Showing 276001 words to 279000 words out of 438336 words
sashenta tsaff. Koda Gwaggo ta kirashi akan ta jisu shiru sai yace mata ai suna gida Halimen zata ɗan ɗakko wasu kaya ne. Har Gwaggo ta yarda, sai kuma zuwa can ta sake kira bayan tayi wani tunani tace Halimen tai zamanta kawai tunda ma ta samu sauƙi. Ba ƙaramin daɗi hakan yayima Abba ba kuwa. Aiko ba kunya ya ɗaga halime sama yana juyi da ita...
Mom bata san wainar da ake toyawa ba, suna can yawan leƙe-leƙensu da Ummanta. Sai dawowa tayi da yamma sosai ta samu part ɗin Halime da hasken fitila. Hankalinta ne yay masifar tashi, dan ta gama zagaye gari da labarin ai Abba ya saki Halime ya korata garinsu. Miye-miye zantuka gasu nan dai barkatai tako ina. Sai kuma ga Halimen ta dawo kamar an jehota daga sama. Shin yaya akai ne haka ta faru, ba malamin nan ya tabbar musu da anyi an gama ba. Haka dai taita ƙullawa da kwancewa ita kaɗai, gashi dare yayi balle ta fita. Ta kira wayar Ummanta bai shiga ba sai daga baya ta tuna bata da caji....
🌜★🌛🌟🌜★🌛
Cikin ƙosawa da zaman shirun da suke tun ɗazun Hajiya ƙarama ta sake kallon Yallaɓai ta gefen ido. Har yanzu dai yana a yanda yake zaune. Sosai takaici ya fara kamata. Ta rasa mi yake tunani haka. Shin maganganun data gaya masa akan abinda ya faru yau a gidan ne komi? Ko kuwa fitar su Awwab data gani yanzu da itama yasa ta kasa zaune ta kasa tsaye sai da ta fito a daren nan. Numfashi da ya furzar tare da ajiyar zuciya yasa ta kallesa da sauri. Sai taga shima ita yake kallo. Murmushin ya sakar mata dake bayyana ainahin wanene shi, dan duk wanda yaga murmushin yasan na baƙin mungunta ne. Dan haka cike da zumuɗi itama ta ce, “Yallaɓai ka samo mana wani abu ne?”.
Kai ya jinjina mata yana ƙara sakin murmushi. Sai kuma ya gyara zamansa da ɗaukar waya yay kira, shiru yay yana sauraren bayanin da akai masa da ga can. Sai da aka gama sannan yay ƴar gyaran murya cikin bada umarni ya furta, “Ina son video ɗinsu da hotuna daga yanzu har sanda zasu baro bakin ruwan.”
“An gama ranka ya daɗe”.
Katse wayar Baba prof yayi, tare da juyawa ya kalla Hajiya ƙarama data tsaresa da idanu. Kafin ma yay magana ta taresa da faɗin, “Amma yallaɓai mi kuma zamuyi da hotonsu ko video? In dama a club ne ko wani wajen daban sai muce munada alamar tambaya a kansu. Amma yanzu minene wani bakin ruwa”.
Ƙaramar dariya ya saki da faɗin, “Ai ke wani lokacin idan kina abu kamar mara wayo. Bari na baki a buɗe. Har yanzu bamu da matsayar sanin alaƙar Awwab da wannan yarinyar. Duk da dai a duk mai hankali zai iya bama alaƙar suna da abinda muketa ƙoƙarin ƙin yarda ko ɗauka saboda wasu dalilinmu. Idan na ɗauki kalmar yarinyar tayi aure, na haɗa da Awwab ya mata fyaɗe amma ko damuwar hakan babu a tare da shi duk da kasancewarsa mutum mai kiyayewa, a mahanga ta hankali mi zai iya baki?”.
Ɗan jimmm Hajiya ƙarama tayi na tunani, sai kuma kamar wadda aka tsikara ta zaburo tana mai waro idanunta gaba ɗaya waje ta ce, “Mun shiga uku ni Lawusa. Yallaɓai kodai yaron nan yaje ya binciko yarinyar ne dan ya aureta. Anya ba shine ke aurenta ba kuwa? Sai dai ta yaya zai yi aure bada saninku ba sai kace mahaukaci. Yo wama zai masa walicci? Sannan shi ba ɓoyayyen mutum bane, babu yanda za'ai yaje neman aure ba'a gane shi ɗin wanene ba? Kai bama wannan ba, Awwab bazai taɓa yin aure bada sanin ku ba tunda bawai wani abu kuka taɓa masa da zai ji a ransa zai yi hakan ba. Ko Jaga da yaso ɓata mana shirin an kawar da shi”.
“Humm Lawisa Kenan. Nima daga daren shekaran jiya zuwa yinin jiya da daren jiyan zuwa yau, duk nayi irin wannan lissafin naki. Har ina tilasta kaina ƙin gaskatawa dan bana jin akwai wata hujja da Awwab zai iya yin hakan. To amma dai yanzu ina da plan, shiyyasa ma nasa commondo ya samo min hotunan da video ɗin”.
Da mamaki ta ce, “Wane irin plan?”.
Wani makirin murmushi Baba prof ya saki da maida kansa ya jingina da kujeran. Kansa tsaye ya ce, “Ki jira zaki gani ai”.
“Amma nake ga kamar ya kamata ace na sani”.
“Zaki sani, amma ba yanzu ba. Give me just one day”.
“Okay ba laifi, ni bara na tashi na wuce. Kasan gidan namu yanzu baya rabo da labarai. Komi kenan zuwa safiya dai ina saurarenka. Dan dole na taƙaita zuwa gidan ka saboda kar a fara mun wata fassara kuma daban gaskiya. Daga suriki...”
“Hakan nada ƙyau. Idan ma ina son ganinki zaki dinga ganin address ɗin wajen haɗuwa”.
“Okay ba damuwa, na barka lafiya”. Ta faɗa cikin girmamawa har da ɗan rankwafawa.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
.......Sosai nake kallonsa ina ƙara jujjya key ɗin motar, shi ko yana zaune zama irin na ƙasaita ya wani yi crossing ƙafafunsa, tare da folding hannayensa a ƙirji ya zuba min ido kawai shima. Idanun nawa na ɗan rissinar, tare da sake kallon key ɗin sannan cikin ƙarfin hali na ce, “Amma Yaya Awwab motar nan ta mun girma, duk da ban san mota ba, kuma zan iya maka rantsuwar yau na fara ganin irin wannan ɗin ma. Mizai hana ma dai ace ƴar ƙarama haka dai-dai ni”.
Shiru baida alamar cewa komai. Sai ma jingina kansa da yay da jikin kujerar ya wani lumshe idanu. Jinai gaba ɗaya na ƙagara yace wani abu, amma bawan ALLAHn nan baida alamar cewar har kusan mintuna goma. Sai da ya mula dan kansa yana a yanda yake zaune batare daya tashi ba ko buɗe idonsa ya ce, “Samrh”.
Ya kirayi sunan nawa so soft. Nima sai na samu kaina da amsa masan a can ƙasan maƙoshi ina ɗan sauke ajiyar zuciya.
“Kin san wa kika aure kuwa?”.
Kaina na ɗan ɗago na kallesa. Kansa ya jinjina min a hankali tare da cigaba da faɗin, “Idan irin wannan motar kike so guda goma za'a kawo miki. Idan wadda ta fita kike buƙata ko kwana biyu bazasu wuce ba batare da an kawo miki ita ba. Ke ko zana hoton mota kikayi da hannunki, kika ce so kike a miki irinta da sunan ki ki zama ta farko kuma ta ƙarshe mai irinta kisa a ranki an gama kawai.”
Sosai na sauke ajiyar zuciya ina mai lumshe idanuna, da gudu hawayen da suka cika shi suka shiga rige-rigen sakkowa. Sake damƙe key ɗin nayi a cikin hannuna, kafin na miƙe a hankali har zuwa gabansa na durƙusa. Muryata na rawa na ce, “Yaya ban san taya zan fara maka godiya ba, bamma san taya zan musalta maka abinda nake ji a raina ba.......”
Ɗagowa yay a hankali tare da mun alamar zipping akan bakinsa. Gashi ya wani kalar zuba idanunsa a cikin nawa. Tashi tsigar jikina take yi saboda mayataccen kallon da yake min a cikin tsakkiyar idanun sosai nake jin tasirin su. ALLAH ya saka baiwa da tsantsar kwarjini a cikin idanun bawan ALLAHn nan. Kuma kamar yasan da wannan baiwar shiyyasa yake yanda yaso da idanun akan mutane. A hankali ya fara motsa lips ɗinsa ta yanda badan kallonsa nake ba, babu yanda za'ai na fahimci mima yake faɗa, dan sam babu sautin murya sai motsin lips ɗin kawai..
“A farin ciki kawai nake buƙatar ki kasance”. Ya ƙare maganar da salon kashe min ido ɗaya tare da wani kalar jan su shuuuu kamar zai lumshe, sai kuma ya miƙe abinsa. Cikin takun nan nasa dake tabbatar da shi a ingarma kuma jarumin namiji ya ƙarasa can ƙarshen jirgin ta inda zai iya kallon ruwa hannunsa riƙe da glass cup dake ɗauke da non alcoholic wine. Hannunsa ɗaya ya dafe ƙarfen jirgin da shi, ɗayan na riƙe da kofin yana kallon uba-uban ruwan da ya isa ka sake yarda cewar ALLAHn fa ALLAH ne, dan duk da dare ne yanda ruwan ke ƙara da ɗan walƙiya ta gefe gefen da fitilar jirgin ta haska shi ya isa ka ƙara godema UBANGIJI. Sai wani irin kaɗa gashinsa iskar keyi tana maidosa baya. A hankali na sauke ajiyar zuciya da ɗan kauda kaina a kallon nasa. Sai kuma na miƙe nima na nufesa. Duk da ina tsoron kallon ruwan haka kawai zuciyata ke ingizani kan na matsa kusa da shi. Duk da ina da tabbacin yaji motsin isowata wajen bai ko kallan ba. Nima sai ban damu ba, dan zuwa yanzu na fara fahimta da haddace halin kayana. Jikin ƙarfen na jingina. Sai dai na juyama ruwan baya ina facing cikin jirgin ne. Batare dana kallesa ba nima hannayena a ƙirji nayi shiru kawai ina kallon cikin jirgin daki-daki. Nafi minti biyu a wajen kafin ya ɗan juyo kaɗan ya kallan. Duk da naji kaifin idanunsa a kaina ban kallesan ba ni.
“Hummm!” ya faɗa yana mai ɗauke kansa tare da kai kofin lemon nan daya kasa shanyuwa bakinsa. Kaɗan ya sha ya sake janyewa. Duk ta gefen ido nake kallonsa ina mamakin baƙin halinsa. Kasa daurewa nayi, dan sai nake ji a raina kamar haushi yaji, dan haka cikin dakiya da marairaita na ce, “Yaya fushi kayi?”.
Nan ɗin ma kamar bazai tanka ba. Sai da ya mula dan kansa kafin a daƙilen nan nasa kamar wanda ya gaji da magana ya ce, “for what?”.
“Saboda nace mota tamun girma.”
Tsaye ya tashi sosai, sai kuma ya kamo hannuna ya maidoni gabansa sosai. Kallona yake sosai ta yanda har nake jin ni banzan iya kallonsa ba. Dan haka na kasa ɗagowa ina dai tsayen a gabansa kaina a ƙasa. Saukar hannunsa saman haɓata ya sani ɗan ɗagowa, muna haɗa idon na maida nawa na rissinar. Sake ɗago kan nawa yayi da kawo fuskarsa gab da tawan ya haɗe goshinmu waje ɗaya, kaɗan na so buɗe idanun nawa, sai dai da gudu na maida su na rufe saboda jin saukar mincili lips ɗinsa akan nawa. Sam ban san akwai abu a bakinsa ba, sai da naji ya fara juyemun lemon cikin bakina a hankali da wani shegen salo mai tada kan mutum. Ya Arrahaman, guy ɗin nan bala'i ne. Ni dai kodan irin wannan rayuwar baƙuwace yanzu gareni shiyyasa nake jin duk wannan oho. Abinda kawai na fahimta nima banda juriya, ja'irar kaina ce, in har yay knocking sai na buɗe masa ƙofar batare dama nasan mi nake ba. Maybe wasu su kalla hakan gazawa, sai dai ni a karan kaina nasan ba hakan bane. Ɓoyayyen sirrin dake a raina ne ke kasa cigaba da bizne kansa. Maash ya cancanci a soshi, sai dai kawai ka basar saboda tunanin bazaka samu ba. Ga marasa iya juriyar riƙewar ne ke kai masa tallar kansu. Tun ban maida hankali akan abinda yake yi ɗin ba har na fara maida masa murtani. Tsabar taɓara da tasirin da hakan ya masa sai kawai naji muku mutumin nan ya saki kofin hannunsa tsulum cikin ruwan. Ya wani ɗaukan camak. ALLAH ya rainani, yanda akoda yaushe yake mun ɗaukar amaryar nan. In sha ALLAHU sai na dage na ƙara ƙiba ko zanyi maganinsa (Sam-G fa na magana. Ashe dai ƙibar nan abin so ne. Mune fa ake yayi yanzu😜😂).
Cusa kaina nayi kawai a jikinsa. Dan wata kalar matsananciyar kunyarsa nake ji har tsakiyar brain. Ashe wannan wasa ne farin girki. Dan daga wannan ɗaukar kawai jina nayi a tsakiyar wani shegen lallausan abu, dole na ɗan buɗe idona sai naga ashe gadone a kuma cikin jirgin ne a wani ɗan ɗaki da akai matuƙar ƙawatawa da wasu irin fitilu da furanni masu azabar ƙamshi. Kai kai duk yanda zan musalta muku ba lallai ku gane ba. Kawai dai anyi babu ku kudai. Kusa rigima kawai kuma mazanku su kaiku wajen nan ku kashe kwarkwatar ido😜. (Kuji min mata da iyayi, anata Masara da hinkafa wake ta wani holewa a jirgi😏, bammu tabarma ma a tsakar gida aka kunna hitilar kwai ya ihemu cin soyayya😒. Yo ALLAH na tuba mu harma... Bara dai nayi hiru amma abar ziga mu ehe😠🌚).
Da farko hankalina ya tashi musamman dana tuna karo biyu wahalar dana sha. Amma dana tuna halin da nake a ciki sai naji nutsuwa. A hakan ma dai ban tsallake ba, dan na cuɗu matuƙa har sai da ya samu yanda yake so ko nace muka.... (😎 Zancen ya tsaya iya nan to😌).
Na jima ban yarda na ɗago koda wasa na kalla sashen da yake ba. Dan wata irin matsananciyar kunyarsa nake ji fiye da yanda kuke zato. Hummm kar kuga laifina, Ni kaɗai nasan karatun da aka ɗaura min a cikin wajen nan. Koda aka kawo abinci ma ya ce na tashi naje nayi wanka na ci, ƙi nayi, dan shi ya riga yayi wankansa. Sai ma sake shigewa cikin lallausan farin duvet ɗin nayi na nutse a katifar da ƙyau. Sai da yace idan na bari ya hauro sai na yabama aya zaƙinta sannan na tashi ina tuttura baki. Cikin shagwaɓa batare dana kallesa ba nace ya ban kayana to. Sai ya miƙamin wata shegiyar rigar baci fara, wadda da iya da babu duk ɗaya. Duk da kuwa a tsaho nasan zata iya kai fin har gwiwa. Kawai yanda take shara-shara ne abin zakkunya. Sauka nai jikina gaba ɗaya nannaɗe a duvet ɗin, ganin zan tafi a haka a daƙilen nan nasa na magana kamar dole ya ce, “Kima dawo ki ajiye musu duvet, in ba haka ba ke da su ne ni zan wuce ne na barki a wajensu”.
Ƙafa na fara bubbugawa a ƙasa ina kukan taɓara. Sai ya ɗauke kansa tamkar bai san inayi ba ya fara kai coffee ɗin da ya sa aka kawo masa baki. Nikam dai na gama shiga ɗari tara da cassa'in da tara, ni kam ina mutumin nan ke son kaini ne?. Ganin bashi da niyyar cewa komai dole na ajiye musu duvet ɗin na kwashi rigarsa da idona ya kai kai na saka sannan na wuce bayin ina murguɗa baki da jajjan rigar ƙasa dan rabin cinyoyina duk a waje. Haka kawai naji a raina yayi murmushi, aiko ina shigewa nace “Fitinanne kawai, shiyyasa ƴammata suka dameka”. (😎Kishi phone store)......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_
......Koda na shiga bayin naji wani irin daɗin ganin p&pad a ciki. Duk da nayi mamakin hakan sai kawai nai tunanin ko suna ajiyewa ne dama in case. (Ko kuma shine yasa aka ajiye miki ba) wani sashe na zuciyata ya ayyana min. Sai abin ya sake bani kunya. Mutumin nan ɗan duniya ne sai dai kawai a barsa. Nima bathrobe ɗin na saka na fito fara tas kamar tashi, ko da wasa ban yarda na kallesa ba, duk da shi bana raba ɗayan biyu kallon nawa yake dan kujerar dana zauna tana facing ɗinsa ne. Su kaɗaine kuma a wajen sai wannan gado. Mugun ƙwaɗayin da nake ji ya sani cin gasashen kifin da aka wani ma gashi na musamman sosai. Sai naji na samu nutsuwa. Duk wata samuwar kwaɗayina ta tafi. A karan farko na ɗan ɗago na kallesa. Ganin yanda hasken