Showing 285001 words to 288000 words out of 438336 words

Chapter 96 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2217

daga cikin ruwan addu'ain da Malam ya kawo ce kuma ruwan zam-zam ne a ciki na miƙa masa bayan na cire murfin. Babu musu ya amsa yasha sosai. Sai ya jingina da kujerar ya lunshe idanunsa a hankali yana wani irin sauke nannauyan numfashi. Har cikin raina naji daɗin saukar tasa, sai kawai na sake kwantowa akan hannun nasa nima na lushe idanun ina sauke nawa numfashin. Mun jima a wajen har na fara tunanin barci yake kafin ya tada motar, sai da muka fara tafiya na fahimci mugun zagaye yayo damu ashe, nafayi mamakin ganin ranar bamu daɗe ba mukaje bakin ruwan, amma yau mun gagara kaiwa gida da wuri.....

❤️🪴❤️🪴❤️

Alhamdullah Halime karatu dai ya kankama, dan kuwa dai ta fara zuwa makaranta. Kasancewar kanta fresh yake kuma akwai karatun addini sosai a tattare da ita sai na bokon yake shiga cikin sauƙi. Gashi ta saka kanta ga kuma zugar aunty Zakiyya a gefe na tasiri. Shi kansa Abba har mamakin brain ɗin Halimen yake. Dan in ya dawo gida tata damunsa da tambaya akan kaza da kaza. Kai har Auta da gantalin uwarsa ya fara jawo hankalin sa ga Halimen dake bashi abinci ita babu ruwanta zama take ya koya mata abu.
Ba a karatun kawai ba, rainon cikinta ma na tafiya yanda ya kamata. Dan yanzu kam laulayi ya ragu sosai. Sai cika da kara ƙyawun dake firgita Mom kawai take zubawa. A hankali iya shegenta ya fara dawowa sabo fil a gidan yanzu tun randa ta kama Mom na zuba magani a abincin Abba. Aiko ta fara raira waƙar, (Ashe makashinka yana nan tare dakai duk inda kake ya bika ga kaina ka riƙe min alƙawari karka sake Imamu na) tun Mom na shareta har dai ta tsargi kanta ta tanka mata. Tana shirin shaƙota ta daka uban tsalle gefe da zazzaro ido waje.
“Ni Halime, Yaya rufamin asiri ina ni ina dambe da ɗan masu gida kwance a mahaifa. Irin wannan jan salalan tsiya ke mai biyar rigis kamar kin saro a kurmi ni ɗan ɗayan ma dako iskar duniya bata sha ba ko ya sha na biye miki ya watse. A'a rabani watsiya Yaya Jalilah”. Ta mata kallon banza ta shige ɗaki. Ji Mom tayi kamar ta shaƙo wuyan Halime har cikin ɗakin, wannan yarinya ita dai ta zama mata jaraba da bala'i. Ji take kamar ta wanke banza da tafasasshen mangyaɗa ko ruwan zafi kowa ya huta. Ga damuwar rashin jin Baby ta fara taɓata. Ga batun Musaddiq yi take amma har yanzu babu wani motsi. Hakama Samraah yanzu kusan kullum sai taji suna waya da Abba ko Halimen. Nasara ɗaya taci shine maida aurenta da Abba yayi. (A haukarta aikintane yaci Abba ya maidata🥱).

✨✨✨✨✨

Isowarmu gida da abinda na tarar ya goge min dukkan abinda muka shigo da shi na damuwa. Sosai nayi matuƙar mamaki da ganin irin gyaran da akama sashen namu. Daɗin daɗawa yabi shawarata ya dawo da Ummie sashensa. An gyara mata nan ƙasa shi kuma nasa ɗakin har ma da nawa a yanzu suna sama. A saman ma katafaren falo ne ashe bana wasa ba. Sai bedrooms guda uku. Yanda aka tsara shi da kayan more rayuwa ya matuƙar saka zuciyata yin rauni har sai da ƙwalla suka cika min idanu. Rasa ma abinda zance masa nayi, sai kawai naita kallonsa. Gira ya ɗan ɗage mun alamar kallon fa?.
Kasa jurewa nayi naje na faɗa jikinsa kawai na saki kuka. Ban taɓa sanin zanga irin wannan ranar ba. Ban taɓa sanin zan iya bama mutum kamar Maash shawara ya amsheta ba. Sosai ya rungumeni shima batare da yace komai ba. Mun jima a hakan kafin ya ɗagoni, a cana ƙasan maƙoshi ya ce, “Kukan bai isa ba?”.
Maimakon amsa masa sai na sake sakin kukan. Hancina ya ja kaɗan da sake faɗin, “Nifa ba'a min kuka”.
“Toni ba kai nake wa ba ai”.
Na faɗa ina tura baki.
“Humm” kawai yace..

Da dare ina ɗakin Ummie na nan sashen nasa a yanzu, ko nace ɗakinsa na da dan daga su biyu ne kaɗai bedrooms anan ƙasa dama muna ɗan hira da Mama balki dake ƙarasa saka kayan Ummien a closet nake tambayarta asibitin Hajiya ƙarama na waye?.
Kallona tayi da mamaki, sai kuma tai ƴar dariya. “Miyasa kika tambaya?”.
“Haka nan Mama. Kawai ina son sani ne. Dan naga asibitin na kuɗi ne kuma kamar itace ke controlling ɗinsa.”
Ajiyar zuciya Mama ta ɗan sauke. Kafin ta cigaba da faɗin, “Asibitin Ummie ne. Dan itace ta gina mata shi da kanta. Da farko ƙaramine, daga baya Abbie ya gyarashi da sake faɗaɗa shi. Shima kuma Alhaji ƙarami ya sake ƙawata shi a shekarun baya. Irin kulawa da shaƙuwar dake a tsakanin Ummie da Hajiya ƙarama bayan haihuwar Alhaji ƙarami ta damƙashi a hannun Hajiya ƙarama ɗin. Sai yazam itace mai kula da komai kuma har yanzu ba'a taɓa canjawa ba. Dan a dalilin asibitin ne ma ita Ummien ta sake tura Hajiya ƙarama ta ƙaro karatu har ƙasar India, daga Nurse ta koma cikakkiyar likita”.
“Kenan yanzu kuɗin shiga da fitar asibitin a ƙarƙashin ikon Yaya Awwab suke?”.
“Eh to, haka ba haka ba gaskiya. Dan duk da asibitin na kuɗine kusan komai ana yinsa ne kamar ƙyauta. Sai dai a dalilin kayan aiki da suke da shi yasa aka ware vip saboda masu hannu da shuni. Sai ya zama kuɗin ana amfani da su ne kuma ta hanyar taimakawa marasa lafiya musamman waɗanda tai tsamari sai an fita da su ƙasashen waje. Sai kuma biyan ma'aikata albashi da ɗan abinda asibiti ke buƙata na gyara, amma bana jin gaskiya Alhaji ƙarami na amfani da komai na asibitin ne. Nasan duk wannan nan ne a dalilin mahaifinku tun asibitin bai kai haka ba. To daga baya dai bayan rasuwar su shi da Abie da kuma faruwar ciwon Ummie ban san mike faruwa ba gaskiya, har ya faɗaɗawa zuwa yanzu ban sani ba ko suna akan wannan tsarin. Sai dai ko zaki tuntuɓi Alhaji ƙarami”.
Kaina na jinjina mata cike da gamsuwa. Nasan kowa zai yi mamakin wannan tambayar da nayima Mama, to akwai dalili, abinda ya faru yau ya dawo min da wani abu da na ɗan taɓa ji sanda ina asibitin. Ana gobe za'a sallameni kusan ɗaya na dare fitsari ya farkar da ni. Bayan naje nayo sai nake jin duk kwanciyar ta isheni. Na buɗe ƙofa na fita dan na ɗan tattaka ko anan inda ɗakunmu suke ne. Ɗan tattakawar yasa naji daɗi sosai har ta kaini da ɗan fita. Shiga nake ko ina batare da nasan ta inda nake ba, har na gota wani ƙofa na dawo saboda jin ƙusƙus ɗin da ake yi a ciki kamar kuma ana faɗa wani kuma na kuka. Ta jikin windown na je naɗan maƙale. Sai naji muryar mace ce ke faɗan mai kukan ma mace ce.
Mai kukan ke rantsuwa da ALLAH ita wlhy bata san yanda akai ba, kuma ita ba'a bata wani kuɗi ba akan hakan. Matar ta sameta ne kawai ta tambayeta aikin mi akama wadda suka fiddo shine ta sanar mata an cire mata appendix ne. Iya kuma abinda tace da ita kenan matar ta juya ta tafi.. wani irin mari aka sauke ma mai kukan da ni kaina saida na zabura, dan har tsakiyar kaina na jisa kamar ni aka mara. Cikin masifa wadda tayi marin da zagi ta ce, “To ubanki yace ki gaya mata koma mi aka cire ɗin. Nawa ake biyanku albashi a asibitin nan, a matsayinku na waɗanda na aminta da su muna aiki tare nawa nake baku a duk ƙarshen wata? Ya ninka abinda asibiti ke baku. Amma har kina da bakin faɗin abinda ba'a tambayeki ba. Kinga kenan zaki faɗi abinda ma yafi haka nan gaba ko?”.
“Wlhy a'a maa. Dan ALLAH ki gafarceni wannan ma kuskure ne. Na kuma miki alƙawarin bazan sake ba. Kuma....”
Tafiya da naji kamar a bayana yasa na zabura na bar wajen. Zuciyata tata min kai-kawo da son jin ƙarshen zancen nan amma dole na haƙura na koma wani waje na maƙale, can sai ga yarinyar ta fito tana sharar hawaye, naji daɗin ganin fuskarta, amma ban mata magana ba na bar abin akan saina warke. Nata jujjuya batun da cuɗawa da kwancewa amma ban iya na haɗa komai ba. Sai kawai na binne maganar a raina na cigaba da harkoki na, koda muka dawo gidan abubuwa kuma sukai yawa sai na manta. Sai yau ne da naji yana batun tura wani yin aiki asibitin matsayin bincike abin ya dawo min a rai. Lallai akwai abinda ke faruwa a asibitin nan, amma yanzu in sha ALLAHU da yayi tafiyar nan nima zanyi nawa hoɓɓasa.q....
Maganar Mama ta katse min tunani. Firgigit na kawo numfashi tare da sauke ajiyar zuciya. Koda na ɗago sai naci karo da shi tsaye ya zuba min ido kawai. Numfashi na ƙara saukewa tare da masa sannu. Dan tun bayan dawowar mu baifi da ƴan mintuna ba ya fice sai yanzu yake dawowa kusan sha biyum dare. Bai ce dani komai ba, sai hankalinsa da ya maida kan Ummie dake barci........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5


.......Shigowarsa gidan kenan yaci karo da commondo na jiransa. Duk da a gajiye yake tiɓis ga dare yayi hakan bai hanashi zaman saurarensa ba. Kamar ko yaushe cikin girmamawa commondo ya gaida shi. Tare da ɗorawa da bayaninsa.
“Boss bayani ne nazo da shi dan na kasa haƙurin haɗiyewa har na kammala binciken nan.”
Cikin ƙara nutsuwa Baba prof ya ce, “Tofa ina saurarenka miya faru?”.
“Akan ahalin yarinyar nan ne, brothers ɗinta biyu da nake faɗa maka bincike ya tabbatar da suna anan Lagos. Ɗaya makanike ne. Watanni bakwai da suka wuce sabon companyn Maash dake Kano sun ɗauke sa aiki........”
“Whatttt!!! Maash Company?”
“Humm boss ai ban kai the end ba. A yanzu haka zancen da nake maka ma sun turashi karatu ƙasar ƙetare, ban dai gano ƙasar ba. Kuma jirginsa ta nan Lagos ya tashi ma. Abinda kawai bamu tabbatar ba shin da sanin Maash ɗin ne ko kuwa companyn ne tunda sun ɗauki yara kanikawa aiki da yawa bashi kaɗai ba. Shi kuma ɗayan yana cikin Lagos ɗin nan har yanzu, a ina yake shine ban sani ba. Amma dai inaga ka bincika a cikin Maash Mansion tunda har yarinyar na gidan to tabbas shima dole za'a sameshi a ciki”
Rasa ma abin cewa Baba prof yayi tsabar shock ɗin da yake a ciki. Da ƙyar ya iya motsa hannunsa ya ɗauki wayarsa domin tabbatarwa. Layin Hajiya Mammah ya kira. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. Ko takan gaisuwar da take masa bai bi ba. Kai tsaye ya ce, “Nafisa! Kuna da baƙi a gidan nan ne daga sati ɗaya zuwa yau?”.
Ɗan jimm tayi alamar tunani, sai kuma ta ce, “Eh tabbas kamar haka kam Baba. Naso ganin baƙon saurayin yaro a rikicin faɗan shekaran jiya na Fahad. Inata so nai magana sai abubuwa suka ɗauke hankalina. Yaron ma kamar yana kama da yarinyar nan matar Hayatu. Dan ni da farko ma wlhy na zata itace sai da na sake kallonsa naga namiji ne shi. Ban kuma sake ganinsa ba tun ranar sai yau ɗin nan. Nama kira ka ɗazun na faɗa maka iskancin da yaron nan ya ƙirƙira. Ashe gyaran da yake yi uwarsa zai maida sashen nasa. Ɗazun nan na dawo su Azizat ke sanar min ai an maida Hajiya Babba sashen Yayansu. An kuma kwashe kayan sashenta duka da alama aiki za'ayi”.
Ita ke bayanin amma zuciyar Baba prof ke bugawa da sauri-sauri. Babu shiri ya yanke kiran tare da dafe kansa dake wani kalar masifar juya masa. Cikin mamaki Commando ke tambayarsa ko lafiya? Bai amsa masa ba har tsawon lokaci. Kafin ya miƙe yana faɗin, “Kaje zan neme ka. Ance min akwai yaro a gidan zanje na bincika da kaina”.
Miƙewa kawai Commando yayi, dan yasan idan ran ogan nashi ya ɓaci baya son ko magana. Amma idan ya huce da kansa ma zai iya kiransa a waya koda a daren yau ne...

Da ƙyar Baba prof ya iya kai kansa ɗakin barcinsa. Yana isa ya wani zube a gado hannunsa dafe da ƙirjinsa. Wani irin zafi mai tururi yake jin yana masa sosai. Dan ko iya haka bincike ya tsaya ta tabbata Awwab shine ya auri yarinyar nan?. Amma ta yaya hakan ta faru? Yaya akayi? Yasan wacece yarinyar ko kuwa shawarar daya bashi ce yasa shi komawa ya auretan? To amma idan har hakanne miyyasa zai koma ya aureta bada saninsu ba? Sannan mizai sa ya ɓoye yayin auren nata a matsayinsu na iyayensa? A barsa ma ya ɓoye ya aureta, minene na shigo da ita gidan matsayin mai aiki har ya ɓoye musu wacece ita? Dolene yana buƙatar bincikar Mu'azz kenan a wannan gaɓar, dan yasan ko zai mutu Awwab sai ya gadama sai masa bayani. Karfa yaron nan ya zame masa ya kashe maciji bai sare kansa ba. Dan abubuwa sun fara canja kansu a tsakanin shi da shi tun akan zancen buɗe Companyn nan na Kano. Idan har baiyi ƙarya ba rabon da Awwab ya ɗaga waya ya kira shi har ya manta. Sannan yanzu sam baya sanin al'amurrasa kamar da da kowanne motsinsa sai ya sanar masa ko neman shawararsa. Mi hakan ke nufi kenan? Lallai yana buƙatar ajiye kwalaben giya ya dawo a hankalinsa. Dan ada farko tunaninsa na nuna masa kawai dai Awwab ɗin yayi busy ne a tsakanin nan, to ashe ba haka bane. Eh dole a yanzu yace ba haka bane. Dan idan ya haɗa 1+1 fa zai iya samo amsar tambayarsa. Anya kuwa yaron nan Jaga bai jiƙa musu aiki ba kafin mutuwarsa. Dole ne akwai abinda Commondo bai sani ba, dan a dalilin Jaga ɗin kawai suka samu ɓaraka.....

Akasin lissafi baba prof 🥱😎.

🪴🪴🪴🪴

Washe gari da kaina na haɗa mana break fast. Na gyara sashen da taimakon Mama duk da inata hanata amma taƙi. Har nayi wanka na gyara jikina bai dawo gidan ba tun fita motsa jiki da yay bayan dawowarsa massalaci. Ummie naje na bama abinci da sabbin magungunan wajen Malam. Ina a haka sai ga Fahad da Hafizzullah. Sanye suke da sports wears suma. Hakan yasa na gane suma fita sukai motsa jikin kenan. Bayan mun gaisa nake tambayar Hafiz batun komawa school. Ya ce min yayima Yaya Hayat magana amma yace ya dakata zai koma a acikin satin nan in ji Yaya Awwab. Ban sake cewa komai ba suka fita da shirin zuwa suyi wanka su dawo suyi break fast. Bayan fitarsu shima na fita duba shi. Sai na samu ya dawo har ma ya shiga wanka. Kofar bayin na harara, tare da fitowa a ɗakin baki ɗaya, yanzu daban zo ba bazan san ma ya dawo ba kenan. Ɗakina na koma na ɗan ƙara gyara inda zan gyara a kwalliyata sannan na sake fitowa. Ina ƙoƙarin sauka ƙasa sai gashi ya fito. Tare muka sauka ƙasan, direct kan dining dana shirya abinci ni na wuce, shi kuma ya leƙa Ummie. Bai jimaba ya fito. Da kaina naja masa kujera ya zauna sannan na fara buɗe masa abinda na shirya. Kallona kawai yake yi baice komai ba. Baki na ɗan tunzura, sai ya ɗauke kansa kawai ya nuna min doya. Ban damu ba, dan na fahimci yau yan miskilancin ne a kusa. Koda yake tun ma juya dai ransa a ɓace yake. Dan kusan raba dare yay yana aiki, na farka kusan 3 na gansa kuma yanata salla. Ina gama saka masa nima na saka. Dai-dai nan su Fahad suka shigo. Ƙoƙarin ajiye spoon yake nai saurin dafe hannunsa. Murya a raunane na ce, “Dan ALLAH kada ka tashi, ka daure kaifa uba ne. Sai kana ƙoƙarin tausar zuciyarka kaita karanta Hasbinallahu wa-ni'imal wakil da izinin UBANGIJI babu abinda zai faru.”
Baice min komai ba, amma bai tashi ba. Har cikin raina naji daɗin hakan. Dan haka na maida hankali kan Fahad da shima suke gab da zuwa ya juya zai koma da alama sai yanzu ya lura da shi. “Yaya Fahad!”. Na kirashi kamar zanyi kuka. Tsayawa yayi, sai dai bai juyo ba. Cigaba nayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login