Showing 327001 words to 330000 words out of 438336 words

Chapter 110 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2227

ba dan tana acan sashensu ne tana shiryama Baba abincin da zai kaiwa Malam can masaukinsa. Koda Ummie ta fito salla ta farayi, ta yi karatun Alqur'ani sannan ta zauna cin abincin dan yanzu kam tana cin abinci saboda magungunan na sakata jin yunwa. Tana farawa Fahad da Hafizzullah suka shigo. Cike da farin ciki take kallonsu. Dan har cikin ranta take jin son Hafizzullah. Duk da har yanzu babu wanda ya faɗa mata wanene shi sai take zargin Mama Balki ce ta haifesa saboda tsantsar kamarsa da Falaq. Zama sukai suka sakata tsakkiya. Fahad ya amshi spoon ɗin hannunta ya cigaba da bata abincin, itama saita dinga basu a baki Fahad nata tsiyaya mata surutu akan halin da su Baba prof ke ciki na harbin kunama dan su da sai da sukaje asibiti dubiya ko nace sa ido, shi dai Hafizzullah nashi dariya ne. Sai in anzo gaɓar daya sakosa ko yace koba haka ba? Dan tabbatarma Ummie sannan Hafizzullah ɗin ya bada amsa. A haka Maash ya shigo ta samesu. Sanye yake cikin baƙar jallabiya mai gajeren hannu data masa ƙyau sosai. Idanu duk suka ɗago suna kallonsa, kafin Hafiz ta fara gaishesa. Shima Fahad sai ya gashesa tare da faɗin, “Yaya irin wannan ƙyau haka, kamar kaine ma ke rainon Babyn wlhy”.
Idanu Hafizzullah ya waro sosai akan Fahad, dai-dai Maash na ɗaukar gwangwanin turare akan mirror ya wulwulo masa. Da gudu Fahad ɗin ya miƙe ya fice. Hakan yasa Hafizzullah dake ƙunshe tashi dariya shima miƙewa ya fita da gudu. Ummie ma dariya take yi, cikin dariyar ta ce, “ALLAH ya shiryeka Fahad”.
Fuska Maash ya narke a marairaice ya ce, “ALLAH ya rainani Ummie. Ranar fa ina jinsu wai zaimun yankan rago”.
Dariya Ummie ta sake kwashewa da shi. Dan itama a ranar komai a kan idonta akayi tana leƙensu ta balcony ɗin sashenta batare da su sun lura da ita ba. Sai dai a tunaninta ma shi baya gidan a lokacin tunda bataga ya fito ba sai Samraah. Sosai dariyar Ummien ke sakashi farin ciki. Dan Doctor ya tabbatar masa duk cikin nasarorin samun lafiya ne. Yanda ya zuba mata idanunsa da ɗan ruwan hawaye ta cika yasata miƙewa ta buɗe masa hannayenta alamar yazo gareta. Babu musu kuwa ya iso. Shigewa yay ta rungumesa. Sai kawai ta sakar masa kuka. Daburcewa yay ya ɗago da sauri jikinsa har tsuma yake. Fuskarta cikin tafukan hannunsa muryarsa na ɗan rawa ya ce,
“Ummie miya faru kuma?. Kar kuyi kuka dan ALLAH”.
Murmushi ta saki tana mai kai nata hannun itama ta shafa fuskarsa. “Muhammad ina kukan farin ciki ne barni nayi. ALLAH ya muku albarka kaji. Gaba ɗaya zancen cikin nan na matarka ya wanke dukkan dattin zuciyata. Na godema UBANGIJI da ya bani rahamar samun waraka tare da ƙyautar zuri'a daga tsatsonka. Ka saka a ranka wannan itace ƙyauta mafi girma da kuka fara bani bayan samun warakata.”
Rungumeta ya sake yi shima cike da farin ciki yana mai ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika masa ido. A hankali ya furta, “In sha ALLAHU Ummie zamu cigaba da baki irin wannan ƙyautar har sai kince sun isheki da amincewar UBANGIJIN rahama mai badawa a sanda ya so ga kuma wanda yaso.”
“ALLAH ya tabbatar Muhammad ɗina.”
Daga haka suka zauna. Sai kallonta yake yi yanaji kamar ya haɗiyeta dan tsananin ƙaunar da yake mata a rayuwarsa. Kamar yanda itama take jin matsanancin ƙaunar gudan jinin nata. Muryarta a sanyaye ta ce, “Ya kamata muje muga su Baba asibiti. Amma harbin nan na kunamu ya bani mamaki kamar an tsara musu hakan”.
Kauda kai Maash yayi kamar baiji ba. Sai da ta ce, “Nasan ka jini ai. Na kuma tabbatar a yanzu cewar kai ne”.
“Ummieeee!”. Ya faɗa fuska a narke.
“Ba wani Ummie anan. Miyyasa kayi haka?”.
Murmushi ya ɗan yi da faɗin, “Kai Ummie sa ido ne fa wannan”.
“Nayi saka idon ja'iri”.
Ƙaramin murmushi yayi kawai, sai zuwa can ya ce, “Yanzu ma aka fara, har sauron da suka saka ya cijeki sai na rama miki”.
Salati Ummie ta sanya tana tafa hannaye. “Oni Ummu-Hidaya kai ɗin ne dai kenan Muhammad. Ya ALLAH ka shirya min wannan yaron da ya girma bai san ya girma ba. To ai basu suka saka kunama ta harbemu ba ALLAH dai ya ƙaddara”.
Ƙin cewa komai yayi sai fuskarsa daya tsuke kamar bashi ba. Juyawa yay ya fuskanci Ummien da ƙyau. Cikin dakewar nan ta shi ya ce, “Ummie ina son na san gaskiyar komai a yau?”.
Murmushi tayi mai ƙyatarwa. Tare da kamo hannunsa ta sumbata. “Karka damu My dear zaka sani amma ba yau ba. Kai nake son ka sanar min abinda duk ya faru da ga lokacin dana sake komawa halin haukar nan har zuwa yau? Amma kafin hakan ina son nasan Companyn dana ce ka buɗe a Kano ya fara aiki?”.
Kansa ya jinjina mata..
A hankali ta saki murmushi mai ƙayatarwa tare da lumshe idanunta ta furta, “Alhamdullahi ya Rabba. Muhammad ALLAH yay maka albarka. Hakan na tabbatar min zuwa yanzu kasan ainahin fuskar kowa a wannan family naku”.
“Tabbas Ummie. Dan komai ya fara buɗewa ne daga ranar bikin buɗe Company. Sai dai komawarki a halin ciwo a lokacin ya sake tayar min da hankali. Sai dai koba komai na fara fahimtar daga ina ainahin komai yake, duk da anyi yunƙurin daƙileni da sihiri fiye dana farkon daya raba tsakanina da ke. Aka kuma sake ta'azzara ƙiyayyata da Fahad. Sai kuma ALLAH ya shigo da Samrh rayuwata a lokacin...” tiryan-tiryan ya kwashe komai ya bata labari hatta aurensa da Samraah. Har zuwa wannan rikicin da ya faru na kwana biyun nan. Kuka sosai takeyi kamar yanda Fahad dake laɓe yana saurarensu yake yi shima. Hakama Samraah da ko Fahad bai gani ba kuka take yi. Dama tazo gaida Ummie ne, saɗaf-saɗaf ta koma da baya tunda ALLAH yasa kowa bai ganta ba.
Daga ƙarshe dai shima Fahad ya faɗa ɗakin. Rungume Maash yayi da Ummie yana mai basu haƙuri. Murmushi Maash da gaba ɗaya yanayinsa ya canja yayi yana mai shafa kansa.
“Kai zan bama haƙuri Fahad, dan na maka abubuwa da yawa marasa daɗi, na kasa riƙe amanar Ummie. Na kasa kula da tarbiyyarka. Ban san cinka ba bansan shanka ba balle muhallin da kake rayuwa. Duk da ina son yin hakan a ƙasan raina amma bazan iya ba. Akwai lokacin danai yunƙurin neman inda kake amma hakan ya gagara, sai da nayi jiyyar sati biyu. A randa nai maka mugun dukan daka bar gidan nan sai da nayi kuka naji sanyi a raina. Ka yafe min kaji Kiddo, dan wlhy ni kaina ban san duk taya nayi waɗan nan abubuwan ba sai da Abbah ya fargar da ni shi da Baba (Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain da Baban Hayatu). Amma duk da haka na gagara basu haɗin kan shan maganin da suka tabbatar min in sha ALLAHU suna fatan ya zama waraka a garemu”.
Kuka sosai Fahad ya sake fashewa da shi shi da Ummie. Sosai ya rungume Maash fiye da farko. “Ni Yaya bakamin komai ba. In ma kamin na yafe maka. Dan koda baka yimun da hannunka ba Yaya Hayat na mun komai. Kuma koda zanji haushi yana sanar min da kuɗinka yamun. Wlhy bazan taɓa yafema mutanen nan ba. Kuma ni dan ALLAH ku gaya min waye-da-waye ALLAH sai na musu yankan kifi”.
Dariya Ummie ta sanya, yayinda Maash yay murmushi da dungure masa kai. “Kai bakinka baya gajiya da ambaton yanka mutane?”.
Cike da shagwaɓa Fahad ya ce, “To yaya ai kaima dai jiya kace zaka yanka min”.
Yanzu kam dole sai da Maash ya ɗan dara da faɗin, “ALLAH ya shirya min kai. Ni tadani naje na duba Matata kaji”.
Cike da shaƙiyanci Fahad ya ce, “Uhhm su Yaya fa an zurma da yawa. Ummie ki ƙara godema Aunty Samraah ita babbar ƴar su ce tunda ta kamo babban kifin nan naki a kogi cikin ƙanƙanin lokaci”.
Mi Ummie zatai banda dariya. Maash ya kama kunnen Fahad ya murɗa har sai da yay ƙara sannan ya sakar masa ya fice yana murmushi kawai...

Rungume Ummie Fahad yayi cike da farin ciki ya ce, “Wlhy Ummie da gaske yana bala'in sonta. Kigafa yanzu murmushi baya masa wahala.”
“Kaima saika dage ka samo min wadda zata maka irin wannan kamun kaji Autana”.
“Kwantar da hankalinki ke dai Ummie ai ni biyu ma zanyi rana ɗaya”.
“Biyu fa Auta?”.
“Yes Ummie na, ba gara na more da ƙyau ba”.
“ALLAH ya shiryeka”.
Ta faɗa tana dungure masa kai. Dariya yayi, sai kuma ya marairaice mata wai ta bashi labarin abinda ya faru a bayan dan shi bai taɓa tunanin ciwonta nada alaƙa da wani abu ba. Saboda babu wanda ya taɓa zama ya nuna masa.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚_


......Ƙarfe biyu da rabi na rana bayan jami'an tsaro sun gama bincike-bincikensu suka saki labarin kama Commondo da Madam Jannifer. Tare da samo Paah da aka tabbatar da Commondo ɗin ne yay kidnapping ɗinsa ya kuma kashe drivern sa. Ita kuma Jannifer suna kan bincike domin sanin dalilinta na yunƙurin sake zuwa domin ɗaukar Paah ɗin a daren jiya.
Sakin wannan labari dai-dai da isowar tawagar motocin Maash har bakwai asibitin. Dan gaba ɗayansu suka taho hatta da Falaq mai jego ba'a bari ba. Samraah ma ce yaso hana ta biyosu. Aiko ta saka masu kukan taɓara. Sam baya son ganin damuwa a tattare da ita, dole ya barta ta biyosun amma ya saka TJ yin tuƙi a hankali. A waje wajen motocin suka bar wasu guards ɗin nasa. Wasu kuma suka take masu baya har ciki. Ummie da Mama Balki ne a gaba su Sha'aibu na jagorantarsu. Sai Falaq da Samraah biye da su, Samraah na ɗauke da Baby Awwab. Maash da Hayatu sai Fahad da Hafizzullah na take musu baya. A ƙarshe sauran guards ɗin. Tako ina suka ratsa daga ƴan dubiya har ma'aikata da patients kallonsu sukeyi. Ɗakin da aka kwantar da Baba prof suka shiga. Yana kwance sharkaf, a kallo ɗaya zaka fahimci ya jigata da cizon kunamar nan. Ga wani uban ƙullutu a goshi da alamu suka nuna ya buga kanne a bango maybe waje neman ceton kai. Ƙafafunsa a wawware suke an yafa masa duvet kamar dai babu wando ne ta maganar Lado(🥱🤭😝).

Ummie ce ta fara gaisheshi da masa yaya jiki. Idanu kawai ya zuba mata batare daya iya amsawa ba. Ba kuma dan baya magana ba sai dan bakin nasa ya gaza koda motsi ne, sai kallon tsana da gargaɗi yake mata kamar zai cinyeta da idanun. Murmushi ta sakar masa tamkar bata fahimcesa ba ta ce, “ALLAH ya kiyaye na gaba”.
Sai su Mama da su Samraah suka gaidashi a jimlace. Fahad kam ko kallon inda yake baiyi ba. Maash ma dai da farko bai tanka ba, sai da ya mula dan kansa ya wani taka cike da ƙasaita da izza hannayensa duka a aljihu ya matsa gaban gadon. Zama yay a kujerar gabansa yay crossing ƙafafunsa tare da folding hannayensa a ƙirji ya wani zuba masa cat eyes ɗin nan nashi masu kaifi da kwar jini. Ji kawai baba prof yay wani abu na tsarga masa. Dan gaba ɗaya kamanin Awwab ɗin rikiɗa masa sukai tamkar Ibrahim Alonso.
A daƙilen nan nashi cike da manners ya furta, “Ya kake?”.
(Ya kake?) Baba prof ya maimaita a zuciyarsa, zuciyarsa tasa na masa zogi. Da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya bashi amsa da, “Awwab kasan a gaban wa kake kuwa?”.
Murmushi rainin wayo Maash ɗin ya wani saki. Sai kuma ya kalla haɗaɗɗen agogon hannunsa mai shegen tsada yana ɗan wani laɓe small pinkish lips ɗinsa. Hannun ya sauke yana ɗan juya idanunsa ya maidasu ga Baba prof ɗin. Kansa tsaye ya furta, “Mahaifin Paah ɗina”.
“Mahaifin Paah ɗin ka?”.
Baba prof ɗin ya sake maimaitawa a fili yana wani tsare Maash ɗin da idanunsa. Ta cikin wando kuwa saboda harbi da wajen ya sha baya iya riƙe fitsari sosai yanzu ma sai da ya tsillo. Dan wani banzan kallo Maash ya sake masa yana faɗin,
“Bayan hakan ko akwai wata alaƙar? Oh sorry ashe yaron Grandpa ɗina ne kuma, sorry Mr Adams K/Mashi”.
Tsuuuu!!
Fitsari ya ɗan sake kufcewa Baba prof again. Jikinsa ko har ɗan rawa yake duvet ɗin da aka lulluɓa masa ne kawai ya rufa asiri. Ashe tsugunne bata ƙare ba. Dan Maash na rufe baki Fahad da idanunsa ke kan television ɗin ɗakin ya ce, “What!! Uncle Abdullahi!!”.
Yanda ya ambaci sunan da ɗan zabura yasa hankalin kowa komawa can banda Maash da bai ko motsa ba. Uncle Abdullahi ɗinne kuwa ke bayani matsayin babban ɗan sandan sirri da yaransa suka samu nasarar cafke Commondo da Madam Jannifer a daren jiya. Ta re da tabbatar da sun amso Alhaji El-Mu'azz k/mashi. Babu wanda baiyi mutuwar tsaye ba a ɗakin, wasu ma har murza idanu suke domin son ƙara tabbatarwa. Kasa haƙuri Fahad yay jikinsa na tsuma ya tako gaban Maash da ke zaune baida alamar nuna yasan mike faruwa. Amma kuma kunnesa na jin dukkan bayanin Uncle Abdullahi ɗin. Riƙo hannunsa Fahad yayi murya na karkarwa ya ce, “Kaga fa Uncle Abdullahi wai ɗan sandan sirri. Imagine”.
Karo na farko Maash ɗin ya ɗago. Idanu ya zubama Fahad ɗin, sai kuma ya janye a hankali ya maida ga television ɗin. Fuskar Uncle Abdullahin kawai ya zubama idanu, sai kuma ya saki murmushi tare da lumshe idanunsa ya sake buɗewa akan Fahad. A taƙaice ya furta, “Na gani”.
Ba Fahad ba hatta Ummie sai da ta waro idanunta waje. Mama Balki kam ai baya tai ɗan mamaki sai da Hafizzullah ya ɗan riƙota. Babu zato suka ji an faɗo ƙasa timm. A tare duk suka juya, mi zasu gani Baba prof ya sulmiyo ƙasa dan kiɗima. ALLAH ma ya taimaka jikinsa cikuykuye yake da duvet da anyi abin kunya. Rawa jikinsa yake sosai yana nuna television da yatsansa. Magana yake son furtawa amma ko harafi guda ya gagara fita a bakin nasa. Sai kawai ya zube gaba ɗaya raƙwam alamar suma.
Hayatu ne yay ƙarfin halin kiran doctor, akai kama-kama aka maida Baba prof saman gado. Dole kowa ya fito aka barsa da doctor. Daga nan suka shiga inda aka haɗa su Hajiya Mammah su duka. Sukam da sauƙi dan tunda akai musu alluran kashe dafi ta sauka. Barcin da aka sakasu yine ya jasu har zuwa yanzu. Sai Hajiya ƙarama ce dai ansha wahala. Sun samu suma duk sun ɗimauce da labaran da ake nunawa a television. Ba labaran ne yaja hankalinsu ba ganin Uncle Abdullahi a matsayin ɗan sanda. Sun samu itama dai Hajiya Ƙarama na mazarin jiki. Dan abu biyu ne ya ɗimautata zuwa uku. Ganin an kama Commondo da Madam Jannifer, sai Uncle Abdullahi matsayin ɗan sanda babba kuma na sirri. Ƙarin tashin hankalin ma wai shine ya kama su commondo. Itama dai sai da aka nemo likita kanta. Daga nan ɗakin da aka kwantar da Paah muka fara shiga. Ɗakine na musamman dake zagaye da tsaro na musamman. Barci yake shi kam hankalinsa kwance. Duk da ya rame alamar yasha wahala. Rawa jikin Ummie ya fara. Ta ƙarasa gaban gadon da sassarfa. Tuni ta manta da wanda ke tare da ita batama san ta kai dirƙushe ƙasa ta kamo hannun Paah ɗin ba hawaye masu zafi na rige-rigen sauka mata a kumatu. Karyayyar muryarta na rawa ta furta, “Azz! kaine haka? Ya Arrahaman”. Sai kawai ta saki kuka tana mai rungumesa.
Da baya-baya na koma na fice a ɗakin, dan haka kawai naji tausayin Ummie ya masifar shigata. Karo naci da mutum, dan haka na ɗaga kai da sauri na kalleta ina mai ambaton ban haƙuri gareta. Itama dai-dai ta ɗago zata bani haƙurin. Ban iya na ƙarasa ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login