Showing 312001 words to 315000 words out of 438336 words
da bashi ƙwarin gwiwa. Daga haka suka cigaba da tattaunawa. Bayan sun kammala Commondo ya ɗauki drivern na baba prof ya fita da shi zuwa mota. Shi kuma sai ya miƙe yana mai cigaba da neman number Zain bin Abideen. Ganin bazai samu ba yay kiran airport cewar yana buƙatar ticket ɗin Dubai. Sun tabbatar masa yau jirgi bazai tashi ba sai gobe dan sunada matsalar hazo. Bai damu ba dan a haukarsa yana da isashen time ɗin kaiwa goben zai dai cigaba da neman Zain....
🌟🌟🌟🌟🌟
A ɓangaren Maash kamar yanda ta faɗa bayan sallar la'asar shi da Hayatu da isowarsa ƙasar kenan suka ɗunguma zuwa gidan Isma'il Kuku. Lokaci Ummie na zaune bayanta goye da jinjirin Falaq da Mama taima wanka. Yayinda Falaq ke kwance kanta a cinyar Ummien tanata mata surutu akan Awwab da Fahad Ummie na murmushi kawai dan bata iya doguwar magana. Da ga Maash har Hayatu sumar tsaye sukai. Dan harga ALLAH shifa Maash ba yarda yay da maganar Isma'il ba ɗazun. Duk da yasan kaɗanne daga hukunci UBANGIJI ace Ummien ta samu lafiyar. Duk da dai tun kwanaki ya ɗan so gano wani abu game da ita amma taƙi bashi kowace irin ƙofa. Wani kalar tsuma jikinsa ya farayi jijiyoyin kansa na miƙewa lokacin da take kai hannu saman kan falaq ɗin ta shafa tana Murmushi. Cikin karyayyen harshenta ta ce, “Muhammad ɗina bai canja ba dai”.
Ƴar dariya Falaq ɗin tayi da faɗin, “Tabb Ummie ai Yayana bazai taɓa ya canja ba ALLAH. Kinga yanzu ƴan gidan nan duk tsoronsa suke fa. Shi dai kinga sai ya gadama in kayi magana goma ya amsa maka ɗaya. Baka isa gane ainahinsa b....”
Ta kasa ƙara sawa sakamakon kaiwa ƙasa da Maash yay rijiff........✍️
Zazzaɓi🥶🥶🥶🥶🥶.
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_
......A firgice duk suka juya suka kallesa. Da ga Ummie har Falaq sai da suka ji shock, bare ma Mama Balki dake kitchen tana haɗa musu abinci dan babu wanda yaji motsin shigiwarsu. Jikin Ummie rawa ya fara yi, duk ta daburce, ƙoƙarin kwance Babyn bayanta take da alama so take ta koma yanayinta na da amma Mama Balki ta riƙe hannunta. Kuka ta fashe da shi tana mai girgiza mata kai. Ta ce, “Dan ALLAH Aunty karkiyi haka. Kada kice zaki cigaba da ɓoyema Alhaji ƙarami wannan ni'imar. Ɗan ZAKI ya riga ya girma aunty. Wannan ba Muhammad Awwab ɗin da kika sani bane da zaki iya zama da yanayin wahala domin bashi kariya. Wannan na yanzu ke zai bama kariya da ƙarfin ikon ALLAH”.
Wani irin kuka Ummie ta fashe dai-dai Maash na kai goshinsa ƙasa yay sujidar shukur. Ya jima dirƙushe a hakan shi da Hayatu da tuni ya bisa shima yayi. Yana ɗagowa Hayatu ya faɗa jikinsa ya wani kalar rungumesa yana sakin kuka tamkar ba Hayatu ba. Ca yake “Yayanmu Ummie ta dawo garemu. Ummie ta dawo? Ummie ta dawo Yayanmu. Dan ALLAH kar kuce mafarkin dana saba yi ne”. Sai kuma ya sake ƙanƙamesa kamar yanda shima Maash ɗin ya wani matsesa a jikinsa dan gaba ɗaya ma shi baya a hayyacinsa.
Karan farko Ummie ta share hawayenta tare da sakin Murmushi tana mai miƙewa. Goyon Babyn ta gyara sannan ta nufesu. A hankali ta kamo kan Maash ta rungume, tare da riƙo hannun Hayatu ta sumbata. Sai kawai ta sake fashewa da kuka. Da gudu itama Falaq ta taso ta rungume Ummie. Miya rage, itama kawai sai Mama Balki ta nufosu. Sun jima a haka suna kuka su dukansu. Yayinda idanun Maash suke a rufe har yanzu dan shi babu ɗigon hawaye a cikinsu. Sai dai jijiyoyin kansa sunyi wani kalar masifar tashi dama na illahirin jikinsa kasancewar rigar jikinsa mai ƙaramin hannu ce. Hatta gashinsa duk sun mimmiƙe.
Wani irin sakin Hayatu yayi ya damƙe Ummie ya rungume tare da sakin kuka mai ƙarfin gaske. Abinda Hayatu da Fakaq basu taɓa gani ba kenan tunda suke a rayuwarsu. Gara Mama Balki ita tasan ƙuriciyarsa. Duk da Maash tun yana yaronsa duk abinda kaga yama kuka lallai wannan abu ya kai intaha kuwa. Fashewa suma sukai da kukan Hayatu na kama hannun Falaq suka shige bedroom suka rufo. Itama Mama Balki dake kuka kamar ranta zai fita sai kawai ta wuce kitchen da sassarfa...
Kuka sosai Ummie keyi da Murmushi a lokaci ɗaya tana mai shafa kan Maash dake kwance a kan ƙirjinta. Sai kuma a hankali ta fara raira masa waƙar da take masa lokacin yana ƙarami. Tare da ɗago kansa tana kama kumatunsa duka biyu ta ja. Dariya kuwa ya saki irin wadda da yawan mutanen da suka sanshi zasu iya rantsuwar basu taɓa ganin yayi ba. Itama Ummien dariya ta fara tana dungure masa kai da jan hancinsa sannan ta fara goge masa hawayen da manyan yatsun hannunta biyu. Sai da ta gama taass sannan ta jingina goshinta akan nasa tana murmushi.
“U...m...m...ie”.
Ya kira sunanta a wani irin rarrabe.
Da harɗaɗɗiyar muryarta ta ce, “Na'am Muhammad Awwab ibn Ummu-Hidaya Ibrahim”.
Dariya ya sake yi da rungumeta da ƙyau. Dan sunane da yake kiran kansa da shi yana yaro a duk sanda ya fahimci Paah ya ɓata mata rai. Duk da tana ƙoƙarin ganin basu fahimta ba amma ƙulafucin Awwab sai ya gano. Dan ko yaya ya ga fuskarta ta canja yata bin ƙwaƙwƙwafinta kenan har sai yasan waye ya ɓata mata ran. Idan Paah ne bazai sake masa magana ba. Zai kuma ce sunansa ya koma Muhammad Awwab ibn Ummu-Hidaya Ibrahim...
Sake ƙanƙameta yay da faɗin, “Da gaske ba mafarki nake ba kamar yanda na saba Ummie na?”.
“Ba mafarki kake ba my heartbeat. Ummien ka ce. Itace a gabanka. Kayi haƙuri Muhammad, kayi haƙuri. Nayi komai ne dan ku. Na karɓi komai ne dan ku. Nayi haƙuri da komai dan ku. Duk da bani da tabbacin zaku rayu ko ni na rayu har zuwa wannan lokaci. Amma ina fatan hakan a raina a duk lokacin da hankalina ya dawo jikina kafin magauta su farga su maida ni ruwa. Nayi haƙuri da rasa Abie a dalilin rashin fahimtar gadar zare, amma bazan iya haƙuri da sadaukar da ku ba a lokacin dana banbance baƙi da fari. Muhammad ina Fahad, ina Autana yake. Ina yarinyata take. Dan ALLAH ka kaini naga Fahad da Samraah yanzun nan”.
Da sauri ya ɗago yana kallonta. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Samrh!”.
“Yes dear. Ina son naganta?”.
Kafe Ummie yay zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri. So yake yay magana amma ya kasa. Fahimtar hakan ya sata sakin murmushi. Ta ɗan girgiza masa kanta tana mai kaiwa zaune dan ta gaji da durƙuso akan gwiyawun nata. Da sauri ya kamata ya zaunar da ƙyau, murmushi ta sake sakar masa da kama fuskarsa ta sumbataci goshinsa. Sai kuma ta lakace masa hanci da faɗin, “Kallon fa. Kana mamaki ne?”.
Kasa cemata komai yay sai idanu daya kafeta da shi. Murmushi ta sake yi da faɗin, “Nifa bana son miskilanci”.
Murmushi ya sake mata a hankali yana kai rissinar da idanunsa. Itama sai ta saki murmushin tana mai sauke numfashi.
“Ummie tun yaushe kika warke?”.
“Muhammad kowane labari nada nashi tushe. Kamar yanda gini ke farawa da tushiya, tsirrai ke farawa da mafari. Ɗa a cikin uwa ke farawa da gudan jini. Samraah na cikin mutanen da suka shigo rayuwata a ƙarshen labarina. Amma tana cikin mutane masu muhimmancin da kwatantashi bazai yiwu da baki ba. Ka bar batun su Bilkisu, waɗan nan sunansu JINI NA, kamar yanda kai da Fahad kuke JINI NA. Amma tabbas warkewa ta ta fara ne daga lokacin da Samraah ta shigo rayuwata bisa hukunci da amincin UBANGIJI. Muhammad ka tashi, maza tashi ka kaini ga Mahaifinku da Samraah da Fahad. Ko kaje ka kawo min su na gansu, ina son mu bar ƙasar nan mu duka a yau kafin maƙiya su farga da mu na roƙe ka”....
“Kinfi ƙarfin barin ƙasar nan saboda WAWAYE Ummie. Sai dai su su GUDU su barta, dan a yau zaki kwana a cikin MAASH MANSION ne ma”.
Ya faɗa da wani irin salo mai nuna gwarzantaka da tsantsar bajinta da babu ɗigon tsoro a cikinta.
Kai Ummie ta girgiza masa cikin rauni. “No Muhammad. No. Bazan sake komawa gidan can ba, kasan kuwa su wanene ke cikin gidan nan? Kasan kuwa ƙarfin bushewar zukatansu? Kasan kuwa ƙarfin rashin imaninsu da abinda zasu iya?.”
“Ummie!!! Please. Kar kice na BARI. Dan kansu kawai suka sani, kisa a ranki kawai yanzu ne WASAN ZAI FARAAAAAAAAA!!!!”.
Yanda yay maganar yana bubbuga yatsarsa a ƙasa jijiyoyin jikinsa na wani irin masifar tashi ruɗu-ruɗu abinka da mai buɗaɗɗen jiki, ga idanun gaba ɗaya sun gama birkicewa. Sai da Ummie ta firgita. Wata irin amsa kuwwa Muryar mahaifinta ta shiga mata a cikin kunne. A lokacin da suka je Spain harda Abie kawai sun fita yawo shi da Abie ɗin sai gasu sun dawo wuyan Awwab zane da tattoo ɗin fuskar zaki a gefen wuyarsa da har yanzu shine dai. Da mamaki ta kamashi tana dubawa. Hankalinta ya tashi ta fara masa faɗan waye ya masa Tattoo? Abie yana ina aka masa. Babu shakka ko tsoro ya ce, “Ni naje aka mun Abie ya biya saboda ni ZAKI NE”.
Haushi ya saka Ummie mangaresa. Sannan rai ɓace ta tafi wajan Abie ta kai ƙara duk da yace mata Abie ɗin ne ma ya biya kuɗin Tattoo ɗin. Sai kawai Abie ɗin ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “An masa ne saboda yana so. Dan JIKANA ZAKI NE!!!”. Sai kawai tama rasa abin faɗa a lokacin, dan yanda Abbie ɗin yay magana babu alamar damuwa tattare da shi sai ma ƙarfi da karsashi...
Kuka ta fashe da shi tana mai ƙanƙame Maash ɗin a jikinta ta ce, “Yeess Abie JIKANKA ZAKI NE”.....
😂YAYANMU ZAKI NE muma mun yarda Abbie😌, dangin Kandala ma sun shaida😝😂.
💓✨💓✨💓
10:12pm na dare da abubuwa da yawa ke kan faruwa wanda ya damalmale na kowa ya faru. A ɓangaren su Fahad da Hafizzullah sun farfaɗo tun bayan Magribar da tai dai-dai da isowar Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain Maash Mansion bisa jagorancin Baban Hayatu da kaɗai yasan da zuwansa. Dan haka suka kasance a ƙarƙashin kulawarsa dan kai tsaye sashen Fahad ɗin Baba ya kai Sheikh Muhammad ɗin batare da kowa na gidan ya sani ba sai Shu'aibu da TJ. Hakan ta farune kasancewar ma'aikatan gidan yau jikinsu duk a sanyaye yake. Hajiya ƙarama bata gidan. Hajiya Mama na asibiti wajen Samraah. Hajiya Mammah tana sama tare da aminiyarta Rubayya data kawo mata ziyara suna tattauna cakwakiyar gidan. Wanka Baba ya sakasu sukayi aka basu abinci sukaci Sheikh ya basu ruwan addu'a sannan yay musu tambayoyi akan ina suka je. Amsa ɗaya suka bashi shine su dai sun kwanta barci daga haka suka farka suka gansu a wani waje daban an ɗauresu. Sai wani dake kawo musu abinci sau biyu a rana. A kuma daren shekaran jiya aka zo aka canja musu wajen zama. Sosai baba da Sheikh suka jinjina zancen, dan haka suka buɗe musu komai dake faruwa harda videos ɗin da aka saki akan Maash da Samraah, dana Maash a asibiti. Wani irin rawa jikin Fahad ya fara, kafin cikin kuka ya fara roƙon su kaisa Dubai ya ga Yayansa. Yanda yake ambaton yayan nasa duk a rikice yasa suka fahimci al'amari fa da alama ya dai-daita. Kallon juna Baba da Sheikh sukayi, kafin su zaunar da Fahad suka lallasheshi shi da Hafizzullah dake kuka sannan a nutse suka warware musu ainahin gaskiyar abin duk shiri ne. Sai dai ba'asan inda Maash yake ba yanzu taka maimai. Suka kuma warwarema Fahad alaƙar Maash da Samraah, yayinda Hafizzullah ya ƙara masa bayani dalla-dalla. Ai kawai gani suka Fahad ya miƙe a fusace, suna kiransa ko saurarensu baiyi ba ya nufi ainahin baban sashen. Sai kawai ihunsa da hargaginsa suke jiyowa yana ƙwala kiran sunan jama'ar gidan ɗaya bayan ɗaya. Ƙoƙarin miƙewa Baba yayi Sheikh ya hanashi yana mai girgiza masa kansa yana murmushi. A dai-dai lokacin Hajiya ƙarama da yau ma Commondo yayma fata-fata ta shigo ranta a ɓace. Cak ta tsaya kamar wadda aka dokama guduma a kai. Hakama Hajiya Mammah ta fito daga ita sai ɗaurin ƙirji Hajiya Rubayya biye da ita ta cikuykuye jiki da zanin gado. Dan irin mafaraucin kiran da Fahad kema kowa na gidan ko a bayi kake zaka iya fitowa a guje tsirara batare daka fargaba musamman idan kanada wani tabon laifi tattare da kai. Hatta su Azizat sun fito. Maman Malika ce kawai ta fito a nutsenta tana ƙoƙarin kiran mijinta da Hajiya Mama akan suzo gida fa ga abinda ke faruwa. Hakama Hajiya Mammah jiki na rawa ta koma ɗakinta ta ɗauki waya tai kiran Baba prof.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
.....A dai-dai lokacin Baba prof ke waya da Teacher ɗinsa dake ƙasar Togo sai ga kiran Hajiya Mammah ya shigo a ɗayar wayarsa. Yanzu baya wasa da kiran kowa, dan haka bama ta gama ringing biyu ba ya ɗaga yana kaiwa kunne da ajiye kiran teacher ɗin nasa. Cike da tashi. Hankali Hajiya Mammah tace, “Baba dan ALLAH kazo gida yanzu babu lafiya. Shima Fahad ya ɓalle gashi nan da zandareren takobin nan nashi ya ce wlhy idan bamu fito masa da Awwab ba da Mahaifiyarsu sai ya ma kowa yankan rago yau a gidan nan”. Bata ta jira cewarsa ba ta yanke kiran ƙittt.
Kasare yay yana kallon wayar. Dan yama rasa yanda zai fassara zancen nata ko hasaso wani abu sai jikinsa ne ke rawa. Sai kuma ya tura wayar a aljihu da sassarfa ya fito yana haɗa hanya da ƙwalama driver ɗinsa kira yama manta ya kaishi fagen rabin mutuwa ɗazun. Sai da ɗaya a cikin ma'aikatan gidan ya iso ya sanar masa ai driver tunda suka shiga ciki tare bai fito ba. Kansa ya dafe tare da masa nuni da mota ya ce, “Kaini Maash Mansion”....
Cikin in ina ya ce, “O...ga ai ban iya mo..ta ba”.
Wani firgitaccen tsawa Baba prof ɗin ya masa cikin ƙara ji yace, “Nace ka kainiiiiii!!!”.
Rawa sosai jikin dattijon ya fara dan tsawar ta ratsashi. Dai-dai nan ɗaya daga cikin guards ɗin sa ya iso ya amshi key ɗin motar.....
Suna fita a gidan Isma'il ya saki murmushi, tare da ciro wayarsa ya ɗanna ma Maash kira. Ya ce, “Ranka ya daɗe saƙo ya samesa. Yanzu haka ɗaya daga cikin guards ɗinsa ya tafi kaisa Maash Mansion kuma zaku iya tafi”.
Sai da yay ɗan jimmm alamar saurare sannan ya saki murmushi da faɗin, “Thanks you Sir ina kan aikina ne”. Daga haka ya yanke kiran......
🌿🤍🌿🤍🌿
A hankali Maash dake rungume da Babyn Falaq ya sauke wayar tare da sake rungume jinjirin yana mai kaima goshinsa sumbata. Sai kuma ya juya ya kalla Ummie da tai sabon shirin cikin wani ubansu lass da aka kawo mata mai shegen tsada da ƙyau. Ga gwala-gwalai Falaq ta mata ɗan simple kwalliya da ya sake bayyana ainahinta na UMMU-HIDAYA IBRAHIM ɗin ta. Sai wani uban ƙamshi da take bulbulawa. Gaba ɗaya wannan shirin an ƙirƙiresa ne daga ɗazun bayan sun gama kukan samun lafiyar Ummie sun koma murnar samun sabon Baby da atake Hayatu yace yaba Ummie wuƙa da namar zaɓa masa suna Maash kuma ya masa huɗuba. Babu ko wani kwana-kwana tace MUHAMMAD AWWAB. hakan kuwa akai masa huɗuba da shi kuma Maash ɗin ne yayi duk da baya jin daɗin jikinsa amma ya kasa gaya musu. Bayan ya kammala yace su