Showing 48001 words to 51000 words out of 438336 words

Chapter 17 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2892

wai tasan yin irin wannan ta'addacin haka. Jiba yau yanda take wani basarwa da shan ƙamshi fa. Ni wlhy dan kawai kace a barta ne ai. Amma har ita wacece da bazamu sa a tattaro mana kaf zuri'ar gidansu ba taga ƙaryar tsagerancin nata. Haba ita wacece da zata zauna tana rainama mutane hankali. Kawai na kira Sani a daren nan ya kawo mana ita gidan nan a amshi wayar tata a gabanta mu goge video ɗin sannan mu danƙata hannun hukuma, muda muke da makami ma a kanta, dan biyowa ta bayan gida fa tai akan hira dakai har yanzu ba'a daina cecekuce a kansa ba a media, wani abun ma nasan sai randa aka saki hirar, tabbacin mutane da yawa na asiri tazo da shi wajen har ka yarda ka amsa matan zai sake gitowa”.
Shi gaba ɗaya ma surutun Hayatun saka masa ciwon kai yake. Dan haka ya wurga masa wani kallon da ya sakashi nutsuwa, tare da jan bakinsa ya tsuke. Shiru falon ya sake ɗauka kowa na cuɗawa da kwancewa a cikinsu. Kafin shi ya miƙama Hayatu wayar yana faɗin, “Ba buƙatar mata komai a yanzu. Ina son ganin iya gudun ruwanta. Ka amsa mata da za'a bata 500m ɗin, amma a ina za'a haɗu da ita ta bada recording ɗin”.
“Amma Sir.....”
Hannu ya ɗaga masa, a daƙile ya ce, “Na gama magana”.
Yawu mai ɗaci Hayatu ya haɗiye. Sai kuma ya jinjina kansa cikin girmamawa ya ce, “Okay Sir, in sha ALLAH za'ayi yanda kace. Na barka lafiya”. Daga haka ya juya ya fice. Ta gefen ido Marsh ya bisa da kallo. Sai kuma yay wani kalar furzar da iska yana maida kansa a kujera ya kwantare tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan mi yake ji a ransa game da yarinyar nan. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta ba. Amma zai bata lokaci ta gama nata kalar ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin saninsa a rayuwarta a kanta. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba neman kuɗi kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Ko abubuwan data dinga yi yau duk a rubuce suke a brain ɗin, ya fahimci tanada taurin kai da tsageranci. Duk zai sauke mata su kuwa nan bada jimawa ba.
Ya jima a wajen zaune har Hayatu ya dawo ɗauke da abincin da Sani yayo order. Amma sai yace bazai ci ba. Ya haɗa masa coffee kawai. Umarninsa Hayatu yabi. Ya kawo masa coffee amma ya haɗo da biscuits mai daɗi. Dan yasan waɗan nan sune kalar ciye-ciyen da ogan nasu yafi so a rayuwarsa. Shiyyasa a duk inda yake baka rabashi da kalolin biscuits da chocolates kala-kala masu shegen daɗi. Sabone tun na ƙuruciya ya riga ya kamashi. Sake fita Hayatun yay ya barsa, shi kuma ya maida hankalinsa ga tv yana kallon film ɗin da sukeyi yana shan coffee ɗinsa da biscuit ɗin kamar baya so. Koda ya kammala zamansa ya cigaba dayi har sai da film ɗin ya ƙare sannan ya shige ciki. Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da yay minti talatin cur ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi uwa kamfanin haɗa turare kamar ba dare ba. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunne. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji. Baiyi mamakin ganin Hayatu a falon ba. Dan duk inda aka gansa dolene aga Hayatun. Duk da yana jin idonsa a kansa bai kallesa ba. Hakan yasa Hayatu ɗauke idonsa shima a ransa yana kirari wa UBANGIJI mahaliccin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta, gaskiya dole ma aso mai ƙyau, dan ko shi dake a namiji, kuma ana yawan sanar masa shima ɗin ƙyaƙyƙyawane har ga ALLAH ogansa na birgesa. Dan mutum ne daya san hakkin tsara ado. Ya iya tsara saka sutura ta zauna ɗam ya haskata kuma tamkar dan shi kaɗai ake saƙa kaya irinsu. Ganin zai ɗago da sauri ya wuce sumu-sumu zuwa bedroom dan ya kashe komai ya gyara kuma abinda ya ɓata tunda basu san ranar dawowarsu Kano ɗin ba kuma. Suda suke kullum a tafiye-tafiye kamar ƴan sama jannati.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


.......Kamar ko yaushe yau ma Mansoor ne ya maida ni gida, koda na shiga na samu gidan tsitt. Banbi takan kowaba na shige ɗaki, auta na samu yana barci, ga books ɗinsa a gefensa barbaje alamar homework yake barcin ya kwashesa. Ɗagashi nai na maida kan katifa. Sannan na tattare books ɗin na ajiye masa gefe bayan na duba abinda yake. Yaron akwai brain, inba ni ba babu mai zama damuwar koya masa homework, sai idan Abba. Wani lokacin ma sai kika yayi da kansa kafin ma na dawo, sai dai na ɗan masa gyararraki kawai. Wanka nai ƙoƙarin shiga, sai dai bayin duk an ɓata shi, nasan Bibaa ce zatai wannan aikin ba wani ba. Na rasa mike damun kan yarinyar nan, amma zan koya mata hankali. Tanada ɗakinta ita kaɗai amma tsabar shaiɗanci tace tsoro take ji a can, shine Abba yace ta dawo nan mu zauna wai sai ta ƙara girma. Da farko na ɗauka haka ɗinne, sai daga baya na fahimci Mom ce ta sakata yin hakan dan ta dinga ɗaukar rahoton duk motsina tana kai musu. Tun wani lokaci da naji tana faɗama Mom wayar da mukai da Mansoor nagane hakan. Bayin na sake gyarawa sannan nai wankan. Harna fito na gyara jikina banji motsin kowa ba. Ba'a wani ɓata falonba yau sosai, dan haka na wuce kitchen. Shi kam yana nan jibge da kayan wanke-wanke tun daga kofunan kalacin safe har na rana da sukaci. Kaina na girgiza ina mai jin tausayin Bibaa da Baby a rayuwa. Dan ita Mom gani take gata take musu bata san kashe musu rayuwar take ba, haka kullum da rayuwar take a gidan, idan nai aikin safe na fita babu abinda suke kaudawa har sai na dawo na sake yi, badan nima na zama jan wuya ba abincin rana ma sai na musu na saka a kula. Sai da na nuna musu nima tsagerar kaina ce sannan, shiyyasa kullum basu da abincin rana a gidan sai taliya ko cus-cus ko macaroni, indomie. Sai idan akwai stew ne zakiga sun dafa farar shinkafa. Stew ɗin kuma zakiga dole nice zanyita, Mom taƙi yarda a ajiye mai aiki wai ita kishi, randa nayi aure to naga ubanda zai zo ya musu. Kwanikan na fara tattarewa na wanke, ƙafafuna duk sunyi tsami saboda tsaiwa. Haka dai na daure na kammala na maida komai muhalinsa sannan shima kitchen ɗin na shiga gyaransa. Ƙaramar indomie na dafa guda biyu, na raba biyu naci tawa anan na juyema auta tasa a plate. Har lokacin babu wanda ya dawo, mamaki ya sake kamani da tunanin ina sukaje haka ne?.
Har akai sallar magrib sai mu kaɗai a gidan. Sai bayan an idar Abba ya shigo. Fita mukai ni da auta daya tashi muka gaishesa. Na wuce na kawo masa ruwa na koma ɗaki abina na barsu anan falo. Sun fita sallar isha'i nima zan kabbara tawa naji hayaniyar shigowar su Mom. Banbi takansu ba na tada sallata. Sai da nai har shafa'i da wutiri sannan na fito musu sannu da dawowa. Kaya na tarar barbaje a falon kashi-kashi. Na sakawa dana kwalliya harda na ciye-ciye alamar dai daga kasuwa suke. Ganin hankalinsu baya kaina dan ko gaisuwar ma da kai Mom ta amsa min na juya na koma abina ina mamaki, dan tabbas da kuɗin Yaya na jiya akai wannan sayayyar kenan. Jinai raina ya ɓaci matuƙa, dan haka na fito na wucesu. Yanzun ma hankalinsu babu alamar yana kaina. Ta ihun murnar kayansu suke kawai. Ɗakin Yaya Musaddiq na nufa, yana tsaye da alama yanzu ne yake dawowa massalaci. Ganina rai ɓace ya sashi faɗin, “Jikin ne?”. Kaina na girgiza masa ina kaiwa zaune. Cikin zafin rai na ce, “Wlhy Yaya zancen kuɗin sarƙar nan shirine kawai. Ko kasan matar can yau kasuwa suka shiga ita da ƴaƴan nata gasu can sun baje kaya a falo kamar za'a buɗe kanti. Kasan kuma babu yanda za'ai hakan ta faru Mom ta iya kashe kuɗin sarƙar nan a banza haka da gaskiya ne”.
Murmushi mai sanyi Yaya Musaddiq yay hana kaiwa zaune kusa dani. Cikin sauƙaƙa murya tare da riƙo hannuna cikin nashi ya furta, “Cool down sweetheart. Sune a ƙasa ai. Bakiji shata na faɗin ku gargaɗi mai gina ramin mugunta ba. Ni nasan dama koda an ɗauki sarƙar ma bata kai ta kuɗin data faɗa ɗin ba. Amma ba komai ALLAH zai bamu wasu. Yanzu ma Abba ya bar ɗakin nan”.
“Miya faru ya shigo?”.
Na faɗa cikin mamaki tunda nasan dole akwai dalili. Hannuna ya saki yana miƙewa da ɗan taɓe bakinsa. Ya zare jallabiyarsa ya ajiye sannan ya koma ya zauna dan jikinsa akwai dogon wando da t-shirt fara. “Yazo ya sameni akan wai tunda yaga inada kuɗi ni ne ya kamata na miki komai na aure. Dan shi gaskiya yana a cikin damuwar rashin kuɗi. Saboda hakane ma yaƙi yarda su tsaida rana a randa iyayen Mansoor suka zo. Amma da yasan har inada wannan kuɗin haka aida an kammala komai. Dan haka zai kirasu suzo weekend ɗin nan a tsaida ɗin. Na kuma bashi aron 200k zuwa ɗan wani lokaci zai bani..”
“Kuttt! Amma mutumin nan ko! Wai mike damun Abban nan ne?. Dama ko bai faɗaba waye ke jiran wani abu da ga garesa mtsowww aikin banza. Sannan kuma bashin ka amsa zaka bashi Yaya?”.
Murmushi Yaya Musaddiq ya saki mai haɗe da dariya, sai kuma ya girgiza kansa. “Kai wannan yarinya masifaffiya ce ke wlhy, wanda basu sanki bane kawai suke miki kallon mai haƙuri. Ni ALLAH har ma na fara tausayin Mansoor bawan ALLAH shi gashi da sauƙin halin tsiya”.
Baki na tura ina faɗin, “Kai Yaya nice masifaffiyar?”.
“Ta bugawa ma kuwa a jarida kandala. Wani lokacin da idan kina abu sai naga kamar ma kece Yayar tawa. Shiyyasa Hafizzullah ke cewa da kece Mamanmu da mun shiga uku”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi. Na ce, “Masherancine yaron nan ai. Dan ALLAH Yaya weekend ɗin nan muje mu gansa tunda wancan ya shuɗe. ALLAH ina kewarsa”.
“Karki damu zamuje in sha ALLAHU. Dan na kammala masa ma siyayyarsa.”
Cike da farin ciki nace “Yauwa Yayanmu, kuma Babanmu. Yanzu dai yaya mi kacema Abban?”.
Sai da yay murmushi ya ce, “Mizan ce masa kuwa Samraah. Na gaya masa kuɗin dana bama Mom ɗin jiya ne kaɗai dama a wajena, sai abinda ya rage baifi saura dubu arba'in ba nama cire wani abu a ciki na haɗama Hafizzullah provision. Dama na tara wancan kuɗinne dan na basa shi da Mom ɗin su rage hidimar biki. Ga kuma abinda ya faru yanzu. Ina gaya miki sai kawai ya hauni da faɗa. Wai to wlhy sai nasan inda zan nemo wasu kuwa. Dan shi dai baida wani kuɗin yin hidimar nan bai kuma da hanyar samunsu. Inba hakaba kuwa sai dai a kaiki gidan mijin a haka.. inada yake shiga dai bata nan yake fita ba.”
Wata shegiyar dariya na bushe da ita harda kwanciya ina hawaye. Yaya Musaddiq kuwa yay sagale yana kallona. Sai da yaga dariyar tawa ta tasamma ta hauka sannan ya ce, “Samraah kin samu motsuwar kai ne?”.
“Babu wani motsuwar kai wlhy Yaya. Show ɗin ne yay matuƙar burgeni. Su Abba an lallaɓo aci banza. Banza bata samu ba, shine ya ƙare da borin kunya. To waye ya faɗa masa na damu a kaini da kayan ɗaki? Ko cokali ma kada su saya waye zaiji kunya”.
“Shirme maganinka ALLAH kenan”. Yaya Musaddiq ya faɗa yana girgiza kansa. Da sauri na ce, “Yaya gaskiya fa na faɗa. Ni wlhy ban damu ba amin kayan ɗaki ko a kar ayin. Badai muna son junanmu ni da Mansoor ɗina ba”.
“Baki da kunya, a gabana kike cewa kuna son juna”.
Hannu nasa na rufe fuskata ina dariya. Shima sai ya shiga tayani...

Washe gari koda na kammala aikina na shirya na fito na samu Abba a falo na gaishesa bai amsa min ba. Ko'a kwalar rigata nai ficewata. Yaya ga ɗaukan muka wuce ina bashi labari ina dariya. Shi kam murmushi kawai yayi yace “ALLAH ya ƙyauta”. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gidan Abba babu daɗi sai haƙurin UBANGIJI kawai. Yayinda a waje aiki ke caja kai kuma. Kamar yanda mukai shiri ranar asabar muka tafi Katsina ganin Hafizzullah. Ƙiri-ƙiri Mom ta nuna baƙin cikinta akan hakan. Ta shiga zuga Abba wai ya hanamu zuwa. Sai dai Yaya ya nuna musu babu abinda zai sakamu fasawar. Haka dai muka tafi Mom na banbaminta na rashin gaskiya. Hafizzullah yayi matuƙar farin ciki da ganinmu. Dan harda kukansa na murna. Ya rame saboda karatu, naita tsokanarsa nikuwa muna faɗanmu da muka saba. Tare da shi muka yini. Da zamu wuce masauki kuma ya bimu akan shi tare damu zai kwana. Nan ma raba dare mukai muna hira kafin su koma ɗakin Yaya Musaddiq su kwanta ni kuma nai kwanciyata ni kaɗai muka sha waya da Mansoor dake bani labarin an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za'a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a ƙasan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu ƴancin kaina. Na kuma samawa ƴan uwana. Dan insha ALLAHU Hafizzullah gidana zai koma, Yaya kuwa zan cigaba da dagewa akan yay aure..........✍️


_Kandala ta malam Mansoor 😘_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_


........Washe gari kamar yanda Mansoor ya faɗa muna a hanyar dawowa gida ya turamin saƙo na jerarrun kalaman godiya ga ALLAH. Tare da sanar min an tsaida wata ɗaya kacal, nanda kwana talatin in sha ALLAHU na zama mallakinsa. A gidansa zanyi azumin watan Ramadan. Duk da naji farin ciki ban maida masa reply ba, dan ina cikin mood mara daɗi na rabuwa da Hafizzullah. Shima mun barosa harda hawayensa. Munko samu gida cike da kayan sweet, biscuits da drinks a falo. Harda su goro sai akwatina guda biyu. Yanda babu wanda yay min magana akan kayan nima banma kowa ba. Sai auta ne ke faɗamin Uncle Mansoor ya gaya masa kayana ne. Sai kuma habaicin da Baby keta saki ranta a ɓace. A kallo ɗaya da nai mata kuma na fahimci tasha kuka. Ban kulata ba dan ba itace a gabana ba. Washe gari Monday na wuce aiki da wuri. Bayan mun dawo na tarar da Gwaggo Gudidi tazo daga Dawanau. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba da mamanmu kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Yanzun ma shine ya kirata ya gaya mata komai ganin Abba baida niyyar saka danginsa ko ɗaya a batun auren nawa. Ƴan Gwarzo kuwa sun kwashi nasu kason kayan da za'a rabama mutane sun wuce dasu tun jiyan, dan bamu samesu ma a gidan ba. Nayi murna ƙwarai da ganin Gwaggo Gudidi. A take na shiga hidima da ita dan naga babu alamar ko abincin kirki ma an bata. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha'i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da ƴaƴanta kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login