Showing 126001 words to 129000 words out of 438336 words

Chapter 43 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2172

yare. Godiya ce kawai yayi a taƙaice tare da roƙon cigaba da tayashi addu'a ALLAH ya bama Ummiensa lafiya. Sai kuma yay shiru kansa a ƙasa fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Kusan minti ɗaya kafin ya ɗago yana mai kai handkerchief saman fuskar sa ya goge. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci guda ya saukesu akan mahaifinsa. Murmushi ya sakar masa, sai kuma ya miƙe tare da nufosa shima. Yana isowa ya rungumesa yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Daga haka ya amshi mic ɗin hannunsa shima ya fara magana. Kusan abinda dai ɗan nasa ya faɗa shima ya maimaita, sai abubuwa kaɗan daya ƙara a kai sannan suka yanka cake a tare. Baban ne ya fara ɗibowa ya kai bakinsa. Cikin wani yanayin narke fuska ya motsa ƙananun lips ɗinsa kaɗan, sai dai baban na zuwa gab da bakin nasa sai ya juya hannunsa zuwa nasa bakin ya cinye cake ɗin tare da lakata masa sauran na hannunsa a saman hanci. A take wajen ya ɗauki tafi da dariya. Shima murmushi yayi yana kauda kansa. Sai baban ya rungumosa yana dariya.
Haka kawai na tsinta kaina da yin murmushi akan wasan nasu, sai kuma na haɗiye da sauri dan tuna akan wa akeyi. Bayan sun je sun zauna Hajiya Mammah, Aunty Mama, Hajiya ƙarama, Hajiya Mubeena, Alhaji Abdullahi duk sun fito sunyi bayani tare da addu'a ga Hajiya Ummu-Hidaya kamar yanda naji suna ambata dama rubutawa da akai jikin ƙaton cake da wani irin golden color mai sheƙi tamkar ba cake ba. Gaba ɗaya zaman wajen bai wuce na awa biyu da mintuna arba'in ba. Aka raba ƙyauta har da mu daga haka taro ya tashi. Bayan tsirarun baƙin da aka gayyato irin su Hajiya sun wuce Aunty Mama ta bama Mama Bilki umarnin zuwa dani garesu bayan sallar isha'i. Ta amsa mata da girmamawa yayinda ni kuma nai kamar ban jisu ba dan hankalina gaba ɗaya ya tafi wani waje daban.....

🌜🌟🌛

Matuƙar tashin hankali Musaddiq da Halime tai gudu ta kira ya shiga ganin Abba cikin jini. Rasama abinda zai yi yay har sai da maƙota suka shigo. Sune suka ambaci asibiti sannan hankalinsa ya dawo jikinsa. Ga Bibaa da Auta na famar darzar kuka. Baby kuwa sai surutai takeyi. Duk wanda ya shigo kuma sai ta nuna Mom data maƙure gefe jikinta na maƙyarƙyata.
“Kun ganta nan itace ta kashe mana Abba. Kawai itama a kasheta dan nice alƙali na yanke hukunci”. Abinda Babyn ke faɗa kenan cikin Muryar ƴan maye da surkulle. Duk da kowa kanji shock da abinda ta faɗa ɗin da kuma yanayin da take ciki babu mai bi takanta. Burin kowa dai a kai Abba asibiti kada ya rasa ransa....

Koda suka isa asibitin da ƙyar aka amshi Abba, dan sai da Yaya Musaddiq yay ƙaryar faɗuwa yay a banɗaki sannan. Da gaggawa suka shiga bashi kulawa, yayinda aka bar su Musaddiq kai-kawo a waje kowa na addu'a a zuciyarsa. Sun kwashe tsahon lokaci kafin doctor ya fito. Bayanin da yay musu na cewa yaji ciwo sosai a kan nasa kuma bai farfaɗo ba har lokacin ya sake tada hankalin Musaddiq. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Dan harga ALLAH duk abinda Abban ke musu shi da ƴan uwansa bai taɓa jin ya tsani ƙanin mahaifiyar tasu ba. Saboda yana kallon fuskarta ne akan ta kawun nasu. Tun a daren yay kiran ƴan Gwarzo da Gwaggo Gudidi. Sai dai suma bai faɗa musu gaskiyar al'amarin ba dai. Hankalinsu ya tashi, washe gari kuwa tunda sassafe sai ga Gwaggo Gudidi. Wajen tara sai ga ƴan Gwarzo suma har da su Kawu Musa saboda kara. Dan su ta ɓangaren mahaifinsu suke bata ɓangaren Abban ba. Har Azhar Abba bai farfaɗo ba, asibiti ya ciga da dangi amma babu Mom. Sai su Bibaa da Baby. Abbas ma sai kusan azhar ya iso hankali tashe. Dan bai san mike faruwa ba sai da yaje gida yake ji a anguwa. Koda ya shiga cikin gidansu ya samu Mom nata darzar kuka gefenta mahaifiyarta Inna zaune jigum ta zuba tagumi da hannu biyu. Bai iya cewa da su komai ba dan yanayinsu da sambatun da Mom keyi ya tabbatar masa da abinda mutanen suka faɗa. Kiran Musaddiq yay a waya ya sanar masa asibitin da suke. Sai ko gashi ya iso. Hankalinsa ya sake tashi da jin Abba fa yaƙi farfaɗowa, harma likitocin na maganar ya tafi doguwar suma........✍️


_Wayyo Abbanmu kada ka tafi ka bar Halime😌😌_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_


.........“Wlhy sai na kashe yarinyar nan da hannuna na jefar da gawarta inda ko angulu basa gittawa!!”.
Yanda take maganar cikin fushi ga idanunta cike da hawaye jikinta na rawa ya tsorata Arwa. Riƙota tayi tana mai danne abinda ke cin tata zuciyar itama kamar yanda ta saba. A take zuciyarta ta hasko mata nasararta, dan tabbas wannan dama ce da zatai amfani da Azizat game da yarinyar nan taci nasarar samun cikar burinta itq. Cikin dakewa tamkar bata ga komai daya faru ba ta ce, “Aunty Azizat cool down mana. Wai mike faruwa? Mi akai miki? ki faɗa min ko ina da taimakon da zan miki. Shin waccan ƴar shishigin ce Malikah ko?”.
Ɗari bisa ɗari Azizat ta yarda da Arwa. Dan ƴar team ɗinta ce, duk da iyayensu basa jituwa hakan bai hanasu aminci ba su. Ta kuma sha bata shawara akan Malikah taci nasara. Hawayen da suka gama wanke mata fuska ta share. A matuƙar zafafe ta furta, “Malikah ɗin banza. Ita har ta isa nai mata kuka Arwa, kada kema ki ɓata min dan ALLAH. Idan baki san abinda zaki faɗa ba fita ki bani waje...”
“Kiyi hakuri to ba yanda kike nufi bane. Faɗa min mike faruwa?”.
Shiru ta sake yi kamar ba zata ce komai ba har sai da Arwa ta sake zingurarta. “Arwa ki ƙyaleni dan ALLAH. Har zaki ce bakiga sanda waccan karuwar sabuwar mai aikin yarinyar da Aunty Mama ta kawo mana gida yau ma ta sake faɗawa a jikin Yaya Awwab ba?”.
“What?!! Jikin Yaya Awwab fa? Bayan na waccan ranar da tayi kuma yau ma ta sake again? Eh lallai kam na yarda dake wlhy yarinyar nan karuwa ce Aunty Azizat. Kuma tabbas ba haka nan ta shigo gidan nan ba akwai asiri tare da ita, sannan akwai manufa, ni dama wlhy tun kallo ɗaya da nai mata nake ji a raina batai kama da masu aiki ba. Idan ba hakaba taya za'ace ranar tayi yau ma ta sake aikatawa kuma? Koda yake babu mamaki ai ba'ai mata gargaɗi ba ne a waccan ranar. Ke kuma da alama ta danne miki baki tunda na ga ko Mammah baki sanar mawa ba”.
Sosai kalaman Arwa suke tasiri a zuciyar Azizat. Zuciyarta ta shiga tabbatar mata lallai akwai asiri a al'amarin kam. In ba hakaba yama za'ai hakan ta kasance. Kuma wai abin ƙarin mamakin ma yanda abin ya faru kowa ya nuna tamkar bai gani ba. Koda yake komai ya faru ne tamkar ƙiftawar idanu dan bai wuce cikin minti biyu ba, tun daga faɗawar tata har tashinta daga jikin nasa. Sannan a yanda shegiyar tayi sai ka ɗauka accident ne bada sani ta aikata ba...
Ganin yanda ta sake tafiya duniyar tunani Arwa ta sake taɓota. Cigaba tayi da fanfata har sai da ta hau ta zauna. Sannan ta tsara mata abinda ya kamata suyi domin ɗaukar mataki. Sosai kuwa Azizat ta yarda, dan a take ta jawo kan wayar telephone tayi kiran sashen masu aiki. Ana ɗagawa ta miƙama Arwa kan wayar, itako dama ALLAH ya bata iya canja murya, a take ta koma muryar Aunty Mama. Tana gama faɗar abinda suka tsara ɗin ta yanke kiran, kallon juna sukai ita da Azizat ɗin suka saki murmushi. Sai kuma suka tafa alamar nasara ta samu....

✨💞✨💞✨

Wajen la'asar ana ƙoƙarin maida Abba wani ɗakin sai ga Mom da Inna da ƙawarta wadda ta kawo mata Halime. Kallon inda take kowa baiyi ba, dan zuwa yanzu kowa a wajen yasan sanadin al'amarin sakamakon Baby data zazzage musu zance. Har an canjama Abba kaya za'a wuce da shi sai ga Nurse a guje yana ƙwala kiran doctor. Kusan dukansu suka afka ɗakin dan azatonsu Abba ya cika, koda Nurse ɗin da doctor suka shigo sun cika ɗakin tare da rufuwa a kansa. Da ƙyar doctor ya samu duk suka fice su kuma suka fara aikinsu.
Kowa ka gani yana cikin farin ciki da farfaɗowar Abba. Sai kuma fatan ALLAH ya bashi lafiya. Bayan kamar mintuna Talatin kuwa Doctor ya sake musu albishir ɗin farfaɗowar Abban. Sai dai ba'a bar kowa ya shiga wajensa ba sai a washe gari. Alhamdullah jikin nasa da sauƙi sosai, sai dai kansa yasha bandage abin tausayi. Babu wanda yace ma Mom komai duk wani rawar kan dafo abinci da take tana kawowa safe da rana da dare. Shima Abban kuma baya ko kallon inda take duk maganar da zata masa bai amsawa. Dama jiyyarsa Kawu Isuhu ne keyi. Ƙani yake a gurinsa dan ɗan wan mahaifinsu ne. Kwanansa uku aka sallamesa. Ya samu rakkiyar dangi data abokai irin su Alhaji Sadisu.
Tun isowarsu ya fahimci Halime bata gidan, bai dai ce komai ba har sai da yay wanka ya samu nutsuwa. Falo ya dawo ya kwanta saboda masu shigowa dubasa ƴan nan cikin anguwa. Su Gwaggo Gudidi na zagaye da shi anan ɗin ma. Basu sami lafawar mutane ba sai kusan goma na dare, alokacin ne fa Gwaggo Gudidi ta fara tsiya saboda tayin shiga ɗaki ya kwanta da Mom ta masa. Gwaggo tace babu inda zaije a ƙarasa hakalashi, Musaddiq ya kaisa ɗakinsa yaje can ya kwana. Sosai Mom ta shiga shock, dan batai zaton sun san ainahin abinda ya farun ba, amma sai ta dake ta shiga bama Gwaggo haƙuri da shi kansa Abban wai sharrin shaiɗan ne bazata sake ba. Harda ƴar ƙwallarta kamar yanda Ummanta tace tayi. Fata-fata Gwaggo ta mata a gaban su Musaddiq, sai da ƙyar aka samu tayi haƙuri. Ita dai Mom yau babu bakin magana kuma sai haɗiyar zuciya.....


💥❤️💥❤️💥

Bayan sallar isha'i dole na haƙura da batun bin su Bahijja Islamiyya domin amsa kiran Alajah. Muna gaba da shiga sashen Mama Balki ta dakatar dani, cikin nuna kulawa da kwantar da murya ta furta, “Ɗiyata dan ALLAH yau ki danne zuciyarki. Kar ki kula Azizat komi zata miki. Mutanen nan da kike gani sunada rigima sosai, idan aka zo fagen faɗa da bare kansu haɗe yake wajen ɗaukar mataki. Ki ringa haƙuri mu neman arziƙi ya kawo mu. Fatanmu mu samu abin rufama kammu asiri shike nan kawai. Kina ƴar ƙaramarki da ke kar ki biyema wanda suka fi ƙarfin ki kinji”.
Duk da zantukanta sun tunzurani sai ban nuna ba a zahiri na haɗiye, sai ma jinjina mata kaina da nayi, a hankali na amsa da “In sha ALLAHU Mama komai ya wuce. Ranar ɗin ma akasi kawai aka samu”.
Cikin nuna gamsuwa da sake lallashina ta sanya min albarka. Daga haka taja hannuna muka ƙarasa shiga ciki. Duk da nasan banjin shakka ko tsoron kowa a raina sai da nayi addu'a sannan na shiga. Da hayaniyar surutunsu yau muka fara cin karo. Kasancewar ta inda muka shigo duk suke a ƙatoton dining yasa sukai min wani farrr cikin ido. A hankali naja numfashi na fesar ina mai karanto (Hasbinallahu wa-ni'imal wakil) a cikin zuciyata. Da farko ba kowa ya maido hankalinsa kammu ba, dan koda mukai gaisuwa bai fi mutane uku suka amsa ba. Ciki harda Alajah data furta, “A'a Mama Balki ba nace sai mun kammala cin abinci ba?”.
Cike da mamaki Mama Balki ta ce, “Eh da haka kikace Hajiya, amma kuma yanzu da kika kira sai kikace kada mu wuce mintuna talatin shiyyasa kuka taho”.
Sosai mamaki ya bayyana a fuskar Aunty Mama. Harma ta gagara daurewa ta ce, “Ni ɗin?”.
Da girmamawa Mama Balki ta amsa mata da, “Eh” tana murmushi. Kai Alajah ɗin ta jinjina, sai kuma ta furta, “Kuɗan jirani na kammala dinner to please, dan ina son mu ƙarƙare komai a yau tasan aikinta ni zuwa gobe zan koma”.
Kallon juna Azizat da Arwa suka yi, sai kuma suka saki murmushi suna kashema juna ido ɗaya. “Aunty Mama! Wai waye ake nufin za'a ɗauka aiki anan gidan? Badai wannan mai suffar mamiyo na ruwan ba?”. Kafin ni ko Mama Balki wani yace wani abu Azizat ta faɗa a zafafe har tana wancakalar da spoon ɗin dake hannunta. Kusan atare duk wanda ke'a wajen ya ɗago, a dai-dai nan mayen sirrintaccen ƙamshin turaren Maash kuma ya mamaye wajen. Dan haka hankalinsu ya rabu biyu. Yaran suka shiga gaishesa. Ban ji ya amsa musu ba, dan ban ɗago ba kaina a ƙasa ina ƙoƙarin danne abinda ke taso min akan wannan shegiyar Azizat ɗin. Zungurin da Mama Balki tai min ya sakani kawo nunfashi, na ɗan kalleta. Nuni tai min na gaishesa. Ban musa mata ba a taƙaice na furta, “Barka da dare” a hankali.
Kamar yanda bai amsawa ƙannen nasa ba nima bai amsa min ba. Dan haka na ɗago kaina cikin takaici, dai-dai yana kaiwa zaune a kujerar da ƙyaƙyƙyawar budurwar da zasu iya sa'anni da Azizat tai saurin gyara masa. Kasancewar kujerar itace ta kamar a ƙarshen table ɗin mu kuma muna daga farko tsaye yasa mukai facing juna. Wani kallon tsana naga Azizat na jefama budurwar, sai kuma ta cije lips ɗinta alamar dai akwai abin faɗa a bakinta amma babu dama. Sai daga baya na fahimci agolar gidan dake kusa da itace ta hanata magana ta hanyar riƙe mata hannu. Alajah ce ta katse yanayin da faɗin, “Azizat wai ina ruwanki da yarinyar nan ne? A kanki zata zauna idan ma anan ɗin zata zauna?”.
Baki sosai ta tura gaba. Cikin nuna jin haushi sosai ta ce, “Ni dai bana sonta Aunty Mama. Ba kuma nason ganinta dan na tsaneta. Idan kuma har akace a gidan nan zata zauna wataran sai na kasheta. Ta kwana da sanin marin da taimin wlhy sai ta biya bashinsa da fansar ranta....”
“K! K! Azizat ban gane ba. Mari? Wa ɗin aka mara? Waye kuma yay marin?”. Hajiyar nan da muka samu a falo randa muka zo wadda kuma Bahijja ta tabbatar min itace mahaifiyar Azizat ɗin kuma Yaya ga mahaifin Maash, sannan mai mulkin komai da kowa na gidan ta faɗa a wani irin fusace.
Kallon Alajah Azizat ɗin tayi, sai kuma ta ɓata fuska tana fiki-fiki da idanu. Da alama dai Aunty Mama ce tai mata gargaɗi. Tsawa mahaifiyar tata ta daka mata. Ba ita ba hatta ni sai da naji hanjin cikina sun wakita. A take kuwa Azizat ta fara rattafo bayanin komai daya faru a ranar da safen dalla-dalla harma da ƙarin gishiri da magi..........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_

........Wani irin huci Mahahaifiyar tata take tana kallon Alajah. Idanu Alajah ta rumtse tana ɗan dafe kanta. Sai kuma ta ɗago idanunta akanta. “Please Aunty Nafee relax. Bafa yanda kike tunanin al'amarin b....”
“Kamar ya ba yanda nake tunani bane Mashi'a! Ƴar aiki ta mari mun yarinya a gabanki amma ki gagara ɗaukar mataki sai ma ki hanata sanar min. Wai ke bazaki taɓa canjawa bane ba. Shike nan nagode, ai kin tabbatar min bake kika haifi Azizat ba. Da Imran ko Sahla ta mara ai da kin ɗauki mataki ko. K!! Kuma zaki ci ubanki. Zan sauke miki rawar kan da kika shigo da shi. Ai dama tun randa tazo dake na fahimci idanunki a buɗe suke irin na marasa mutunci.”
Idanu na na runtse sosai dan har cikin ƙwaƙwalwar kaina nake jin hargagin nata.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login