Showing 204001 words to 207000 words out of 438336 words
A hankali ta ɗago ta kallesu.
Sai da zucuyata ta motsa da ganin waɗanda banyi zato ba. Idanuna na maida na rissinar ina ƙoƙarin haɗiye mamakina da ƴar tsorata. Sai da suka gama zama a inda Mama Balki ta nuna musu sannan na gaishesu cikin muryata da sam bata fita saboda kukan da naci na kwana da yinin jiya. Wasu sun amsa wasu basu amsa ba. Ni kuma sai banji damuwar komai ba tunda nasan dama ba lallai duk su amsa ɗin ba. Kasa cigaba da shan tea ɗin nayi ban kuma ɗago na kalla kowa ba a cikinsu, suma kuma babu wanda ya sake yin magana. Dai-dai nan aka ɗan sake knocking ƙofar. Mama Balki ta zabura domin buɗewa. Jin yanda take jaddada kalmar sannunku da zuwa cikin jin daɗi ya sani ɗan ɗago idanuna na kalla ƙofar. Tamkar abin shiri sai karaf suka faɗa a cikin nasa. Wani irin ɗan jan nasan yayi yuuuu zai lumshe nai saurin fara ɗauke nawa da maida kaina na duƙar. Sai kuma naji duk zaman yama gundireni, ga wani bugawa da zuciyata keyi dan harga ALLAH ko ganinsa tsoronsa yake ƙara min, ni kaɗai nasan kalar masifar dana gani a daren shekaran jiya hannun mutumin nan, dan haka ko matsoraciya kika kirani a wannan gaɓar Bily ni bazan damu ba. Kofin tea ɗin na ajiye a side drawer ɗin gadon na zame a hankali na kwanta tare da lumshe idanuna. Ƙasa-ƙasa na tsinkayi wata muryar dattijo da kamar na taɓa jinta na masa magana. Banji amsar daya bashi ba kasancewar shi dama idan zai yi magana sai in yaso kowa ya jisa ne. Ya ringa yinta acan ƙasan maƙoshi kamar mai jin haushin mutane. Kaɗan nai ƙoƙarin buɗe idanuna dan ina son ganin mai muryar nan sai naga ya nufo inda nake gadan-gadan. Sai da zuciyata ta sake harbawa. Babu shiri na maida idanun nawa na lumshe. A bazata, matuƙar bazata naji alamun rankwafowar mutum da mayataccen ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa akan fuskata. Ai babu shiri na ware idanuna. Shi ɗin ne kuwa, gaba ɗayansa yamun rumfa hannayensa duka biyu ajiye a saman gadon ta gefe da gefena. (Kambu! Anya mutumin nan nada kunya?) Na faɗa a zuciyata ina waro gaba ɗaya idanuna waje. Amma shi sai ya wani kaɗa min cat ɗin nasa da ɗage gira hankali kwance. Tuni ƙwalla sun cika min ido, cikin marairaicewa na shiga motsa lips ɗina zanyi magana. Sai kawai naji saukar yatsarsa a saman bakin nawa, idanunsa cikin nawa, cikin salon lumshe idanu da maida muryarsa low sosai ya ce, “Shiii!! Bana son surutu”.
Kunya takaici suka lulluɓeni a lokaci ɗaya. Gefe na kauda kaina tare da ture yatsansa daga saman lips ɗina, dan kalmar baya son surutun faifan taswirar daren shekaran jiya ta dawo min da shi fes. Hannun ya saka ya taro fuskar tawa ya maidota inda take. Baki na tura masa, ina son na hararesa amma shakkarsa da kwarjininsa sunyi masifar min ɗaurin goro, ga mayataccen ƙamshinsa dake tsarga min zuciya.
“Bakin nan yana buƙatar wani abu ne halan?” ya faɗa cikin soft voice yana ƙoƙarin maida yatsarsa a saman lips ɗin nawa. Hannu na na kai da sauri na rufe bakin ina zaro idanu, amma shi ko gezau zama ka iya rantsewa ba shine ke maganar ba. Hankalina sake tashi yayi na saci kallon inda ƴan gidansu suke. Duk suna nan a ɗakin har Mama Balki ma. Tamkar zan fasa ihu idanuna cike da ƙwalla na ce, “Duk suna kallonmu fa”.
Ƙoƙarin juyawa yay zai kallesu, ai bamma san na kai hannuna ba da sauri kan fuskar tasa na dawo da shi.
“What? kuma. Bakin ce na faɗa musu ne su fita kina son mijinki ya ɗanyi kissing ɗinki ba”. Ya faɗa cikin salon kashe ido da ɗan ɗage gira sama murya can ƙasa kamar mai raɗa yana ɗora hannunsa kan nawa da nake ƙoƙarin janyewa daga fuskar sa.
Harararsa na ɗan yi hawaye na cika min ido na ce, “ALLAH ya kiyaye ni yaushe na ce hakan? Kuma ni ba ƴar iska bace”.
“Oh really”. Ya faɗa cikin ɗage gira sama yana ɗan taɓe baki kaɗan da sake matso da fuskarsa daf da tawan. Wani irin bugawa zuciyata ta shiga yi da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirjina ta fito. A hankali na fara jin saukar iska da ƙamshin mouth freshener mai ƙamshin strawbarry. Luff nayi zuciyata na sauka a hankali daga bugawar da take da motse-motse a cikin ƙirjina, harda tura baki batare dana sani ba.
Ɗal ya ɗalle lips ɗin da yatsunsa murya can ƙasa ya furta “I'm not interested maida bakin”.
Cikin sauri na buɗe idanuna wani irin tuƙuƙi na turnuƙe min zuciya da takaicinsa. Dai-dai nan yake ɗagawa da ga duƙowan yana wani yin fuuuu da idanun nasa. Jinai kawai hawayen da nake riƙewa sun wani irin silalowa a hankali...
Maash kam da ya ɗago kallo ɗaya yayma kowa na ɗakin ya ɗauke kansa tamkar baiga irin kallon da duk suke masa ba na tsantsar mamaki da tu'ajjibi. A zafafe Hajiya Mammah ta yunƙura zatayi magana Baba prof ya girgiza mata kai alamar kar tace komai ba. Badan taso ba tai shiru, sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yanda ta gama cika tai famm. Duk abinda ke faruwa hankalinsa na kansu ta wutsiyar ido, amma yay tamkar hankalin nasa akan file ɗinta daya ɗauka yake dubawa. Dai-dai nan likitar da ke dubata ta shigo ɗakin Nurse biye da ita. Ita ta fara gaishesu, dan duk inda akaga Family ɗinsu ana gurmamasu saboda Maash ɗin.
Sai da suka gama gaisawar sannan shi da bai ko kalleta ba ya ɗago shanyayun cat idanunsa ya ɗan kalleta, sai kuma ya kauda kansa cikin dakewar nan tasa ya mika mata takardar daya zare jiya a cikin file ɗin ya miƙa mata. Amsa tayi cikin mamaki, sai kuma ta kalla takardar. Ɗagowa tai cikin rashin damuwa, sai ma gani da take ai tayi abin arziƙi dan haka baki a washe ta ce, “Sir komai da ya kamata mun rubuta kamar yanda binciken mu ya bamu akan fyaɗen, dan a yanzu haka ma muna muku albishir ɗin samar da ƙwararriyar lawyer da zata tsaya mata akan case ɗin. Yau kuma zan kai report ɗin ma police dama izininku kawai nake jira kasancewar ita Hajiya tace ba huruminta bane sai kai yayanta kazo. Amma gaskiya sir ina ƙara bada shawaran kowa ya aikata irin wannan zalincin ga baiwar ALLAHr nan shima ya ɗanɗana kuɗarsa. Dan ALLAH ne kawai ya taƙaita al'amarin da zata ma iya kamuwa da matsalar yoyon fitsari. A yanzu haka ma dole tana buƙatar kulawa sosai saboda ɗinkin dake jikinta abin sam babu daɗi, dan ban taɓa ganin case ɗin fyaɗe na tsagwaron zalunci irin wannan ba. Banama jin mutum ɗaya ne ya aikata abi.....”
“Ina buƙatar sallama by now”.
Ya faɗa cikin katseta da yanayin da kowa ya kasa fassarawa daga garesa. Sororo likitar tayi tana kallonsa. Sai kuma ta ɗan marairaice fuska cikin nuna damuwa ta ce, “Sir ko akwai wani kuskure da mukayi ne anan ɗin? Wlhy duk kulawar da kake buƙata muna kan bata ita yanda ta kamata. Yanzu fa nake maka bayanin har lawyer ƙwararriya mun samar akan case ɗin”.
Komai baice ba, sai ma ɗauke kansa da yay cikin nuna ƙosawa da maganar tata. Da yaga bata da alamar fahimtar shirun yake buƙata sai kawai ya nufi gadon da Samraah take cikin takun ƙasaita da bajinta hannayensa duka zube a aljihu. Duk abinda ke faruwa ina jinsu, dan haka zuciyata ke wani irin gudu raina fal mamakinsa. Guy ɗin nan he is stubborn mutum wlhy. Rayuwarsa har mamaki take matuƙar bani, mutum kamar wani dutsi baka taɓa iya gane gabansa da bayansa. Cak ɗin da aka ɗagani ya dawo dani hayyacina, sosai na zazzaro idanuna waje cikin matuƙar mamaki da ruɗani, rawa lips ɗina suka kamayi. Da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi...miye haka kake yi?”.
Ko kallona bai yi ba, sai ma takawa daya fara a hankali babu wani alamar jin shi yayi ba dai-dai ba ya bi ta tsakkiyarsu ya fice. Nikam ai sai naji bazan iya jurewa ba kawai na cusa kaina cikin ƙirjinsa tare da saƙalo duka hannayena ta wuyansa na saki kukan da ban san dalilin yinsa ba........✍️
_Ehem ehem Yayanmu ikon ALLAH, na Samraah bada kanka a sare kace ma su baba prof ya faɗi🤣🤣🤣_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_
.......Da sauri Hayatu dake tsaye daga bakin ƙofa yaja da baya kansa a ƙasa yana ƙoƙarin ƙumshe dariyar dake neman kufce masa. Isowarsa dai-dai saitinsa ya sashi haɗiye dariyar da ƙyar ya buɗe masa ƙofar da sauri yana ƙoƙarin matsawa.
“Kuzo da kayan”.
Ya faɗa a hankali dai-dai yana ficewa gaba ɗaya daga ɗakin.
“A lallai Mu'azz ka haifoma kanka jaraba wlhy.”
Hajiya Mammah ta faɗa cikin tafa hannaye da riƙe haɓa. Babu wanda ya iya cewa da ita komai dan duk abin faɗar ya gudu musu a bakuna. Sai ma Baba prof ne daya motsa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki yabi bayansa. Dole duk suma sauran duk suka motsa suka take masa baya. Sai da suka gama fita Hayatu ya ƙarasa gaban doctor ɗin. Kallon Mama Balki yay yayi murmushi. Itama sai ta murmusa tare da nufar kayayyakin su kawai ta shiga haɗawa. Doctor data gama shiga cikin ɓacin rai kallon Hayatu tayi zatai magana. Da sauri ya katseta da faɗin, “Doctor kiyi haƙuri kawai ki bada takardar sallamar nan. Dan wlhy boss da kike gani baya magana biyu. Tunda ya yanke hukunci ya yanku, ya kuma fiki sanin muhimmancin wannan patient ɗin taki”.
Cikin ɗan ɓacin rai ta ce, “Wane muhimmancin ta ya sani anan?. Ana gaya masa haɗarin da yarinya ke a ciki saboda zaluncin da akai mata yana nuna kamar ma baya fahimta. Ni ban taɓa sanin guy ɗin nan stubborn bane sai yau. Idan ma ɗakin ne bai masa ba way not yay magana sai a canja mata da wani”.
Murmushi kawai Hayatu yayi dan ya fahimci bafa zata fahimta ba. Itama sai ta fita rai a ɓace tana mita dan gani gake shima Hayatun neman raina mata hankali yake yi. Binta kuwa yayi bayan ya amshi kayan da Mama Balki ta haɗa suka fito tare. Yana zuwa office ɗin doctor ta miƙo masa takardar sallamar a harzuƙe. Komai baice mata ba ya ɗauka ya juya abinsa ya fito.
Samunsu yay suna shiga mota, dan shi gogan nasa ma har ya shige abinsa. Gaba ya buɗe ma mama Balki ta gefen sa ta zauna, shima yana ƙoƙarin shiga Baba prof ya ƙaraso wajen, umarni ya bama Mama Bilki kan ta fito ta koma motarsa, shi kuma ya shiga gaban ya zauna yana bama Hayatu umarnin suje *_KARAMCI HOSPITAL_* asibitin Hajiya ƙarama kenan. Amsawa Hayatu yay yana satar kallon Maash dake a baya tare da Samraah ta cikin mirror. Jingine kansa yake da kujera idanunsa a lumshe tamkar bai san mike faruwa ba. Shi kuma ya tabbatar duk yana jinsu. Kallo ɗaya yay ma Samraah dake kwance kanta a saman cinyar Maash ɗin itama idanunta a rufe ya ɗauke kansa yana ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya......
🌿❤️🔥🌿❤️🔥🌿
Hajiya Sakeena na kai ƙarshen bayaninta Mansoor ya fasa wata gigitacciyar ƙara da ɗaga Centre table ɗin gabansu ya wancakalar. Babu wanda bai firgita ba. Ƙafa yasa ya bugi table ɗin da masifar ƙarfi, badan takalmin dake a ƙafarsa ba babu abinda zai hanashi jin ciwo. Da sauri Attahir ya miƙe yana ƙoƙarin riƙo hannunsa da kiran sunansa. Amma sai shima yay wani irin wancakalar da shi gefe har sai da Attahir ɗin ya zube a kujera. Cikin zafin zuciya da basu taɓa sanin yana da ita ba ya nuna Hajiya Sakeena da Mamynsa da take wani irin kuka tamkar ranta zai fita. Cikin kaushin murya da rufewar idon da fushi ya haifar masa ya ce, “Na tsane ku. Ku biyun nan ba bana son sake ganinku a rayuwata har abada. Kuma yanda kuka zama sanadin rabani da ita kuma na barku har abada!!!!!!”.
Daga haka ya figi bag ɗinsa fuuuu zai fice. Ƙoƙarin miƙewa Attahir yay cikin ƙarfin hali yana kiran sunansa. Yayinda Mamy tai wani irin fashewa da kuka ta bisa da gudu ta riƙo rigarsa. Ko juyowa ma baiyi ba yasa hannu ya kaɓe natan tare da hankiɗata yay ficewarsa. Kafin ta miƙe tabi bayansa tuni yama fice a gidan ko mai kama da shi babu a compaund. Nan ɗin ma fita Attahir yay a guje, sai dai yana fitowa napep ɗin data ɗauki Mansoor na barin ƙofar gidan. Komawa yay cikin gida da gudu bawan ALLAH duk ya ruɗe. Dan key ɗin mota yake lalube amma ya gagara ganin ko guda ɗaya. Haka ya sake fitowa da gudu ya fita shima ya tare napep ya shiga suka bi bayan Mansoor. Amma ko mai kama da shi basu gani ba. Har airport yasa suka bishi a tunaninsa can zaiyi. Sai dai nan ɗin ma babu alamar Mansoor ɗin. Abinda bai sani ba kuma Mansoor bai je airport ba, dan ya fahimci abu na farko da zasu farayi kenan dan haka yaje ya kama hotel anan anguwarsu da yasan bazasu taɓa tunanin zai tsaya anan ba. Na kwana ɗaya ya kama, dan daga yau zuwa gobe yake son sake barin ƙasar nan. Sam bazai iya zama ba. Gara yayi nesa nesa can inda bazai sake ganin kowa ba a cikinsu har ƙarshen rayuwarsa...
Duk wannan budiri da ake Dad bai ko motsa ba. Yana zaune ne kawai kamar saƙago a falon. Ba haka Hajiya Sakeena taso ba. Taso ace tana gama bada labarin nan yanda Mansoor ya fusata shima Dad ya fusata ya dinga ɗirkar Mamy da jera mata kalmomin saki uku sannan yace ta bar masa gida. Amma ba komai, ko yanzu ma ai tasan ƙurar bawai ta ƙare bane ba. Dan ita shaidace akan zuciyar Dad tamkar akku kuturu yake. Kusan zuciyar tasa ce ma yau Mansoor ya kwatanta. Shi kansa shirun da yayi ta tabbatar zuciyar ce ta kume ƴan maza wayaga kutu-ban-ban. Haka ta fito babu tausayi babu imani ta tsallake Mom da nunfashi ke neman ƙwacewa tai ficewarta. Acewarta ai itama haka Mansoor ya tsallake tata ɗiyar ɗaya kwallin kwal a duniya ya tafi babu tausayi balle imani bayan ya gama zana mata kalaman saki uku da gasa mata magana iya son ransa...
Duk neman daya dace Attahir yayi ma Mansoor amma bai gansa ba. Dole ya haƙura cikin maɗaukakin tashin hankali ya koma gida ransa duk a dagule. Yana zuwa kuma ya iske Mamy a sume a farkon shiga falo. Tashi hankalinsa ya sake yi, dan ga Dad zaune tamkar saƙagon gunki zuciya ya kumesa tamkar shima ɗin ya suma. Baima san ya sunkuci Mamy yay waje ba cikin tashin hankali yana kwala kiran sunan drivernsu.....
🪴🪴🪴🪴🪴
*_KARAMCI HOSPITAL_* asibiti ne da zamu iya kiransa tsaka tsaki a girma. Dan bai kasance ƙaton gaske ba, bai kuma kasance ƙarami ba. A ɓangaren kayan aiki komai an wadatashi da shi. Duk da sunansa asibitin kuɗi ana aiki a cikinsa tamkar ƙyauta ne saboda sauƙi da sauƙaƙama al'umma. Hakan yasa mafi yawan talakawa suke saurin garzayowa jiyya da karɓar magani a cikinsa. Sai dai da yake komai nasu a tsare yake bazaka taɓa samunsa barkatai ba komansu a tsare yake.
Kamar dai yanzu daya kasance rana ta fara ɗagawa, tako ina tsaftace yake sai ma'aikata dake ɗan kai kawo. Sannan shiru yake babu wata hayaniya ko yawan kai-kawon mutane bayan ma'aikatan saboda dokarsu ce irin yanzu ba'a zuwa duba mara lafiya sai yamma daga huɗu zuwa shida. Koda motocin su Maash suka iso ma da farko securitys ɗin ƙin tashi sukayi su buɗe saboda dokarsu ce ba'a ganin mara lafiya da dare ko safiya zuwa kafin cikar huɗu ko kai wanene, sai da Hayatu yay kiran number Hajiya ƙarama sannan securitys ɗin suka tashi cikin rawar jiki suka wangale gate ɗin. Suna gama parking Tsaki Hajiya Mammah tayi tana mita harda zagin Hajiya Ƙarama lokacin da take fitowa. Babu dai wanda yace da ita komai.
Hajiya ƙarama da kanta ta fito tana musu barka da zuwa dan ita tunda safe tana anan asibiti batama san sunje duba Samraah ɗin ba, ana gama case ɗin human right ta baro gidan. Cikin girmamawa ta gaida Baba prof.. ya amsa mata tare da mata