Showing 189001 words to 192000 words out of 438336 words
can side ɗin hannunsa ɗauke da blanket ɗin dake a gadon ya lulluɓa mata dan yanda ta takure waje ɗaya yasan sanyin acn nan ne ya takurata. Shi kuma harga ALLAH bama zai iya zubar da kansa ya tashe ta ta koma side ɗinsu ba. Tunda zuwa yanzu ya gane a side ɗin Ummien sa take kwana. Dan baya ma jin ta cika sati a biyu tabar kwana a side ɗin masu aiki......
💞✨💞
Duk yanda Mom taso amfani da maganin nan hakan ya gagara, dan Halime ta kafa ta tsare kamar ta fahimci mi take shiryawa. Gashi koda ta kira Abba akan itafa sai dai a raba abinci Halime tayi nata ita tayi nasu ita da yara kai tsaye yace bai amince ba. Daga ƙarshe ma sai gashi ya dawo gidan. A gabansa Halime ta gama girki ta ɗibar musu ita da shi ta samo kula mai ƙyau kuma a kayanta ta zuba wani. Koda Abba ya tambayeta na waye, kai tsaye ta sanar masa na “Yaya Musaddiq ne. Yana babba a gida amma aita bashi abinci a wulaƙantaccen kwano bayan shike cefanen. Ni ba haka naga su Gwaggo nama su Yaya Buhari ba a gidanmu”.
Shiru Abba yay yana kallonta dan ya gagara yin magana. Sai ma wani nauyi ne yaji kansa ya masa tamkar Musaddiq ɗin na gabansa. Wannan abu ya ƙonama Mom zuciya. Tako shiga surfama Halime zagi, amma ko tari ƙinyi tai, sai da taga zagin na neman zama na fitar hankali ta fashe da kuka. Hankali tashe Abba yay kanta yana tambayar ta lafiya. Kukan ta sake fashewa da shi sosai. “Innata na tuna, tana cikin kabari amma ana zaginta. Kaicon wannan rayuwa, ban ja mata addu'a ba sai zagi, gaskiya bazan iya zaman gidan nan ana zagarmin mahaifiya ba”.
Rikicewa Abba ya sake yi, tuni ya manta da wata Mom a wajen ya kama Halime ya rungume. “Haba Halimatussa'adiyya na, ke da barin gidan nan ai sai dai in mutuwa. Kiyi haƙuri ai duk wanda ya zagi wani iyayensa ya zaga. Karki sake faɗar haka kinji, ALLAH yay miki albarka”.
“Amin nagode _my Rabon alkairi_. Na kuma yarda da kai bazan sake damuwa ba. Ai lobiyu irin kamar kainuwar tafkin bayan gidanmu ɗin nan”. Ta ƙare maganar da fakar idon Abba tai ma Mom da tai mutuwar tsaye sagale tana kallonsu. Sai kuma ta wani sake narkewa jikin Abban tana shashashar kukan ƙarya. Ai tuni Abba ya sake rikicewa, hannunta ya kama tare da ɗaukar kular abincin Musaddiq data zuba ɗin suka shige ɗaki yana sanarma Mom ga nasu nan a tukunya ta ɗauke su sun shige. Rasa ma abinyi Mom tayi, sai kawai taji hawaye na rige-rigen sakko mata. Shiru tai tsaye a wajen hawayen na tarara, tana ɗagowa suka haɗa ido da Halime na leƙenta ta window tana dariya. Gwalo tai mata dayin fari da ido ta saki labulen.
Yuuu Mom taji jiri na neman ɗibarta, har sai da ta kaita da dafe bango zuciyarta na mata zafi kamar zata buga. Wai ita Jalilah dake juya gidanta yanda take so, idan ta bama Imam umarni har rawa jikinsa yake don ganin ya cika mata akan lokaci. Amma yau a gabanta yake rawar jiki akan yarinya ƙarama sa'ar ƴarta har yana faɗa mata magana a kaikaice wai wanda yay zagi iyayensa ya zaga. Kai wane irin juya baya duniya ke son yimata ita kuwa a rayuwar nan....
To bari na tayaki tambaya momcy🤣🥱
💞⭐💞⭐💞
A ranar ni na samar da Number, na kuma tura saƙo ga Maash ta hanyar yaron mijina, amma ita har tsawon sati tana fakon wayar Mansoor, randa ta samu kuma tace bataga video awayar Mansoor ɗin ba iya bincikenta. Hankalinta duk ya tashi, amma sai na kwantar mata da shi ta hanyar tunatar da ita ai in shi babu a wayar tasa ya goge ko ya kwashe yarinyar nada shi. Bai kuma zama lallai ace an rasashi ta wajenta ba. Ta gamsu da zancena, dan haka tace nabar komai a hannunta zata samo video ɗin. Amma ya kamata a fara turama Maash saƙo fa kafin samuwar video dan guri nata ƙurewa kada wani ya rigamu. Ta bani dariya sosai, dan son kuɗin Aunty mai lasisi ne. Na yarda da shawarartata duk da ban gaya mata na fara turawa ba, dan haka a ranar muka fara turama PA ɗin Maash saƙo. Munyi hakane saboda saƙon zaifi isa garesa fiye da mu tura a wayarsa. Koda muka tura dai shiru babu wani reply har tsawon kwanaki, dan haka muka sake turawa. Anan ma babu amsa ga video ya gagara samuwa a hannun budurwar Mansoor. Sai kawai wani tunani yazo min. Munfa riga mun danganta video da ita yarinyar, Maash kuma ba sakarai bane zai iya bibiyarta. Gashi mu kuma babu video ma a hannunmu. Sai kawai muka yanke shawarar kidnapping ɗinta. Komai kuwa yazo mana cikin sauƙi da taimakon maigadi na dana bama dubu ɗari. Sai dai abin takaici babu video a wayar Samraah. Munyi-munyi kuma ta bada shi amma taurin kan yarinyar taƙi badawa........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_
......Muna akan haka sai kawai ga reply PA ɗin Maash a randa muka aika saƙo na uku. Akan an amince za'a bamu 500m, amma da sharaɗin sai mun bada footage ɗin nan sannan a cika mana. Munta nazari akan hakan da tunanin akwai talala a batun, daga baya aunty tace babu abinda zai faru in sha ALLAH. Wannan ƙwarin gwiwa ya sakamu zuwa muka buɗe sabon account da sunan mai gadina, kai komai ma da nashi akai amfani har account ya samu muka turama Maash. Kuɗi kuwa a ranar suka shigo. Munta murna da ganin madarar kuɗin nan ziryan, sai hakan ya ƙara mana ƙaimi sosai.
Cikin abinda bai fi mintuna talatin ba muka cire kudin zuwa account ɗin aunty, shi kuma wancan muka rufesa gaba ɗayansa. Ga kuɗi sun samu amma video ya gagara samuwa a garemu. Sai ma wani tsautsayi daya so giftawa. Yarinyar ta samu nasarar cirar waya a jikin mai tsaronta tai kiran da aiki ya kusa buɗe mana. ALLAH ya taimakemu dai-dai sanda Mansoor ke kiran Attahiru akan ya kira dcp ya sanar masa Aunty na tare da shi. Shine tai kiran yaron namu akan yayi maza yabar gidan da yarinyar kada kuma ya kuskura yabar wani abu a gidan. Hakan kuwa akayi, sai dai labarin ya canja kansa a dalilin satar data saci sata. Dan kuwa dai an tare yaronmu an ƙwace Samraah, shima kuma anyi ram da shi. Mun shiga tashin hankali da baida misali, musamman ma Aunty, dan kuka ta dinga min a waya kan na rufa mata asiri dan ALLAH kada wanda yaji wannan magana. Niko na tabbatar mata zanyi hakan amma da sharaɗin bayan auren Mansoor da Samraah da sati ɗaya zamu saka ya saketa ya auri Husnah.
Tace ta yaya?.
Na amsa mata da zamu bar Mansoor ya auri Samraah ne dama dan mu amshi video ɗin hannunta. Da zarar mun amsa zamu ƙulla mata sharrin da bama shi kaɗai ba kowa sai yaji ya tsaneta. Ta jinjina al'amarin tare da sanar min ita ba itace abin ji ba Yaya ne da Mansoor. Niko nace mata karta damu komai zamu yisa a tsare ne, yanzu dai mu jira Samraah ta fito dan a lokacin bamu san Maash bane ya amsheta mun zata ƴan sanda ne. Sai daga baya muke jin ba ƴan sandan bane sai kuma hankalinmu ya sake tashi. Muna cikin yanayin ƙullawa da kwancewa sai ga Samraah ta fito. Farin ciki babu irin wanda bamu yi ba, dan mun san plans ɗinmu zasu cigaba da tafiya kenan.
Mun cigaba da tsarinmu yanda ya kamata ana gobe ɗaurin aure kuma sai komai ya canja daga yanda yake. Dan mun tafi amsar kayanmu wajen tela da wanda amarya zata saka da ba'a kai ba akai ram da mu....
💞✨💞✨💞
Shirin kwanciya yayi, lokaci-lokaci yana ɗan jan ƙaramin tsaki dan yunwa yake ji. Da farko chocolates ɗin nashi na fama ya ɗebo, sai kuma ya maidasu yana jan gajeren tsaki. Harga ALLAH abinci kuma yafi buƙata dan rabonsa da cin wani abu matsayin normal abinci 2days kenan. Daga kayan fulawa sai fruits da chocolate yake zubama cikinsa. Saukar idanunsa akan tray ɗin data shigo da shi ɗazun ya sashi nufar wajen. Kwanikan ya buɗe tamkar wanda akaima dole. Dan sai faman yamutse fuska yake da ɓata rai. Fruit salad ɗin daya ɗan sha ɗazun ya zuba ma ido da gasashen naman kaza daketa ƙamshi alamar zai yi daɗi. Harya maida ya rufe kamar bazai ci ba sai kuma dai ya sake buɗewa dan gwara yaci koda kaɗan ne so yake yay barci kada yunwar ta takurasa. Saboda in har yaji damuwa da yunwa tofa da gaske yunwar yake ji. Duk yanda kuma yaso riƙe kansa bashi yiwuwa.
Ya tsakuri kazar zai kai baki akai kiran wayarsa. Yaso sharewa sai dai ganin Abubakar ne babban yaronsa ne shima dake riƙe da harkokinsa a ƙetare ya sashi saka ta hannunsa daya ɗiba a bakin nasa yana ɗaukar wayar. Yaci kusan lauma biyar yana wayar, sai da ya kammala magana da Hayatun ya fahimci ko bissmillah baiyi ba. Kansa ya dafe yana yamutse fuska. Sai kuma yayi bissmillar sannan ya cigaba da ci. Da yake yunwar yake ji sosai yaci ya kuma sha fruit salad ɗin shima sannan ya koma bathroom yay brush ya fito. Kansa tsaye ya nufi gadon zai kwanta sai kuma ya tsaya cak yana kallonta. Gefen lips ɗinsa ya ɗan ciza sai kuma ya ƙarasa ya ɗauki pillow biyu ya koma saman sofa ya kwanta. Bawani yaji daɗin kwanciyar bane ba kasancewar bai saba kwanciyar a hakan ba. Iska ya furzar kaɗan tare da lumshe idanunsa kawai.
Barcin ya ɗan jashi da nisa kaɗan saboda gajiyar da yayi aka fara masa mintsine-mintsine a jiki. Idanunsa ya buɗe kawai batare daya motsa daga kwancen da yake ba. Tun yana ɗaukar al'amarin wasa har dai yaji yau fa dabance, a farko ya ɗauka normal ne kamar kullum, dan ya jima yana fuskantar irin wannan yanayi amma jarumtarsa na tattare komai ta bizne saboda ya riga ya sakama ransa in har ba Ummie ta samu lafiya ya ganta a farin ciki ba baya jin yana da wani spiece a rayuwarsa na kallon wata mace da wannan siffar. To tayaya ma zai yarda hakan ta kasance. Ace mahaifiyarsa na kwance cikin lalura mai ban tashin hankali shi kuma hankalinsa nakan samawa gangar jikinsa abinda take buƙata. Kai impossible. Cikin cizar lips ya sake lumshe idanunsa a yanayin tilastama kansa kamar yanda ya saba. Dan shi bai taɓa shan wani magani domin hana faruwar haka ko samun sassauci ba. Ya dai riƙe azumi tare da takure kansa matuƙa saboda jarumta. Sai idan al'amarin yayi tsamarine yake amfani da lemon tsami bisa shawarar abokinsa Taj.. daga ba hakanba baya shan komai.
Cikin ƙanƙanin lokaci wata irin zufa ta gama jiƙe masa jiki, amma bawon ALLAH ko motsawa baiyi ba yana daga kwancen yana sauraren hukuncin UBANGIJI. Tsanantar al'amarin ya sashi yunƙurawa a karo na farko ya tashi zaune haƙoransa ya datse da lips ɗinsa kamar zai huda shi. Zaman ma gagararsa ya nema farayi, ya miƙe tsaye zuciyarsa na tsananin bugawa. Taku ɗaya biyu ya tsaya cak, saboda ƙullewa da cikin yay sosai ƙafafun ma kansu riƙewa suke. Ga idonsa ya sauka akan wadda ke kwance a saman gadonsa tana barcinta hankali kwance. Duk da ba ganin fiskarta yake da ƙyau ba saboda ƙarancin haske yanda tai luff cikin lallausan blanket ɗinsa ya tabbatar masa da hakan. Kansa ya kauda, sai kuma ya nufi Bathroom da ɗan yanayin sassarfa na tilastama kai jarumta. Babbar shower ɗin mai ƙarfi ya sakarma kansa. A cikin ƙanƙanin lokaci jikinsa ya gama jiƙewa sharkaf, sai dai ta saman kansa yayi amfani da shower cap gudun kada ruwa ya taɓashi yay mura. Dan shi bashi da wahalar yin mura. Sosai ruwan ya dakesa amma baiji komai ya canja ba. Sai ma sake ruruwa da yake jikinsa na sake tabbatar ma da yau ɗin fa yau ce. Cire kayansa yayi ya fito bayan ya ɗaura alwala. Sai dai raka'a biyun farko ma da ƙyar ya iya kaisu saboda yanda al'amarin ke sake ta'azzara. Shiru ya cigaba da zama a saman sallayar, kafin kuma dai ya miƙe da ƙyar. Saman gado ya tafi da nufin hawa sai kuma ya tsaya cak, karan farko ya zubama fuskar Samraah dake shaƙar barcinta a nutse idanunsa da suka juye gaba ɗaya. Ba wani tar-tar yake iya ganinta ba, sai dai yanayin ƙarancin hasken sai ya ƙara ƙawata masa ƙyawunta abinka da wanda ke cikin yanayi. A hankali ya fara takawa tamkar hawainiya mai tsohon ciki. Ya kai hannunsa duka biyu yaja igiyoyi biyu dake ɗaure da net ɗin da aka zagaye gadon tamkar rumfa. Cizar lips ɗinsa ya sakeyi yana mai duƙar da kansa tamkar wanda ke jin abinda zai aikata ba dai-dai bane. Har ya motsa jikinsa da nufin komawa sai kuma ya sake tsayawa cak sakamakon nauyin da ƙafarsa tai masa. Ga zuciyarsa na ƙara tabbatar masa da (Awwab matarka ce fa, ALLAH ya halatta maka miyyasa zaka cutar da kanka kaƙi karɓar ni'imar da yay maka. Kaje tareta, kaje) Da wani irin tashin hankali ya tura yatsunsa cikin sumar kansa ya harmutsata ya furta, “Ya rabbah Ummie! Ummie! Na, ban mata adalci ba. My ALLAH help me! I beg you”.
A dai-dai nan Samraah tayi juyi, bargon daya rufa mata har wuya ta janye ƙasa alamar ya isheta. Tamkar wadda ake juyawa da remote ta juyo sosai ta inda yake tana facing ɗinsa. Saukar idanunsa a saman ƙirjinta ya sashi runtse idanunsa da ƙarfi tare da cije lips ɗinsa har sai da ya fasashi da haƙori. Sai kawai ya zube a saman gadon hannayensa duk biyu dafe da kansa. Tsawon mintina ya ɗauka a hakan kafin zuciyarsa ta gama yanke masa shawarar mafita. Fitilar dake cikin gadon ya kunna tare da haurawa gaba ɗayansa.
Cikin barci na dinga jin saukar numfashi mai ɗumi a saman fuskata. Sosai zuciyata ta yanka na buɗe idanuna. Tar-tar na saukesu akan fuskarsa data gama canjawa zuwa yanayin da ban taɓa ganinsa ba. Sake faɗuwa gabana yayi na waro idanun gaba ɗaya a kan fuskarsa. Idanunsa dake a kaina fes ya lumshe a bala'in slowly sai kuma ya sake buɗesu cikin tsakkiyar nawa. Yanzun kam kasa jurewa nayi, cikin rawar murya data lips na furta, “Na shiga uku Awwab minene haka kake y.....”
“Shiiii!!!!” ya faɗa yana sake matso da fuskarsa daf-daf da tawa tare da ɗaura yatsarsa saman lips ɗina dake rawar tsorata. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da zama low can ƙasan maƙoshinsa, ta kuma shaƙe ya furta, “Bana son surutu”........✍️
________________
*Aleenah’s Refreshing Scent*
Ta kawo muku ingatattun turaruka na ruwa (perfumes), oil, Humra, Turaren wuta and more. Kunsan kamshi dai rahama ne, ingantaccen kamshi me rike jiki da Kaya me sa nutsuwa da shiga taro cikin kasaita.
Ina hajiyoyi, uwargida, Amare da kuma masu niyyar shiga daga ciki? don’t afford to miss this golden opportunity.
Aleenah’s refreshing scent ta kawo muku kayan kamshi masu kyau, inganci da kuma sauki…….
Akwai Kaya Kala kala na nau’in turaruka Akan farashi me rahusa.
Muna Nationwide delivery 🚚
09034259662
08081693351
Koda kuɗinka sai da rabonka. Ai ƙamshi duniya ne 😘😌😌
__________
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
......Hajiya Mammah na ganin Samraah ta wuce da aikar da tai mata ta wani saki ƙayataccen murmushi. Sai kuma tabar kitchen ɗin da sauri. Fita tayi daga sashen baki ɗaya zuwa na Maash. Cikin sanɗa ta leƙa ta window ɗin falon. Kusan abinda ya faru na farko a idonta ya faru. Sai dai ganin Maash zai fita yasa hankalinta tashi. Da sauri tabar wajen, ɗakinta ta koma, ranta a dagule ta rarumi waya tai kiran Rubayya. Bugu biyu kuwa ta ɗaga...
“Gaskiya na gaji Rubayya. Ni fa shiyyasa kikaga sam babu ruwana da wani tsigunne-tsugunnen malaman nan. Gara na tashi da kaina nayi