Showing 360001 words to 363000 words out of 438336 words
na rufe. Wannan kuma shine ya zama tushen fara fitar damuwata. Daga kuka sai tasa yarana gaba naita kallo dan na fahimci a wannan gaɓar sune kaɗai gatana. Sune kaɗai abinda ya rage min na kalla naji daɗi kamar yanda mahaifina ya sanar min. Sai kuma matsanancin tausayin rayuwarsu da nake ji, dan bana jin nima zanyi tsawon rai batare da nabi bayan mahaifina ba. Saboda ina jin yanda ƙirjina da zuciyata ke mun nauyi. Bani da wata madafa, na rasa wanda zan fiddoma ainahin damuwata. Duk da kuwa bazanyi butulci ba Mahaifiyar Bilkisu tsaye take a kaina. Itama kuma Maman su Azz a ɗan tsakanin ta jani jikinta sosai. Kasancewar nayi shiru da bakina ban taɓa cewa kowa komai ba akan abinda ke damuna yasa kowa ke fassara al'amarin nawa da kasa yin tawakkali da rashin mahaifina da nayi. Ni kuma ni nasan ainahin matsalata. Bilkisu ta dawo saboda kwanciya ciwo da nayi a tsakanin, sai yazam ita da Lawisa da Fatima ke kula da ni da yaran, jin na yarda da su a raina saboda yanda suke nuna damuwarsu a kaina yasa na damƙa musu amanar yarana batare da su sun san dalili ba ashe Lawisa munafukata ce. Jiyyar kusan sati ɗaya na fara ƙarfafa kaina kodan ƴaƴana, bazan so na tafi na barsu a ƙananun shekarunsu ba. Lokacin Azz yayi tafiya, sai dai ban san takamaiman inama ya tafi ba, kamar mahaifinsa ya barni sai gashi ya dawo a kwanakin dana fara murmurewa. Ni yanzu ganinsa baya bani wani mamaki ko ɗar dan na gama sakashi a layin da ya dace da shi. Ashe ma ya wuce hakan dan sai a ranar yake tabbatar min. Banko kalli inda yake ba na gaisheshi da tambayarsa ko yau kuma miya kawoshi?. Kai tsaye yace dani cika alkawarinsa. Banji komai a kalmarba na ce, “Humm”. Shima Humm ɗin yace min tare da cigaba da faɗin, “Kin mun taurin kai da tunanin babu abinda zan iya gareki saboda baki san wanene Adams ba. To bari na fiddo miki da saninsa. Ni ba kanwar lasa bane ba yarinya. Dan shi kansa mahaifin naki ya buga da ni na kaisa ƙasa balle ke ƙaramar ANT. Na biki ta lallami da hanyar sulhu ta yanda zaki rayu cikin aminci da ƴaƴanki amma kin tabbatar min baƙya buƙata. To abinda na saka Mu'azz yake miki yanzu ƙarami ne. Ni nawa kashe ki zanyi kamar yanda na kashe uban naki, na kuma kashe uwarku da uwar uwarki da iyayen ubanki. Je kabarin Abdul-wahab drivern ubanki ki tambayesa labarin yaya karon battarmu da shi. Alwashi ya ɗauka zai ƙare rayuwarsa a kare rayuwar ubanki shiyyasa na haɗa da shi na kashe a randa nai shirin kashe uban naki. Sai ko gashi shine ya rigashi tafiya batare da ya karesan da ya ɗaukar min alwashi ba. Dan haka zaɓi ya rage naki, tattaro dukkan dukiyar ki danƙa min yanzun nan a hannuna. Ko kuma na ƙwata ta ƙarfin tuwo bayan na kashe ki, na kashe waɗan nan ƴan kuyi-kuyin yaran naki.”
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Harga ALLAH bazan iya ma fassara muku halin dana tsinta kaina a wannan lokacin ba. Dan kalaman wannan baƙin azzalumin ba ƙaramin dukan zuciyata sukayi ba. Duka mai girma da gigita brain da tarwatsa zuciya. Cikin rawar jiki na ce, “Kai ne ka kashe Mamana da mahaifiyarta? Sannan ka kashe mahaifina da iyayensa? Ka kuma kashe Abdul-wahab?”.
Dariya ya bushe da ita harda buga ƙafa. Sannan yay min kallon sama da ƙasa ya ce, “Saura ma ke cikason su tare da yaranki biyu idan kika cigaba da mun gadara da taurin kai akan abinda aka tara da gumina aka bar miki da sunan gado. Da kike ganina cikakken ɗan hau ne wlhy, sannan gagararre ne a ƙauyenmu ki bibiyi tarihi na, taƙadaranci yasa na baro gida, samun ubanki yasa naji a raina kakata ta yanke saƙa amma ya nuna min shi ɗin ma shege ne kansa kawai ya sani. Ko karatu dana daure nayi nayine saboda na fahimci baka amsa sunan wane sai da shi. In da yay ma kansa adalcin bani abinda yake hakkina tun farko da yanzu yana rayuwarsa, amma ya nuna min shi wani kwallon shege ne. Hhhh yanzu yana ina? To kema kinada zaɓin rayuwa ko bin bayansa. Na baki daga nan zuwa dare na ga saƙo”. Ya ƙare maganar yana wata shegiyar dariya da miƙe....
Wani irin abine ya tokare min kafar numfashi, sai dai nayi jarumtar fisgoshi cikin azaba da ƙunar zuciya. Dai-dai yana saka ƙafa zai fita na dakatar da shi da faɗin, “Kai matsiyaci maci amana azzalumi, fasiƙi. Naji kaci nasarar kashe zuri'ata bisa dalilai daban-daban. Sai dai na maka alƙawarin ni Ummu-Hidaya Ibrahim ko zaka dinga yankan naman jikina wlhy bazaka mallaki wannan dukiyar da kake kwaɗayi ba. Kuma koda nima ya kasance ƙaddarar mutuwata a hannunka take sai na zamewa rayuwarka bala'i ta inda bakai zato da tsammani ba. Ka kira kanka taƙadari ko, to ai kan naka kawai ka sani, kuma na maka alƙawarin jinin zuri'ata daka salwantar bazai taɓa tafiya a baza ba sai ka biya da FANSA. FANSA a lokacin da baka da madafar dafawa, FANSA a gaban alƙalin alƙalai. FANSA a ranar da gangar jiki ke amsa tambayoyi ba baki ba. FANSA a ranar da ake roron ayyukan alkairi. FANSA a ranar da ake biyan bashi da aiki bada abinda aka karɓa a duniya ba. Idan babu aiki za'ai FANSA da zunubin mai hakki. Kamar yanda wannan dukiyar ta gagareka amsa a hannun mai ita duk da kanada damammaki da gadarar kai shege ne a hannun UMMU-HIDAYA ta ƙara maka nisa ne, nisa mai matuƙar tazarar da sai dai yaro da babba su hangi sararin SAMANIYA a samanta badai taɓawa da hannaye ba. Ai kai matsoracine ma tunda kashewa kake, cikakken namiji fili yake sharewa a gwabza yaƙin nuna ƙwanjin NASARA, Gwarzo na gaskiya ya ɗauki KAMBUN IKO!!!. Na faɗa, na kuma sake maimaitawa, zan kuma sake shelantawa. Ka kuma rubuta ka ajiye kona mutu a dalilin ƙaddarar mutuwata a hannunka take sai an maimaita maka hakan. Kuma koda bana raye wannan dukiyar tafi ƙarfin mallakar ka kai da kaf ZURI'ARKA baƙin TSINANNE, sai dai ku ƙare rayuwarku a ƙarƙashin ALFARMAR ZURI'AR MAHAIFINA”.
“Hahhhhh!! Lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka. Oh ya TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE kenan. To bari mu gani ni da ke waye shegen. Bazaki mutu ba. Zan barki a raye kuwa ta yanda sai na ɗanɗana miki azabar ruwan DALMA a tsakkiyar tafin hannu. Zakiyi rayuwar da gara mutuwa da ita. Zakiyi rayuwar da ke kanki sai kin tsani kanki da kanki. Zakiyi rayuwar da yaƴanki sai sunji sun tsaneki fiye da komai a rayuwarsu. Zan nisanta su da ke, na rainesu raino irin na bawa da uban gidansa. Fiye da irin rainon da UBANKI yay min. Dan sai na maida su KARNUKAN farauta ta da zan dinga jefama NAMA suna bi da gudu suna ɗauka tamkar wulaƙantatu. Dukiyar da kike gadara da ita ɗanki ne zai juyata ni da kaf ZURI'ATA muna kwance muna ci a cikinta. Sai ya ƙare ƙarfinsa da ƙuruciyarsa akan bauta min kamar yanda na ƙare nawa ƙarfin da ƙuruciyata akan naki uban. Sannan daga ƙarshe na miki alƙawarin zan shinfiɗe miki gawarwakinsu a gabanki bayan koman da kike taƙamar da shi ya dawo hannuna. Muje zuwa wasan ƴar Alonso”. Ya faɗa cike da gadara yana ficewa kafin nace komai. Bamma san yanda akai ba, yanke jiki kawai nayi na faɗi a wajen. Ban tashi farkawa ba sai bayan kwana biyu kamar yanda Bilkisu ta sanar min kwanana biyu a halin suma shiyyasa suka kaini asibiti. Halin da naga Muhammad a ciki ne ya ƙara ɗaga min hankali. Cikin kwanaki biyu duk ya fita a hayyacinsa. Dan haka na tambayeta shine take sanar min ai shima yana dawowa a makaranta lokacin ina sume kasancewar shi ya fara cin karo da ni sai ya ɗauka na mutu ne, shine ya yanke jiki ya faɗi shima. A tare ma aka kawomu asibitin. Sai dai shi bai jimaba ya farfaɗo. Tunda kuma ya farfaɗo basu sake gane kansa ba. Baya cin abinci sai ruwa kawai. Magani kam dama ya tsaneshi sai da ƙyar ake danna masa shi. Kamasa nayi na rungume ina hawaye. Shima yana kuka. A zancen nan da nake muku fa Azz baya gari, tun abinda ya faru na kawo min wata ɗakin barci daya gudu ban sake ganinsa ba har lokacin. Bamma san inda yake ba. Kuma har cikin raina ina son sani kodan jin abinda babansa ya faɗa da saka hannunsa yake mun komai tun farkon auren mu. Waɗan nan damuwar ta Muhammad da Azz ta sake ƙarfafa ciwona har nai jiyya kusan ta sati uku. Daga lokacin kuma komai ya canja daga yanda yake. Ummu-Hidaya ta gaskiya ta gushe. Ciwon HAUKA ya maye gurbi. Tun abin na buga min na ɗan dawo hankalina a wasu lokutan har komai ya rincaɓe ta yanda bana gane komai sai tsananin tsanar Muhammad. Gashi dai shine a mafarkina da ƙasan zuciyata. Amma a duk sanda ya tunkaroni ji nake tamkar na kasheshi na huta. Bana taɓa samun nutsuwa har sai na raunatashi... Kuka ya sarƙeta. Maash ta kamo ta rungume tsam a jikinta..........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
.......Kowa a falon kuka yake fiye da zaton mai zato. Idan ka cire prof da muƙarrabansa sai Hajiya ƙarama da tai tagumi kawai. Sai Maash da ke kukan zuci dan babu ɗigon hawaye akan fuskarsa. Sai da kowa yay mai isarsa kafin Ummie ta cigaba da faɗin, “Kuji tsoron ALLAH duk da anan mafi rinjayenku zuri'arsa ne, kuyi alƙalanci na gaskiya. Minene laifin mahaifina ga wannan mutumin? Shin dama ALKAIRI kan zama SHARRI? Ta ina mahaifina ya tauye mutumin nan? Minene laifin su Muhammad idan yace ni na masa ko mahaifina ya masa. Adamu baka tunanin ALLAH yay maka talala ta tsahon rayuwa har zuwa wannan lokacin da kaci alwashi a kansa ba? Ko a tunaninka isarka ko gadarar taka ce ta jagiranceka zuwa yau? Lawisa mina miki a rayuwa? Wane mummunan abu na taɓa aikata miki da aka haɗa hannu da ke wajen cutar da ni. Ke ɗin fa ƴar uwa na ɗauke ki. Jawoki nayi daga rana a lokacin da kike matuƙar buƙatar hakan zuwa cikin inuwa. Na haɗu dake a secondary school first ranar da aka kaini nima kema aka kaiki. Yanda kike ƙazama daga ganinki anga jigatacciya yasa kowa a ajinmu baya son haɗa mu'amularsa da ke. Kin bani matuƙar tausayi dan koba komai rana guda aka kawo mu. Hakan yasa na janyoki jikina hatta da kuɗin break ɗina tare mike rabawa. A randa kika bani labarin aikatau aka kawoki garin Lagos kasancewar baki gane komai baki jin turanci gidan da kike aiki suka sakaki a makaranta yasa na ƙara jin tausayinki. Haka na kaima Abie kuka a kanki. Na roƙesa ya amsoki a gidan da kike ki dawo gidanmu. Soyayyar da yake min tasa bai musa ba ya amsa min ya kuma aiwatar. Sai dai wadda ta kawoki aiki ashe ƴar uwarki ce ta jini dan haka ta nuna bazata bamu ba dole mukai haƙuri. Amma Abie yace zai cigaba da ɗaukar nauyin karatun naki kibar aikatau ɗin. Haka akayi kuwa, duk abinda Abiena yay min a fannin karatu sai ya haɗa da ke, hatta da sutura a lokuta da dama idan aka siyamun nakance kema a saya miki. Haka zai saya miki batare da ƙorafi ba. Hatta da ƴar uwar taki yakan hidimta musu duk dan soyayyar dake tsakaninmu. Hatta da karatu da taimakonna kike yinsa dan baƙya gane komai ba gori ba. A haka muka kammala secondary. Duk da Abiena ya mun aure da Azz mun bar Nigeria bai daina ɗaukar nauyin rayuwarki ba. Kina zuwa masa da batun komawa karatu a fannin lafiya ya biya miki bayan ya tallafa miki kika fara. A haka na dawo na sameki kin zama ma'aikaciyar jinya. Abin ya birgeni na fara tunanin buɗe miki asibiti. Ina gayama Abie ya bani goyon baya ɗari bisa ɗari. Haka ya bani kuɗi na zuba aka gina ƙaramin asibitin shan magani da karɓar haihuwa kawai aka damƙa miki. Sai dai ƙarancin ƙwarewa yasa nai ƙoƙarin sake turaki ƙaro karatu, kafin ki dawo aka sake faɗaɗa asibitin. Ya zama kowa zai iya jiyya aka ƙara sabbin ma'aikata da kayan aiki da bako ina zaka iya samunsu ba aka shugabantar dake kula da komai na asibitin. Abubuwa da yawa kin sani a kaina Lawisa. Rayuwar aurena da sirrina da mahaifina ne kawai bana shering ɗin sa da kowa a rayuwata. Dan haka har mahaifina yabar duniya bai taɓa sanin a halin ƙuncin da nake a gidan aurena ba, na saka a raina watarana komai zai zama labari. Domin ina ƙyautatama mijina zato da fatan watarana girma zai sa ya ajiye wasu abubuwan kodan yaransa dake tasowa. Ko'a lokacin dana dawo a hayyacina na shakera kusan ɗayar nan na buɗe ido na ganki matsayin matar Azz ko sau ɗaya na taɓa canja miki fuska? Kona taɓa bincikarki yaya kika auri mijina? Gashi nan shima da ransa da lafiya Azz na taɓa tuhumarka ya akai ka auri Lawisa? Na taɓa nuna maka ba kayi dai-dai ba har na koma a halin ciwo?. Bama kuba ga ƴaƴana nan, ga Bilkisu nan da ake ganin inada kusanci da ita fiye da kowa akwai wanda na taɓa tambaya yanda akai Lawisa ta auri mijina?. Ba kuma dan banji zafi bane ko banyi mamaki bane, kawai na bar al'amarin matsayin ƙaddara kuma aurene ai ALLAH ya halasta muku dammi ni kuma zan butulce masa bayan yamun ni'imomi daban-daban a rayuwa da ban san adadinsu ba, sannan a halin da nake ciki dolene Azz yay aure ai. Zaman Lawisa da Azz matsayin ma'aurata bazai ƙaran da komai ba, ba kuma zai rageni da komai ba. Hatta da wannan yarinyar (ta nuna Arwa) dana buɗe ido na ganta akace ƴar Lawisa ce har yanzun ban sani ba Azz ne mahaifinta ko wani daban. Dan a sanina nasan gab da rasuwar Abie Lawisa tazo mana da zancen ta samu mijin aure acan garinsu. Sai dai har Abie ya rasu ba'ai auren ba ni kuma nazo na shiga halin dana shiga. To ban sani ba ko tayi wancan auren ko batayi ba, da kuma na dawo hayyacina ganinta matsayin matar Azz ban tambayeta komai ba. Lawisa a cikin wannan duk dana faɗa ta ina na cutar da ke? Minene laifina a gareki? Minene laifin mahaifina da har kika iya bada gudummawar aka halakar da shi akan abinda yake hakkinsa. Ki faɗa min Lawisa! Ki faɗa min....”
Kuka yay bala'in sarƙeta har bata iya jan numfashi da ƙyau. A mamakin kowa sai muka ji Hajiya ƙarama na dariya. Babu wanda bai zuba mata ido ba a cikinmu dan mamaki. Sai prof ne ya wani taɓe baki da jan tsaki mai ƙarfi yana gyara zaman ƙasaitarsa shi a dole ga tantirin tsoho. Sai da Hajiya ƙarama tayi mai isarta sannan ta miƙe tana tafa hannaye da yima Ummie wani kallon zako ki sani yau. A gadarance ta ce, “Ummu-Hidaya kenan. Naji duk lissafinki da gorinki akan abinda kika min ke da babanki. Na kuma gode da gori. Dama kuma nasan irin wannan ranar zata zo, gata kuwa tazo. Dalili dai kike buƙata ko, to gashi zan faɗa miki yanzun nan. Komai ya faru ne a dalilin MAHAIFINKI. Tun a ranar farko da aka kaini makaranta kema aka kaiki na gansa son sa ya shige min zuciya sururuf....”
Kaff falon nan hatta da Prof a wannan gaɓar sai da ya kalla Hajiya ƙaramar. Cikin halin ko'in kula ta ce, “Eh ku kalleni da ƙyau abinda na faɗa shine gaskiyata. So ne na gaskiya na aure ya shiga cikin ZUCIYATA a ranar farko dana fara ganinsa. Ban damu da zai iya haifata ba, danni ba shekarun na kalla ba NAGARTA da jin soyayya ta gaskiya. Sai dai abin kaico da tashin hankali a gareni ban san ta yaya zan mallakesa ba. Dan haka na shiga ƙulla ta wace hanya zan samu? Kwatsam sai kika shigo rayuwata kika jani jikinki. Nayi farin ciki da hakan domin son da nake ji inama mahaifinki kema ya shafeki. Ƙaunarki ta ƙara tasiri a raina a lokacin da kika kaini ga Mahaifinki matsayin ya taimaka min ga halin da nake a ciki. Bai kumayi musu ba ya amsheni, kinyi ƙoƙarin ganin na dawo gidanku da rayuwa amma innata ta hana hakan. Naji zafin abinda tai min amma na ƙyaleta da tunanin a hakanma zan iya mallakar babanki, idan ta hanani zama ai aure zai maidani zaman din-din-din. Na ɗan fiddo da hanyoyin nuna masa manufata duk da ƙarancin shekaru na amma ya nuna baima san minake yi ba. Banji haushi ba, na kuma ɗauka har cikin raina bai fahimta ɗin ba kasancewar Bature. Idan baki manta ba a cikin hikima nazo miki da labari makamancin irin namu gab da zamu gama karatu. Na nuna miki ƙawar na bala'in son baban ƙawarta amma buɗar bakinki sai kika ce wai bata da tarbiyya ne da kunya. Idan da kece kuma wannan ƙawar wlhy sai kin rabu da ita. Har misali kikai da ni da ke akan naga dai babanki baida mata ko,