Showing 330001 words to 333000 words out of 438336 words

Chapter 111 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2195

ni, sai idanu dana zuba mata zuciyata na wani irin sauka a hankali. Raɓani tai zata wuce na damƙo hannunta, sai ta juyo a girgice zatai magana nai azamar girgiza mata kaina da zipping ɗin bakina alamar tai shiru. Cikin rawar jiki ta haɗiye maganar da take son yi kuwa. Ni kuma naja hannunta muka bar ta wajen duka. Sai da muka bar ƙofar ɗakin na tabbatar ba idon kowa ata inda muke sannan na ce, “Miye sunanki?”.
Sosai fuskarta ya nuna alamar mamakin tambayar da nai mata. Amma ganin na haɗe fuska babu alamar wasa a tattare da ni, ga shi na tabbatar tasan wacece ni dan yanda muka shigo suna kallonmu ko ita bata gammu ba nasan za'a bata labari, ga kuma tranding da hotunana dana Maash sukai a kwanakin nan koma nace suke kanyi. Amma duk da haka sai da na ƙara mata da faɗin, “Sunana Samraah Abdul-wahab Gwarzo, Mrs Awwab El-Mu'azz Maash. Nasan kin sani. Minene sunanki?”.
Kanta ta shiga jinjina min tana ƴan waige-waige, mutyarta na karkarwa ta ce, “Murjanatu Usman”.
“Masha ALLAH Murjanatu kwantar da hankalinki ba wani abu bane ba, magana nake son nayi da ke amma bazai yiwu anan ba. Ko zaki iya bani number naki?”.
Yawu masu kauri ta haɗiye da ƙyar. Cikin ƙara daburcewa ta ce, “Dan ALLAH Maa kiyi haƙuri idan akan turekin nan da nayi ne. Wlhy ban san kin tahoba sam shiyyasa”.
Murmushi na mata dan naga ta firgice. Cikin son dai-daita yanayi na na ce, “No kwantar da hankalinki ba wannan bane ba. Tambaya zan miki akan wani abu daya shafi mace mai ciki, amma bana son yi anan shiyyasa”.
Da masifar ƙarfi ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta sake sauke numfashi da faɗin, “Wlhy ranki ya daɗe harna tsorata. Kin san abunne akwai tsoro balle ku manyan nan. Na zata ko na miki wani laifine. Ba damuwa ko gida kike son nazo zanzo na same ki ai. Sai dai matsalar baza'a barni na shiga ba”.
“No karki damu zansa azo har nan ɗin a ɗaukeki. Ko zaki iya bani number ɗinki?”.
Cike da zumuɗi ta amsa min tana amsar wayar hannuna. Ni saima taso bani dariya. Dan hannunta har rawa yake wajen loda number ɗin. Amsa nayi nai saving. Da murmushi na ce mata, “Zaki iya ji kirana akoda yaushe in sha ALLAHU. Amma fa maganar nan ta tsaya iya ni da ke kawai. Dan na fahimci kina da hankali da nutsuwa tun wancan kwanciya asibitin da nayi shiyyasa”.
Sosai ta sake washe baki cike da farin ciki tana Murmushi. Da ga haka muka baro wajen. Sai da naji shock da hango Maash tsaye da alama ta inda zan fito yake son gani. Amma sai na dake abina a nutsena na ƙarasa inda yake. Batare da nayi magana ba na zare wayar da yake dannawa daga cikin hannunsa. Sai da yana wani sakanni kafin ya ɗan ɗago cat eyes ɗinsa ya kallan. Ido ɗaya na kashe masa cike da salon basar da shi na ce, “Tsaiwa anan kamar wani dogari”.
Maimakon tanka min sai ya wani cigaba da kallona, kusan minti ɗaya sannan ya motsa lips a hankali ya furta, “Let's go”. Yana kama hannuna. Banda zaɓin daya wuce bin nasa. A haka muka dinga keta mutane ana kallonmu. A karan farko naji banji kunyar hakan ba. Sai dai a raina ina jin wasu fa zasu iya ɗaukar hotonmu musamman a wannan gaɓar da dama ake neman labari a kammu. Kamar ko ina gani har hanji, dan bamu ƙarasa gida ba sai ga hotunanmu sun fara yawo a media. Sosai na tsarkake sunan UBANGIJI da jinjina halin gulamar mutane da ƙaikayin hannayensu nason yaɗa abinda sam bai shafesu ba. Dan su birge ne ko dan ace a bakinsu aka fara ji oho musu........✍️


Zazzabi ya tasani gaba posting yanzu sai a slow. Ayi hakuri dai in sha ALLAHU muna gab da tsargewa kowa ya huta🥲.


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_


.......Washe gari tunda Baba prof da Hajiya ƙarama suka dawo hayyacinsu duk sai suka matsa a sallamesu a safiyar. Iya ƙoƙari doctors ɗin sunyi dan ganin sun fahimcesu musamman ma Baba prof da tai masa illa a inda ya kamata ya samu kulawa amma sam hakan yaƙi yiwuwa. Dole suka haƙura suka sallamesun. Dama shi Paah tun a daren Maash yasa aka sallamesa saboda Ummie ta tada hankalinta akan zataje asibitin zaman jiyyarsa. Shiko bai amince da hakan ba. Shiyyasa ya yarda da a dawo da Paah ɗin gida likitan ya cigaba da zuwa dubashi anan.
Kai tsaye sashen Maash ɗin aka kaisa ɗakin da Ummie take. Sai ganinsu kawai tayi. Sosai ta nuna farin cikinta taita sanya musu albarka. Su dai basu ce komai ba musamman ma Maash da ke matuƙar jin zafin Paah har yanzun. Isma'il ne yay kiran Maash ya sanar masa ai an sallamo Baba prof gashi a gida. Baiyi mamakin hakan ba, dan haka baice komai ba sai murmushi. Lokacin da kuma yake fitowa ya shiga ya duba Paah ya fito zasuyi break fast su Fahad ke sanar da itama Hajiya ƙarama ta dawo gida yanzun nan. Dama su su Hajiya Mammah tun jiya aka sallamosu. Uffan shi dai Maash baice ba, sun kuma san bazai ce ɗin ba daman....

✨✨✨✨

Iya faɗin yanayin da Baba prof ke ciki kawai sai dai kintace, dan a matuƙar harmutse yake. Duk da yanda yake jin rashin ƙarfi a jikinsa suna isowa gida wanka yay tare da yin shiri cikin manyan kaya. Sai da ya fito sannan ya tuna babu drivernsa fa a gidan yanzu. Gashi bai san ina Commondo ya kaisa ba. Zaune ya kai cikin kujerar falon kawai yay shiru. Sai da yaja tsahon lokaci a haka kafin ya ɗauka waya yay kira. Ana ɗagawa da ga can batare da ko sallamar da akai masa ya amsa ba cikin bada umarni ya furta, “Ka sameni a gida yanzun nan”. Ƙitt ya yanke kiran.
Sake zabga tagumi yayi na wani lokaci, sai kuma ya miƙe ya fara safa da marwa a falon cikin rashin ƙarfin jiki. Tsahon awa ɗaya ciff sannan Uncle Abdullahi ya iso gidan. Ya nuna mamakin ganin mahaifin nasa a gida, kasancewar duk sun san bai isa a sallamesa ba haka da wuri dan jikin nasa da saura. Ga Doctors ɗin ma sun tabbatar da yana buƙatar hutu..
“Baba ina kwana? Yaya ƙarfin jikin?”.
Ya faɗa cikin ƙoƙarin danne komai dake a ransa. Shiru Baba prof bai amsa ba, sai da yaja lokaci mai tsaho sannan ya juyo a wani irin yanayin mai wahalar fassara yake kallon sa. Kasa jurewa Uncle Abdullahi yay ya duƙar da kansa ƙasa, ya san minene laifinsa, ya kuma shirya amsa komai da za'a tuhumesa da shi. Kamar ko yanda yay zato a zafafe Baba prof ya furta,
“Abdullahi!! Wanene ni a wajenka?”.
Sosai tambayar ta bama Uncle Abdullahi mamaki, amma ya daure kansa a ƙasa ya amsa da, “Baba mahaifina ne kai, wanda yay sanadin kawoni duniya, ya tarbiyyace ni ya tufatar da ni da ciyar dani a lokacin ƙuruciya da kula da ilimina duk bisa amincewar UBANGIJI”.
“Ban yarda da hakan ba Abdullahi. Ƙarya kake yi!. Da ace ni ɗin mahaifinka ne da baka zaɓi wata rayuwa bayan idanuna ba. Da ace ka yarda ni Adamu ni na ciyar da kai, na tufatar da kai, na biya maka kuɗin makarantar da har kayi kaurin wuyan aikata abinda ka aikata to lallai fa da baka kasance wani abu a bayan ganina ba. Abdullahi idan ban manta ba ni da kaina na hana ɗan uwanka aikin interpol a sanda ya ƙwallafa ransa. Amma shine kai ka zagaye ka zama jami'in sirri bada sani na ba. Hakan na nufin akwai wani abu a ranka ke nan ko kake shiryawa”.
Hankali tashe Uncle Abdullahi ya ke girgiza ma Baba kai. “Wlhy Baba sam ba abinda kake zargi bane ba. Kuma a lokacin daka hana Yaya Mu'azz zama jami'in interpol na ɗauka wannan aikinne kawai baka ra'ayin muyi. Zama wannan jami'in kuwa wasu dalilai ne suka kaini ga zama hakan. Ban kuma ɓoye ba domin wata manufa tawa sai dan yanayin aikina kenan. A jiyan ma dole ce ta tilasta ni fitowa har duniya ta sanni da wannan matsayin. Amma idan har na ɓata maka rai ka gafarceni dan ALLAH”.
Shiru Baba prof kamar bazai tanka masa ba. Sai da ya mula dan kansa kafin cikin bada umarni ya furta, “Bazan taɓa aminta da kai ba Abdullahi a yanzu sai na tabbatar. Sai dai a matsayina na mahaifi ina baka umarnin ka saki wannan yaron Commondo....”
A bala'in firgice Uncle Abdullahi ya ɗago yana kallonsa. Har bai san sanda ya furta, “Baba saboda mi? Akan mi kuma zanyi hakan bayan shi ɗin mai laifi ne. Dukkan bincikenmu ya tabbatar mana da cewar da hannunsa a yin kidnapping ɗin Yaya Mu'azz. To wai kai minene ma haɗinka da shi da har kake so a sakesa Baba?”.
“Babu ruwanka da alaƙar dake tsakanina da shi. Kidnapping Mu'azz kuwa ni da kaina zan hukunta shi na kuma ji ba'asinsa nayin hakan”.
Wani murmushin ɓacin Rai Uncle Abdullahi yay da faɗin, “Baba to ai kai ba jami'in tsaro bane. Dan mi zan barka kayi hakan? Sannan babu ta inda dokar ƙasata ko aikina suka bani damar sakin Commondo a halin yanzu. Saboda yanzu haka ana kan binciken mugayen ayyukansa ne ma. Shawarar dazan baka ma shine Baba kai gaggawar barranta kanka da shi idan ma wata alaƙa ta taɓa alaƙantaku. Dan wannan mutumin mugayen ayyukansa zasu iya kaisa ƙasa dama duk wanda yake tare da shi. Ka gafarceni Baba na barka lafiya”. Ya ƙare maganar yana miƙewa ya fice. Dan gaba ɗaya kansa juya masa yake. Idan bai bar gaban Mahaifin nasa ba zai iya rasa control ɗinsa ne gaba ɗaya...

Ko sau ɗaya Baba prof ya kasa motsi. Sai kalaman Uncle Abdullahi ne ke masa wani irin amsa kuwwa acikin kunne har bai ma san ya fita a falon ba. Cigaba da jin sautin muryar Uncle Abdullahi na masa ihu cikin kunne ya sakashi fassa wani ihu shima yana wancakalar da Centre table ɗin gabansa. A guje wasu a cikin ma'aikatan gidan suka fara rige-rigen shigowa ciki harda Kuku da ke lafe yana jin komai. Sai dai shi kansa a yau ba ƙaramin girgiza zuciyarsa tayi ba da ganin abinda bai taɓa zato ba. Yanzu nan duk irin aibanta Baba prof da tsiyatakunsa da ya dinga yi a wajen ogan nashi ashe mahaifinsa ne. Kan bala'i jan. Wannan wace kalar cakwakiya ce haka. Sai yanzu ya fassara sunan Uncle Abdullahi da ƙyau. *_Abdullahi A.KM_* wato (Abdullahi Adams K/Mashi) kenan dai. Jiyyar gaba ɗaya haddarsa ta gama gogewa. Jiyay kawai buƙatar ganin Maash yake, shin shima yasan ogansa kawunsa ne ko kuwa sai a jiya da yay bayani?.
Da ƙyar suka samu Baba prof ya zauna. Haka suka shiga kimtsa falon shi kuma ya shige bedroom. Giyarsa ta samu ya kwankwaɗa ya zube ƙasa sai barci. Dan inba hakan yayi zuciyarsa zata iya bugawa a yanzun nan.....

🌿🩸🌿🩸🌿

Da mamaki Uncle Abdullahi ke kallon Maash da ke shigowa office ɗin nashi. Sam baiyi zaton shi bane ba. Dan shigowarsa station ɗin kenan rai a ɓace daga gidan Baba prof. Baifi zaman mintuna biyar ba akace yayi baƙo. Da farko yace baya buƙatar ganin kowa. Sai kuma yanda yaga yaron nasa ya yi shiru kamar mai son cewa wani abu yace yaje ya shigo dako waye. Amma mintuna goma kawai zai iya bashi. Shine fa kawai sai ya ga Maash ya shigo alamar shine dai baƙon da aka nemawa iso kenan.
Da ƙyar ya iya ɗaga hannu yay masa nuni da wajen zama. Shima sai Maash ɗin ya kai zaune batare da yace komai ba. Sai da yaron Uncle Abdullahi ya fita a office ɗin sannan a hankali Maash ya furta, “Good morning Uncle”.
Murmushi Uncle Abdullahi yayi da faɗin, “Morning Awwab. Daga ina haka?”.
Ƙaramin murmushi shima Maash ɗin ya saki a karo na farko. Sai kuma ya ɗan kalla Uncle Abdullahi ya ɗauke idanunsa a daken nan nashi ya ce, “Daga gida, kuma wajenka nazo”.
“Dama nasan zan ganka, amma banyi zaton da wuri haka ba. Kar dai na jaka da nisa mike tafe da kai?”.
Numfashi mai nauyi ya sauke da gyara zamansa da ƙyau babu alamar wasa tattare da shi. “Uncle basai munja komai da nisa ba tsakanin ni da kai kamar yanda ka faɗa. Nasan kasan abubuwa da yawa da suka shafeni wanda ba kowa ya sani ba a gidan nan. Wasu ma da kaina na buɗa maka saninsu saboda na jima da sanin kai ne ogan Isma'il da Shu'aibu. Nasan hakanne tun lokacin da ka bada su Shu'aibu matsayin guards ɗina....”
“What a surprise!.”
Uncle Abdullahi ya faɗa cikin nuna matuƙar mamaki da al'ajab har yana miƙewa. Ƙasa kawai Maash yay da kansa yana furzar da isa. Ɗan bugar desk Uncle Abdullahi ya ƙara yi yana sake jinjina al'amarin sosai. Kallonsa Maash kawai yay ya sake ɗauke kansa kamar mai ɗan jin nauyin Uncle ɗin nasa.
Zama Uncle Abdullahi yayi zuciyarsa na sake mamakin hatsabibancin yaron nan. Amma sai ya dake........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_


.......Cikin girgiza kai ya ce, “Nama rasa mizan ce Awwab. Kenan da ban fito a wannan gaɓar na bayyana kaina ba haka zamuyita tafiya ina maka kallon biri kana min na ayaba?.”
Murmushi Maash yay da faɗin, “No Uncle! No! Just forget. Hakan ya kasance ne saboda wasu dalilai. Kamar yanda yanzu ma dalilan ne suka kawoni nan. Isma'il ya sanar min duk yanda kukayi da Baba. Duk da bai kamata ace ya sanar min ɗin ba. Sai dai ruɗanin da ya shiga shima na gane cewa munada alaƙa har haka mai ƙarfi ya kaisa ga hakan. Uncle Please ina riƙonka ka bama wani case ɗin nan. Saboda....”
“Saboda ban cancanta ba? Ko saboda Baba ya kasance mahaifina kai kuma ɗan ɗan uwana?”.
“No Uncle Understand me. Abin zai zamar min wani iri nima. Shiyyasa ba kowane imformetion zakaga nake baku ba, wasu lokutan nake yin wasu abubuwan da kaina ta bayan fage. Magana ta gaskiya case ne da bazan iya bari ba, ba kuma zan so sarƙaƙiyarsa ta shafi har waɗanda bai kamata ta shafa ba irinka.”
Sosai Uncle Abdullahi ke jinjina kai idanunsa da suka canja launi akan Maash. Murya a shaƙe ya ce, “Muhammad Awwab!”.
“Yes Uncle”.
“Kasan mi nake so da kai?”.
Kai kawai Maash ya girgiza masa.
“Kasa a ranka sunana Abdullahi A.km. da yay rantsuwa wa UBANGIJI zaiyi aiki tuƙuru domin kare ƙasarsa dayin adalci wa mutanen cikinta walau talaka ko mai arziƙi, ko mai mulki. A tsarin aikinmu babu zancen family. Babu zancen kasuwanci, babu zancen abota ko makwaftaka. Tabbas a lokacin dana amshi wannan case ɗin ban san nasu wanene ba. Sai da aka hari rayuwarka ta farko sannan har na yanke komawa cikin Maash Mansion. Bayan nan ne na zauna nayi bincike mai zurfi tare da saka mutane da yawa a cikin ku. Abinda yasa na ɓoye kaina gareka dan ka samu damar sanar min komai batare da kaji wani ɗar ba. Ashe ma nayi shuka a idon maƙwarwa ɗan nawa ƙwaron kansa ne”.
Murmushi nan ɗin ma Maash ya ɗan yi kaɗan batare da ya yace komai ba.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login