Showing 252001 words to 255000 words out of 438336 words

Chapter 85 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2162

ɗan buɗe idanuna kaɗan.

“What a surprise, ni ne fa? To nayi me?”.

Ai babu shiri na buɗe idanun gaba ɗaya ina harararsa da tura baki. Sai kuma na yunƙura zan tashi ina ƙunƙuni. Sake maidani yay ya zaunar ya ce.

“Answer me”.

Shagwaɓe fuska nayi ina kaucema kallonsa na ce, “Ni dai ba ruwana. Ka sakan na saka kaya na je na ga Ummie na”.

Ɗan lumshe idanunsa yay ya sake buɗewa, sai kuma ya ɗan sauke numfashi, kamar wanda ke shirin sakin murmushi ya ɗan taɓe baki. Yatsun hamnuna dake cikin nasa ya ɗan matsa da murza farcen. “Shi wannan hannun yaushe za'a masa lalle?”.

Hannun na kalla nima, sai kuma a hankali nace, “Ai babu lalli ne. Da dai nasan su Yaya zasu zo da sunzo min da shi. Kuma ma ina son wanke kaina ya fara cushewa.”

Kansa ya jinjina min alamar amsawar kenan. Nima sai nai ƙoƙarin miƙewa. Taimaka min yay na tashi, ina shirin barin wajen shi kuma zai maida laptop ɗin sa a ƙafa ya ce, “Mi zaki ci?”. Kallonsa na ɗan juyo nayi muka haɗa ido, sai kuma na kalla ledodin chocolates ɗin da yasha batare da nayi magana ba na nuna su. Idanunsa ya ɗan ƙanƙance a kaina. Sai kuma ya girgiza min kai a daƙilen nan nasa. “Kince ba abinci bane ai”.

“To kaima ai shi kake ci”.

“Humm”.

Kawai yace ya maida kansa ga wayarsa daya ɗauka. Ganin ya kai kunne alamar wani ya kira ya sa na wuce abina dan na shirya. Ban wani jima ba na fito cikin skirt da riga na atamfa. Sosai kayan sun min ƙyau tare da fiddo ainahin surar jikina. Ni kaina sai da na sakarma kaina murmushi ta cikin mirror. Dauri nayi mai sauƙi bayan na shafa turarensa da mansa. Koda na juyo sai na samu ni yake kallo shima. Da sauri na ɗauke kaina kunya na kamani. A ɗan daburce nace, “Zanje can sashen na ɗakko kayan kwalliyana Please Ya Awwab.”

Sai da ya maida kansa ga aikinsa kamar bazai kulani ba kafin a hankali ya ce, “No”.

Baki na ɗan tura batare dana sake cewa komai ba na nufi gadon. Tsaff na gyarashi, na tattare net ɗin. Dai-dai nan shima ya miƙe ya shiga bathroom. Babu jimawa ya fito alamar yin alwala.........✍️

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆- thirty


......Ina a inda ya tashi ina gyara wajen da tattare ledodin chocolates ɗin da ya zubar naji tsaiwarsa gefena. Juyowa nayi na kallesa, ya ɗan ɗage min gira alamar kallon fa, ƙoƙarin kauda kaina nayi ya kamoni, a bazata naji saukar sumbata a goshina. Idanuna na lumshe a hankali. Shi kuma ya kai lips ɗinsa kan kunnena a matuƙar low voice ya furta, “You are beautiful tiger girl”.

Da sauri na buɗe idanun a kansa. Kamar zan yi kuka na ce, “Tiger fa?”.

Ido ɗaya ya kashe min kawai yay gaba batare da ya amsa min ba. Yana buɗe ƙofar nima cikin shagwaɓa na ce, “Kaima Lion”.

Wani shegen murmushi kawai ya sakar min batare da yace komai ba ya buɗe ƙofar ya fita abinsa. Nima sai na samu kaina da sakin murmushin har haƙorana na bayyana. Sosai murmushinsa ke sakani farin ciki da nishaɗi. Dan yana bala'in ƙara ƙyau a duk lokacin da yayi sa. A gurguje na ƙarasa gyara ɗakin, nasa turare na fito falo bayan nayi salla. Fes na samu ko'ina anan alamar yasha gyara. Sashen Ummie na nufa ta hanyar da yabi da ni daren jiya. Na jima a can dan yau ma har sai da Mama Balki tace naje gasu Yaya Musaddiq nan zuwa harda Falaq. Cike da farin ciki da zumuɗi na tafin kuwa. Tuni na manta da halin da nake ciki saboda farin cikin ganin ƴan uwana duk uku. Nan fa na zauna muka buɗe sabuwar hira, har sai da Aunty Falaq ta tsareni naci abinci wai inji Yaya Awwab. Ni saima abin ya ban mamaki. Sai dai ban ja zancen ba na basar dan tunda na shigo na fahimci baya nan. Bayan sun tafi sallar la'asar nace mu shiga muma muyi a bedroom Aunty Falaq taƙi, nayi-nayi da ita tace ALLAH bazata taɓa iya shiga bedroom ɗin Yaya Awwab ba. Zata je sashen su Mama tayo. Sosai nake mamakin yanda suke mugun girmamasa, sai kuma hakan ya birgeni. Tare muka nufi sashen su Maman da ita. Bayan nama guard ɗinsa magana sun kulle sashen. A hanya muka gamu da Hajiya ƙarama ta dawo maybe daga asibiti ne oho mata. Sai dai muna gaisheta sai ga hajiyar nan data ɗakkoni da ga Abuja ta fito a mota itama. Sosai na zuba mata ido, dan tun ranar birthday ɗin nan ban sake ganinta a gidan ba. Itama kallona take kamar wata tsohuwar mayya. Dan haka na tsuke fuska ataƙaice na gaisheta naja hannun Falaq muka wuce. Har muka shige sashen Mama ina jin idanunsu a kammu su duka biyun..

Koda mukai sallar a sashen Mama Balki muka cigaba da zama. Suma su Yaya Musaddiq nan suka samemu. Sabuwar hira muka sake zamanyi yanzu kam harda Mama Balki da mijinta. Sunata bamu labarin Baba muna jin daɗi, sai gab da magriba Hayatu ya shigo yake cewa sun dawo. Yaya Musaddiq yazo suje ya ƙarasa kimtsawa jirginsa na nine ne. Gaba ɗaya kuma duk sai jikinmu yay sanyi, amma babu yanda muka iya tunda cigaba ne yazo mana. Sai kuma munyi haƙuri zamuci ribarsa. Anan mukai sallar magrib ɗin, sannan muka ɗan sake gyara jikinmu dan muma muna son masa rakkiya airport ɗin. Ana kuwa idar da sallar isha'i sai gasu sun dawo. Nasiha sosai Mama Balki da Baba suka sake ma Yaya Musaddiq, sannan muka haɗu mukai masa addu'a. Ya sake kiran su Abba yay musu sallama har nima muka gaisa. Mun fito muka samu har mitsocin da zamu tafi da su airport ɗin an shirya. Da farko nayi mamaki, sai da naga boss ɗin ya fito alamar da shi za'ai rakkiyar sannan na fahimci dalilin shirya motocin da yawa haka. Dan kusan mota biyar. Biyu ta guards ɗin sa. Sai Mama da Baba da Yaya Musaddiq suka shiga ɗaya. Hayatu, Falaq, Hafizzullah suma suka shiga ɗaya. Sai ni da shi a ta tsakkiya duk da ba haka naso ba. Amma Falaq ta turani a motar da tsiya-tsiya tana dariya. Waya yake sanda na shiga, dan haka muna haɗa ido nayi saurin kauda kaina. Sai da mukai nisa da gidan sosai sannan ya kammala wayar, batare dana kallesa ba nace, “Ina yini”.

Bai amsa min ba, sai kaifin idanunsa da nake ji a kaina. Kasa jurewa nayi a hankali na ɗago na ɗan kallesa. Caraf kuwa ya cafke idanun nawa a cikin nasa kamar dama mai jiran hakan. Wani irin kallo yake mun mai tada tsigar jiki da saka jini tsinkewa. Bamma san sanda cikin rawar murya da shagwaɓa na ce masa, “Ni ka bar kallona”.

A hankali ya lumshe idanun ya sake buɗewa, sai kuma ya riƙo hannuna batare da yayi magana ba yanzu ma ya jawoni jikinsa kawai ya rungume. Luff nayi dan nima da alama abinda gangar jikin nawa ke buƙata kenan. Tuna bafa mu kaɗai bane akwai driver ya sani saurin yunƙurin tashi, amma sai ya maidani ya sake matsewa. A marairaice na buɗe baki zanyi magana ya dakatar dani.

“Bana son surutu”.

A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiye abinda nake son faɗar kuwa. Dan ji nai bazan iya masa musu ba sam. A hakan muka isa airport ina a jikinsa. Munfi tsahon mintuna biyar bayan isowar tamu kuma kafin ya bari muka fita. Jinai gaba ɗaya kunya ta kamani ganin kowa ya fito ashe sai mune kaɗai a mota. Yaya Musaddiq yaja gefe sukai magana. Ban san mi suka tattauna ba dai naga Yayan nata murmushi da kallonmu. Sai kuma ya ɗan sosa kansa kamar wanda yaji kunya. Daga haka kuma naga shima Yaya Musaddiq ɗin yazo yaja Baba da Mama suka koma can. Anan ɗin ma sun ɗan jima, kowa fuskarsa ɗauke da murmushi idan ka cire uban gayyar da shi daman sai yaso yake murmushin. Shiyyasa da wahala ka gane farin cikinsa da akasinsa sai ka masa farin sani na haƙiƙa. Bayan sun gama zantukansu muma munata hirarmu suka dawo inda muke. Baifi mintuna biyar ba aka buƙaci ganin su Yaya a ciki. Tofa ai tuni kuma kuka ya tashi ni da Hafizzullah. Ganin haka itama Aunty Falaq ta fara. Mama Balki da Hayatu na ta mana dariya. Baba ko sai lallashinmu yake, shiko ai kamar ma bai san munayi ba. Haka dai muna ji muna gani Yaya Musaddiq ya wuce ya barmu da kewa.

Hafizzullah da Hayatu da Falaq can gida suka wuce. Mu kuma muka nufi gida muma inata mita dan nazata yau a wajenmu muma Hafizzullah ɗin zai kwana. Bai dai tanka min ba har muka isa gida. Hakan ya ƙara tunzurani. Dan haka nama rigashi fita a motar. Badan su Mama Balki dake wajen ba ma da bazanje sashensa ba. Nafi mintina goma da shiga sannan ya shigo. Lokacin har na shiga wanka. Na fito na sameshi zaune a bakin gado yana waya. Wucewa nai cikin closet ɗinsa na shirya. Ina fitowa yana shiga bayin shima. Sai na saka sallaya nayi shafa'i da wutri. Na idar na tashi na fita. A karo na biyu na shiga kitchen ɗin sashensa. Kai tsaye store na shiga na ɗakko catton biyu na bottle water na fito. Bedroom ɗin ba dawo dasu. Har lokacin kuma bai fito ba. Gaba ɗaya na fito da ruwan tare da buɗe musu murfi sai dai ban cire su a jiki ba sannan na ɗauka Alkur'ani na fara karatu. Surorin da duk akace suna karya sihiri nake karantowa ina tofawa a cikin ruwan bayan na ɗaɗɗaga murafan. Nayi nisa sosai a karatun sannan ya fito. Duk da nayi mamakin daɗewar tasa a ciki ban kula ba na cigaba da karatuna a nutse...

Sosai karatun nata ke ratsa masa zuciya. Ga yanda zazzaƙar muryarta ke fita cikin nutsuwa da bama komai hakkinsa na wani irin shiga masa har cikin jinin jikinsa. Cikin jin wata irin kasalar dake saukar masa ya ƙarasa closet ɗin sa. Shirin barci yayi shima, ya fito gaban mirror ya saka turare sannan ya ƙarasa saman sofa ya zauna yana satar kallonta ta gefen ido....

Barci nake ji amma tsoron abinda zai iya biyo baya ya hanani tashi naje na kwanta. Koda na kammala addu'oin ma sai na miƙe na kabbara salla. A mamakina sai naga shima ya miƙe ya saka sallaya ya kabbara salar. Mun jima muna miƙama UBANGIJI kukanmu dai sai wajen uku ya katseni cikin bada umarni yace naje na kwanta. Bazan iya masa musu ba. Dan sam banga hayar yin hakan ba a garesa, ga zazzaɓi ya rufeni haka dai na daure naje na kwanta. Duk yanda naso nayi barcin na kasa, sai dai nayi luff a kwancen har ya kammala tashi sabgar yazo ya kwanta. Lokacin da ya sakani a jikinsa wani irin dukan ɗari-ɗari zuciyata ta dinga min, na gama sadaƙarwa yau ma zansha wata azabar sai naji saɓanin haka. Sai ma tadani da yay ya bani maganin zazzaɓi ya sake maidani jikinsa muka kwanta. Babu jimawa kuwa mu duka barci yay awan gaba damu. Koda muka tashi a washe gari babu zazzaɓin, sai dai yanda nake tafiya da ɗan ɗingishi ya sashi min tambaya. Kasa bashi amsa nayi sai idanuna da suka cika da ƙwalla. Shima sai baicedani komai ba ya ƙyaleni kawai yama fita. Kusan ƙarfe goma na idar da sallar walha bayan naje naga Ummie sai gashi ya shigo, kaina a ƙasa na gaidashi, dan rabona da shi tun fita motsa jiki. Kai tsaye yace min ga Doctor tazo dubani. Sosai mamaki ya sani kallonsa, sai dai shi tuni ya ɗauke kansa ma. Ficewa yay abinsa kamar baiga kallon da nake masa ba. A dai-dai nan akai knocking ƙofar, tashi nayi na buɗe, sai ko ga Doctor naci karo da ita. Haka kawai nake jin nauyin matar, dan a haife ta haifi waɗanda ma suka fini, kaina a ƙasa na gaisheta. Yayinda ta amsa min tana kama hannuna muka dawo cikin ɗakin.........✍️

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 thirty-one



......Ina ji ina gani dole na bar doctor ta dubani, kanta kawai naga tana girgizawa cikin damuwa. Sai dai bata iya cewa komai ba tamun allura da buƙatar ganin Mama Balki. Kaina a ƙasa na bata amsar cewar ba'a nan side take ba. Amma za'a iya kiranta a waya ta bari ya shigo. Babu jimawa kuwa sai gashi ya shigo kamar dama kunnensa a kammu yake. Kallo ɗaya na masa na ɗauke idanuna, sai ma kawai na zame na kwanta abina na juya musu baya.

Ina jin lokacin da Doctor ke sanar masa tana buƙatar ganin Mama Balki yace ta sanar masa koma minene ke faruwa karta damu. Ta ɗan jima shiru jimm kafin ta fara masa bayanin daya gama sakani a kunya. Dan bayani ta masa akan lallai ina buƙatar hutu da kulawa. Saboda ciwukan farko basu gama warkewa yanda ya kamata ba. Ga shi kuma an famasu shiyyasa ma nake jin zazzaɓi nake kuma ɗingishi. Badan ma jikina nada ƙyau ba ciwo na saurin warkewa da za'a iya samun matsala. Ta sake tabbatar masa da ina da dauriya, dan ba kowacce mace ke iya ɗaukar irin yanayin ba haka gab-da-gab gaskiya. Ko fargaba da tsotata ya ishi mutum ai. Ta dai jima suna magana da bashi dabarun daya kamata a kula dani domin samun dai-daiton komai yanda ya kamata kuma cikin ƙanƙanin lokaci. Daga haka ta sake bani wasu magungunan ta wuce bayan ta tabbatar masa zata dinga zuwa kullum dubani har na tsawon sati, kuma dan ALLAH na ɗan sami hutu kona satin ne.

Koda ta wuce ban iya motsawa ba. Sai dai ina jin kaifin idanunsa a kaina tsahon lokaci kafin ya shige bathroom. Kafin ya fito barci ya kwasheni. Ban tashi farkawa ba sai gab da azhar. Babu kowa a ɗakin sai ɗan short note da naci karo da shi ya ajiye min a gefen fillon da nake kwance. Na jima ina kallon rubutun mai ƙyau kamar ba hannu yayisa ba kafin na saki murmushin daban shirya ba. Na ɗan ji daɗin jikina fiye da yinin jiya dana wuni a ƙuntace, kasancewar su Yaya Musaddiq kawai yasa na dinga dauriya. Wanka na ƙarayi na gyara ɗakin sannan nai zaman cin abincin da yace ɗin, kai tsaye na fahimci Mama Balki ce ta kawosa. Sosai naci na sha magani, sai da nayi salla sannan na tattara kayan abincin na fita zuwa sashen Ummie....

🪴🪴🪴🪴

Su amarya Baby an isa ƙasar California lafiya. Sai faman iyayi take da wani yauƙi ita a dole ga amarya. Ƙalubale na farko data fara fuskanta a wajen angon nata shine tun a airport ya sakata a taxi wai taje zai ƙaraso. Ya bama mai taxi address ɗin hotel ɗin daya riga yay booking musu tun kafin su iso. Hankalin Baby ya ɗan tashi, amma dai tai ƙoƙarin dannewa tunda yace mata uzirine daya shafesu. Batasha wahala ba kasancewar ta samu mai jiran isowarta cikin ma'aikatan hotel ɗin. Da alama dai mijin nata sananne ne a wajen. Sai ta sake jin kanta ya fasu sama sosai. Wani irin santi da sambatu ta dingayi ganin irin katafaren ɗakin da aka kawota, gashi ya jiƙu da kayan alatu. Dama tun a wajen hotel ɗin take faman sambatu a zuciyarta. Sai da ta gama taɓe-taɓenta da kalle-kalle da santi sannan ta kwanta barcin gajiya, babu batun salla ko duba lokaci, dan a cikin jirgi ko tuna tashi tai salla batayi ba. Yanzu kuma sun sauka maimakon tayi ƙoƙarin ramawa ko'a jikinta. Wankan ma tunda ta shiga tai fitsari taga ta kasa amfani da kayan bathroom ɗin shiyyasa ta haƙura. Tayi nisa a barci sosai aka tasheta. A firgice ya buɗe ido babu addu'a babu komai ta mike zambar tana ƙoƙarin ɓarka ihu. Tsawa ya mata da zabga mata harara da manyan idanunsa.

Sosai tsoro ya kamata da ganin yanda duk kamaninsa suka canja. Idanunsa sunyi wani irin jazur kamar ba mijin nata ba. Har ga ALLAH ba wani sonshi take ji ba, kawai kuɗinsa da zigar su Mom yasa ta amince da aurensa. Ta kuma gama shiryama ranta da shawarar ƙawayenta zaman shekara biyu zatayi da shi ta tara abinda ta tara tasa ya saketa ta samu dai-dai da ita yaro mijin wuce sa'a ta aura. Da ƙyar ta danne wata irin tsanarsa da ta sake ji na tsarga mata. Dan komawar idanunsa jajayen nan sai ya sake fito da tsufarsa. Duk da kuwa a fuska ƙyaƙyƙyawane, sai dai ƙaton cikin nan ya masa cikas da tsufa daya fara taso masa. Ɗan murmushi tayi cike da wayancewa da danne abinda ke ranta ta faɗa jikinsa ta rungumesa tana zabga masa kalamai wai tayi missing ɗin sa. Shiru bai rungumeta ba, bai kuma tureta ba, har sai da ta gaji dan kanta ta ɗago.

Matsawa yay daga gaban gadon yana ƙoƙarin cire kaya. Da sauri ta kauda fuskarta, dan tulelen cikinsa kamar na mace mai cikin ƴan uku dake gab da haihuwa. Tas ya gama sannan ya nufi hanyar bayi daga shi sai boxer. Yana gama shigewa ta sauke ajiyar zuciya. Itako taga takanta, wai tayaya zata iya dauriyar bin shawarar ƙawayenta? Tuna burikanta ya sata sauke numfashi. Tana nan zaune abin duniya ya isheta sai gashi ya fito. Yanzu dai towel ne a jikinsa. Zaram ta miƙe tana faɗin, “Bara nima nayi wankan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login