Showing 108001 words to 111000 words out of 438336 words
“Yes nan gaba ma idan aikinta yay ƙyau har ƙyauta ta musamman zaki iya samu. Dan gidan girma za'a kaita dake kanki sai kin san kin zama mai sa'a a wannan gaɓar”.
A take kuwa Madam ta sallama. Babu ɓata lokaci matar tai kiran waya driver ɗinta ya shigo da jakkar da bamu san minene a cikinta ba. Daga ganin yanda yayma Hajiya gaisuwa kasan shima ɗan gida ne. Suma sauran duk sun zaɓi ƴammatan ɗaɗɗaya. Bayan suma an kawo tasu jakar da bata kai ta Alaja girma ba Mama ta umarcemu da mu fito. Ni gaba ɗaya ma sai naji kamar an ƙara ɗaureni da sarƙa. Sannan yanda nake jina ko wuta Hajiya tace na faɗa zan iya hakan. Sabbin kaya Mama ta bamu mu ukun nan wai mu saka. Bayan mun kammala tace muyi sallama da sauran ƴan uwanmu dan zata iya yiwuwa rabuwar kenan, idan iyayen gidanmu sunji daɗin zama damu ba lallai mu sake waiwayen nan ɗin ba. Mu dukanmu tamkar waɗanda ake sarrafawa da remote mukai sallama da su. Sai dai ƙasan zukatanmu mu kaɗai muka san halin da muke a ciki sai UBANGIJINMU. Haka muna ji muna gani aka fiddomu harabar gidan inda hamshaƙan motoci suke har guda uku. A ta farko da tafi kowacce ƙyau da tsaruwa akace na shiga gaba. Yayinda aka buɗema Alaja baya ita kuma ta shiga. Sauran ma duk shiga sukai motocin suka fice.
Haka kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga sakkomin. Duƙar da kaina kawai nayi na cigaba da kukana batare da na bar sautin ya fita ba. Haka kawai nake jin takaicin kaina da sauyawata. Jina nake tamkar bani Samraah Abdul-wahab Gwarzo ba. Gaba ɗaya tamkar an kashemin zuciya da kuzari. Abinda kawai nake ganewa shine bin umarni. Munyi tafiya mai nisa kafin na share hawayena na ɗago. Bansan lokacin dana furta (Masha ALLAH) ba a zuciyata ganin wata irin ginanniyar anguwa da muka shigo. Sam tsarin anguwar baiyi kama da a cikin ƙasata Nigeria ba. Victoria island na gani rubuce a babban symbol. Hakan na nufin sunan anguwar kenan. Tun a farkon shiga street da shima aka rubuta a symbol sai dai banga farkon sunan ba securitys suka tsaidamu. Sai dai ganin Alaja yasa suka bamu damar shigewa alamar dai sun riga sun santa.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒆𝒏_
_______________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah
Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975
____________
.......Su Alaja na ficewa a gidan dasu Samraah Madam tai wani ƙasaitaccen murmushi da cije lips ɗinta. Wayarta ta shiga daddanawa tana tafiya har ta shige ciki. Dai-dai tana kai wayar kunnenta takai cikin kujera. Cikin wani salon gogaggun matan bariki ta shiga jera kirari ma wadda tai kira a maimakon gaisuwa. Bamu ji abinda aka faɗa mata daga can ba. Sai dai yanda ta saki siririyar dariya zai baka tabbacin mai daɗi ne. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗaura da faɗin, “Ina godiya da wannan ƙyauta hajjaju masu Lagos da wajenta. Kai Africa ɗin ma duka taku ce. Na kiraki ne domin wani babban albishir da nai imanin zai faranta miki ranki matuƙa”. Ta ɗan yi jimm alamar saurare. Wani murmushin mai faɗi ta sake saki da cigaba da faɗin, “Godiya nake hajjaju. Dama akwai babbar haja da a yanzu akai cinikinta zuwa gidanku. Na tabbatar irin kalarki ce shiyyasa ma na sayar babu ja'inja bayan na gane daga ina masu sayen suka fito. Na tabbata idan kikaga wannan hajar sai kin sake min sabon biya dan ni kaina buƙatar kuɗi kawai ta sakani sallanawa amma raina ya biya sosai.”
Amsar da Hajiyar ta bata daga can ya sata sake sakin dariya. “Ayyah! Hajjaju Ayya. Ai ku manyanmu ne. Kodan girmamawa ma kauda kai ga abinda ya dace daku. Sai dai kinga kayan dan na tabbatar yanzu suna gab da zuwa gidan naku. Duk da dai tace zata bada as gift ne. Kuna wani shagali ne a gidan naku babu gayyata Hajjaju?”.
Shiru alamar saurare, sai kuma ta tashi zaune da ƙyau tana furta, “Woow fantastic Hajjaju. Ai dolene muzo wannan birthday party kuwa kodan ke. Dan haka sai kin gammu”.
Daga haka sukayi sallama ta yanke wayar tare da ajiyeta gefe tana wata kalar shaƙiyyar dariya. A ranta tana ayyana (lallai yarinyar nan tazo da arziƙi. Ai tun da na ganta nasan mabuɗin arziƙina ce ita, dan zoben da babalawo ya bani yay wani irin haske da bai taɓa yi akan sauran yaran da nasarata ke samowa ba. Sai dai fa nima yawuna ya biya, dan komai yaji a jikin yarinyar nan, ga wani shegen fata kamar na dorinar ruwa. Dan haka sai na ɗanɗana koba yanzu ba) ta saki wata dariya a zahiri. Hakan yay dai-dai da shigowar Janny. Ko kaɗan batai mamakin gani da jin dariyar da Madam ɗin tata keyi ba. Sai ma takowa da tai cike da yauƙi jiki na girgiza ta faɗa mata a jiki......
(Hummm🥱)
💥💥💥💥
*_MAASH MANSION_* Shine rubuce da manyan baƙi da akai da kalar ruwan gold a jikin babban makeken baƙin gate ɗin gidan da ya mamaye kaso mai yawa na street ɗin. Ƙirjina yay wata irin masifar harbawa, ba sai an min bayani ba, hakan na nufin wannan katafaren gini shine gidan su Maash ko gidan Maash. (Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un) to yaya hakan ta faru? Maash ɗin dana sani ne a Lagos ko kuwa wani ne mai irin sunansa?. Bani da mai bani amsa sai jikina dake rawa sosai amma babu wani yinƙuri da zan iya yi. Dan tuni wasu garɗa-garɗan securitys dake tsaren ƙofar sun miƙe, sai da suka gama kallemu ɗaya bayan ɗaya da gaida Alaja cikin girmamawa sannan ɗaya daga cikinsu ya danna remote da ke hannunsa, a hankali gate ɗin ya shiga zuge kansa. A jere motocin uku duk suka shiga makeken compaund ɗin da sam baida iyaka ga mai kallo, kowacce ta tsaya a muhalin da ake son ganinta. Dolene ka shigo wannan gida ka tsarkake sunan UBANGIJI mai rahama mai jinƙai, dan shike samarwa ga wanda ya so a lokacin da yaso. Gini ne daya ginu karkashin mahaukatan maƙudan kuɗaɗe da sam zaka iya rantsuwa da ALLAH ba'a Nigeria kake ba idan kana a cikinsa. Dan a iya compaund kawai da abinda ke zagaye da gidan, da kallon ginin a tsaye ya isa tabbatar maka da naira tayi kuka. Wani irin ɗunƙulallen gini ne mai matuƙar armashi da ƙayatarwa. Ga wasu irin korayen ciyayi da furanni masu azabar ƙamshi da sanyaya gida da ƙawatashi da sukaima ko'ina ado. Ga jibga-jibgan motoci jere a cikin rumfuna kusan biyar a tsare acan nesa sosai, wasu ma rufe suke da tempol. Sosai ma'aikata ne ke kai-kawo, dan dole irin wannan gidan yana da masu kulawa ta kowanne fanni. Driver ne ya fara fita a motar ya buɗema Alaja. Kafin ita kuma tai min nunin na fito. Jikina a matuƙar sanyaye na fito ina mai bin katafaren harabar gidan da kallo. Brain ɗina gaba ɗaya ta gama kwancewa, dan tunanina ya rabu biyu ne tsakanin haɗuwar gidan da sunan dana gani rubuce ɓaro-ɓaro matsayin mamallakin gidan.
“Oya muje”.
Furicin Alaja ya katse min tunani. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki na fara takawa a hankali ina bin bayansu. Drivern ta ne yay saurin buɗe dankareriyar ƙofar mai wani irin zubin ƙyau da ɗaukar hankali da duk mai kallo zai iya tabbatar da an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi. Alaja ce ta fara shiga da sallama, yayinda ni kuma ke biye da ita kamar bindi. Sai sauran abokan tafiyarmu biye damu. Sai dai babu sauran yaran da aka ɗakkomu tare da alama an barsu a mota. A haɗaɗɗen falo dake matsayin main perlor muka fara ratsawa. Komai na cikinsa a tsaftace yake ga ƙamshi da sanyin ac kamar ka ɓingire barci. Sai dai babu kowa a cikinsa ko television ma a kashe yake. Bamu tsaya anan ba, mun shiga falo na biyu daya kasance katafaren gaske. Haɗuwar falon ba'a magana. Dan ya ƙawatu da ƙawatuwa ta musamman. Komai sai ƙyalli da ɗaukar ido yake tamkar ba'a talauci a duniya. Shima dai ƙamshin ke tashi mai nutsuwa, sai ƙafar bene da suka zama mahaɗar sassan gidan guda uku. Gashi ƙaton gaske bana wasa ba, dan duk da set na kujeru kusan biyar da ke cikinsa group-group zama a iya kawo wasu set goma sha biyar duk ya ɗauka batare da wasu sun matsi wasu ba.
Anan kam akwai mutane. A hankali dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 1sitter da laptop a gabanta tana sarrafawa a group na set ɗin kujerun dake farkon shigowa ta ɗago fuskarta ƙawace da murmushi, laptop ɗin da tun shigowarmu ta dakata da sarrafawa ta ture gefe, cikin ƙasaitacciyar muryarta ta furta, “Idanu na ne kemin gizo ko kuwa mafarki nakeyi? Da ganin Auta”.
Dariya Alajah tayi tare da nufarta ta rungumeta. Dai-dai nan wasu ƙyawawan ƴammata uku dake can ɗayan rukunin kujerun suka taso suma a guje suna faɗin, “Oyoyo Aunty Mamah. Juyowa tai ta rungumesu suma cike da kulawa da farin ciki. Sai da suka gama murnarsu suka nutsu kafin su maida hankalinsu garemu. Ni suka fara zubama idanu, kafin su maida ga sauran hajiyoyin fuskokinsu a washe da murmushi suna musu barka da zuwa cikin nuna girmamawa. Ni dai ina daga tsaye gefe dan haka kawai naji shakkar ƙarasawa garesu har sai da Alajah tai kirana tare da nuna min na zauna. Inda ta nuna min ɗin nakai zaune ƙasan carpet. Kaina a ƙasa batare dana kallesu ba na shiga gaishesu. Hajiyarce kawai ta amsa, amma ƴammatan nan ko kallo ban ishesu ba. Musamman ma babbar ciki wani kallon tsana data wurgamin tun farko sai da najisa har a ƙasan raina. Dan haka nima sai banbi takansu ba...
Munyi zama na kusan mintuna talatin a wajen kafin hajiyoyin nan biyu da muke tare da su su miƙe alamar zasu wuce. Hajiya da Alajah ne sukai musu rakkiya. Yayinda ni kuma aka barni nan maƙure waje guda ƴammatan nan na bina da kallon banza. Kusan mintuna biyar sai gasu sun dawo. Basu zauna anan ba, sai umarni da suka bama ƴammatan cewar ai kiran Mama Bilki shugabar masu aikin gidan taje dani sashensu zasu nemeta. Hakan kuwa akayi, dan atake babbar cikin ƴammatan ta ɗaga telephone tai kira, cikin gadara da izza ta isar da saƙon Alajah da tuni sun haye upstairs ta ɗaya daga cikin ƙafar bene ukun data ƙawata makeken falon na alfarma. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsaho ba sai ga wadda nake ƙyautata zaton Mama Bilki tazo. Babbar mace ce sai dai baza'a kirata tsohuwa ba. Abin mamaki kuma jikinta fes kamar bamai aiki ba, amma tabbas zata iya haihuwar kamata. Cikin fara'a da kulawa ta bani umarnin tasowa na bita. Nima sai na miƙe jiki a sanyaye nabi bayanta ina mai sakin ajiyar zuciya. Dan dama zama a tsakiyar shegun yammatan duk ya gundireni. Ina jin wata a cikinsu na sakin tsaki amma sai nan juyoba balle naga wacece.
Tafiya mukai mai tsaho sosai data bani mamaki dan kamar bama a cikin gidan muke ba. Kasancewar bata hanyar da muka shigo dasu Alaja bane yasa ban iya na fahimci komai ba. Sai ma sake zama wata baƙauya nayi dan kalle-kalle nakeyi iya iyawata. Sosai nake sake girmama girma da ƙudira ta UBANGIJI. Dan wannan gida sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba saboda ƙawatuwa da ɓannar dukiya da akai wajen saka masa kayan alatu. Ban sake tabbatar da gidan ƙaton gaske bane sai da muka ɓullo wata hanya data fiddomu wajen ginin tanan ma. Ashe ta gaban girmansa ba komai bane. Ta can baya da ginin apartment na masu aiki yake ɓangaren maza daban na mata daban shine ainahin ƙaton gaske. Dan shi ta can gefe akwai ƙaton garden da ko ba'a faɗa maka ba kasan shi ɗin ne. Sannan daga hannun dama akwai wani ƙaton wajen wasanni na yara da manya. Akwai wajen ƙwallo, wajen..... Kai dama wasu daban da ban gama tantancewa ba dan iya abinda idona ya hango kawai nake sanar miki Bily. Shi kansa sashen masu aikin da muka shiga sai da notikan kaina suka nema kwancewa. Dan tamkar ba na masu aiki ba. Komai fes akwai kuma kayan ƙawar suma duk da basu kai na sashen masu gidan ba ko kusa ko kaɗan. Amma dai duk mai hankali ya kalla yasan an girmamasu an mutuntasu. A tare ƴammata kusan takwas da muka samu a falon zaune suna kallo suka zuba min ido fuskokin wasunsu da fara'a, wasu ko kallo ɗaya sukai min suka ɗauke kawunansu. Sannu wanda suka nuna kulawar su suka shiga yi min, hakan yasa nima na amsa musu da kulawa tare da gaishesu duk da sukansu bazasu wuce sa'anni na ba har ma da waɗan da zan iya girma..........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_
__________
_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
___________
......Wajen zama Mama Bilki da naji sun ambata da Mama ta nuna min, babu musu na zauna. Ta nuna wata dake gab da inda nake tana faɗin, “Sayyada kawo ma baƙuwarmu ruwa da abinci ko”. Cike da fara'a wadda aka kira Sayyada ta amsa tana miƙewa. Wata ƙofa dake a falon can inda ƙaton dining table yake na katako ta nufa, mintina ƙalilan kuwa sai gata da tire madaidaici a hannunta. A gabana ta dire tana murmushi da faɗin, “Sister ga abinci ko.”
“Nagode”.
Na faɗa a hankali nima ina murmushin yaƙe. Wajen zamanta ta koma ta zauna. Yayinda ni kuma na zuba ma abincin ido nai shiru har sai da Mama Balki ta zungureni sannan na kawo numfashi. Abincin ta nuna min alamar naci, na ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin tausasa murya nace, “Mama dan ALLAH zan fara salla tukunna”.
Cike da fara'a tace min, “Lah ai babu komai ɗiyata. Kinga A'i tashi ki rakata ɗakinku sai tayi a can kunga kun samu abokiya kuma kun zama ku uku kamar kowa. Ɗan tsuke fuska wadda aka kira da A'i tayi, sai dai kuma batace komai ba ta miƙe. Nima miƙewar nayi nabi bayanta ɗan lungun da naga ta nufa. Dogon corridor ne mai ɗauke da ƙofifin ɗakuna kusan goma. Hannun dama biyar haggu ma biyar. Babu yabo babu fallasa bayan mun shiga ɗaki na biyu a hannun dama ta nuna min ƙofar