Showing 303001 words to 306000 words out of 438336 words

Chapter 102 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2239

BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


.....“Lallai kai ka tabbata ɗan kunama Adams, har ni kake bada kwangilar a kashe yau? To lallai kayi babban kuskure, dan Lawisa da kake gani ƙadangaruwar bakin tuluce. A barni na ɓata ruwa, a karni kuma a kar tulu. Kuma wlhy kayi kuskuren barin abinda ke ranka ya fito fili har na jisa. Wato dama planning ɗinka kenan kasheni. Kai wannan tsohon ban taɓa ganin asararre irinka ba tsohon najadu da zai ƙare rayuwarsa a rumfar asara. Koda yake bazanyi mamaki ba, tunda har hassada ta kaika ga cin amanar wanda ya ɗaukeka daga rana ya kaika inuwa dama nima nasan za'azo wannan gaɓar, sai dai kuma ita wannan Lawusar ba Alonso bace. Ba kuma Ummu-Hidaya bace da ka raina. Wlhy sai naga bayanka. Baƙin azzalumi, dama wannan ruɓaɓɓen plan ɗin ka shirya shiyyasa kaketa wani ɓoyema mutane ko, to kaje ka samu likitoci su maka wankin brain, dan naga alamar taka dattin giya ya cikashi. Na kuma maka alƙawarin ni Lawisa sai na fara ganin bayanka. Kai kuma ɗan koranka an saka ka kasheni ko, idan zaka gwada bissmillah”.. ta ƙare maganar da karkaɗa yatsunta a gaban fuskar Commondo ta juya fuuuu ta fita a falon. Babu wanda ya iya motsawa a cikinsu. Dan kowa da abinda yake tunani. Sai zuwa can Commondo ɗin ya ja numfashi ya fesar. Cikin yanayin nan nasa na ciccijewa ya fara magana.
“Oga kafayi kuskuren saka mace a wannan sabgar taka. Musamman ma wannan mai buɗaɗɗen idon, dan wannan daga ganinta kaga hatsabibiyar da zata iya aikata komai dan cikar burinta. Tabbas da ace ina nan ka shirya ƙulla alaka da ita da bazan bari ba. Amma karka damu, ko yanzun saina nuna mata babba babbane. Badai duk abinda take taƙamar da shi a ƙarƙashin ikonka yake ba. Sai na koya mata darasi kafin na kaudata. Amma saka batunta a gefe, ina son wannan abun dake neman ƙwaɓewa mu gyarashi da shiri na musamman dan na fara zargin itace ma ta kuɓutar da matar nan a gidan”.
Karo na farko da tun bayan fitar Hajiya ƙarama Baba prof ya ɗago ya kalla Commondo. Kai ya jinjina masa alamar tabbatarwa. Tare da faɗin, “Yes oga ka auna mana. Idan babu rami miya kawo rami?”.
Sosai Baba prof ya gamsu a wannan gaɓar, domin kuwa ya ɗan buɗe mata wani abu a lokacin da sukai kiciɓus a ƙofar sashen Awwab ɗin kallon data masa ya kamata ya saka masa alamar tambaya, amma duk da haka ya mata nuni da ta kauda matar da ƴarta, shine tai amfani da Ummu-Hidaya ta fitar kenan a gidan?. To anya kuwa ba itace ma tai kidnapping masa Mu'azz ba?”.
Kallon Commondo yayi cikin jinjina kai ya ce, “Zan iya yarda da zancenka dan ƴarta ce ta ankarar damu sanda suke guduwa. Sannan itace taja motar sanda muke binsu. Ta kuma kasa cimmusu har suka gudu. Sannan na fara zargin Mu'azz na hannunta. Dan idan ka haɗa 1+1 amsa guda zai baka. Dama tana da shirin cin amanata kenan?”.
“Bazamu tabbatar da haka ba sai mun bita a sannu. Idan ta tabbata cin amanar taka take shirin yi kuma. Aiko sai tayi nadama Boss. Ka bani nan da zuwa dare zanyi tunani. Amma kaima kayi wani abu guda. Yana da ƙyau na dinga sanin mi ka shirya saboda gudun samun matsala. Dan tun farko da nasan abinda ka shirya kenan baza'a saki wannan maganar data karaɗe lungu da saƙo ba har sai mun fara yin abu biyu. Sannan zamu rushe uku a ciki”.
Kai Baba prof ɗin ya kaɗa masa. “Dama banyi aikin don yin wani abu ba. Nayi ne kawai dan ɗauke hankalin mutane. Dan nasan zancen zai ɗauki lokaci ana tattaunashi”.
“Hakane kuma oga. Amma abinda ya fi tsaya min a rai shine batun Maash na asibiti. Taya hakan zata kasance bayan lafiyarsa ƙalau?. Sannan Maash FURAR DANƘO ne akan shekara ana damunsa bashi farau-farau.”
“Lafiya Lau yake. Yana Dubai a cikin gidansa. Na saka an katse network ɗin gidanne kawai da wuta da ruwa, an kuma zagaye da securitys yanzu haka shi baima san mike faruwa ba sam. Yaronsa kuma na hannunmu.”
Kasa magana ma Commondo yayi, dan yasan wanan ramin sam bai ginu ba. Gaskiyar Lawisa wannan tsohon dattin giya ya gama cinye masa ƙwaƙwalwa wlhy. Jiba wani wawan shiri dan ALLAH. Amma ba damuwa, shi bari yayi wasa akan nashi wasan dana Lawisa. Tunda yanzu ya fahimci tun a duniya ake fara nafsi-nafsi. “Oga ka bani nan zuwa dare zanyi tunanin mafita. Kaima ya kamata kayi wani tunanin mu haɗa plans kamar biyu mu gani. Yanzu mu dukanmu muna buƙatar hutu”.
Sosai Baba prof ya gamsu da hakan. Dan tabbas kansa ma shi gaba ɗaya a juye yake. Sannan ya yarda da Commondo fiye da ɗari bisa ɗari a rayuwarsa. Baya taɓa kawoma ransa zai iya cin amanarsa. Kallan Commondo ɗin yayi, cike da yarda ya ce, “Suma ahalin yarinyar nan ya kamata muyi tunani a kansu. Dan nayi tuya na manta da albasa kasancewar ban san makirin can ne ya karɓi waliccin auren ba. Bana son maganar nan ta lafa da ga nan har zuwa randa zan saka a buɗe Awwab. Dan ina son lokacin da zai fito kansa yay matuƙar ɗaukar zafi ya rasa ina zai fara kamawa, ta hakanne kawai zan iya cimma burina a kansa. Sai maganar Ummu-Hidaya, bana son akai safiya bamu san inda suke ba. Hakama Mu'azz”.
“Ka ɗauka wannan matsalar na maganceta ma. Dana fita daga nan zan fara samar da masu binciken ne ta ɓangarori biyun”.
Kai kawai Baba prof ya jinjina masa. Sallama commondo ya masa, shi kuma ya samu giyarsa ya kwankwaɗa sannan ya tashi ya shige ciki....

Commondo na barin gidan Baba prof gidansa ya wuce. Bai yi mamakin samun Hajiya ƙarama ba, gaba ɗaya ta hargitse masa falo da hayaƙin shisha. Ƴar dariya yayi tare da kaiwa zaune. Dan yasan dai bata shan komai yau kuma gata da shisha. Lallai ran manyan mata ya ɓaci kenan. Yanda take bulbula hayaƙin sai kawai yaji yana buƙatar kasancewa da ita. Miƙewa yay ya shige ɗakinsa. Babu jimawa ya fito da allura. A kusa da ita ya zauna tare da kama hannunta kawai ya fara mata. Kan shisha ɗin ta wurgar tare da juyowa a fusace. “Oh har ya baka allurar guban da zaka mun ɗin na mutu ne?”.
Murmushi yayi tare da rungumota jikinsa yana magana ƙasa-ƙasa kamar ba commondo ba. “Haba kema kin san bashi da wannan matsayin, ya sani na kashe uwar ƴata da hannuna. Never for ever sai dai shi ya wuce. Cool down na miki allurar nan ne dan ki samu nutsuwa musan miya kamata muyi. Dan na jiyo mana komai akan plan ɗin nasa”.
Jikinta ta janye tana mai sauke ajiyar zuciya. Daga haka barci ya fara rinjayar idonta. Wata shegiyar dariya yayi da ɗaukarta gaba ɗayanta duk da tana da jiki badai can sosai ba yay cikin ɗakinsa da ita. Duk tana jinsa, sai dai bata da ƙarfin hanashi. Daga ƙarshe ma allurar na fara mata aiki a jiki da kanta ta fara kai masa kanta. Haka ya shiga yin yadda yaso da ita. Ya kuma tabbatar daga nan har zuwa gobe allurar zata iya kaiwa jikinta, dan haka daren yau na party ne gaba ɗayansa kawai...

💢🌿💢🌿💢

Matsanancin ciwon cikin dana farka da shi ya sakani fara fisge-fisge. Tuni na fincike ruwan da aka saka min. A dai-dai nan naji wata muryar da nake da tabbacin nasan mai ita tana ma ƴan sandan dake bakin cell ɗin da aka sakanin tsawa. Har rige-rigen buɗe ƙofa suke su shigo. Ciwo yaci ƙarfina bamma tantance maza bane ko mata suka ɗaukan, sai da aka shiga da ni mota na iya kallon mutum ɗaya a cikinsu wadda mace ce. Da ga haka na maida idanuna na lumshe gaba ɗaya.
Sama-sama nake jin kai-kawon komai har isarmu asibiti da taimakon da likitoci suka shiga bani. A ɗan maganarsu nake jin wai ina zubar da jini. Daga haka ban sake fahimtar komai ba sai farkawa nayi na ganni kwance a gadon asibiti police mace a gefen gadon da nake zaune. Sannu tayi min, tare da kiran likita. Ya ɗan dudduba ni ya tabbatar ma da ƴar sandar yana buƙatar ganin mijina ko wani a cikin ahalina. Kai tsaye ta bashi amsa da ina a ƙarƙashin kulawar su ne. Za'a iya sanar musu minene matsalata.
Ɗan jimm likitar tayi kamar mai tunani sai kuma ta ce, “Mijin nawa dai tafi buƙatar gani. In har za'a iya yi mata wannan alfarmar zata so hakan”.
Cikin rashin damuwa jami'ar tace zata duba. Daga haka likitar ta sake fita ni kuma barci ya sake rinjayata. Ban sake farkawa ba sai cikin dare sosai. Na tashi da wata masifaffiyar yunwa. Tun ina juye-juye har na fara kuka da roƙon a bani abinci. Tsaki ƴar sandar tayi cikin masifa take faɗin itafa na takura mata na hanata barci, a ina zata samo min abinci yanzu cikin daren nan. Ban iya amsata ba na cigaba da murƙususu na kawai. Sai kawai ta tashi ta fita rai ɓace. Tun ina saka ran zata dawo harna fidda rai, ga cikina yay wata irin masifar ƙullewar yunwa na cure waje guda ina hawaye. A hankali wani irin daddaɗan ƙamshi ya dinga ratsa min cikin hanci, tun yana a nesa da inda nake har na fara jinsa a gab-gab da ni. Ƙoƙarin buɗe idanuna dake alumshe nayi jin saukar hannun mutum akan jikina. Bana iya ganin ko waye da ƙyau, sai dai a tsaye yana da tsayi, akwai kuma facemask a fuskarsa, gashi ya ɗaura hular rigar jikin nasa a saman kai ta yanda har ba'a iya gane ainahinsa, dan hatta idanunsa akwai glass........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


........Kamani yay gaba ɗaya ya tada zaune, shima ya kai zaunen tare da sakani a jikin nasa ya rungume. Wani kalar nutsuwa ce ta fara ratsani, irin wadda nake ji a tare da mutum ɗaya kacal a duk sanda ya rungume ni irin hakan. (Tabbas bana tantama wannan Maash ne, Awwab ɗina ne). Na faɗa a zuciyata hawaye masu zafin gaske na gangaro min suka sauka a kan ƙirjinsa, sake ƙanƙameni yayi sosai. Munfi mintuna biyu a haka kafin ya ɗagoni ya gyara min zama da ƙyau, wani ɗan mitsitsin flaks ya ciro a jikinsa mai ƙyau sosai ya buɗe. Sai da ya ɗan kalla abinda ke ciki kafin ya kawosa saman lips ɗina, ganin na tsaya kallonsa ya jinjina min kai alamar na sha.. kamar wadda ake bama umarni a hankali na ɗaura nawa hannun akan nashi dake da handglove na gyara zaman flaks ɗin a bakina da ƙyau, ai ko tunda na kafa kai ban janye bakina ba sai da na shanye shayin dake a ciki mai matuƙar daɗi da kauri duka. A take wata irin zufa ta shiga karyo min tako ina a jikina. Sake kwantar da kaina nai a jikin nasa ina sauke numfashi, na jima a hakan kafin na ɗan ɗago ina kallonsa. Hannu na kai a hankali saman fuskarsa zan cire facemask ɗin fuskar tasa ya hana hakan ta hanyar riƙe min hannun yana ɗan jujjuya kansa gefe.
Cikin dasashjiyar muryata na ce, “Why?”.
Maimakon bani amsa kafaɗuna ya kama da hannu biyu ya kwantar dani a gadon tare da jamin bargo ya rufa min. Sai kuma ya min nuni dana rufe ido batare da yayi magana ba har yanzu. Babu musu nayi hakan, kamar abin tsafi sai wani irin barci ya sake yin awon gaba da ni da alama dama yunwar ce ta tada ni....

*_WASHE GARI_*

Yana tsaka da aiki a kitchen kusan shidda na safe kira ya shigo wayarsa. Ringing ɗin da yaji wayar nayi ya nema birkita masa lissafi. Dan ya tabbar ringing ne daya saka shi domin mutum ɗaya. Sai ogansa ma nasa daban. Sai dai kuma mai wannan kiran a daren jiya ya gama jin cewar baya ma ƙasar, shima kuma ya shaida hakan. Da ƙyar ya iya ƙundunbalar ɗaukar wayar ya duba. Tabbas shine kuma da no ɗin Nigeria. To mi hakan ke nufi kuma? Rashin samun amsa ya sashi ɗagawa kafin ta tsinke. Yana kaiwa kunne tare da yin sallama aka katsesa da faɗin, “GGC GARDEN yanzu” daga haka aka yanke wayar ƙittt. Shiru yayi yana mai nazari tare da mamaki. Shi jami'in tsaro ne mai matuƙar fiƙra na sirri. Yasan kaɗan da ga aikin mutanen banza tsara komai. To amma kuma tabbas wannan muryar mai number ɗin ce. Kenan mi hakan ke nufi? Wani ne ya kwaikwayi muryar? Bayan ya samu nasarar samun wayar. Ko kuwa dai su Baba prof sunyi BONONO ne rufe ɗaki da ɓarawo kamar yanda yay zato. Sun shuka ne an tone. Kai shi kam dama dai yayi mamaki ace Maash aka rutsa a Dubai. Duk da hakan zata iya faruwa kasancewar shiri ne babba amma kuma idan za'a haɗa 1+1 ai amsa ɗaya zata bada. Dan shima Maash ɗin shegen kansa ne akwai hatsabibanci... Wayar ya sake ɗagowa ya ƙura ma number ɗin ido, da ga ƙarshe dai ya yanke shawarar fara neman ogan nasa ya sanar masa. Yana ko ɗagawa ya zayyane masa komai. Shi kansa ogan nasa yayi mamaki ƙwarai da gaske da jin wai Maash a Nigeria. Amma sai yace ya dakata bari suyi bincike. Yana nan zaune cikin shirin kira da tafiya ba'a cika mintuna biyu ba kuwa ciff ogan nasa yay kiransa yace yaje Maash ɗin ne dai. Rasama abin faɗa Isma'il Kuku yayi. A ransa kam faɗi yace, (anya Maash ɗin nan kuwa ba aljani bane, anya).....
(😂Nima dai Isma'il na fara tsoron Yayan nan namu gaskiya😝😝).

Koda ya isa GGC GARDEN ƙoƙarin sake kiran Maash ɗin yayi, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Sai ma knocking window ɗin side ɗin da yake akai masa. Sauke gilashin yayi, batare da wanda yay knocking glass ɗin yayi magana ba yay masa nunin ya sakko. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Fitowa yay ya kulle motar yabi bayansa. Duk da akwai ƴar tazara a tsakaninsu bazaka taɓa ma tunanin tare suke tafiya ba. Sai dai a ransa yana mamakin a maimakon su bada umarni matsayinsu na jami'ai sune ake bamawa, lallai ƙarfin dukiya na nuna iko a wannan tafiyar. Can cikin vip na garden ɗin ya kaisa, bai kumayi magana ba anan ma ya juya ya fita. Wajen yayi ƙyau sosai, ga haske tako ina kamar rana. Idanu ya ɗan zubama bayan wanda ke tsaye ya juya ma ƙofar shigowar baya. Baƙaƙen kaya ne a jikinsa hatta da hannunsa dake zube a cikin aljihun wando da alamun handglove a tare da su. Hakama kansa yaja hular rigar. Sallama ya sake yi a karo na biyu, zuciyarsa na masa ɗari-ɗarin Maash ɗin ne ko kuwa ba shi ɗin bane. Shiru har fin minti ɗaya kafin ya juyo. A hakan ma fuskar a rufe take da facemask ga gilashi ga hular ta taimaka wajen hana ganin fuskarsa da ƙyau, batare da yayi magana ba ya nuna masa wajen zama shima yana kaiwa zaune. Hannayensa ya harɗe a ƙirji ya zubama Isma'il ɗin ido na tsawon sakanni. Kafin a hankali cikin silent voice ɗin san nan ya furta, “Gaba ɗaya wasan ya canja a gaɓar da banyi zaton fara yaƙin ƙarshen ba.”
A karo na farko Isma'il ya saki murmushi, dan tabbas yanzu ya sake yarda da Maash yake magana. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, tare da faɗin, “Ranka ya daɗe wlhy gaba ɗaya zuciyata a ɗari-ɗari take, na kasa gaskata kai ɗin ne ko waninka.”
Hannayensa ya warware da ga ƙirjinsa, tare da kai yatsu biyu saman fuskarsa ya zame mask ɗin zuwa ƙasan haɓarsa. A daƙilallen yanayi ya furta, “Ina Ummie na da Mama da ƙanwata?”.
Mamaki ne ya ɗan kama Isma'il amma sai yay niyyar latsashi. Cikin ɗan nuna firgita ya ce, “Ranka ya daɗe ban gane ba?”.
Shiru yay kamar bazaice komai ba kansa a duƙe, kusan mintuna biyu sannan ya ɗago yana kallonsa. Duk da idanun sakaye suke a cikin gilashi sai da Isma'il

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login