Showing 21001 words to 24000 words out of 438336 words

Chapter 8 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2139

baki ci ba, ke da zaki shigo cikin taro babu daɗi kaita zaryar toilet ai”.
“Haka ne, nima na shafa'a ne kawai. Amma in sha ALLAHU ina fatan ma bazan sake zuwa toilet ɗin ba. Akwai maganin da nake sha a bag ɗina bari na sha shi”.
Kanta ta jinjina min tana sake min sannu. Inda muke zaune na koma na zauna dan hakan sai yafi min sauƙi. A dai-dai nan aka saki tafi alamar har an yanka. Na sake tafiya a tunani naji saukar muryar Mansoor a kaina. Firgigit na dawo hayyacina ina kallonsa. Sai kuma nai saurin ɗauke idanun a kansa ina ƙoƙarin dai-daita nutsuwata.
“Samraah mike damunki?”.
In har kaji sunana kai tsaye a bakin Mansoor babu wasa sam a ciki. Saurin girgiza masa kai nayi da faɗin, “Babu komai fa. Na dawo nan nasha magani ne kawai”.
“Ƙarya kike”.
Ya faɗa kansa tsaye kawai. Nasan za'ayi hakan. Dan Mansoor ya gama sanina matuƙa kasancewarsa mutum mafi shaƙuwa a rayuwata bayan ƴan gidanmu. Shekara biyar ai ba wasa ba. Ƙasa nai da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma na ɗauki wayata nai rubutu na tura masa. Ganin yanda ya cigaba da tsaiwa yana kallona ya sani ɗagowa ina masa nuni daya duba wayarsa. Baiyi musu ba ya zarota ya duba. Da sauri ya ɗago yana kallona. Sai kuma babu shiri shima ya kai zaune a kujerar kusa da ni. Sai da ya wawwaiga gefe da gefenmu sannan ƙasa-ƙasa ya ce, “Da gaske Baby”.
Kaina na jinjina masa kawai ina ƙoƙarin riƙe hawayen da suka ciko min ido. Sai kuma na kallesa na ce, “Ina son nabar wajen nan yanzu. Dan na yarda face mask ɗina a ciki ya ɗauka. Na tabbatar zuciyarsu dole tana musu wasi-wasi akan dole wani ya shiga wajen. Dan na fahimci hankalin yaron nasa kamar tun ɗazun ma ya rabu biyu akan mutane.”
“Ba tafiya bace mafita Samraah. Ki ƙara daurewa a kammala komai kawai. Sannan ki dawo da hankalinki jikinki, dan fitarki yanzu a wajen nan bazata zama mai sauƙi ba, sannan zasu ma iya ganewa ta hakan tunda baki da wani dalilin fita na zahiri. Kinga ma tashi mu shiga ciki kinga mutane sun kusa gama shiga za'a zagaya cikin companyn ne”.
Badan naso ba dole na miƙe. A zuciyata kam sai addu'oi nakeyi. Kar kiga fa kamar na cika tsoro. Wlhy babu abinda ke tada min hankali sai ganin gawar mutum cikin jini. Dan abune da bai taɓa faruwa da ni ba. Kinga ko sanda Babanmu ya rasu banda wani cikakken hankalin daya kamata irin hakan yaban tsoro. Tunda shima har aka binne gawarsa yana a yanayin zubar jini saboda accident. Mamanmu kuma bamma san rasuwarta ba sam, tunda ban wuci 3years ba kwata-kwata. Haka dai da ƙyar na cigaba da riƙe kaina mukabi ayarin ƴan ganin cikin companyn. Ya haɗu matuƙa gaya. Ga wasu manyan machines a wani ƙaton hall da baida iyaka. Da alama daga nan za'a dinga ƙera motocin ko haɗa su ne ma oho musu. Bayan nan akwai wajaje daban-daban masu ɗauke da abubuwa kala-kala da bamusan na miye ba, duk da wani bature a cikin abokan nasa sunata ƙoƙarin yin bayani, ni dai ba wani fahimtarsu nake ba sam. Dan duk yanda wajen ya kai ga haɗuwa a yanzu ni sam baya birgeni. Sai ma ganinsa nake baƙiƙƙirin da duhu. An ɗauki kusan mintuna talatin a ciki kafin a fito. Ɗayan sashen da ya kasance shine ake fara gani daga titi, wanda an yisane da zallar gilashi aka sake nufa. Anan ne offices ɗin ma'aikatan yake ashe. Tun daga hawan farko har zuwa na biyar sai da muka shishshiga da taimakon lift... Duka offices ɗin sun haɗu, hatta na ƙananun ma'aikata dake a hawan farko ma duk da na haɗaka ne komai tsaf. Amma nasa na matsayin oga kwata-kwata yafi kowanne tsaruwa, dan tamkar ba'a Nigeria kake ba. Daga office ɗin kuma akan iya ganin cikin ƙwaryar Kano da ƙyau ta kowanne ɓangare. Sosai abin akwai ƙayatarwa. Sai dai ni bai ƙayatar dani ba. Dan yanzu baƙiƙƙirin ma nake kallon mai Companyn kamar baƙin maciji. Nan ma an kwashi wasu mintuna kafin a fito. ALLAH ALLAH nake kawai yayi jawabin ƙarshen nan na masa tambayar da zan masa na bar wajen. Amma sai akace abinci za'aci a yanzun, sannan aje salla a dawo a ƙarasa. Kamar zan fasa ihu haka naji, sai dai yaya zanyi. Dole yanda suka tsara haka kowa zai bi. An fara gabatar da abincin a nutse, za kuma azo har inda kake a baka zaɓin abinda kake son ci sannan aje a kawo maka. Koda aka yambayen nikam nace a'a. Dan na ɗau alwashin bazanci kuɗin jinin mutane ba. Wama ya sani ko tsafi yake yi ne. Ai dama al'amarin dukiyar tasa da mamaki, shiyyasama mutane suketa wasi-wasi a kansa. Haba mutumin nan ai yayi ƙarami da tara irin wannan dukiyar haka. Kwata-kwata fa bazai wuce talatin ba. Inma zai haura hakan kaɗanne kuwa. Yo ko iya wannan companyn akace ya mallaka a shekarun nan nasa ai abin ayi wasi-wasi ne balle kuma ace yana da ninkin baninkin hakan har dasu jirage. Jirgi ake magana fa dake tashi sama da ɗaruruwan mutane bawai kwale-kwale na katako da ake tsallaka ruwan ɓagwai ba. Sannan bama ɗaya ba, ba biyu ba fa....
“Baby!!”.
Mansoor ya sake katse min tunani, dan yanzu a gefena yake. Firgigit na dawo hankalina. “please be smart mana. Ko so kike abokan tafiyarmu su fahimci wani abu ne?.”
Kaina na girgiza masa. Cikin dauriya na kalla abincin da ya saka a kawo min. Maimakon naji sha'awar cinsa kodan ƙyawun da yay a cikin ido ga kaza har rabi a ciki sai naji sam baya wani birgeni. A hankali na sauke a jiyar zuciya da ce masa, “Na ƙoshi da abincin nan wlhy. Kayi haƙuri dan ALLAH.”
Kallona kawai ya tsaya yi, ni kuma na ɗauke idanuna daga sashensa gaba ɗaya. Da ga ƙarshe ma na ɗauka wayata na shiga buga game wai duk dan dai na dawo da hankalina jikina. Sai dai tuni na kasa cigaba da buga game ɗin, na koma kallon mutane a ƙasan ido musamman ma yaronsa da duk wani motsin sa......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_


........Kusan kowa da ke a wajen abincin yake ci. Amma banda sarki banda gwamna. A kansa idanuna suka sauka shima. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da takardu a saman cinyarsa yana dubawa. Gefensa baturiyar matar nan ce ke masa magana da nuna masa abinda ke a takardun. Babu komai a gabansa sai bottle ɗin ruwa alamar ba abincin zai ci ba shima. (Jibesa kamar na ƙwarai). Na ayyana a zuciyata cike da taicinsa, ji nake kamar naje na shaƙe mar wuya na kwarara ihu tare shelantama mutane wanene shi. Amma dai na dake. Mansoor ne ya farga da mugun kallon da nake masa, sunana ya kira a hankali. Hakan ya sakani dawowa hayyacina. Ina ɗauke idona daga inda yake kuwa yana ɗagowa shima. Da alama yaji a jikinsa ana kallonsa ne. Harararsa na ɗan yi ta gefen ido na ɗauke kaina gaba ɗaya da ga sashinsa.
Bayan duk an kammala cin abincin aka fara shirin shiga salla. Akwai ƙaton massalaci a cikin companyn. Ƙasa na maza, upstairs na mata. Sarki ne da kansa yaja sallar. Bayan an idar aka fito domin cigaba da abinda ya tara mutane dan lokacin tashi ya kusa. Zaune nai a massalacin na kasa fita. Sai da Khulsoom tai kirana a waya. Mansoor na samu a ƙofar massalacin tsaye yay shiru alamar yayi zurfi a tunani. Tsayawa nai kawai ina kallonsa, kafin na ƙarasa gabansa naɗan jujjuya hannuna a saitin fuskarsa sannan ya kawo numfashi. Alamar (lafiya?) Na masa da kaina. Ya sake sauke numfashi da sakin murmushi. “Lafiya Lau Babie. Damuwarki ce ta daman. Gaba ɗaya bana jin daɗin yanayin nan da nake ganinki a ciki. Dan ALLAH ki saki jikinki har mubar wajen nan zamu san mafita, kinga lokacin da zakiyi aikin ki ya kusa cika”.
Kaina na jinjina masa da faɗin, “In sha ALLAH zanyi ƙoƙarin hakan.”
Cikin gamsuwa ya nunamin hanya alamar muje. Babu musu muka jera har wajen zaman mu. “Cikin ne har yanzu dai?”. Khulsoom ta faɗa dai-dai ina kaiwa zaune. Guntun murmushi na mata ina girgiza kaina. “A'a na tsaya ƙarasa addu'a ne kawai. Ga zaman nan na waje ɗaya baka ɗan motsawa kuma akwai gundira”.
“Sosai ma kuwa. Bakiji yanda ƙafafuna sukai dayi ba. Amma ai an kusa tashi in sha ALLAH tunda naga ga shi ma yana shirin miƙewa yay jawabin ƙarshe. Sai ki shirya lokacin aikinki yayi”.
Jinai ƙirjina yay wani kalar harbawa. Har sai da na ambaci hazbinallahu wa-ni'imar wakil sannan na ɗan ji sassauci. Cigaba da ambaton hazbinallah... ɗin nayi, yayinda shi kuma ya fara jawabinsa. Kamar dai ɗazun haka yake faman gwamutsa mana gurɓatacciyar hausarsa da turanci da faransanci. Dan in yay hausar yaji ya kakare sai kawai ya kwakuso turanci ya maka abinsa..
Gaba ɗayanmu ƴan Jaridar da aka bari muka shigo wajen munzo da ga gidaje bai fi takwas ba ne. Dan haka tambayoyin da zamu masan ma daga inda muke zaune ne zamuyi su. Kuma za'ayi ɗaya bayan ɗaya ne. Bayan ya kammala jawabansa ya kawo dubansa garemu. Da yanayin gajiyawa dan hatta muryarsa ta nuna hakan ya furta, “Bismillah zaku iya yin tambayoyinku. Sai dai Please akan abinda ya shafi companyn nan kawai. Bana son wasu silly questions da basu shafi abinda ya taramu anan ɗin ba”.
Cikin gamsuwa duk suka jinjina masa kai, dan ni dai bakina na taɓe ina mai jan tsuki ciki-ciki da ni kaɗai naji kayana, wannan ma ai rainin hankali ne, yanama mutane magana a gadarance. Wani dattijo ne ya fara miƙewa rigarsa da tambarinsu ya fara tambaya. Idanu ya zuba masa tamkar bazaice komai ba, harma kowa yay tunanin ko bazai amsa bane sai akaga ya ɗan murmusa kaɗan iya lips ɗinsa dake ƴan ficit. Gasu pink sosai dan sun ciza. Sai kuma ya nuna PA ɗinsa dake bayansa alamar shine zai amsa wannan tambayar. Hakan kuwa akai PA ɗin nasa ne ya bada amsar, hakama tambaya ta biyu da ga wasu. Duk yanda naso na motsa nayi tamu tambayar na kasa hakan. Gashi mune kuma ya kamata ace mun ma zama na farko. Ganinfa bani da niyyar tashi kamar ma hankalina baya tare da su dan har ya rage saura ƴam gida ɗaya Khulsoom ta zungureni. Firgigit na dawo hayyacina. Sai dai kafin na tashi ma waɗan can sun tashi. Dole na haƙura har sai da ya amsa tasu sannan na ɗaga hannu da taimakon Khulsoom. Dama ya bani kamar yanda yake bama kowa.
A hankali na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Yanda ya zuba min ido da ma kusan duk jama'ar dake wajen ya sani taune lips ɗina dake cikin face mask da ƙarfin tsiya ina mai karanto hazbinallah wa-ni'imar wakil a zuciyata. Da ƙyar na iya dai-daita numfashina ina mai janye idanuna da suma ke a cikin eyeglasses tare da sauke mask ɗin ƙasan haɓata sannan na furta.
“Sir a matsayinka na matashi da za'a iya shiga mamakin ganin yanda ka gina katafaren kamfani irin wannan da ya zama na farko a Africa, a duniya na uku kuma bama shi kawai ka mallaka ba, akwai wasu manyan cibiyoyi daka kafa a ciki da wajen Africa ma ba Nigeria kawai ba, ko nace duniya, shin ko zaka iya jan hankali matasa irinka dake tasowa dangane da neman na kai da asalin tarihinka dan su san kaima ba daga kwance ka kai wannan matsayin ba, sai da kai aiki tuƙuru, tare da tsallake ƙalubale masu yawan gaske kuma duk kai haƙuri ka jure har gashi a yanzu ka zama wani babban ginshiƙi tauraron duniya dake haska yankinsa da ƙasarsa, yarensa harma da addininsa?”.
Bashi da naima tambayar ba, hatta sauran ƴan jarida ƴan uwana dama duk jama'ar dake wajen sai da suka zuba min ido, harma da masu hangame bakuna sama. Bama sai sun faɗi abinda ya basu mamaki ba, ni na sani. Yace kar a masa tambaya sai akan abinda ya shafi company, sannan tambaya ɗaya kacal zakayi. Amma ni dana tashi na haɗa kusan tambaya goma ne a cikin ɗaya, na kuma yi tambaya akan kamfani kawai da ya buƙata amma na saka abinda yake gudun a tambayesa ta yanda dolene sai ya amsa min ɗin. Yaja kusan mintuna biyu cif yana kallona kawai cikin wani irin yanayi, sai yatsun hannunsa daya dafe dogon tables ɗin da aka cika da mic.. yake ta motsawa, musamman biyun tsakkiya. PA ɗinsa ne ya ɗan yunƙuro amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya dakata. Tsayawar yayi, sai dai shima wani mugun kallo yake jefamin fiyema dana uban gidan nasa. Oho ko'a jikina, ni dai tunda nayi tambaya ta ai shikenan, amsa kawai nake buƙata. Motsawarsa da sakin wani shegen makirin murmushinsa ya saka kowa sake maida hankali kansa. Murmushin ya sake saki yana ɗan cizar lip ɗinsa na ƙasa. Yay wani ɗan diri-diri kamar wanda ya rasa abin faɗa sai kuma ya nuna ni yana sake sakin wani lalataccen murmushin. A hankali ya furta, “Hmmm you are very smart girl. A karo na farko na yarda zan bada wannan amsar, amma ba yau ba, ba kuma anan ba saboda munada ƙarancin lokacin hakan.”
Wani ƙwarin gwiwa ne naji ya sake zomin. Kai na tsaye na ce, “Thanks you sir. Amma taya zan sake samun wannan damar kamar haka ku da ganinku ba wasan yara bane. Gashi kuma ina matuƙar son gamsar da ƴan uwana matasa da sake farkar da waɗanda suka shagala. Zan so ace na samu date da time tun anan tare da location kodan ni da ƴan uwana matasa mu kasance a cikin shirin ji da ga bakin gwarzon mutum irinka”.
Ai da ƙarfi yanzu kam ya cije lips ɗinsa, yana wani kalar tsatstsareni da kaifafan idanunsa, dan duk da a cikin eyeglasses suke dolene ka fahimci hakan musamman yanda kai tsaye direction ɗinsa yake gareni. PA ɗinsa ne ya ɗan matso ya masa maganar da shi kaɗai ya ji abinsa. Yana gama faɗa masa ya ɗan ja baya kaɗan shi kuma ya juyo gareni. A bazata ga kowa ya furta, “Na baki dama, kisa date, kisa time ki faɗi location koda a office ɗin ku ne”.
Kutumelacy, ai jina ƙafafuna na neman gagara ɗaukata. Yayinda gaba ɗaya wajen yay wani irin ɗaukar shiru duk aka zuba masa idanun mamaki. Dan abune da bai taɓa faruwa ba. Maash a gidan tv ko jarida ko rediyo ko mujalla ana masa tambaya akan tarihinsa ba harkar business ba yana bada amsa. Abin mamaki. In taƙaice muku har taron nan ya tashi ban dawo dai-dai ba. Dan duk da hakan shine burina a kwanakin nan, sai nake jin kamar bazai yiwu ba. Koda yake hatta a ƙiyamullaili ɗina na satin nan sai da naita saka addu'ar fatan ALLAH ya ɗorani a kansa banyi zaton zan samu damar ba sam, kuma a cikin sauƙi ma haka. Hummm al'amarin da ban mamaki kam....

Kasancewar duk abinda ake a office ɗin mu suna kallo ne live dama mutane wata kalar gagarumar tarba muka samu. Musamman ma ni. Dan mata-matan staffs ɗin nan namu rungumeni suka dinga yi da kwarzanta ƙoƙarina. MD kam bakinsa tamkar zai yage ne. Wannan abin alfaharine a garesa ace mutum kamar Maash ya amsa gayyata da ga gidan tvn sa a gaɓar da kowa ke matuƙar buƙatar hakan. Oho su suke shirmensu ni nawa hankalin ma ba'a kansu yake ba. Maganar kisan can ne yay matuƙar tsaya mun a rai da zuciya. A dalilin sallar la'asar na samu damar zame musu. Dan bamu tsaya munyi acan ba kasancewar an tashi gab da za'a fara kiran salla. Ana idar da salla na MD yace muje gida mu huta. Haka dama nake buƙata. Dan burina kawai na keɓe da Mansoor na ji yaya za'ayi da batun video dake a cikin wayata. Muna barin office ɗin kam zancen dana fara masa kenan. Shima da alama abinda ke cimasa rai kenan. Dan haka muka shiga tattaunawa. Koda ya isa dani ƙofar gida ma ban fita a motar ba. Zancen muka cigaba da yi. Ni dai ina a matsayar mu kaima hukuma video ɗin. Tunda dai duk hanyar da zasu bibiyi batun gawar zai zama mai sauƙi kasancewar ya faɗi inda za'a kaita. Amma sai Mansoor ya ce nadai bashi dama yayi nazari tukunna. Na kuma tura masa video ɗin. Babu musu na tura masa, nima na adana wanda ke wayar tawa da ƙyau duk

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login