Showing 3001 words to 6000 words out of 438336 words
Mansoor sun kammala karatunsu, sai dai kuma muna nane da juna ta waya. Yana kuma zuwa gida duk da ban taɓa yarda kowa yasan da batunsa ba bayan Yaya Musaddiq. Koda yake su Baby sun sani, dan nasha jin ma wai ai Baby ta jima tana son shi, sai dai bansan minene ya faru koya katangeta da sanarwa a gida ina soyayya da wani ba, sannan ita bata taɓa tarata da batun Mansoor ba kai tsaye, sai dai tai habaici a wasu lokutan ko shaguɓe, ni kuma sai ban taɓa kulata ba ko nuna na fahimta. Ina zangon ƙarshe na kammala karatuna na fahimci ashe Yaya Musaddiq shike biyamin kuɗin makaranta babu wani scholarship dama. Ya haɗa baki da malamin namune kawai, dan a yanzu haka shima Hafizzullah yana a level 100 a jami'ar Umaru Musa ƴar-aduwa dake Katsina. Shima kuma dai da batun scholarship ɗin nan aka rufe bakunan su Uncle Imam duk da an kwashi tashin hankali sosai fiye da nawa lokacin kasancewar shi Nabil bai samu ya tafi ba har yanzu. Ranar da nasan wannan sirrin nasha kuka a gaban Yaya Musaddiq. Shiko ya dinga lallashina yana murmushi, a ranar ya sanar min da komai bai ɓoye min ba. Dan yace bazai taɓa iya zama bamuyi karatu ba, dan haka ya zaɓi bi ta wannan hanyar domin gina gobenmu. Shiko aikin kanikancinsa ya ishesa in sha ALLAHU. Na nuna masa ban yarda ba, shima dole ne musam yanda zamuyi ya koma karatu, dan kuwa zuwa yanzu yana samun kuɗi sosai, sai dai duk a hidimar gidanmu da karatunmu suke tafiya, dan har yanzu bai tsinanama kansa komai na rayuwa ba irin burin matasa na son gina gida da sauransu, hatta budurwa ma baida ita shi sam. Ya min alƙawarin idan lokacin komawar yayi zai koma in sha ALLAHU.
Alhmdllh na kammala karatu cikin nasara, yayinda na riga Abbas da Baby da suka rigani farawa kammalawa saboda su sun saka wasa a karatun nasu. Bakuma su da niyyar gama school ɗin da alama, maybe sai an korosu su shiga hankalinsu oho, dan gasu nan koda yaushe cikin maimaita shekara suke. Bayan kammala karatuna da wasu watanni Mansoor yay uwa yay maɗaukiya ya sama min aiki a wani gidan tv da rediyo dake tashe a wannan lokacin. Hakan ya saka Yaya Musaddiq farin ciki, yayinda ran su Abba yay baƙi har suka kasa ɓoye hassadarsu a fili musamman ma Mom, dan da farko ma tuburewa tai akan tunda na gama karatu aure kawai ya kamata Abba yay min, wai akwai wani ɗan yayarta ya jima da cewa yana so na. Abba har ya ɗauki zancenta da muhimmanci niko na tibire nace wlhy idan aka aura min shi kashesa zanyi, dan ni ban shirya aure ba sai na fara aiki na. Ganin fa da gaske nake kuma sun san tsurin idona dan randa yaron yazo hira wajena zagin ƙare dangi na masa, hakan yasa Abba ya kashe maganar, sai dai ban san yaya sukai da matar tashi ba a ɓoye, a zahiri dai yace ya kashe wannan batu naje nai aiki na. Amma ya bani nan da ƙarshen shekarar nan na kawo miji. Oho ban wani damu dasu ba na fara aiki na, dan nasan dai inada Mansoor ɗina a hannu. Cikin nasara kafin kace mi na samu karɓuwa, albashina na farko dana biyu dana uku na haɗa da shi na sayama Yaya Musaddiq fili da taimakon Mansoor. Lokacin dana damƙa masa takardun sai kawai ya fashe da kuka. Nima kukan na fashe da shi tare riƙe hannunsa ina roƙonsa dan ALLAH ya daina, shifa uba ne a garemu yanzu, idan bamu masa hidima da abinda ALLAH ya azurtamu da shi ba wa zamuyimawa. Da ƙyar dai mukai shiru dan dama a wajen aikinsa na samesa, gudun kada na bashi a gida wani yaji a ƙwace. Tom Alhmdllh, yanzu dai a taƙaice watanni na shida kenan da fara aiki na, ina kuma matuƙar jin daɗin da nuna kwazo matuƙa. Dan bada ƙwaƙwalwa kawai nake aikin nan ba, harda zuciyata da ƙwanjina gaba ɗaya. Gashi ALLAH ya bani farin jinin mutane, dan tunda na fara gabatar da wani shiri akan matasa shikenan kamar nayi kiranyen masoya, dan da a iya rediyo ne kawai, amma wata guda kenan da fara gabatar da shi a television saboda yanda oganmu yaga shirin ya amsu yana sake jawo hankalin mutane ga channel ɗin tamu sai abin yay matuƙar birgesa. Dan haka aka sake ƙarfafa shirin ta hanyar fiddoshi a fanninmu na television ma, Alhmdllh kuma komai na tafiya fiye ma da yanda akai zato da tsammaninsa.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒐𝒖𝒓_
______________
💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫
*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327
*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Hadin amarya budurwa ko zawara*
*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*
*Maijego package (virgin gain)* 📦
*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*
*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*
*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*
*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*
*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*
*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*
*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327
*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace*
*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura*
http://wa.me/+2347069711327
*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*
_________________
......A gurguje nake faman shiryawa saboda makarar da naso nayi. Ba kuma komai ya jawo min hakan ba sai sharaɗin girka breakfast ga masu gidan a kullum kafin na fita bisa umarnin Mom bayan gyara ko ina. Ban isa nace bazanyi ba, dan na fahimci hanyar da zata tuzguɗe ɗan aikin nawa take nema. Dan haka na tsarama kaina time table ta yanda bazan cutu ba. Kullum ƙarfe huɗu na asuba na tashi, zan shiga kitchen na ɗaura breakfast. Inayi ina ɗan wasu aikin gyara gidan har na kammala, dana gama na maida hankali ga sauran ayyukan, ALLAH na taimakona kafin ai kiran sallar farko zaka samu na kammala komai, da Yaya Musaddiq ya fahimta ma sai ya zam shima yana tasowa muyi tare dandanan saina kammala nai shiri. To yau an samu akasi ne da alama Yaya ya makara, dan har na kammala bai shigoba, gashi ma har na gama shirina. Nayi ƙyau sosai cikin baƙar abayar dana saka, nai rolling veil ɗin ta da ya sake fiddoni tsamm kamar wata ɗiyar larabawa. A ɓangaren ƙyawun fuska dana jiki babu abinda zance sai Alhmdllh, sai dai ban taɓa jin alfahari ko son yin ɗagawa da wannan baiwar da ALLAH yay min ba. Nakan gode masa ta hanyar suturta kaina da ƙyaƙyƙyawar shiga, dan kullum cikin dogon hijjabi nake da nose mask. Dan ƙaryane kace ka ganni babu nose mask a fuska. A lokacin dazan fara gabatar da shirin nan a sashen tv ansha gumurzu dani a ranar farko dan har hawaye saida nayi saboda ciresa, dole dai na haƙura daga ƙarshe ma toshe idona da eyeglasses sannan na iya gabatar da shirin, a hakanma ina jin kaina kamar ba daidai ba.
Kamar kullum mask ɗina na saka, sai dai yau baƙi ne, yay min ƙyau sosai dan ƙyawawan fararen idanuna masu girma da cikar gashi kawai ake iya gani. Cikin takun nutsuwata na fito, ga wani ƙamshi mai sanyi yana tashi a jikina, sai dai bamai ƙarfi bane, dan sai ka kasance a kusa dani sosai zaka iya jinsa yanda ya kamata. Sauri nake, dan haka bana fatan haɗuwa da kowa na gidan. Sai da na leƙo na tabbatar babu kowa a falon sannan na ƙarasa fitowa. Nan ma da sanɗa na fita, inayi ina waigen bayana. Ban sami nutsuwa ba saida na ganni a waje, na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina sakin murmushi, bag ɗita mai zubin school bag na rataya hannunta guda a bayana, ɗakin yaya na fara leƙawa, sai muka kusa cin karo dan shima yana niyyar fitowa ne.
“Kandala ƴar jaridan Yayanta”.
Ya faɗa cikin tsokana yana mun murmushi. Murmushin nima na mayar masa ina ɗan rufe fuskata da tafin hannuna. Sai kuma na janye ina ɗan ɓata fuska da faɗin, “Ai ni fushi ma nake da kai yaya. Na manta nai maka murmushi ma.”
Cikin dariya ya ce, “Oh oh Tom ayi haƙuri Ƴar ficika, nasan laifin Yaya dai rashin shigowa taya aiki, wlhy jiya na matuƙar gajiya ne a gareji, shiyyasa tunda na samu na kwanta ko juyi banyi ba sai kawai naji ana sallame salla. Dan yau ma sai a ɗaki nayi tawa dan abin kunya”.
Dariya na ƙyalƙyale da ita sosai saboda yanda yay da fuska kamar wani ɗan yaro. Sai kuma na kalla agogo da sake kallonsa. A zabure na ce, “Uhm Yaya zan makara. Ni dai taho muje ka saukeni, dan yau a mashin ɗinka zanje office, ina son na baka wani labari a hanya”.
Babu musu yace min muje, saboda karna makara bai shiga gidan ya gaidasu kamar yanda ya saba ba. Ya kuma san sai yasha masifa akan haka ɗin, amma yafi buƙatar farin cikina. Cike da farin ciki muka bar ƙofar gidan tamkar bamu da wata damuwar rayuwa. Maganar da nace masa zamuyi na fara masa. Ba komai bane face batun fara gininsa, dan ina son a fara ya samu yay aure. Bai dai ce dani komai ba face murmushi kawai har muka isa, a ƙofar gate ya ajiyeni. Har lokacin fuskarsa da murmushi ya kalleni. Sai kuma ya ɗan ja fasali da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallona.
“Samraah!”.
Ya kirayi sunana da tsantsar kulawa. Amsa masa nai nima da girmamawa. Numfashi ya sake furzarwa da ɗan duƙar da kansa ƙasa kamar mai nazari, sai kuma ya ɗago yana sake kallona. “Samraah inaga ba batun gini ya kamata muyi ba yanzu. Kamata yay ace mu tattali abinda muke samu domin kayan aurenki. Kin girma Samraah, kin kammala karatunki cikin aminci, ga aiki kin samu cikin sauƙi, kina da Mansoor a hannu, a ganina batun aure ya kamata ace kunyi da shi yanzu kafin ma lokacin da Abba ya baki ya cika. Kin san dai halin Mom basai na faɗa miki ba, wannan shirun da kikaga tayi wlhy bazai zama na alkairi ba. Gara mu fiskanci zahiri. Wannan ƙaramin jikin naki yabar kwasarki ba baya kike komawa ba shekaru ne ke ƙaruwa. mutanen wajene kawai suke miki kallon ƴar ƙarama ganinki ƴar ficit. Ni nawa batun mai sauƙi ne, namiji ne ni, konan da shakara goma bazan tsufa da aure ba ai. Ga Hafizzullah yanzu ya fara karatunsa, kamata yay har sai shima ya kammala koda zan yi batun wani aure, sai nake ganin kamar hakan zai fi, ni dama ba wata budurwa ba a ƙasa”. Ya ƙare maganar da zolaya.
Baki na kumbura cikin ƴar shagwaɓa nace, “Yaya ni duk ban amshi wannan ƙorafin naka ba sam. Kadai bari mu samu lokaci mu zauna mu tattauna. Amma batun bazakai aure ba sai nayi ko Hafiz ya kammala makaranta duk baima taso ba. In dai Dan budurwar ce zan maka, amma bazan bari ka cigaba dama waɗan can mutanen bauta ba. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Wannan lokacin ya wuce muma yanzu munsan kammu”.
Kansa kawai ya girgiza, nasan kuma ba komai ya sakashi yin hakan ba sai ganin yanda na ƙarasa maganar a hasale. A bayyane fushina da zafin mariƙanmu ya gama bayyana. Maimakon yace wani wani sai kawai yaymin nuni da gate alamar naje ciki. Banyi musu ba nai masa sallama na nufi shiga ciki ina kumbura baki da fiki-fiki da idanu najin haushi........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒗𝒆_
______________
💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫🔥💫
*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K'ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K'ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* .http://wa.me/+2347069711327
*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*Hadin amarya budurwa ko zawara*
*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*
*Maijego package (virgin gain)* 📦
*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*
*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*
*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*
*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*
*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*
*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*
*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni'ima sha'awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni'ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni'ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar danna wannan blue rubutun* 👉🏻 http://wa.me/+2347069711327
*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni'ima da jimawa sosai ajikin mace*
*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha'awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha'awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura*
http://wa.me/+2347069711327
*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*
______________
........Ina zama office ɗinmu daya kasance mu biyar ne a ciki Asiya data kasance duk tare muke anan ta shigo da sallama. Ganin takardu a hannunta ya tabbatar min da ba yanzu ne ta shigo ba. Gaisawa mukai farko, kafin ta ɗora da faɗin, “Samraah MD na kiranki kuwa. Ya ce ki maza kuma dan zaiyi baƙi”.
Kaina na jinjina mata batare da nayi magana ba na miƙe ina sake gyara zaman facemask ɗina daya ɗan zamo ta saman hanci. A cikin takuna na nutsuwa da yanga da mutane da yawa ke fassarawa na fito. Duk wanda na gamu da shi nakan ɗaga masa hannu da cewa good morning, wasu sukan ɗan tsokaneni. Sai dai iyakata murmushi kawai dan nifa idan ba kayi dogon zama dani ba bazaka taɓa tunanin inada surutu ba sam. Ban cika yawan magana a ko ina ba sai in nice naga damar hakan. Shiyyasa da yawan mutane