu kuma bai sanarma Mom ba. Dan bama shiga sabgarta yake ba har yanzu. Itace dai take son su shirya saboda ko abincin gidan baya ci. Ga abubuwa teacher ya bata amma ta rasa yanda zatai da su. Yau ne ma da saurayin Baby ya sake zuwa Abban ya ɗan sake a gidan har suka ga haƙoransa a waje. Kai tsaye kuma batare da kwana-kwana ba ya bashi damar turo magabatansa har hakan yaso bama Mom ɗin mamaki. Amma dai batace komai ba sai da ta kira Ummanta take sanar mata sai tace mata aikin malamin ne ya fara cinsa. Tunda dama yace zai musu wani a bayan fage bayan na abincin da aka basu a saka masa. Wannan ne ya sanyaya zuciyar Mom ta samu nutsuwar cigaba da warisarta akan kuɗin da saurayin Baby ɗin ya danƙara musu yau ma.
Kwana ɗaya da zuwan saurayin Baby kwana biyar da ɗaura auren Abba ya fara gyaran gidansa. A haukar Mom dama kowa dake gidan shine Abba ya ƙirƙiri gyaran ne domin auren Baby ɗin. Shiko baicewa kowa komai ba. Garama kwana biyu da fara aikin ya zauna da Musaddiq ya buƙaci ya bashi aron kuɗi. Babu musu kuwa Musaddiq ɗin ya bashi kuɗin, jin daɗin hakan ne ya saka Abba kwancemasa abinda ke faruwa game da auren nasa. Duk da zuciyar Musaddiq ta girgiza sai da ya saki murmushin da har ya so bama Abba mamaki.
“ALLAH ya sanya alkairi Abba. Amma baka ganin akwai damuwa a haɗa Mom da Auntyn a gida ɗaya kuwa?”.
Murmushi shima Abba yayi a karo na farko, sai kuma ya dafa kafaɗar Musaddiq ɗin. “Gaskiya ka faɗa Musaddiq, sai dai hakan da zanyi zai fi bani kwanciyar hankali ni kuma. Dan Maman nan taku zata iya aikata komai saboda bata ƙaunar kishiya. Amma kaga idan suna a tare waje guda koyaya zamu dinga sani wani motsinta ai ko”.
“Hakane kuma Abba. ALLAH ya sanya alkairi to. Ya kuma kauda fitina”.
“Amin ya rabbi Musaddiq. ALLAH yay maka albarka. Ku ƙara haƙuri dani kunji”.
Murmushi Musaddiq yay kawai amma baice komai ba.
An kammala gyaran gida tsaff a cikin kwanaki uku, duk wanda ya kalla fa sai ya yaba. Yayinda kan Mom ya sake girma ta fara hurama ƴan anguwa kai. Daɗin wannan gyara ya sata sake sauke kai ƙasa ta sake bama Abba haƙuri. Shi kuma bai ja ba yace mata komai ya wuce. Cikin farin ciki ta rungumesa ana sakar masa kisses. Shi dai komai baice mata ba, sai ma zame jikinsa yay cikin dabara. Bata damu ba ta gyara zama tana tsara masa yanda zasu gyara gidan. Dan ita a haukarta sashen da Abba ya gyara ɗin nasu Bibaa ne zasu koma. Saboda ta daɗe dama tana masa nacin ayi hakan ba'ayi ɗin ba, yanzu kuma a tunaninta yayi gyaran ne dan su shirya.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_
.......Wani ɗan iskan Murmushi Abban ya sake mata da cewa to kawai. Hakan ya sakata sake shiga cikin farin ciki da tabbatar da lallai aikinsu ya ci Abban. Washe gari kuwa sai ga kaya ana kawowa danƙara-danƙara. Sosai farin cikin Mom ya kasa ɓoyuwa a wannan yini, dan har sai da ta kira Ummanta ta sanar mata. Da yamma kuwa masu aikin na gab da kammalawa sai gata ta isa gidan. Har sashen suka shiga ita da Mom ɗin, sunata faman santin kayan da yaba aikin malamin. Tun a ranar Mom ta fara haɗa ƴan kayanta, dan a bata haukar itace zata koma can abarwa yaran inda take. Da Abba ya dawo gida da yamma ya sami tarba ta mutunci daga Mom ɗin, hatta da abincinsa ranar da kanta ma tayisa bata saka sabuwar mai aikin ta ba. Shi dai komai baice mata ba, duk abinda tace shi yake yi, a can ƙasan ransa kuwa dariya take bashi...
★★★....
Bayan wucewar su Samraah ya jima zaune a wajen batare daya tankama duk surutun su Hajiya Mammah dake a falon ba. Sai da Paah ya kira sunansa sannan ya ɗago ya ɗan kallesa sai kuma ya sake maida kan nasa ya duƙar ba tare data amsa masa ba shima. Shiru falon yayi dan kowa zuwa yanzu ya fahimci ransa a ɓace yake har shi Paah ɗin. Ilai kuwa basu gama zancen zucin nasu ba ya sake ɗagowa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya tamkar mai lissafa yawansu. Da sauri yaran suka shiga rige-rigen barin wajen, hakama Hayatu saurin fita yayi hankalinsa a tashe, dan dama duk a ɗari-ɗari yake da yanayin ogan nasa. Suna gama fita Maash daya tsare iyayen nasa da kallo cikin daƙilallen yanayin nan nasa dake sake fiddo tsantsar ɓacin ransa ya furta, “Paah sayin mi na gani a hannu da ƙafar Ummie? Ina masu kula da ita da har yarinyar nan ta shiga inda take?”.
Kai Paah ya shiga girgizawa, kafin cikin nuna damuwa shima ya furta, “Muhammad tare da kai muka bar gidan nan a shekaran jiya. Na dawo jiya da dare ka dawo yau da safe. Ban san komai ba kamar yanda kaima baka sani ba”.
“Har yanzu baka shiga duba Ummie kenan?”. Ya faɗa a zafafe.
Dabircewa Paah ɗin yayi, zai fara kare kansa Maash ya katsesa ta hanyar maida kallonsa ga Hajiya Mammah. Sosai ta fara mazurai. Sai dai shi ko'a kwalar rigarsa dan itama tasan baya tsoron duk wani hargaginta. Kame-kame ta fara tunma kafin yace da ita komai.
“Ko yau da safen nan na shiga duba ta ni dai, kuma banga wani ciwo a jikinta ba Awwab. Sai dai idan munafukar yarinyar nan ce ta aikata mata wani abun. Shiyyasa sam yarinyar bata min ba tun randa Mashi'a ta kawota. Ni inama zargin wani ne ya aikota dan ta cutar damu, yarinyar fa sam bata shakkar gasawa mutane magana, kai ma shaida ne ai tunda a gabanka ance ta mari Azizat....”
Idanunsa ya runtse da ƙarfi yana mai masifar cije lips ɗinsa. A take jijiyoyin kansa duk suka firfito ruɗu-ruɗu. Idanunsa suka kaɗa gwaiduwar tsakkiya ta koma siririya. A matuƙar zafafe da akan daɗe ba'a gansa a yanayin ba ya miƙe. Gashin jikinsa har mimmiƙewa suke saboda masifar dake cin zuciyar ƴan maza. Cikin daka tsawa ya ce, “Mammah!! Idan itace ta jimata ciwo shi kuma dattin dake a sashen itace ta zuba shi kenan?! Dama wannan dalilin ne yasa a duk lokacin da nake gari ake maido Ummie falon sashenta na farko!!!”.
“Muhammad!!”.
Paah ya kira sunansa a tsawace shima. “Kana cikin hankalinka kuwa? Addata kake ma tsawa haka kamar kana magana da wata sa'arka?!!”.
“Ni kuma ina magana ne akan mahaifiyata idan ita ɗin Addarka ce Paah! Idan kuma kana son tuna min kana nan baka canja ba to nima fa akan Ummie ban canja ba. Ba kuma zan taɓa canjawar ba. Kaf ɗinsu har kai ɗin ban ma kowa tilas a zaman gidan nan ba, tunda dama ban gayyaci kowa yazo ya zauna da mu ba a cikinku kune kuka kawo kanku. Ku gaya min na taɓa tsallake dai-dai da rana guda wajen biyan masu kula da Ummie ne? Ko na taɓa tauye wani likita a cikin masu duba lafiyarta. Kai da Baba kuka tirsasani wannan kai da kawon kasuwancin badan ina so ba. Kuka kuma min alƙawarin kulawa da mahaifiyata bakin rai bakin fama har takai da an tattaro wannan gayyar an zube a gidan nan. Idan kun manta bari na tuna muku wannan gidan mallakin wadda kuke wulaƙantawar ne. Amma ku kuna zaune cikin