Showing 144001 words to 147000 words out of 438336 words

Chapter 49 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2220

da ƙawayenta. Zabura tayi hankalinta a tashe zata fice a ɗakin dan dama kwalliya ake mata ƙawayen nata suka dakatar da ita. Sune suka tausheta kan ta dakata dai Abban ya shigo taji mike faruwa a bakinsa kamar zaifi. Badan taso hakan ba ta dakata sai dai ta shiga dokama Abba kira ta waya dan rabonsa da gidan tun da safe. Shiru bai ɗauka ba har kusan kira biyar, sai da wata ƙawar tata dai ta fargar da ita lokacin salla ne maybe yana massalaci sannan ta dakata. Bayan kamar mintuna biyar dan ita ko sallar ma bata nema yi ba, dama can ba damunta tai ɗin ba balle yanzu da aka zuba kwalliya. Bugu ɗaya kuwa Abba ya ɗauka, sai dai tana fara magana ya dakatar da ita da cewar gashi nan tafe gidan. Wayar ta cillar tana kaiwa zaune wutar bala'i na cin zuciyarta. Ko mintina ashirin kuwa ba'a cika ba su Abba suka iso. Tsaiwar motoci da jin buɗe-buɗe ya saka zuciyar Mom harbawa da masifar ƙarfi. Hakama ƙawayenta gaba ɗaya sukai tsitt da surutun da sukeyi dan tabbatar da inda ghuɗa ke fitowa....

💞✨💞✨💞

Muna fitowa mukaci karo da mama Balki. Ita ta bama umarnin rakani sashen ita kuma tayi gaba. Gani nayi Mama Balki ta sauke ajiyar zuciya. Kamar ba itace duk na ga cikin damuwa ba yanzu. Har ƙofar da zata sadani da sashen nasa dake ta cikin main perlor ta nuna min. Nai mata godiya na shige kaina tsaye dan naji farin cikin sakani wannan aiki da akayi. Hanyace mai ɗan tsayi daga main perlor ɗin kafin akai ainahin sashensa. Tun daga cikin dogon corridor ɗin zaka iya shaida mayataccen ƙamshin turarensa da baya ɓoyuwa a duk inda yake. Baki na taɓe tare da yamutse fuskar takaici. Dan ni kaɗai nasan kalar rashin mutuncin da yau zan zazzage masa tunda na samu damar ganinsa matsoraci kawai, ba ruwana da rashin lafiyarsa ba raga masa zan ba. A rufe ƙofar da zata sadaka da sashen nasa take. Dan haka na danna bell da ɗan ƙarfi ina hararar ƙofar. Shiru babu alamar za'a buɗe min har cikar minti ɗaya. Sake dannawa nayi nan ma shiru, na bada wasu sakanni babu dai alamar za'a buɗe ɗin. Cikin fusata na danna bell ɗin da ƙarfin tsiya batare da na ɗaga yatsana a kai ba harda su cije baki. Sai gashi kuwa an buɗe ƙofar kamar a fusace. Baki na taɓe da ɗaga ido dan ganin wanene ya buɗe ɗin, sai a cikin mayun cat eyes ɗinsa kuwa. Yanda yay wani masifar yin kicin-kicin da fuska gashi ya tsatstsareni da idanu ya sani sake tamke tawa nima ina laɓe baki. Ɗauke nasa yayi tare da juyawa ya bar wajen. Da kallo kawai na bisa cikin yanayin harara. Sosai ya zube a tsaye cikin ƙanƙanin lokaci, sai dai a zahirance bazaka taɓa ma yarda baida lafiya ba dan yana nan a dakensa. Kamar bazanbi bayansa ba sai kuma dai nabi shawarar da zuciyata ta bani, dan haka na sunkuya na ɗauki basket ɗin nabi bayan nasa ina kwaikwayon yanda yake tafiya. Ina saka ƙafata a katafaren falon da ya haɗu ya gama haɗuwa shegen karen nan nasa dana taɓa gani a Kano ya taso a zabure. Ai bamma san na fasa ƙara da ƙoƙarin sakin tray ɗin ba. Sai dai jin ban faɗi ba ni da tray ɗin ya sani buɗe idanun nawa a hankali ina mai sauke ajiyar zuciya. Kallon cikin ido mukaima juna. Ban san lokacin da numfashina ya fisga ba alamar neman barin ƙirjina da gangar jikina, da ƙyar na fisgoshi na maidoshi cikin ƙirjina ina sake waro idanun nawa waje gaba ɗaya. Shima sake tsatstsareni yay da nasa tamkar zai cinyeni da su duk yanda naso haɗiye razanata ta ganin karen nasa tsaye a kusa damu na kasa hakan. Illahirin jikina da duk wata gaɓa da jini ke gudana ta cikinta sun bar aiki.
“K! Baki gajiya da pretending ɗin faɗuwa dan a tare ki”. Ya faɗa a daƙile cike da rainin wayo.
Har cikin tsakkiyar kaina naji haushin furucin nasa. Da sauri na sakesa gaba ɗaya tare da ƙoƙarin turashi nima nai baya. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar bai fahimci abinda na jima haushin ba. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin yayi maganar ne dan raha. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga mamakin mutumin nan da rashin mutuncinsa ga shegen sonma mutane sheri. Kamar ko yasan mi nake tunani akan nasa ya raɓani ya wuce yana mai kiran sunan shegen karen nasa acan ƙasan maƙoshi. Da gudu kuwa ya bisa yana wani kaɗa bindi. Da harara ba rakasu su duka tare da ajiye basket ɗin hannun nawa ina bin falon da kallo. Dan babu ƙarya ya haɗu iya haɗuwa. Karaf kuwa sai idanuna suka sauka akan wayoyinsa dake a saman Centre table ɗin har uku, sai laptop a gefensu. A take wani tunani yazo min. Cike da rawar jiki da zumuɗi na ɗauka ina addu'ar ALLAH yasa babu password. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da shiga loda number ɗin Mansoor. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba. Kamar zan sake kira sai kuma na fasa na saka ta Yaya Musaddiq.
“Mr M” ya fito ɓaro-ɓaro. Da mamaki nake kallon sunan da sake duba numbers ɗin. Number ɗin Yaya Musaddiq ɗin ce dai. To miya kawota cikin wayar wannan mutumin? Bani da mai bani amsa, dan haka nai dialing kawai dan tabbatar wa. Bugu biyu kuwa aka ɗaga, na ɗan yi shiru. Sai ko ga muryar Yaya Musaddiq tar-tar yana sallama. Sai dai muryar tasa a ɗashe alamar barci ya tashi ko yake son yi. Maimakon amsa sai hawaye suka cika min ido. Muryata na rawa na furta, “Yaya!”.
Ina jin alamar yanda ya zabura. Sai kuma cikin rawar harshe ya furta, “Samraah ke ce?”.
Kuka na sakar masa kawai maimakon amsawa. Sai naji duk ya sake rikicewa. Kukan na sake fashe masa da shi da faɗin, “Yaya anya kana sona har yanzu kuwa?. Tsahon wata guda mutumin nan ya sace ni ya sace min Mansoor ɗina amma babu ku babu labarin ku. Yaya ina Mansoor ɗina kada ya halakar min da shi.....”
Cikin wata irin sautin sauke ajiyar zuciya Yaya Musaddiq ya tari numfashina. “Samraah relax. Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya ɗauki Mansoor yana gidansu. Shi kuma wannan ɗin shine mijinki yanzu ba Mansoor ba. Yayanki kuma na sonki har gobe da jibi da gatan gata ma”.
“Yaya!!!”.
Na faɗa a matuƙar razane jikina na rawa, dan duk da shi ɗin ya sanar min shi mijina ne jin tabbaci a bakin Yaya Musaddiq ɗin sai ya sake sakani a matsanancin ruɗani. Sake tareni yay da faɗin, “Nace ki kwantar da hankalinki dan ALLAH Samraah. Yanzu yaya jikin naki kuma?”.
“Yaya taya kake son na kwantar da hankalina? Ta yaya kake son kaji naji sauƙi? Bayan an ɗaura min aure da Mansoor na ganni kuma tare da wani ace na kwantar da hankakina”.
“Samraah dama ba'a ɗaura miki aure da Mansoor ba. Da shi ɗin dai wannan mai suna Muhammad aka ɗaura miki aure. A yanzu kuma shine mijinki. Ki manta da Mansoor da duk abinda ya shafesa dan ALLAH ki fuskanci sabuwar rayuwarki da in sha ALLAHU muna fatan bazamuyi nadamar kaiki cikinta ba. Haba Samraah kefa mai ilimice. Har kin manta da wannan rayuwar izayar ta gidan Abba da kika sha ne?”.
Baki na buɗe zanyi magana hawaye na rige-rigen sakko min kawai naji an zare wayar. Gaba ɗayana na juyo, dai-dai yana yanke kiran da jefa wayar cikin aljihun wandonsa. Afusace nake kallonsa, shima ɗin kallona yake tsakiyar ido. Tsahon minti ɗaya muna a haka batare da ɗayanmu yayi yunƙurin janye nasa ba wayar daya ƙwace a hannun nawa kira ya shigo cikinta. Nasa idanun ya janye tare da zaro wayar daga aljihun daya sakata, ya ɗan tsira mata idanu na sakani kafin naga ya kaita kunnensa tare da barin wajen ya nema kujera ya zauna. Da farko ban fahimci dawa yake wayar ba, sai da ya ɗago ya kalleni cikin yanayin ɗage gira da amsar da naji ya bada sannan. Da sauri na nufesa, babu zato yaji na zare wayar nima kamar yanda yay min. Kafin yay wani yunƙuri na nufi ƙofar dana shigo da gudu. Sai da naje jikinta sannan na juyo na masa gwalo nai ficewata.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_

______________

Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah

Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975

___________

.......Ba Mom kawai ba hatta ƙawayen nata sumar tsaye duk sukayi. Sai da suka sake jinfa tabbas a cikin gidanne sannan suka fara rige-rigen fitowa. Tamkar Mom zata tashi sama tai dirar mikiya a gaban wanda ke riƙe da amarya Halime. Cikin huci da fara birkicewa ta furta, “Kai lafiya? Daga ina haka? Su wanene ku?”.
Murmushi Hajiya Asabe uwargidan mai anguwa ta saki. Cikin dattako da cikar kamala ta bata amsa da, “Baƙi ne na alkairi da ga jihar Katsinan dikko ɗakin kara, kunya garemu tsoro babu”.
Duk da har cikin rai Mom taji shakkar matar, dan duk da mazauniyar ƙauye ce irin matan nan ne da aji a cikin jikinsu yake. Duk da dama can ita ba haihuwa da girman ƴan tumakin bace aurene ya kaita ƴar asalin cikin birnin Katsina ce. “Ke matsayinku ya dama, ni ba wannan ne matsalata ba. Wannan abar da aka lulluɓo nake son sanin matsayinta da dalilin shigowarku gidana”. Tai maganar tana nuna Halime da ke lulluɓe lafe a jikin Innarta Suwaiba. Duk abinda Mom ɗin keyi kuma tana jinta. Dan murmushi ma take yi ta cikin gyalen.
Kai tsaye Hajiya Asabe ta sake bama Mom ɗin amsa da, “Wannan ba huruminmu bane ba, inaga mijinki ne ya cancanci baki amsar kamar”. Daga haka ta sake jan hannun Halime zasu wuce. Idon Mom ya fara rufewa kuwa. Tana shirin sake magana Gwaggo Gudidi ta iso wajen, dama tana sallane shiyyasa bata fito a ƴan tarbar amaryar ba. Ko kallon inda Mom take batai ba ta shiga yima baƙi lalale marhaban, tare da isa inda Halime take ta kama hannunta tana faɗin, “Sannu da zuwa ɗiyata sannu kinji ƴar albarka”.
Yunƙurawa Mom ta sake yi a fusace zatayi magana wata maƙociyarta ta riƙeta. Cikin raɗa-raɗa ta ce, “Maman Baby kwantar da hankalinki, inagafa mutanen nan so suke kawai suyi yawo da hankalinki. Anya ba matar ɗanku bace Musaddiq”.
Da dauri Mom ta dubeta da idanunta da sukai jazur, cikin ɓacin rai da tashin hankalin daya gagara ɓoyuwa gareta ta ce, “Maman Nana Musaddiq kuma? Shine dan Musaddiq zaiyi aure sai a munafunceni? Sannan tayaya ma shi Imam zaiyi gangancin kawo min matar Musaddiq mu rayu a gida ɗaya. Kenan ma su ƴaƴana sun rako na wasu ne duniya”.
Ɗan jimm Maman Nana tayi, sai kuma ta jinjina kanta cike da gamsuwa. “To amma Maman Baby idan fa har ba hakan bane to tabbas Abban Abbas ne yayo aure batare da kin sani b....”
Wata muguwar ashariya Mom ta lailayima Maman Nana tare da wanke fuskarta da mari. Tuni hankalin kowa ya fara dawowa kansu. Dan kafin Mom ta sauke hannunta itama Maman Nana ta sauke mata marin. Su kam dangin amarya tuni sun gama shigewa cikin ɗaki da amaryarsu batare da sunbi takan hayaniyar data kaure tsakanin Mom ɗin da Maman Nana ba. Zaburar Mom da nufar sashen amaryar ya saka Gwaggo Gudidi cimmata ta tare ƙofar. Ƙoƙarin tureta Mom keyi cike da raini Aunty Na'ima ta janyeta rai ɓace. “Wai ke Jalilah miyasa baki da isashiyar tarbiyya ne? Ke yanzu sai ki ture Gwaggon kike nufi?”.
“Yo mizai hana nayi hakan, ai ni idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba, nima bazan ji kunyar kado shi ƙasa ba kuwa wlhy.”
“K Jalilah ki shiga hankalinki wlhy dan yanzu ba da bace. Kin kuma san ko ada ɗin ma ana ƙyaleki ne darajar wanda ya kwasoki cikinmu amma badan ana jin tsoronki ba. Hauka kuma dama kin saita kanki kafin ɗan sauran mutuncinki daya rage ya ƙarasa zubewa. Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys”.
Cak numfashin Mom ya tsaya tare da harbawar zuciyarta. (Dan amarya dai ce Yaya Imam yayi babu yanda kika iya da ita zama daram anan gidan da izinin UBANGIJI. Sai dai ke ki fita ki barta kuwa dan nan da wata tara ma in sha ALLAH muna nan muna bikin sunan babys) kalaman suka shiga maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarta cikin amsa kuwwa. A hankali ta ɗago tana kallon Aunty Ni'ima, sai kawai idanunta suka sauka akan Abba daya shigo. Rawa jikinta ya farayi, cikin ɗimuwa da sassarfa ta nufesa. Cak ya tsaya yana kallonta harta ƙaraso inda yaken. Yanda ta cakumo hannunsa zai tabbatar maka da bata a cikin hayyacinta, dan harshenta har sarƙewa yake wajen faɗin, “Abban Abbas wacece wannan aka kawo min gida? Matar wacece? Dan ALLAH kace min Abbas kaima aure”.
A hankali ya girgiza mata kansa tare da riƙo hannunta. “Jalilah Please relax mana..”
“Naƙi nayi relax ɗin Imamu ka faɗa min wacece ita?”.
“Zan faɗa miki amma ki muje daga ciki”.
“Wlhy babu inda zanje sai ka faɗa min anan. Kuma kaima ɗin baka isa kabar wajen nan ba....”
Gwaggo Gudidi ce ta ƙaraso wajen. Idonta akan Abba ta ce, “Miye kake wani zazzame mata Imamu, ka fito fili ka faɗa matan tunda ita ta nema da kanta. Ai shiyyasa ake son mace ta zama matar ƙwarai kodan irin wannan ranar. Idan ka zama ɗan arziƙi mai tarbiyya taya har miji zai ɗakko maka abokiyar zama batare da saninka ba. Ai dama halinka sabulun wankanka. Mata dai taka ce muma duk mun shaida. Hargowarta ko shirmenta bai isa sakawa a goge hakan ba. Dan in har kai gigin sakin wannan baiwar ALLAHr daka auro koda bayan raina ne wlhy kaf mu ahalinka bazamu yafe maka ba. Ballema nasan bazaka fara kwatanta hakan ba dan kaima kana ƙaunar matarka. Dan haka ka fito ka sanar mata aure ka ƙara dan bazaka cigaba da zama daga kai sai ita a cikin gida ba ta kasheka watarana kamar yanda ta rabaka da duk danginka damu iyayenk.....”
Babu wanda ya san ta yanda akai kawai hannun Mom aka gani a wuyan Abba ta cakumosa. So take tayi magana amma hakan ya gagara saboda numfashinta ma fisga yake. A mamakin kowa sai gani sukai tayi baya gaba ɗayanta alamar suma. Ƙasa take neman zubewa sai da Abban ya riƙota.....

🌜🥱🌛

Tunda tabar falon bai iya ya motsa daga inda yake zaune ba. Sai ma tsurama ƙofar da tabi idanunsa yay tamkar tana a wajen har yanzu. Yana nan zaune kusan mintuna goma shigowar Hayatu ta katse tunanin nasa. Koda Hayatun ya gaisheshi ma hannu kawai ya ɗaga masa. Shi dai Hayatu ya riga ya saba shiyyasa bai damu ba. Sai ma kaiwa da yay zaune bayan yaje gabansa ya ajiye takardun dake a hannunsa dan yau shi bai fita office ba sakamakon yini da sukai akan Hajiya Babba da likitocinta, tare da tsaftar sashenta aka fidda duk kayan da Samraah ta tattara dama sauran duk na sashen aka canja mata katifa kafin a kawo wasu. Shiyyasa Hayatun ya kawo masa duk wani document mai muhimmanci da zai duba ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login