Showing 141001 words to 144000 words out of 438336 words

Chapter 48 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2208

salama da tsafta ita tana cikin ƙazanta. Saboda son zuciya kuma kuna lulluɓe duk wata hanya dazan fahimci haka. Shin dama kun tirsasani barin kulawa da itane dan ku tozarta min it...” ya kasa ƙarasawa saboda hawayen dake neman kufce masa. Ga wani irin masifar sarawa da kansa yayi cikin ƙanƙanin lokaci falon ya shiga juya masa. Hannu ya kai da ƙyar yana ƙoƙarin dafe kan amma hakan ya gagara, sai ma layi daya fara. Gaba ɗayansu sukai kansa hankali a tashe. Dai-dai ƙarasowar Paah inda yake ya tafi gaba ɗayansa zai zube ƙasa babu alamar numfashi tattare da shi. Da ƙyar Paah da Hajiya Mammah da Mummy suka iya tallabesa. Dan Maash tsayayyen mutum ne ƙaƙƙarfa a tsayensa. Ihun Azizat dake laɓe daga upstairs tana sauraren komai ya jawo hankalin su Hayatu dake main perlor. Da gudu ya shigo hankalinsa a tashe. Dama abinda yake gudu kenan tun farko. Tunda ya fahimci ran ogansa a ɓace yake yasan akwai matsala. Ba shi ba ko shi kansa ransa ya ɓaci da ganin yanda sashen Ummie ɗin yake. Yana ji a ransa kuma an jima ana wannan ha'incin sai yau ne ALLAH yayi asiri zai tonu. Dan a watan nan zai iya cewa ko sau ɗaya basu shiga ainahin sashen Ummie ba. A falon farko suke isketa a duk sanda suka dawo suka shiga dubata, kuma Hajiya Mammah ce kan tsatstsare ta babbake komai ta hanasu shiga can cikin. Ashe akwai abinda ake ɓoyewa.

★★★★...

Da taimakon Mama Balki na gasa jikina da ruwa mai zafi, dan duka dai kowa yasan na sha shi. Ina fitowa daga bayin zazzaɓi mai zafi ya rufeni, sai rawar sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan ciwo sosai har washe gari ina kwance, ban san abinda ke faruwa ba a gidan sai da safe bayan su Bahijja sunje sunyi aikinsu sun dawo kowa ya dawo sai naga ya dawo jiki a sanyaye. Hankali tashe na shiga tambayar Bahijja mike faruwa? Kuka ta fashe min da shi, kafin ta sanar min ai gidan ne babu lafiya ciwon Uncle Boss ya tashi. Da mamaki nake kallonta, kafin na ce, “Ciwonsa? Dama yana da wani ciwo ne?”.
Kai ta shiga jinjina min tare da sake fashewa da kuka. Cikin sarƙewar harshe da jan ajiyar zuciya irin ta mai kuka ta ce, “Eh, sai dai nima tunda nazo gidan nan sau ɗaya ya taɓa tashi masa. Amma yau naga hankalin kowa a tashe yake sosai alamar abin babbane. Dan naga har Baba prof ma yazo shi da akan daɗe ba'a gansa a gidan nan ba sai idan yazo duba Hajiya Babba ne ko wani babban dalili.”
Idanu kawai na zuba mata cike da nazari, kafin na ce, “Wane irin ciwo ne ke damunsa?”.
“Nima ban sani ba aunty Kandala. Yakan dai yanke jiki ya faɗi ne, daga nan yakanta ciwon kai mai tsanani har sai wani bawan ALLAH babban masani yazo ya bashi magani daga ƙasar Togo. Dan ance ya taɓa bama Hajiya Babba ma magani harta samu sauƙi sai kuma abin ya sake dawowa sab......” ta kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Mama Balki. Sai ma miƙewa da tai cikin wayancewa ta fice wai tana zuwa. Da kallo kawai na bita kamar yanda itama Mama Balkin ta bita da kallo. Sai da ta fice na sauke ajiyar zuciya mai nauyi ina maida kallona ga Mama. Itama ni take kallo yanzu. Sannu tai min da tambayata yaya jikina. A hankali na amsa mata, sai kuma na tashi zaune sosai dai-dai itama tana ƙarasowa inda nake ta ajiye kwanon hannunta. Hannun nata na kamo dan haka ta juyo tana kallona. Hawayen da nake ta riƙewa ne suka ziraro min.
“Ya salam Kandala miya faru kuma? Jikin ne?”
Kaina na shiga girgiza mata ina ƙoƙarin share hawayena. Itama sai kawai ta riƙoni jikinta tana lallashi. Tsawon lokaci muna a haka har sai da na daina kukan sannan ta ɗagoni, cike da kulawa ta ajiye abinci a gabana. Kaina na girgiza mata. Cikin damuwa na ce, “Mama na ƙoshi, sai dai ina son kimin wata alfarma”.
“Alfatma kuma Kandala? Ta mi?”.
“Ta bani tarihin wannan gida. Dan ALLAH mama ina son sani. Idan har kema kin sani badan ni ba dan rahamar da UBANGIJI yay mana.”
Jimmm tai alamar tunani, kusan mintuna biyu sannan ta nisa a hankali. “Kanda kin roƙeni tare da haɗani da wanda bazan iya bijirewa ba. Sai dai abinda kike buƙatar sani jinsa a bakina zai iya zama haɗari idan har wani ya jimu. Amma ina mai baki haƙuri da in sha ALLAHU watarana zan gaya miki duk abinda na sani. Dan ina aiki a ƙarƙashin wannan ahali tun ina da ƙarancin shekaru koma nace miki iyayena ma sun hidimta musu suma. Wannan baiwar ALLAHr da kika gani a halin jarabawar rayuwa yau itace ta suturtani da ilimin addini dana zamani dan kusan tare muka tashi da ita amma ta girme min. Ta kuma yimini aure da mutumin kirkin da ƙaddara ta rabamu badan mun shirya ba. Bayan rasuwarsa ne na sake auren Malam Umaru dake koyar daku karatun addini a yanzu. Abinda kawai nake so dake ki kula, gidan nan ya wuce duk yanda kike zatonsa. Ki bi komai a hankali kinji. Muma badan bazamu iya bane muka zuba ido sai dan anfi ƙarfinmu ne kawai.”
Ajiyar zuciya na sauke ina jinjina mata kaina. “Shike nan na gode Mama. Amma dan ALLAH ki amsa min tambaya ɗaya”.
“Ina jinki”.
“Dama haka ake ɗaureta?”.
Sai da ta ɗan waiga ta kalla ƙofa kafin ta juyi tana ƙara sauke murya ƙasa cikin raɗa.........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


.......“Sai idan Alhaji Ƙarami baya nan suke mata hakan. Da sunga zai dawo suke kwanceta su dawo da ita falon nan na farko shiyyasa bai sani ba. Yau ɗin ma ALLAH ne yayi da rabon zai gani kuma akai sa'a sarƙar taci mata jiki dan kwana biyu kenan da ɗauretan randa yay tafiya. Da alama kuma basu san yau zai dawo gidan ba ne shammatarsu yayi. Ban kuma san yaya akai yaransu basu sanar musu da shigowarsa ba dan mafi yawan masu aikin gidan nan su sukema aiki”.
Kasa daurewa nayi a zafafe na ce, “Mama dan ALLAH su waye wai?, Nasan dai harda Hajiya Mammah ɗin nan ko?”.
Kai ta girgiza min tana miƙewa. “Duk yanda kike tunanin al'amarin ya wuce haka kandala. Ke dai kawai kar ki saka kanki a masifa”. Daga haka ta nufi hanyar fita abinta.
Badan naso ba na yarda na haƙura. Sai dai maganganunta sun sake ruɗar dani matuƙa. Har takai damuwar dana sakama raina ta sake assasa zazzaɓina. Dan yinin ranar gaba ɗaya a kwance na yisa rijif cikin ciwo har washe gari ma. Sai a cikar kwanaki uku da faruwar al'amarin zuwa yamma ya ɗan sakeni naji dama-dama. Amma a haka Hajiya Mammah ta aiko a kirani a wannan ranar. Cikin dauriya da ƙarfin hali na isa sashen nasu. A falon ƙasa na samu su Azizat zaune kowa na harkar gabansa. Ko kallon inda suke banyi ba nai nufin wucewata. Amma sai kawai gani nayi ansha gabana. Ban yi niyar ko kallon ma wanene ba, na raɓa zan wuce aka sake shan gabana. A hakan ma ɗauke kaina nayi na koma damana nan ma aka sha gabana. Runtse idanuna nayi da ƙarfi tare da cije lips ɗina ina ƙoƙarin controlling kaina. Kafin na ɗago gaba ɗayana babu alamar wasa a tattare dani.
“Oh da kika ɗago a fusace kamar wata zakanya zaki dakeni ne?”. Maleeka ta faɗa a wulaƙance cikin huci. Maimakon amsa murmushi na sakar mata mai sanyi. Sai kuma na lumshe idanun na buɗe cikin yanayin isa da ƙasaita. A hankali na motsa lips ɗina na furta, “Karki fara abinda bazaki iya ba. Dan wannan kogin ko manyan jirage da takatsantsan suke gittashi balle ke da baki wuce matsayin jirgi mai saukar angulu ba”. Daga haka na raɓata na wuce abina. Da alama hausar tawa take ƙullawa da kwancewar fassarawa. A falon sama na sami Hajiya Mammah ɗin da Alaja. Cikin girmamawa na gaishesu, Hajiya ƙarama ta tambayi yaya jikina. Na amsa mata cikin nuna jin daɗi da kulawarta. Baki Hajiya Mammah ta taɓe, kafin ta kalleni a wulaƙance ta jefo min tambaya. “K kin iya girki?”. Ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sannan na amsa mata da, “Eh na iya Mammah.”
Sai da ta ɗan ƙara taɓe bakin ta cigaba da faɗin, “Kije ki mun abu mara nauyi yanzun nan. Ba kuma nason ɓata lokaci”. Kaina na jinjina mata ina miƙewa. Dai-dai zan bar wajen muka haɗa ido. Sosai zuciyata ta harba da ganin wani irin shegen kallo da take bina da shi na ƙwaf-ƙwaf. Sai dai ban kawo komai ba nai tafiyata ina mai karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta gareni. Inda nabar ƴammatan gidan anan na sake samunsu. Sai dai a yanzu hankalinsu baya kaina, amma da alama cecekuce da zagin da suke duk a kaina ne, dan haka har na wuce basu sani ba. Karo na farko na fara shiga kitchen ɗin gidan. Da mamaki su Aunty Kubrah duk suka watso min idanu, cikin dakiya na gaishesu tare da sanar musu abinda ya kawoni kitchen ɗin. Sai gani nai Aunty Falilah da Aunty Kubrah ɗin sun kalla juna suna yamutse fuska. Kafin Falilah taja tsaki ta cigaba da aikinta. Hakan da sukai min yay min ciwo, dan haka nima na watsar da su na ƙarasa shiga kitchen ɗin ina kallon tsarinsa da haɗuwarsa tamkar ba'a Nigeria ba. Dai-dai nan sai ga Mama Balki tamkar an jehota...
“Kandala miya kawoki nan keda baki da lafiya?”.
A shagwaɓe nace mata “Mama an sani aiki ne?”.
Cikin nuna mamaki tace, “Aiki kuma? Waye ya sakaki ke da baki da isashen lafiya? Kuma banan bane sashen aikin ki”.
“Nice ko ban isa ba?”.
Aka amsa mata daga bayanmu. A tare duk muka juya, jikin Mama Balki na rawa ta ce, “A'a Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki ai ban san kece ba.”
Tsaki taja tana ɗauke kanta ta dawo da shi gareni. Cikin isa da bada umarni ta lissafo min duk abinda take buƙata. Kafin ta kalla Aunty Kubrah tace ta sameta da black tea bedroom ɗinta tai ficewarta. Ina kallon Aunty Kubrahn ta bita da uwar harara, ni dai sai na fara ƙoƙarin neman tukunya hannuna dafe da kaina dan bana jin daɗin jikina da har yanzu. ALLAH sarki da taimakon Mama Balki nayi girkin, yanda take ta nuna damuwarta akan sakani aikin da Hajiya Mammah ɗin tayi sai ya dinga bani mamaki. Amma sai ban ce da ita komai ba ni dai dan bama fahimtar inda ta dosa ɗin nayi ba, na dai dinga ƙarfafa kaina dan na rage mata damuwa. Mun kammala da ƙyar ina faman dafe kai sai ga Hajiya Mammah ɗin ta dawo. Tsaf take cikin sabuwar kwalliya da alama wanka ta sake. Abubuwan dana zuba abincin ta shiga buɗewa a yamutse. Sai da ta gama tsaff sannan ta kalleni.
“Kije kiyi wanka ki sameni da kayan abincin bedroom ɗina”.
Karan farko na ɗan kalleta. Kamar zanyi magana sai kuma na fasa ganin harta juya abinta ta fice. Side ɗin da Mama Balki take na duba. Ganin yanda fuskarta duk ta nuna damuwa ya sani sakar mata murmushin ƙarfin hali. Itama murmushin ta ɗan sakar min. Fuska na ɗan ɓata cikin marairaicewa na ce, “Amma Mama matar nan ta cika mulkin mallaka da iyayin tsiya. Yanzu kai abincin ne sai nayi wanka? ALLAH kaina ke ciwo ina son naje na kwanta”.
Cikin yanayin damuwa ta amsa min da, “To yaya zamuyi Kandala. A ƙarƙashinsu muke ai. Sannu kinji ALLAH ya sawwaƙe. Kije kiyi wankan sai ki sameni na tayaki ɗauka kinji. Ni dai bana fatan a dinga yawan kuka da ke a gidan nan balle har a fara kaima Alhaji ƙarami ƙararki.”
Zuwa yanzu na fahimci wa take cema Alhaji ƙarami a gidan, dan haka bance komai ba na fita hannuna dafe da kaina. Kai tsaye sashenmu na wuce, na samesu duk sun koma dan yanzun lokacin hutunsu ne. Bedroom na wuce na shiga wanka. Bayan na fito na gyara jikina da ƙyau kamar yanda na saba sannan na fito. A'i ce ke tambayata ina zanje. Kai tsaye na bata amsa aikin da zanyi na dawo. Babu wanda yace komai face a dawo lafiya da Bahijja tai min. Nayi mamakin samun Hajiya Mammah a kitchen ɗin yanzu ma, sai dai ban nuna ba face gaisheta da nayi na fara ƙoƙarin haɗa kayan abincin. Ita kaɗaice a ciki babu Mama Balki. Ina gab da kammalawa akai kiran wayarta, sam ban maida hankali a kanta ba balle nasan da wanda take wayar, sai da ta ajiye kan wayar ta kirani da “K!” sannan na juyo.
Cikin yanayin kafeni da idanu tamkar zata cinyeni da su ta ce, “Ki haɗa abincin nan a wani tray ki kaima Awwab sashensa ki dawo yanzu ina jiranki.” ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sai da ta daka min tsawa sannan na amsa mata da to. Yanda ta bada umarni haka nayi, na haɗa komai a wani tray ɗin daban sannan nace mata, “Mammah ban san sashensa ba ai”. Shiru babu amsa, na ɗago na kalleta sai naga ta zuba min idanu ne kawai kamar ɗazun. Jinai raina ya fara ɓaci da kallon ƙurillar nan nata. Amma sai na dake na sake maimaita mata tambayar tawa. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tana mai ɗauke kanta daga gareni, sai kuma ta fice tana faɗin na biyo ta....

💢🌟💢🌟💢
💢✨💢✨💢

Cike da kulawa da tattali bayan Abba ya kammala cin abinci Mom ta kwanto jikinsa. Sai da ta saka hannunta cikin nasa murya a narke ta fara magana da kissa. “Nagode sosai Abban Abbas. Dan ALLAH ina sake roƙonka ka yafemin kuskuren da nayi, wlhy sharrin shaiɗanne amma bazan sake ba. Ni nasan kai mutumin kirki ne, dan gashi ka tabbatar min da hakan ta hanyar gyaran gidan nan da kayi. Kaga zamuyi bikin nan cikin mutunci batare da muma anga raggarmu an rainamu ba”.
Shiru Abba baice mata komai ba. Sai wani murmushin da ya saki mai faɗi da akwanakin nan baya barin fuskarsa. Ganin haka itama sai ta sake lafe masa a jiki da kai hannunta saman fuskarsa tana shafawa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata ba dan shima yana buƙatar hakan duk da gobe in sha ALLAHU amaryarsa zata iso gidansa. Amma yasan cakwakiyar da gobe zatazo da shi ba lallai ne ya kai ga hutawar ba. Dan haka ya biyema Mom ɗin. Sosai kuwa ya sami nutsuwa dan an bi da shi ta hanyoyin da shi a karan kansa sai da ya manta kan nasa.........✍️


_Hummmmm Abba adai bi a sannu ehe🥱_


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama




_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


......Washe gari Mom ta tashi da shirin komawa sashen da akaima gyara. Sai dai tsabar wuce wuri batayi hakan kai tsaye ba ta shiga gayyato ƙawayenta da maƙwafta ta waya wai zata shirya walimar komawar tare da bikin baikon Baby. Aiko zuwa sha biyu sai ga gida cike da ƙawayenta da maƙwafta da take ɗan gaisawa da su. Gida fa yaci decorretion harda su dj. Ana gab da fara shagali Gwaggo Gudidi da yaranta da wasu a dangi suka fara isowa da kulolin abinci. Duk da al'amarin ya bama Mom matuƙar mamaki sai tayi ƙoƙarin ajiye komai gefe tai tunanin ko Abba ne ya sasu suzo dan su tayata murnar baikon Baby ɗin. A take kuwa ta hau musu gwalangwaso har da habaici ƙawayenta ke jefa musu. Isowar su Gwaggo Gudidi baifi da mintuna talatin ba sai ga mata har mota guda daga Gwarzo. Sai ga Musaddiq da ruwa da drinks masu yawa. Anan ne fa al'amarin ya fara girmar kan Mom, ta tare Musaddiq da tambaya. Rasa amsar da zai bata ya sashi faɗin, “Mom kuyi magana da Gwaggo kamar zaifi”. Daga haka ya juya yay ficewarsa ya barta da kallon kallo tsakaninta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login