Showing 213001 words to 216000 words out of 438336 words
duk wanda ya tsaya koda ace ya fisa a shekaru da matsayi. Saukar tattausan tafin hannunasa saman fusakata ya sani sake ɗago idanu da sauri na kallesa. A cikin nashi cat idanun suka sake faɗawa. Kallon juna muke a wani irin yanayi har na tsawon shuɗewar wasu sakanni. Kafin a kasalance na motsa nawa dake tara ƙwallan da ban san na minene ba. Shi ko har a lokacin kallon nawa yake yi batare da ya ƙyafta ba, sai ma cikin wani irin soft voice and silent and slowly ya furta, “She is missing you, and she need you”.
“I miss her too”. Na faɗa nima a hankalin ƙwallar data cika min idanu na gangarowa. Idanunsa ya sake ɗan lumshewa tare da buɗewa a lokaci guda ya cigaba da kallona ina kuka sosai harda shashsheka. Shi bai lallasheni ba, bai kuma janye hannunsa dake a kan fuskata ba har yanzu. Tsawon mintuna biyu ina kukana, dan shirunsa sake tunzurani yake. A bazata matuƙar bazata cikin low voice ɗin sa ya furta,
“Samrh”.
Cak na tsaya da kukan da nake, tare da ɗago jiƙaƙƙun idanuna na kallesa. Kallon nawa shima yake da shanyayun nashi da suka canja launi zuwa golden an blue.
“Why are you crying?”.
Ya sake faɗa muryarsa na sake komawa can ƙasan maƙoshi. Samun kaina nayi da sake sakar masa sabon kukan. Tare da riƙo hannunsa dake akan fuskata na ƙan ƙame.
Idanunsa da suka gama canja launi kawai ya zuba mata. Sai Adams apple ɗinsa ne ke faman kaiwa da komawa a cikin maƙoshinsa. A hankali ya kai ɗayan hannunsa saman kafaɗarta, riƙota yayi tare da ɗagota gaba ɗayanta batare da ya janye hannun nasa data ƙanƙame ba sai da ya kaita gab da jikinsa sannan ya janye ya turata cikin jikin nashi gaba ɗayanta. Tsam ya rungumeta yana mai lumshe idanun nasa ƙam-ƙam shima saboda zafin da jikinta ya ɗauka duk da da akwai kaya a jikinsu su duka sai da ya bala'in ratsashi.
Ni kam jina a jikin nasa ya sakani sake fashewa da kuka. A hankali na fara ɗan dukan bayansa ina faɗin, “Why! Why? Why? Suke wahalar da rayuwarta? Mita musu da zafi haka? Da ga ganinta She is an innocent and strong woman. Basu barta haka ba, sun rabata da ku jininta da zata ji sanyi a wajen ku. Natsane su, wlhy na tsanesu. I promise my self sai na ɗaukar mata fansa koda zasu maidani fiye da yanda suka mata. Sai na sakasu gudun ceton rai da babu mafaka Ya Awwab. I promise....”
Kuka ya sake sarƙeta. Sai wani irin jan nunfashi take a sarƙe kamar mai ciwon asthma. Da sauri ya rabata da jikinsa, tare da kwantar da ita a kan cinyarsa. Sosai numfashin nata ke fisga, hannayensa ya saka duka biyu a kumatunta ya shiga ɗan bubbugawa da kiran sunanta.
“Samrh! Samrh! Please keep calm. I know you can, please calm down. Hundred percent I am with you.”
Ina da gaske ƙoƙarin ƙwacewa numfashin nata yake. Ai baima san ya figi bottle na ruwa dake a side drawer ba ya zuba a hannu ya shafa mata duk da kuwa tana numfashi, sai kuma yay saurin kai mata ruwa a baki amma bakin ya gama datsewa ruwan yaƙi shiga. Da sauri ya kai kan nasa bakin ya zuƙa, batare da wani tunani ba ya ranƙwafo kanta ya ɗaura lips ɗinsa a saman nata ya shiga juye mata ruwan tare da riƙe hancinta. Wani masifar jan nunfashi tayi ta baki sai gashi ta zuƙe ruwan gaba ɗaya. Hancin nata ya saki tare da janye bakinsa. Ita kuma ta fara tari sosai. Sake ɗagota yayi a hankali ya maidata jikinsa ya rungume suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sunfi mintuna uku a haka sai da ya tabbatar zuciyarta ya gama sauka sannan ya raba jikinsu ya kwantar da ita a gadon a hankali...
Kasa buɗe idanuna nayi, sai ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jajjere. Jin saukar abu mai taushi da ƙamshi a saman fuskarta ya sani buɗe idanuna a hankali. Shine ke goge min hawaye da farin handkerchief ɗinsa tass. Idanunsa ya saka cikin nawa har ya gama. Batare da ya janye handkerchief ɗin ba da ɗan yanayin lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Miyasa fitina baya miki wuya? Samrh! Ba'a gaggawa a al'amarin maƙiyi, idan ba haka ba zai fika gudu ne wajen cimma manufa. Lokacin da zaka isa sai ka samu shi har ya gama ya juyo. Be a gentle okay”.
Sosai zantukan nasa suka shigeni tare da canja min wasu tunanina da yawa a kansa. Cikin suɓutar baki muryata a dusashe na furta, “Kana nufin kaima duk abinda ke faruwa kana sane?”.
A bazata naga ya wani ɗan taɓe gefen small pinkish lips ɗinsa da lumshe idanunsa sannan ya saki murmushi. Bily idan nace miki kaɗan ya rage zuciyata ta ɓaro akan murmushin nan nasa da salon da yayisa ki yarda da ni kawai. Badan yafi kowa iyawa bane, sai dan murmushi ya kasance ba ɗabi'arsa bace. Amma tabbas magana ta gaskiya murmushin ya ɗebeni iya ɗiba. Dan kaɗan ya rage na fallasa ɓoyayyen al'amarin da na jima ina binnewa a kansa.
(Kin sani a duhu mutuniyar, kodai kin jima kina son Maash ne?).
“Hummm Bily kenan abar dai zancen sai lokacin yinsa yayi”. Na faɗa cikin ƴar dariya.
(Lallai kam, to shike nan na bari muje zuwa labari).
Yanda yay murmushin har ban san na kafesa da mayataccen kallo ba. Idanunsa ya ɗan waro min waje da ɗagesu alamar kallon fa?. Cikin sauri na kauda fuskata gaba ɗaya ina tura baki da faɗin, “Miye abin kallon ma anan”.
Bai tanka min ba, sai ma ɗan kauda kansa da yay gefe. Banyi zaton jin shirunsa a wannan gaɓar ba. Amma nima dai sai na basar kawai tare da ture hannunsa na janye sauran jikina dake a nasa tare da jan bargo na juya masa baya. Dan in banyi hakan ba akwai babbar matsala, dan komai zai iya fitowa saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri abinda ke can ƙasanta a ɓoye na azalzalota.
Shiru ban sake jin motsinsa ba. Ban kuma yarda na kallesa ba har fin mintuna biyar. Sai a lokacin naji motsin buɗe ƙofa, ɗan juyawa nai kaɗan. Sauka idanuna sukayi akan bayansa dai-dai yana ƙarasa ficewa da jan ƙofar ya rufe a hankali. Nima lumshe idanuna nayi ina sauke ajiyar zuciya. Sai kuma na sake dunƙule jikina a cikin bargon dan ji nake kamar zazzaɓin na ƙaruwar min ma. Mintuna bai fi huɗu da wasu sakanni ba aka sake buɗe ƙofar, idanun na sake buɗewa a hankali. Yanzun kam Mama Balki ne da Doctor sai shi a ƙarshen shigowa. Hannayensa duka biyu a cikin aljihun baƙin wandonsa. Idanun na maida kawai na rufe, dan nasan bai wuce akan zazzaɓin jikina yaje yayo min wannan gayyar ba.
🩸🌟🌟🌟🩸
A hankali take faman kaiwa da komawa a cikin ɗakin nata kai kace safa da marwa take ko motsa jiki. Sai dai sam ba haka bane. Abubuwane masu yawa ke matuƙar damunta da cizar mata zuciya. Dan tun zaman da sukai da Yallaɓai ɗazun da magrib ta gagara samun sukuni. Gaba ɗaya taji ta kasa komawa asibitin da taci burin komawa dan akwai wani baƙo da zatai mai muhimmanci. Maganganunta da Yallaɓai ne suka shiga dawo mata dalla-dalla tamkar a yanzu suke tattauna su....
“Yaushe yarinyar nan tazo aiki gidanku? Waye kuma ya kawota?”.
“Lokacin muna Dubai muma zuwa kawai mukai muka sameta anan. Amma ance Mashi'a ce ta kawota”.
“Mashi'a?!”.
“Yes ita fa. A cewarta kuma ta kawota ne as a birthday gift wa mahaukaciyar matar can. Tunda masu aikinta sun sake guduwa a lokacin babu mai kula da ita”.
“A ina ta ɗakkota?”.
Ɗan jimm tayi, sai kuma ta ce, “Gaskiya wannan ne ban sani ba”.
Kasa sake cewa komai yayi, sai ma kai-kawo daya shiga yi hannayensa goye a bayansa..........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
___________
.......Yayi kusan sau fin huɗu sannan ya dawo ya zauna. Cikin kaushin murya da dakewa ya furta, “Dole ne yarinyar nan ta mutu a asibitinki. Kuma a yau zuwa gobe nake buƙatar sanin daga inda ta fito? Miye dalilin Mashi'a na kawota?. Zaki cigaba da riƙeta har zuwa kwanaki uku da za'a gama min bincike na”.
Idanu Hajiya Ƙarama ta zubama mutumin zuciyarta na gudu da sauri-sauri a ƙirjinta. Cikin ɗan rawar lips muryarta na seizing ta ce, “Amma yallaɓai hakan fa zai iya zama kuskure. Dan yarinyar nan gaba ɗaya komanta ya gama dai-daita raunin daya jimata ne kawai ya rage ya ƙarasa warkewa mu sallameta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko jibi. Sannan case ɗinta bama fa a hannuna yake ba doctor Larai ce ke kula da ita. Daɗin daɗawa Awwab. Yaron nan fa ya wuce duk inda kake zato da tsammanin sa kaima ka sani. Ni wlhy zuciyata ma ta fara bani kamar a ankare yake da abubuwa da yawa. Gashi sam baya jin tsoro ko shakkar kowa. Yanzu ka dubafa yarinyar mutane yama fyaɗe a cikin gidansu amma komansa bai canja ba face ma wani irin kulawa da yake bata ga girman kai sabo da yake ji da sam na gagara fassara al'amarin nasu”.
“Mtsooww Lawusa, ke kin san dai idan na faɗi magana ko zartar da hukunci bana canjawa ko? Dukan waɗan nan hujjojin naki basa gabana. Gawar yarinyar nan kawai nake buƙatar gani fine and done”. Ya ƙare maganar a wani irin hankali yana zazzaro mata idanunsa da sukai mugun kaɗawa saboda giyar da yake ta faman lodama cikinsa tun kan tazo. Yawu masu kauri ta haɗiye. Sai kuma ta shiga jinjina kanta. “Okay shike nan naji zan kashe yarinya bayan ansan wacece. Sai dai fa kaima ya kamata ka tuna lokaci yayi da zaka yi komai a wuce wajen. Nifa ina buƙatar shares ɗina, dan lokaci yayi da zan mora wahalata ta shekaru gaskiya. Tunda ba ƙuruciya nake ƙarawa ba. Yaron can Fahad banga amfanin saba ai, shima ya cancanci mutuwa. Sannan magana ta gaskiya mahaukaciyar matar nan na gaji da shiga da fita ina shan warin sashen ta itama. Ya kamata kayi wani abu, dan nasan dai zuwa yanzu kaima ka fanshe dukan alƙawarinka da alwashinka a kanta. Kaga sai muje next target wato Awwab. Dan Doctor Ram ya tabbatar min ko a yau muke son poison ɗin nan a shirye yake da aiko mana shi Nigeria.”
Iska mutumin da tunda ta fara maganar ke kallonta yake ta faman furzarwa. Sai da ta kai har ƙarshe kafin ya ɗauka kofin giyarsa ya kai baki, ƙarasa shanye wanda ya rage a ciki yayi ya dire glass cup ɗin a saman Centre table ɗin gabansa yana wani girgiza kansa. Sai kuma ya maido jajayen idanunsa ya zuba mata. “Dont warry Lawusa. Komai da kika sani a tsare yana nan bai canja ba. Sai ma ƙarin shares da kowannen mu ya samu sakamakon sake hauhawar dukiyar nan. Dan yaron nan ba ƙaramin mahaukacin arziƙi ya tara mana ba. Shiyyasa nake son ki fahimceni akan kashe yarinyar nan. Dan sam na kasa jin nutsuwa akan barinta raye tun kan nasan wacece ita. Kije ki ƙarasa aikin ki a next zama zaki ji mina tsara game da Fahad ɗin shima”.
“Shike nan yallaɓai ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana. Na barka lafiya a huta gajiya”.
Hannu kawai ya ɗaga mata da maida idanunsa luuu ya rufe cikin mayen barcin buguwar da yayi......
Iska ta furzar mai zafin gaske. Tare da tura hannunta cikin hular kanta. A take hular ta zame ta faɗi, gashinta mai ƙarancin tsayi da cika ya bayyana. Bata damu ba, dan abinda ya dame ta shi ya dameta. Tunda ta haɗu da Yallaɓai bai taɓa saka mata doka ko sanyata aiki ta gagara yinsa ba, saboda ra'ayinsu bai taɓa banbanta ba. Sai dai a wannan gaɓar an samu akasi. Dan yallaɓai ya sakata yin aikin da ita kanta tasan idan tayisa sai ta cutu. Matuƙar cutuwa. Domin kuwa ita kaɗai tasan irin son da takema yarinyar nan with all her heart. Duk da tana jin zafin abinda shegen yaron nan mai kama da ɗanyen attaruhu yay mata ɗigon sonta bai ragu a zuciyarta ba. Jinta take a yanda ta jure kwanakin baya akanta yanzu bazata iya ba. Dan wani irin mayataccen buƙatar son kasancewa da ita takeyi. A jiya kaɗan ya rage tabi dare a asibitin ta lalubeta. Sai dai ba haka take so ba. Tafi son su mori juna yanda ya kamata. Dan tana jinta a ranta banban da sauran waɗanda ta mu'amalata daga fara wannan harkar zuwa yanzun. Yarinyar akwai kayan marmari fresh a jikinta matuƙa da har wani sashe na zuciyarta na ƙin ganin bebekin Awwab akan abinda yay mata. Yo ita mace ma ta kasa nutsuwa balle shi namiji mai ji da shekarun ƙuruciya da hutu. Sosai tana jinta a tsaka me wuya...
“Yau ma wani ɗinne ya mutu da kika kasa nutsuwa?”.
Firgigit ta dawo hankalinta tare da juyawa tana kallonsa. Shima kallonta yake fuska babu yabo babu fallasa. Paah ya sake watsa mata kallo murya a kausashe ya furta, “Dan iskanci kinzo nan kin shanyani bayan ina can ina jiran ki kawo min coffee”.
Ajiyar zuciya Hajiya ƙarama ta sauke da ƙoƙarin controlling kanta. A hankali ta saki murmushi tare da canja yanayinta like she is innocent woman, cikin kwantar da murya ta ce, “Kayi haƙuri Abban Awwab. Ƙafata ce fa ta riƙe daga fitowa a bayi shine nake ɗan mammotsata. Amma wlhy kana raina tunda naga lokacin shan coffee ɗinka yayi. Amma ganin baka kirani ba yasa nai tunanin ko baku dawo daga masallaci bane”.
“Tunda nine limamin masallacin ba”.
Ya faɗa a gatsine cike da sake tunzura. Sake kwantar da murya tayi da shiga bashi haƙuri. Uffan bai sake cemata ba ya fita fuuuu yana harare-harare dan dama borin kunya ne kawai ya naɗe da hauka. Tun ɗazun yana a garden ɗin Maash tare da Siyama suna holewarsu. Dan tunda ya fahimci Maash baya gidan ya tura mata saƙo a waya kan ta samesa a garden ɗin Kasancewar yasan anan ɗine zasu iya zama safe fiye da ko'ina a gidan irin wannan lokacin. Sai yanzu ne yake fitowa dan yasan duk inda Awwab yake yana gab da dawowa gidan....
Itama da kallon harara ta bisa. Kafin taja tsaki da faɗin, “Nadai kusan yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda stupid man. Dan ɗauke beauty yarinyar nan zanyi mubar ƙasar zuwa can muyi aurenmu mu more rayuwar mu. (Umarnin yallaɓai fa?) Zuciyarta ta ayyana mata. Kanta dake wani irin sara mata ta dafe kawai zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Lallai dole ne tasan mafita a daren yau basai gobe ba. Dan tafi kowa sanin wanene yallaɓai akan duk abinda ya sa gaba. Amma bari taje ta bama wannan sakaran coffee dai ta dawo.....
(Tofa 🤔 kaji kuma wani lissafin 🥱🤫)
💢🪴💢🪴💢
A gidan Abba Imamu rayuwa ta matuƙar juyama Mom baya. Dan sam ta kasa gane komai akan al'amarin Halime. Yarinya ce shu'uma matuƙa. Ga kalolin baƙin ciki da take tura mata iri daban-daban. Yanzu har takai Abba ya sallami mai aiki yace kowa tai aikinta ranar girkinta. Mom son jiki, Bibaa da Baby basu iya komai ba. Sai yazam a gidan duk ranar aikin Mom yini ake da yunwa, dan ko anyi abincin da wahala ya ciyu. Daga ƙarshe su ƙare da rigima ita da Abba. Dan ya tabbatar mata shi kam bazai ɗauki wannan banzan halin ba da almabazarancin abinci. Ashe da can duk wahalar gyaran gidan da abinci dama Samraah ce keyi ita kaɗai nata ƴaƴan na kwance. To ta sani bata cutar masa ɗiyar ƴar uwa ba kanta ta cuta. Dan ba baki ya mata ba ƴaƴanta in har a haka zata kaisu gidan miji to