Showing 168001 words to 171000 words out of 438336 words
tazo da gardama. Ganin za'a iya rasata ita da abinda ke cikinta aka yanke shawarar yimata cs. ALLAH sarki rayuwa, kana naka ne ALLAH na nashi, dan kuwa ana fiddo ɗan Rabi'ah daga ciki tace ga garinku nan itama. Ɗimaucewa Ibrahim yayi gaba ɗaya, dan takai sai da aka kwantar da shi asibiti shima. Kwanan jinjiri biyar a duniya shima ALLAH ya amsa abinsa...
Shike nan komai ya ƙare komai kuma ya tsaya ga Ibrahim. Dai-dai da harkar Companyn ma ya tattara ya watsar sai Adams ne ke kula da komai. Gaba ɗaya rayuwarsa ya tattara akan Ummu-Hidaya ne. Shike mata komai, sai mahaifiyata da aka ɗakko aiki domin kulawa da ita a lokacin, amma hatta barci a tare sukeyi har sai da takai shekaru goma sannan ya raba musu wajen kwanciya. Zuwa yanzu ya ɗan fara haƙura, sai dai babu abinda ke saka rayuwarsa a farin ciki sai Ummu-Hidaya, musamman idan ya ganta a farin cikin itama, itako indai tana cikinmu yaran masu aiki tana wasa zaka sameta cikin walwala da yawan fara'a. Gata yake mata da cikakkiyar tarbiyya mai ƙayatarwa. Tare da fara koya mata harkokin kasuwanci daban-daban. Tun ma bata fahimtar komai a kasuwancin harta fara ganewa. Tana da shekara goma sha bakwai a duniya ta kammala secondary. Zuwa yanzu ta zama budurwa. Sai dai yanayinta da suffarta da bai kama da na baƙar fata ba yasa sam bata da wani jikin girma. Sai dai akwai ilimi ga tarbiyya da nutsuwa. Bata da yawan magana sam. Idan kaganta tana surutu sai da Babanta ko Mu'azz ɗan Adams na biyu ko Drivern Ibrahim Abdul-wahab da muke kira Jirgin mota a gidan. Amma Mu'azz shine abokinta a gidan sosai, sai kuma autar Adams ɗin da matarsa ta sake haifa masa bayan rasuwar Rabi'a mai suna Mashi'a, Nafisa yayarsu gaba ɗaya kuwa masifarta tasa ko harkarta Ummu-Hidaya bata shiga, sai dai tana girmamata. Tun ana kallon rayuwar Ummu-Hidaya da Mu'azz a matsayin shaƙuwa har kowa ya fahimci akwai soyayya mai ƙarfi a tsakaninsu. Sosai Adams da Ibrahim sukayi farin ciki da hakan. Dan koba komai zasu hada alaƙar jini a tsakaninsu bayan ta zuminci da ALLAH ya riga ya haɗa musu. Dan zuwa yanzu idan baka sani ba sai ka ɗauka Ibrahim da Adams yan uwane uwa ɗaya uba ɗaya. Sai dai kawai siffar jiki data banbantasu. Shi Ibrahim daka gansa zaka san dan ƙetare ne. Shiko Adams baƙine kuma ƙyaƙyƙyawa. Gogewa da ilimi da ya sake yi ga dukiya ta zauna gwargwado yasa idan ka gansa bazaka taɓa tunanin shi ɗin nan ne ba na ƙauyen k/Mashi da yazo leburanci garin Lagos. Saboda tuni Ibrahim ya bashi wani abu mai kauri a dukiyarsa shima ya kafa kansa. Shi kuma ya maida komai nasa daya mallaka matsayin na Ummu-Hidaya tare da tsayawa akanta ta koya harkar kasuwanci tun tana ƙaramarta. ALLAH kuma ya sanya albarka a tare da ita dan komai sai sake bunƙasa yake tamkar ba yarinya ƙarama ba.
Bayan ta kammala secondary Ibrahim da Adams suka yanke shawarar aurama Mu'azz ita. Haka kuwa akayi aka musu auren gata. Bayan auren babu jimawa Ibrahim ya nema musu makaranta su duka. Dan shima Mu'azz ɗin zai sake ƙaro karatu duk da ya kammala degree dinsa na farko tun kusan shekara biyu kenan shima yana aiki a companyn Ibrahim.....
Next please 🚦🚴
💕💕💕💕
Mahaukacin bugun da akema gate ɗin gidan ya saka maigadi tahowa da sauri ya buɗe. Zai yi magana Mansoor yasa hannu ya ingijesa ya danna kai ciki. A ƙofar falo suka kusan cin karo da Hajiya Sakina da bugun itama ya fiddota. Kallon kallo suka tsaya yima juna. Kasancewarta gogagguyar mace da idanunta suka gama buɗewa sai ta saki murmushi. “A'a masha ALLAH Son kai ne a gidan namu? Alhamdullah jiki yayi sauƙi kai barka-barka ALLAH mun gode maka”.
Abinda ya tokare maƙoshinsa da ƙyar ya haɗiye, kafin ya kalleta a ɗage ya ce, “Ina ƴarki?”.
Murmushi ta sake yi da faɗin, “Son ƴata ko matarka dai? Ina fatan dai ba zuwa kai kace a yau zata tare ba?”.
Tsaki yaja mai ƙarfi da watsa mata kallon raini. “Ai bana tunanin ta cika macen da har zata tare a gidana. Ballema ni Bamma san da aurenta ba”.
Cikin sosuwar zuciya Hajiya Sakeena ta ce, “Idan kai baka sani ba ai uwarka da ubanka sun sani Mansoor. Kai karfa kaga ina lallaɓaka ka nema gayamin magana. Ƙanwar uwarka ce ni idan ka manta na tuna maka”.
“Na gode da kika fahimci sunanki ƙanwarta ba ita ɗin ba. A tunaninki munafuncin da kika ƙulla aka rabani da wadda nake so zai sa na auri ƴar iskar ƴarki sauran mazan Dubai ne. To kinyi kuskure, dan ko mata sun ƙare ballagazar ƴarki bata cikin matan da zan kalla matsayin mace dan bata da suffar matan. Dan haka na saketa saki ɗaya biyu uku”. Ya ƙare maganar da jefa mata takarda akan fuska ya juya abinsa. Mutuwar tsaye Hajiya Sakeena tayi a wajen, yayinda Husnah ta ƙwalla ƙara ta zube a wajen gaba ɗayanta. Sai a lokacin uwar ta dawo hankalinta. Itama ƙwala ƙarar kiran sunanta tayi da zabura kanta.......
💢✨💢✨💢
💢🌟💢🌟💢
A shekarar farkon aurensu ALLAH ya azurtasu da samun ƙaruwar ciki. Tunda labarin ciki ya iso kowa ke farin ciki, musamman Ibrahim (Abbie) daya kasa zaune ya kasa tsaye. Ƙarshe ma sai ya shirya shi da Adams (Baba prof... sukaje duba Ummu-Hidaya ɗin. Satinsu biyu sai gasu sun dawo, sai dai yanayinsu na komawa sanyi-sanyi duk ya bama kowa mamaki, sai daga ƙarshe muke jin labarin ai cikin ne ya zube ashe. Daga lokacin Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Ba kuma su dawo Nigeria ba sai da ta kammala karatun ta. Irin farin cikin da kowa ya tsinta kansa na dawowar tata bashi da misali. Daga ita har mijinta sun ƙara wani irin ƙyau da cikar haiba. Kai da ka gansu kasan hutu ya zauna a jikinsu. Musamman ita dake mace. Tunda suka dawo ta fara jana a jikinta, yayinda kuma taita faɗan miyasa ban cigaba da karatu ba. Mamana ce ta sanar mata ai Babana ya hana, yace boko kafurci ne. Murmushi kawai tayi bata sake cewa komai akan karatun nawa ba, sai ma maida akalarta da tayi akan batun ya kamata nayi aure. Ganin ta damu nan ma Mamana ta sanar mata ai babu tsayayye. Dariya mukaga tayi, tare da juyawa ta fuskanci mahaifinta dake zaune a gefe yana duba wasu takardu. Cikin nutsuwarta ta ce, “Abbie niko mizai hana ka bama Yaya Abdull auren Bilkisu ne?”.
Mu duka sai da muka kalleta da mamaki, dan kowa yasan wa take cema Yaya Abdull a gidan. Wato dai drivern Mahaifin nata da muke kira jirgin mota. Girmama sunan duk ma'aikatan gidan tarbiyyar Ummu-Hidaya ce haka. Dan kowa bata faɗar sunansa kai tsaye sai ta haɗa da Yaya ko Baba ko Mama ko Aunty. Yanda take daraja mu masu aiki yasa kowa yake ƙaunarta sosai, babu mai son ganin ɓacin ranta sam hatta mu ƙanana.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_
.......A mamakinmu sai mukaga Abbien nata yayi murmushi mai ƙayatarwa da birgewa. Cike da kulawa ya ce, “To Ummuna kin tambayesu suna son juna? Ko kina ganin ya dace ai musu auren dole?”.
“Lah a'a Abbie ba haka nake nufi ba. Nifa na jima da sanin suna son juna. Kawai dai sunƙi bayyanawa ne kasan duk matsorata aka tara daga Yaya Abdull ɗin har Balkisun”.
Dariya kowa ya sanya, yayinda na miƙe da gudu nabar falon. Daga haka ban san yaya aka ƙare ba sai jin ana shirye-shiryen bikinmu kawai. Abdul-wahab mutum ne mai kunya dan haka shima ya gagara mun magana. Duk sanda ma muka haɗu sai dai yayi murmushi kawai ya sunkuyar da kansa. Nima hakan take a gareni. Cikin kwanaki kaɗan aka dasa hidimar biki, zakisha mamakin yanda akai bikin aurena tamkar yarinyar gida ba ƴar masu aiki da drivern gida ba. Bayan kammala bikin anan dai cikin gidan muka cigaba da zama. Sai dai mahaifiyata Ummu-Hidaya ta buƙaci tayi ritaya ta huta hakanan. Hakan kuwa akayi, ta ajiye aikinta suka bata ƙyautar ƙaramin gida ta koma can. Sun buƙaci shima Abdul-wahab ya ajiye aikinsa amma yaƙi, acewarsa bazai taɓa iya rabuwa da mutumin kirki irin Abbie ba. Haka dole suka barsa badan sun so ba. Da a ganinsu shima yanzu ya kamata a martabashi kafin matarsa ta fara haihuwa..
Watan aurenmu biyar da Abdul-wahab sai ga ciki ya bayyana a jikin Ummu-Hidaya. Kowa yasha mamaki dan ciki har kusan wata biyar amma babu wanda ya san da shi. Sai daga baya na fahimci ita fa tasan da abinta tana ɓoyewa ne kawai. Na shiga mamaki ƙwarai da gaske akan ɓoyewar tata. Dan nasan yanda kowa ke fata da zumuɗin samun cikin amma har ta iya ɓoyesa na tsawon lokaci haka. Rashin mai bani amsa yasa na tattara komai na watsar. Kulawar Ummu-Hidaya gaba ɗaya ta dawo kaina. Dan ta tabbatar min na sanya mata ido akan komai da zataci a gidan. Hatta da abinci idan tana so sai tace mu shiga kitchen ɗin tare, tana zaune zan dafa na bata taci abinta anan sannan mu fito. Hatta da ruwan shanta Abdul-wahab kawai ta aminta ya kawo mata daga Company. Ko wani abu take son ci shi kaɗai take aika ya saya mata. In ba shi ba ko an kawo bata ci. Abubuwan suna bani mamaki da ɗaure kaina sosai. Gashi ta gargaɗeni akan kada kowa yasan wannan tsarin nata hatta da mahaifinta. Dole kuwa na haɗiye duk wani abinda ke'a raina da damuwata, na dai cigaba da bada ƙaimi wajen kulawa da ita. Sauƙin ma cikin nata bamai laulayi bane sosai. Dan hatta company bai hanata zuwa ba. Tana gab da haihuwa suka sake buɗe katafaren companyn yin kayan gine-gine da kwalliyar gida. Ummu-Hidaya kuma ce ta samar dashi bisa fiƙirar da UBANGIJI yay mata. A randa akai shagali buɗe Company a ranar naƙudar ta tashi mata. Batare da kowa ya sani ba tasa na kira mata Mamana, ni da ita muka karɓi Haihuwar a gida batare da kowa ya sani ba. Sai wata Nurse ƙawarta da sukai secondary tare mai suna Lawisa (Hajiya ƙarama ina fatan kin gane). Alhamdullah ta sauka lafiya, yaronta santalele namiji mai tsananin kamanni da ita. Dan tsayin mahaifinsa kawai ya ɗakko amma kamanni tako ina na Ummu-Hidaya ne. Hatta da idanunta irin na maguna da gashin kai mai yalwa bai bar komai ba. Sai da ta haihu da kusan awa uku zuwa huɗu sannan tace mu sanar da mutanen gida, dan Abbie baya nan yayi tafiya. Da alama kuma ta sanar da shi, dan zuwa dare sai gashi ya dawo gida. Hakama Mu'azz baya nan a lokacin, shima washe gari ya dawo. Faɗa miki yanda ahalin biyu dama duk mai alaƙa dasu ke farin ciki ba'a magana. Dan hatta fitinanniyar surukarta a wannan rana cikin farin ciki da walwala take. Kafin wani dogon lokaci labarin wannan haihuwa ya zagaye jama'arsu na nesa dana kusa. Dan danan fa shagali ya tashi, abinka da akwai kuɗi, tako ina facaka ake da su tamkar ba'a san ciwonsu ba. Ranar suna yaro yaci suna *_Muhammad Awwab”_*. Yanda akai wasa da kuɗi a wannan shagalin suna al'amarin har ba'a magana. Sai dai abinda zai baki mamaki duk wani motsi Ummu-Hidaya na kaffa-kaffa da ɗanta ne. Daga ni sai Mamana ta yarda mu ɗauke sa. Sai ko Abbienta da Mu'azz. Sai surukanta Adams da mahaifiyar Mu'azz. Bayan bikin suna ya tashi kulawa da Awwab ya dawo kaina. Sai kuma ita Ummu-Hidaya ɗin idan tana gida. Dan tana gyagijewa ta koma harkar kasuwancinta. Kafin Awwab ya cika shekara biyu sun sake buɗe sabon kamfani na yin lass da atamfa da yadika. Sun kuma saka resunansu a jihohi ukku na kudancin ƙasar bayan Lagos.
Muhammad Awwab yaro mai masifar wayon tsiya. Ga ƙyau da shiga ran mutane Masha ALLAH. Sai dai miskilancin tsiya. Baya yarda da kowa sai ni sai Ummien sa sai ko kakansa Abbie da Abdul-wahab. Hatta da mahaifinsa ƙiwa yake masa. Yaro ne mai zafin naman tsiya, dan haka ɓarna sam bata masa wahala. Yayi kuma ya cisgune fuska tamkar bai aikata ba. Yana da shekara huɗu aka sakashi a makaranta, a lokacin ne kuma aka sake kawo mana wata mai aikin, dan acewarta ni ba mai aiki bace ƙanwarta ce. Har kuka nayi kuwa da jin wannan furuci nata, dan haka na ƙara ƙaimi wajen kula da Awwab fiye da komai a gidan. Shekarar sabuwar mai aikin nan ɗaya a gidan itama ta aurar da ita ga drivernta. Shima mutumin kirki ne dan baida hayaniya, ƙani ne ga kai bayin bulawoyi a gidan shima. Shekararsu guda suma ALLAH ya azurtasu da samun haihuwa yaro. Lokacin Awwab nada shekara biyar cur a duniya. Yaronsu yaci suna Hayatu. Tunda aka haifi Hayatu Awwab ya ɗauki son duniya ya ɗora masa. Koda yaushe yana nanne da jinjirin nan. Makaranta ma da ƙyar ake samu ya tafi, yata fitina kenan sai da Hayatu. Tun abin na bamu mamaki har ya koma bamu dariya da birgemu. Shaƙuwar Awwab da Hayatu yasa shima rainonsa ya dawo hannuna dan har lokacin ni ko ɓatan wata ban taɓa yi ba. Hakama Ummu-Hidaya bata sake samun ciki ba. Tama maida hankalinta akan kasuwancinta sai mijinta da shima dai harkokin kasuwancin da suke yi taren yasa ba wani zama yake ba sosai. Dan haka har lokacin Ummu-Hidaya dai na a gidansu ne tare da mahaifinta da bai taɓa ko kwatanta sake yin aure ba. Zuwa yanzu ma shi ya ajiye komai na harkoki ya damƙa a hannun ɗiyar tasa. Yini yake damu a gida da Awwab da Hayatu. Sai idan Adams da ayanzu ake kira Baba prof.. a gidan yazo sunsha hirarsu ko sun fita wata sabgar. Awwab nada shekara bakwai cikin ta takwas Ummu-Hidaya ta sake samun ciki, abin mamaki nima sai ga ciki a jikina. Musalta miki irin farin cikin da muka tsinta kammu a ciki ma ɓata lokaci ne. Mun cigaba da rainon ciki a tare har zuwa watan haihuwa. Itace ta fara haifo ɗanta namiji mai kama da Mu'azz da a yanzu Awwab ke kira Paah matuƙa. Dan tamkar yayi kaki ya ajiye shi kuma. Idanun Ummu-Hidaya kawai jaririn nan ya ɗakko shi kuma. Ranar suna anyi shagali sosai, yaro yaci suna Fahad. Washe garin sunan Fahad nima na haihu mace. Sosai Ummu-Hidaya ta nuna farin cikinta dana duk wanda yake gidan. Ranar suna yarinya taci Ummu-Hidaya. Wannan abu yama Ummu-Hidaya daɗi, dan haka ta ɗauki son duniya ta ɗorama yarinya. Saboda sunata aka sakaya ake kiranta da Falak. Bayan sunan Falak suka tilasta Abdul-wahab ajiye aikinsa. Acewarsu shi yanzu uba ne. Alkairi suka masa mai yawan gaske da zai iya kafa kasuwanci mai ƙarfi, amma duk da haka ya roƙa Abbie akan shi dai zai cigaba da tuƙashi koda zai koma wani kasuwancin ne. Hakan kuwa akayi, duk da ma yanzu shi Abbie ba wani fita yake ba sai idan ta kama dole. Kusan rainon Falak da Fahad ya tashi ne a hannun Ummie da su Awwab, sai da ya shiga primary 5 sannan ya sakarma su Hayatu. A shekarar da Awwab ya shiga jss 2 a secondary ranar wata alhamis Abbie da Abdul-wahab sukai accident a hanyarsu ta zuwa Katsina daga Kaduna duba sabon companyn da Abbie ɗin ke ginawa na sarrafa karfe. Jirgi zasu bi sai aka tashi da hazo, dan daga nan Lagos ta jirgi suka je Kadunar. Mun shiga matsanancin tashin hankali a wannan rana da bazai taɓa musaltuwa ba. A daren ranar ALLAH ya amshi rayuwar Abdul-wahab yayinda Abbie ke cikin mawuyacin hali. Anso yima Abdul-wahab sutura anan Lagos sai dai bai yiwuba, dan yan uwansa tun daga kano sukaje can Kadunar suka ɗaukesa, shi kuma Abbie aka wuto da shi nan Lagos. Ina son tafiya Kano hakan ya gagara, dan ban san irin tarbar da ƴan uwansa zasu min ba saboda basa son auren tun fil azal. Shiyyasama bai taɓa kaini garinsu ba. Ina dai jin sunan a bakinsa. Sai matarsa da mukan ma juna aike idan zai je ko zai dawo. Sai bayan sati ɗaya da rasuwar bisa tirsasawar mahaifiyata muka shirya muka je. Da ƙyar muka iya gano garin Gwarzo. Hakan yasa muka isa a wahalce. Sai dai me duk da azabar tafiya da mukaci bamu sami tarba daga ahalin Abdul-wahab ba. Sai ma kaca-kaca da sukai mana, tare da tabbatar min su basu san Abdul-wahab nada wata mata ba bayan matarsa da suke tare anan gida da ƴaƴansa uku. Dan haka naje can na nemawa ɗiyata ubanta su bazasu karɓa ba tunda tun farko sun tabbatar min basa buƙatata a cikinsu amma na nace sai da na auri musu yaronsu.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.