Showing 267001 words to 270000 words out of 438336 words
zata fincikoni. Kamar walƙiya Fahad ya sha gabanta. Cikin nuna tsantsar fusata ya ce, “Mi zakiyi? Dukanta wai? Aiko da sai na datse wannan hannun naki ta yanda bazaki sake morarsa ba har abada Mammah”.
Wani irin tsuruu Hajiya Mammah tayi tana kallonsa. Dan gaba ɗaya fuskar yayansa take gani akan tashi fuskar. Mamaki take wai yaushe ma yaron nan ya zama ƙwallon ɗan iska haka shima. Ko duk karuwancin yarinyar nan ne dai halan?........✍️
_Gaskiya dangin Sam-G kuna mata nasiha, rashin ji bashi da ƙyau Hajiya Mammah da Hajiya ƙarama sukanta ne fa🥱😝😂._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_
......Ba Hajiya Mammah kawai ba, kowa dake wajen sai da mamaki ya nema kasheshi. Dan babu wanda bai saki baki ba. Sai ma Hayatu ne da abin ya bashi dariya. A zuciyarsa ya ce (pepper ƙanwar mu is back). A zahiri kam yana a layin ƴan kallo ne shima.
Hafizzullah ma dai dariya yake ƙoƙarin dannewa, shima a ransa ya ke gulamar (Humm Adda ƙarfin halinki dabanne a rayuwa). Mama Balki ma dai mamaki take, a ƙasan ranta kuwa jin wani alfahari take yi, lallai yanzu ne in sha ALLAHU aikin su zai tafi dai-dai. Baba kansa murmushi yake a zuciyarsa, lallai ya sake tabbatar da yarinyar nan jinin Abdul-wahab ce, dan sam Abdul-wahab bai san wani abu tsoro ba a rayuwarsa. Shiyyasa ya ƙare rayuwarsa a bama ubangidansu da bazasu taɓa mantawa ba har abada garkuwa...
A ɓangaren Hajiya ƙarama baki ta saki kawai, ga ƙafafunta na wani irin rawa. Mamakin yarinyar da tu'ajjibinta na neman halakata. Gaba ɗaya hoton mahaifinta ke dawo mata da abubuwan da suka dinga faruwa a tsakaninsu. Ta ɗayan gefen kuma shi kansa Fahad yau ya goge mata hadda tas. Dan gaba ɗaya ya juye Maash sak. (Yallaɓai muna cikin tashin hankali) ta faɗa a zuciyarta wata irin zufa na ketoma illahirin jikinta.
A ɓangaren ma'aikatan gidan musamman su Bahijja kusan suma a sumen suke da mamakin Kandalar, duk da dama a cikin shock ɗin ganinta ma suke a gidan kasancewar sunji ƙus-ƙus ɗin da akeyi a gidan na wai Boss ɗin su ya mata fyaɗe. Duk da mafi yawansu basu yarda ba sudai, dan wani irin kima da mutuncin Maash suke gani a rayuwarsu saboda ya musu abubuwa da yawan gaske da suka rasa a gidajen iyayensu...
🩸🩸🩸🩸
Koda ya shiga ɗakin kai-kawo ya dinga yi tamkar mai safa da marwa kafin ya ɗauki waya ya danna kira. Kasancewar ba number Nigeria bace ya jima kafin ya samesa. Dan har ma ya fara tunanin komawa ta WhatsApp suyi video call, sai kuma akai sa'a ta shiga. Bugu biyu aka ɗaga, bai tsaya ko sauraren gaisuwar da yaron nasa ke masa da ga can ba ya wani daka masa tsawa.
“Na baka awa ashirin da huɗu na ganka a gabana. Idan ba haka ba, wlhy! wlhy! Sai na saka an yo maka ɗaukar amarya da ga UK zuwa Nigeria. Wawa kawai, har ni zaka yaudara, ina baka ci da sha da ɗaukar buƙatunka ashe sakarai ka maidani wanda baima san abinda yake ba...”
“Yallaɓai wlhy! Wlhy ba yanda kake zato bane. Ni kaina ina a cikin tashin hankali. Tun ɗazun na rasa ta yanda zan kiraka na sanar maka yaron nan ya gudu. Wlhy sai da aka tsara komai dan a yanzu haka akan yazo Dubai hutawa ne shida abokansa, kuma na sanar maka a ranar. Nima na sayi ticket ɗin tafiya Dubai ɗin kamar yanda kace ama jirgi ɗaya zamu wuce aka samu matsala a airport ɗin, na cigaba da ƙoƙarin ganin na samu next flight sai kawai na tsinta zancen wai Nigeria ya wuce da ga bakin abokin nasa. Nayi yunƙurin biyosan tun a jiya jami'an tsaro suka kamani ko awa ɗaya banyi da fitowa ba. Yanzu haka cikin ƙoƙarin ganin jirgin da zai tashi nan da awa ɗaya dani ne dan na fahimci komai an tsara shi ne har kamani da akayi set-up ne kawai. Amma dan ALLAH yallaɓai ka gafarceni. Ina nan tafe”.
Kasa iya cewa da shi komai Baba prof yayi, sai ma wurga wayar da yay saman gado yay wani irin kaiwa zaune hannayensa duk biyu dafe da kansa dake wani kalar jujjuya masa kamar brain ɗinsa zata wulƙice. Ya jima a haka, sai da yaji bugun zuciyarsa na neman canjawa sannan ya kai kwance. Barci ya sha sosai, sai dai kafinma yayisa ya jima yana sambatun ambaton sunan Ibrahim Alonso da zuri'arsa. Sai da ƙyar barcin yay awan gaba da shi. Bai tashi farkawa ba sai yanzu kusan goma sha biyu na dare. Ya jima idanunsa akan agogon ɗakin nasa tamkar mai lissafa adadin daƙiƙun da suka rage a rayuwarsa, kafin ta miƙa zuwa bayi. A cikin ma ya kwashe lokaci kafin ya fito ya rama salloli sannan ya zura jallabiya ya fito falo.
Tamkar fitowar tasa kuku ke jira, dan tuni ya fito ya jere masa kayan abinci a gabansa kasancewar yasan da dare baya hawa dining cin abinci. Duk yanda yake jin matsananciyar yunwa bai iya cin abincin ba ma, sai black tea ɗin nashi na fama ya buƙaci a kawo masa. Shine ya ɗan samu ya sha. Fitilar falon ya rage batare da kunna tv ba ya zauna shiru yana nazartar abubuwa yanda ya kamata. Dan ɗazun gaba ɗaya a birkice yake, shiyyasa hatta bayanin Commando bakwai komai ya gane ba. Dawowar nan ta Fahad ta matuƙar dagula lissafinsa. Sai batun yarinyar da bai taɓa sake maida hankali kanta a lissafinsa ba tun randa ta gitta tamkar walƙiya a tsakkiyar hadarin daya kankama zai zubda ruwa.
File ɗin da commondo ya kawo masa ya sake ɗauka, ya shiga binsa daki-daki dan ɗazun kamar sama-sama ya duba shi. Sai da ya duba tsaff sannan ya fara lissafi. Tayi aure, an kaita gidan miji, har gidan da aka kaita commando yaje amma babu kowa sai maigadi. Ya binciki maigadi, amma bai samo komai ba, dan babu abinda ya sani face ogansa da yake kira da oga. Abinda ya kawo masa ruɗani a wannan gaɓar shine kwanan amaryar ogansa ɗaya a gidan ta gudu da safe, har tai yunƙurin fasa kansa idan bai buɗe mata ƙofa ba. A binciken Commando bata koma gidansu ba, amma tayi jiyya a wani pravet hospital. Ya bibiyi asibitin amma bai samu komai ba sai sunan likitar data kula da yarinyar tama kawota asibitin, a yanzu kuma bata asibitin wai, bincike iya bincike na commando kuma bai ganota ba ko inda take har yanzu balle ita yarinyar sai iya kawai an mata transfer zuwa Abuja. Abuja wane asibiti? Basu gano ba shima.. Kansa yay wani irin dafewa yana mai furzar da huci. Sai kuma ya jawo waya yay kiran Commondo. Bai tsaya amsa ko gaisuwarsa ba yace ya samesa gida. Kawai ya yanke kiran.
Bako a cika mintuna talatin ciff ba sai ga amintaccensa yazo ya sanar masa Commando yazo yana falon baƙi. Hannu kawai ya ɗaga masa alamar yaje. Bayan ya wuce shima ya miƙe yabi hanyar da zata sadashi da falon baƙin tanan cikin falonsa. Da sauri commando dake zaune a kujera ya miƙe tsaye kansa a ƙasa domin girmamawa. Ba zamu kirashi yaro ba gaskiya. Dan shekaru kam zasu iya tasamma hamsin da wani abu. Sai dai yanayinsa ya nuna lallai a lokacin ƙuruciya anyi rashin ji sosai, a yanzun ma bai zama lallai an bari ba. Nuni Baba prof ya masa kan ya zauna. Babu musu ya kai zaune sannan ya sake gaidashi. Nan ma kansa kawai ya ɗaga masa sai kuma sukai shiru. Kusan minti ɗaya kafin baba prof ɗin ya ɗago yana sauke ajiyar numfashi.
“Commando aikinka yayi ƙyau sosai, bance komai bane saboda rana a ɓace yake a ɗazun”.
“Na sani boss, babu wani damuwa kayi komai ba komai girmanka ne”.
Murmushi Baba prof yayi da gyara zamansa. Sai kuma ya ɗan furzar da numfashi. “Ya akai bincike bai ƙarasa inda nafi buƙata ba. Dan ina son sanin wanene mijin nata fiye da komai”.
“Na sani boss, nima naso nakai har can ɗin amma komai ya datse kansa. Sai dai duk da haka bawai na dakata bane. Na kawo maka wannan ɗin ne saboda naga ka matsu. Amma akwai ƴan uwanta Maza guda biyu zan maida akalar aikina kansu, ai dole dai su san wanene ta aura? Sai shi wanda ya riƙeta shima yana cikin tsarina. Kar har walliyin auren da wahala ya tsira”.
Murmushi mai faɗi Baba prof yayi, dan yanda yaron nasa ke wani magana a ciccije yana birgesa. Kansa ya jinjina da gyara zamansa. “Shiyyasa kake birgeni sosai, dan nasan in har zan damƙa aikina a hannunka banda wata matsala a kai. Yanzu ma inada wani aiki a ƙasa, yana da alaƙa kuma da wannan ɗin da kake yi”.
“A to oga lafiya lau ne. Watso umarninka kawai a shirye nake na cafesa da hannu biyu”.
“Ina godiya. Zan ɗan baka aikin kaɗan a buɗe yanda zakafi fahimtarsa. Ita yarinyar da kake wannan binciken a kanta yanzu haka tana a Maash Mansion ne”.
Wani irin dalalo ido Commando yayi waje. Tare da dafe bakinsa ya ce, “Kan ubancan kai. Amma ta barni naketa walankeɗuwa kamar wani shaho. A to lallai tana buƙatar ɓalli-ɓalli a kan fuskarta kenan”.
Murmushi Baba prof yayi kawai, tare da cigaba da faɗin, “Ai bamu zo nan ba Commando. Abinda nake son kamun a kanta biyu ne zuwa uku. Na farko ina son sanin mi tazo yi Maash Mansion. Na biyu ka tabbatar min da tanada alaƙa da Awwab ne tako wane irin fanni ko bata da? Na uku a cikin gidan tanada alaƙa da wani ne? Misalai, masu aiki, ko cikin masu gidan, ko masu huɗɗa da gidan ta waje. Na ƙarshe wanene ya shigo da ita Lagos dan a matsayin mai aiki take a Maash Mansion”
“Oga duka aikinka masu sauƙine a garan kaima ka sani, sai dai magana ta ALLAH tsaurin a waje guda yake. Nifa kasan in dai sabga da Zakin gidan nan naka a ciki tsoronta nake gaskiyar magana. Ka sani na sani aljani ma nan ya ga Maash ya barsa. Dan duk iskancina na tsawon shekaru yaron nan yakan goge min hadda tsaff. Kaga dai Jaga, duk yanda na gatanta yaron nan daga turashi aiki jikinsa sai da yaron nan ya saɓemin ya koma bayansa. Badan munyi wuff mun ƙaddamar mas ba da yanzu ya buɗe mana aiki fa. Boss kasan da haka ta faru fa babu tantama China Maash zai kaimu a markaɗe namominmu da ranmu a ɗurisa a gwangwanaye a dawo dashi Nigeria a dinga sayarwa matsayin naman tsakkiyar shawarma. Kai kanka yanda nake ganin idanunsa zai iya sawa a masa bandarka...”
“Commando!!”.
Baba prof ya faɗa a fusace cikin daka masa matsanancinyar tsawa.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
......“Kaiyya oga sa'a dai sa'a dai. Kafa san ni a ɓangaren gaskiya ba ruwana feɗewa nake filla-filla. Amma dai tunda baka son ji bari nayi kurumm. Zanje na fara aiki amma dai ka ƙara tunani akan Maash, Nima zanyi tunani muga. Matsalar shi ba mata yake bi ba, baya hawa network kuma, amma da komai yazo da sauƙi ai”.
Gaba ɗaya Baba prof ya gamsu da bayanin Commando. Shi kansa shiyyasa yake a cikin ruɗani akan batun yarinyar nan da kuma abinda ya faru tsakanin Awwab ɗin da ita. Maash baya neman mata, shi shaida ne akan hakan. Sannan akwai wani dalilin da yasa baima kawo cewar shine ya aureta a ransa ba, dan yayi imani da shirinsa a kansa matuƙa. Shiyyasa ko fyaɗen nan har yanzu zuciyarsa bata gama yarda shine ya aikata ba. To amma abinda ya faru a asibiti fa? A gabansu fa yaron nan yay kissing yarinyar (Randa Maash ya samesu a asibiti, su a tunaninsu ma lokacin kissing ɗinta yayi🤣). Dan ɗauka bai wani ɗauketa da muhimmanci ba, hakama kulawa a asibitin, komai zai iya yi dan yana da tausayi. Kai gaba ɗaya shi yama rasa ina zai kama gaskiya..
Waya ya ɗauka har zai dannama Hajiya ƙarama kira sai kuma ya fasa. Saƙo ya tura mata ya kashe wayar tare da miƙewa ya fita. Amintaccensa ya kira suka fita a gidan duk da kuwa dare ne dan har ƙarfe ɗaya ma ta gota....
🤍🌿🤍🌿🤍
Tunda na janyo ra'ayin Fahad muka nufi sashen Ummie ban sake bi takan ahalin gidan ba. Dan ko Hayatu da Hafiz anan suka samemu. Da yake muna a falon farko ne na shiga sashen sai muka baje munata hira abinmu harda Mama Balki. Kamar wasa abota ta ƙullu tsakanin Hafiz da Fahad duk da kuwa Fahad ya girmi Hafiz sosai. Dan koni ma ya girma balle shi. Da alama hakan ya faranta ran Hayatu, dan daga ƙarshe cayay su tashi suje yawo tunda yau boss na hutu. Har zasu fice na ma Hayatu magana. Duk da dai yanzu kunyar abinda na dinga masa nake ji, amma dai na daure na ce, “Yaya Hayat dan ALLAH idan babu damuwa kuma oganka bazaiyi faɗa ba mizai hana a sayo kayan amfani na kitchen ɗin sashensa naga wanda suke ciki basu da wani yawa. Tare da kayan abinci sai na dinga mana girki acan. Naga sam bai damu da abinci ba sai kayan chocolate. Sannan ita kanta Ummie ya kamata ace nike mata abinci hidimar nama Mama Balki yawa. Ga kuma Fahad ma ya ƙaru”.
Sosai fuskarsa ta ƙawatu da murmushi. Ya ce, “Wannan shawara ce mai ƙyai Auntynmu. Kuma naji daɗi kamar yanda nasan Boss zaiji daɗi fiye ma da yanda naji ɗin. In sha ALLAHU ki bamu nan zuwa anjima duk abinda kike buƙata za'a kawoshi. Yanzu hakama zanyi waya da companyn da zasu zo su gyara kitchen ɗin su saka komai daya dace, kafin su gama mu kuma mun haɗo cefanen”.
“Nagode sosai Yaya Hayat”.
“Muke da godiya Auntynmu. Koba komai kwanan nan Yayanmu zaiyi kaurin wuya da tunbi”.
Dariya sosai zancensa ya bani, amma sai na murmusa kawai. Shima fita yay yana murmushin dan su Fahad tuni sun fice abinsu...
Kamar ko yanda ya faɗa ɗin haka ce ta faru. Dan na fita zuwa yin sallar la'asar daga nan na dubasu na samu drivern sa (TJ) da Guard ɗinsa da nake yawan ganinsu tare shima (Shu'aibu) tare da baƙi. Gaisheni sukai TJ ɗin ya bani waya. Jin Muryar Hayatu ya sani sauke ajiyar zuciya, shine yamun bayanin na basu damar shiga tare da masu company da zasuyi aiki. Duk da nayi mamaki ganin yammafa tayi yaushe har za'a kammala? Sai ban musa ba na basu dama ni kuma na shige ciki domin duba shi.
Da sallama na shiga ɗakin kamar mai jin tsoro, ganinsa tsaye gaban mirror yana fesa turare ya sani jin farin ciki. Ɗan kallonsa nayi na ɗauke kaina. Dan fesa turarensa yake kamar ma bai san da shigowata ba. Wannan halin nasa na shariya da ɗaukar kai na ban mamaki. Jinai kamar na watsar da shi nima na wuce abina. Amma sai na daure tunda koba komai na barsa babu lafiya. Muryata can ƙasa batare dana sake kallonsa ba na ce, “Ashe ka tashi, yaya jikin?”. Nai ƙoƙarin wucewa abina. Har na gittashi naji ba'a amsa min ba, sai na tsaya cak, dan magana ta ALLAH ban san wulaƙanci sam. Cikin ɗan yanayin jin haushi na ɗago manyan idanuna na kallesa. A mamakina sai na samu shima ni ya zubama ido. Dan ya daina fesa turaren ma ya jingina da mirror kawai yana kallona. Baki na tura masa tare da juyawa zan cigaba