Showing 162001 words to 165000 words out of 438336 words

Chapter 55 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2211

sake jawota jikinsa ya rungume....

★“Umma ki buɗe min, na rantse da ALLAH Imamu bai isa ya kwana ɗakin tsinanniyar yarinyar can ba.”
“Jalilah bazan buɗe ba. Wai miyasa ke baƙya jin nasiha ne a rayuwarki. Wannan shirmen naki wai kina tunanin zai haifar mana da ɗa mai ido ne? A gabana a gaban ƴaƴanki fa ya rantse ya maya akan in har kika cigaba da ɗaga masa hankali sai ya sake ki babu ko shakka balle kunyata. Amma har kike kasa maida hankalinki jikinki ki nutsu mubi hanyar mai ɓullewa. Imamun yanzu fa ba irin na da bane ba. Ko so kike ya sake kin ki tafi ki bar mata gidan ne shike nan taci nasara a kanki?”.
Kuka mai ƙarfi Mom ta saki. Batare data amsawa Umman tata ba ta zube a wajen tana kara ƙarfin kukanta har numfashinta na seizing tamkar zai rabu da gangar jikinta. Duƙawa Umma dake cikin matsanancin damuwa tayi itama tana cigaba da lallashinta...

★Zumbur Halime ta miƙe tana zare idanu jin hannun Abba akan jikinta. Shima Abba sai ya miƙe cikin mamakinta ya kunna fitilar ɗakin. “Lafiya kuwa Halimatu?”.
Kai ta girgiza masa tan ƙoƙarin sauka a gadon, riƙota ya sake yi, sai kawai ta fisge hannun ta sauka gaba ɗaya har tana haɗawa da kamar gudu. Zuba mata ido kawai Abba yay mamaki na neman kasheshi. Itako tana lafe jikin bango sai zare idanu takeyi. Murmushi Abba yayi da girgiza kansa. Sai kuma cikin ɗan rage murya ya furta, “Kina son wani abu ne?”.
Kanta ta girgiza masa. Shima sai ya sake jinjina kan. “Okay miya faru to?”.
“Zan je falo na kwanta?”.
“Saboda me?”.
“Naga zaka kwana anan ne”.
“Ai nan ne ya dace dana kwanta Halimatussa'adiyya”.
Da sauri ta ce, “Hu'imm tabb”.
(Badaƙala) Abba ya faɗa a zuciyarsa yana cizon lips ɗinsa. Sai kuma yay ƙoƙarin sakkowa a gadon. Tana ganin zai nufota ta kwasa a guje zatai falo. Ai baima san lokacin daya buga tsalle ya cafkota ba. Kuka ta fashe masa da shi. “Dan ALLAH kayi haƙuri Alhaji. Ni wlhy babu ruwana bana so. Kai fa babba ne”.
Hankalin Abba tashi ya nema yi, a zuciyarsa ya ayyana (Haba Halimatu taya zan iya haƙuri da wannan baiwar taki) a fili kuwa sai ya jawota ya matse a jikinsa. Duk yanda take mutsu-mutsu yaƙi ya saketa. Dan ya tabbatar tana samun sa'a wlhy sai dai yaji a salansa. Shiko yanda ya samu ya killafa Mom ai gara dai ya angwance dan ganin Halime matsayin amarya zuwa gobe sabon show ne yasan zai tashi. Gara ya mora yasan ya mora duk ma wadda za'ayi sai ayi kawai ko.
Cak ya ɗaga Halime zuwa saman gadon. Aiko ta ƙwalla ƙara tana ƙoƙarin turesa. Duk da su Abba an girma ai ƙarfin ba ɗaya ba. Ganin ma tana neman tona mas asiri gida cike da ƴaƴa ga suruka ga Gwaggo sai kawai yay maganin bakin ta hanyar rufesa da nashi. Daga haka ya shiga tabbatar ma Halime shima ɗin da duk da shekaru sun ja da sauransa....

Wani masifaffen ihu da Halime ta fasa tuni ya gama karaɗe gidan. Sai ko a kunnen kowa musamman Mom data gagara rintsawa ita da Ummanta. Dan Gwaggo Gudidi tuni tayi barcinta hankali kwance. Wani irin masifar yankawa zuciyar Mom tayi. Sai ko gata ta ɓaro daga saman gado jikinta na masifar rawa da karkarwa. Ƙofa ta nufa cikin rufewar ido tana dannama Abba zagi da tsinuwa. Tana buɗe ƙofar tayo baya da sauri tare da saka duka hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta tana mai fashewa da kuka.. Cikin sauri Ummanta ta miƙe. Kanta tayo da sassarfa. Sai dai me, itama tana zuwa jikin ƙofar ta jiyo kukan Halime da roƙon da takema Abba. Tare da surutan Abba cikin sakin layi...
“A'uzubillahi minnashshaiɗanirrajim. La'ilaha illalahu Muhammadurrasulillahi Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Imamu ka gama tambaɗewa. Imamu kayi asara kayi girman kwabo. Wlhy ka gama watsewa Imamu gagararre mara mutunci” ta danna ƙofar da ƙarfi cikin sambatu da ruɗewa. Tuni tsohuwa ta rikice taji abinda yafi ƙarfin rashin kunyarta🥱. Yayinda Mom ta sake gigicewa dalilin salatin Ummanta. Sai kawai ta dinga numfashi da ƙyar kamar zata shiɗe.....

😒Mom ƙyale Abba kinji, ai zai dawo ne zaici mutanen garinsu gwarzo 🥱🤥.


💢💢💢💢

*_INDIA_*

A India kam sama da ƙasa an nema Mansoor an rasa. Dan a daren jiya ya gudu daga asibiti. Matuƙar ƙololuwar tashin hankali iyayensa da ƴan uwansa sun gama shiga. A take suka shiga bincike. Sai gashi an gano cewar yabi jirgin zuwa Abu-dabi a daren jiya. A yanzu hakama awanni biyu kenan da saukar jirgin.
Hankalin Mamy ne yafi na kowa tashi a wannan karon. Dan haka ta azalzalesu akan su bishi. Da farko Dad yaƙi bata goyon baya, sai da Attahir yayta roƙonsa dan shi baisan mike faruwa ba sannan ya amince bisa shawarar da tashi zuciyar ta bashi shima na bari suje ɗin yaga ƙarshen abinda Mamyn ke shiryawa. A ranar basu sami jirgin wucewa Dubai ɗin ba. Sai kuma hakan ma ya zame musu alkairi dan Mamy a daren ta samu labarin zuwan ƙanwar tata Nigeria, dan haka ta sauya akalar tafiyar tasu suma zuwa Nigeria. Dan ta tabbatar in har Mansoor yaje Dubai bai samu Sakinar ba shima Nigeria ɗin zai nufa.
Hakan kuwa ce ta faru, sai dai a washe garin ma basu sami jirgin Nigeria kai tsaye ba sai na Dubai ɗin. Hukuncin UBANGIJI a Dubai ɗin kuma sai jirgi ya haɗasu da Mansoor da shima zai wuce Nigeria ɗin. Nunawa yay ma kamar bai gansu ba, sai da Attahir yaje har inda yake ya masa magana cikin tsokana da lallashi sannan ya kulashi. Suma su Dad ya gaidasu a ciccinkushe. Shi dai Dad ɗin bai kulashi ba. Sai Mamy ce keta nan nan da shi.

Koda suka iso Nigeria tun a airport suka sake nema Mansoor suka rasa. Tashi hankalin Mamy ya sake yi, bata ko saurari Dad ba ta shiga taxi tace ya kaita anguwar su Sakina. Dan suna da gida anan Kano da in sunzo suke sauka. Attahir ne cikin damuwa yay ƙoƙarin tsaidata, amma sai bata ko sauraresa ba dan haka yay zuguy yana kallon motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Dad da shima yake tsaye cikin matsanancin ɓacin rai bai ce komai ba. Rasa abin cewa Attahir ɗin yayi, sai kawai ya duƙar da kansa yay shiru zuciyarsa duk a dagule dan shi kam ya rasa mike faruwa haka kuma a tsakanin iyayen nasu cikin kwanakin nan.....

💞⭐💞⭐💞

MAASH

Har dare bai san inda hankalinsa yake ba. Sai gabannin asubahi zazzaɓin ya sakesa. Ajiyar zuciya ya ringa saukewa a jajjere. Kafin ya miƙe zaune cikin dauriya saboda kiraye-kirayen sallar asubahi da ake tayi tako ina. Cikin nauyin jiki da rashin ƙwari ya nufi bathroom yana haɗa hanya. Ruwa mai zafi ya samu ya shiga. Sai da ya tabbatar ya ratsashi tare da watsakke masa jiki sannan yay wankan da alwala ya fito. Dukkanin sallolin daya rasa jiya saboda yanayin da yake ya fara ramawa. Bayan ya idar da sallar asubahi har zai kwanta sai kuma zuciyarsa ta gargaɗesa akan hakan. Alkur'ani ya ɗauka ya fara karatu, tun yanayi da ƙyar har jikinsa ya fara sakewa nutsuwa ta fara riskarsa. A jajjere ya dinga sauke ajiyar zuciya nan ma. Sai da ya kai har inda yake buƙata kafin ya miƙe ya hau gadon ya kwanta. Shi ba ma'abocin yawan kwanciya barci bane musamman ma na safe saboda yawan uziri. Amma rashin samun na dare yana kwanciya barci mai nauyin gaske yay awon gaba da shi...

A lokacin da Maash ke a sashensa yana fama da ciwo a ɓangaren Samraah tsaye take ƙyam akan ƙafafunta tana miƙama UBANGIJI kukanta. Kaso biyu bisa ukun daren ta rayashine da ƙiyamullail. Kafin ta ɗora da karatun Alqur'ani har asubahi. Tana idarwa duk da barcin dake a cikin idanunta haka ta ɗora shi ta cigaba dayi. Tanayi tana tofama a ruwan data ajiye botiki guda. Da yake tasa himma kafin goma tayi taci kusan izifi ashirin da wani abu. Motse-motsen da Ummie keyi ya fargar da ita, (yunwa) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin miƙewa. Ilai kuwa sai gashi tana farkawa da kiran sunan “Muhammad yunwa. Yunwa Muhammad” ta fara cin karo. Zumut ta miƙa ta nufeta har tana tuntuɓe da katifa............✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


........Sosai mamaki ya kama Paah jin wai Maash ya sake barin gidan. A take ya ɗaga waya yay kiran Hayatu dan yasan ko kiran Maash ɗin yay a yanzu ba lallai ya ɗaga ba. Dan a ganinsa har yanzu fushi yake akan abinda ya faru. Amsar da Hayatun ya bashi na tabbacin sun wuce ya sake tsaya masa a rai. Sai kawai yaji duk yana ƙara zargin kansa da kansa. Da sauri ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Babba. Sai dai me ya samu sashen a kulle. Kai tsaye zargin Maash ne ya kulle yazo masa. Jiki a sanyaye ya sakko yana jin lallai dole shima ya nufi Chaina a yau ko gobe su haɗu da Maash ɗin.


🌟🌟🌟


Cikin barci ya farka da matsanancin ciwon kai. Duk da yanda yaso samun nutsuwa hakan ya gagara. Har magani yasha duk da tsanar da yay masa amma ina. Ya jima yana tsintar kansa a irin wannan halin a mabanbanta lokuta. Sai dai na yau ya tsananta sosai. Dan duk yanda yaso sake komawa ya duba Ummie ya gagara hakan. Har dare yana cikin mawuyacin hali. Salla kawai ke tada shi. Ai kusan ƙarfe ɗaya babu shiri dole yabar gidan. Dan ji ya dinga yi tamkar ana masa yayyafi da garwashin wuta. Ya tsani gidan da komai na cikinsa matuƙa. Kasancewar cikin dare sosai ya fita a gidan babu wanda ya sani da ga ALLAH sai shi sai mijin Mama Balki da ya kira ta waya. Hatta da securitys ɗin gate sanin matsayin Malam Baba agidan yasa koda zai fita da baƙo babu wanda ya iya cewa komai. Azatonsu ma ko mai magani ne tunda yau ciwon Hajiya Babba ya tashi sosai tun safe aketa fama..
Can wani gidansa ƙarami dake a wata anguwa daban dole Malam Baba ya kaisa, anan yay jiyyar kwanaki uku ya dawo ragal, sai sannan yake ji a bakin Malam Baba ai jikin Ummie ya motsa sosai amma itama dai da sauƙi. Dan baƙuwar yarinyar nan na tsaye akan al'amarin dan ma taji mata ciwo. Kasa cewa komai Maash ɗin yayi, sai guri ɗaya daya zubama idanu kawai a yanayin da baka isa tantancewa a kansa ba....

★★★★

Sam gidan babu kwanciyar hankali. Dan tun washe garin da naima Ummie kitso jikinta ya birkice. Sai ma abin ya nema fin na baya. Dan a ranar naci ɗan karan dukan da kowa sai da ya tausaya min. Dan har asibiti sai da aka kaini. Duk da azabar wahalar da naci a hannunta hankalina nakanta. Sam na kasa samun nutsuwa. Akoda yaushe cikin nazari da aune-aunen abubuwa nake. Dan motsawar ciwon nata ya tsaya min a rai. Ga duk wannan abun da akeyi banga ko giccin ɗanta ba a gida. Alamu kuma sun tabbatar da baya nan kenan. Sosai naji takaicinsa ya mamayeni. Har inaji a raina anya mutumin nan da curin hankali a brain ɗinsa kuwa. Rashin man kan yayi yawa matuƙa. Mahaifiya ai tafi gaban wasa. Amma shi duk motsinsa dai a neman kuɗi yake kawai baya tuna gabansa da bayansa. Kai dolene na saita masa layi ko zai tsireni, tunda na fahimci maganata ta ranar bata dawo dashi a hayyacinsa ba.
Bayan kwanaki uku jikinta yayi sauƙi Alhamdullah. Haka na sake komawa gareta. Ranar kuka nayi sosai ganin sun ɗaureta. Haka na kwanceta ina zubda hawaye. Na rungumeta a jikina duk da nasan komai zai iya faruwa. Sai dai alhmdllh babu abinda tai min face kukan yunwa-yunwa. Yau ma kamar ranar haka na fita na nemo mata abinci, ina bata ta ɓingire barci. Gyaran sashen na shiga yi bayan nayi kiran Mama Bilki ita kuma ta taimaka ta mata wanka. Dan sabbin masu aikin nan da aka kawo fa sun gudu tun daren da abin ya faru ta fashema ɗaya kai. Bayan Mama Balki ta mata wanka da taimakonta na ƙarasa gyaran sashen. Sai ko gashi ita da shi duk sun dawo a hayyacinsu. Duk wanda ya shigo ma sai yayi sha'awa. Nata yima Mama Balki tambayoyi akan wannan al'amari sai dai bata ce da ni komai ba. Dan haka nima na haƙura na duƙufa kula da al'amarin Ummie ɗin tare da ƙara ƙaimi. Dan yanzu ruwa na samu na ajiye na gorori a cikin kowane kwana biyu saina sauke Alkur'ani a ɗakin da tofawa cikin ruwan. Sam na hana kaina isashen barci. Nama daina fita a sashen gaba ɗaya sai neman abinci. Da farko Hajiya ƙarama taso taka min birki akan abinda nake yi ɗin, sai Hajiya Mammah tace ta barni. Duk da abin ya bani mamaki dan ita ma nai zaton zata hanani sai bance dai komai ba. Sai daga baya nakema Mama Balki zancen, shine tace ai Paah ne yace a barni na cigaba da kula da Ummie ɗin, sai dai bata san dalilin Hajiya ƙarama na son hanani ba. Kodan ita likitace tana ganin kamar Ummie zata iya cutar dani ne oho.
Na gamsu da hakan, dan haka na cigaba da sabgata. Sai dai na sakama kowa na gidan ido dan ina son sanin wanda ke ɗaure Ummie ɗin a duk lokacin da ciwonta ya motsa....

✨✨✨💫

Tun asubar fari Mom ke bugama su Abba ƙofa. Amma babu alamar ma ya jita balle amaryar tashi. Sai dai abinda bata sani ba duk zagi da bugun da take musu yana jinta. Bashi da lokacinta ne kawai dan hankalinsa nakan Hamile dake faman masa kuka har yanzu. Babu irin taimakon da bai bata ba harda su magani amma yarinyar nan ta tasashi da kukan iya shege da duk ya hargitsashi. ALLAH ya soshi ma har kayan shayi ya shigo mata da su, akwai kuma kettle a ɗakin nata kasancewar ba'a haɗa mata hitter ɗinta ba na toilet yasa yayi dabarar ajiye mata kettle ɗin.
Tsabar iya shege irin na Halime Mom na buga ƙofar ɗakin tana zaginsu sai ta sake sakama Abba sabon kuka. A rikice ya riƙota jikinsa yana tambayarta mi take so. Baki ta laɓe tana sake saka kukan da turza ƙafafunta. “Ai dai Abba kai kace na girmamata. Amma gashi can tana zagar Innata da Babana bayan kuma Innata ta rasu. Ni wlhy bazan yarda ba.”
Cike da lallashi Abba ya sake sakata a jikinsa yana faɗin, “Kinga yi haƙuri barta, haba Halimatussa'adiyya na. Keda kike tare da mijinki ina ruwanki da duk abinda take. Ko kina so nima nayi miki kukan ne. Jibafa jikinki zazzaɓi ne ki kwanta ki huta ko na sake sakaki a ruwan ɗumin”.
“Uhm uhm” ta faɗa tana maƙe kafada da tura masa baki. Murmushi yayi da sake sakata sosai jikin nasa. Komai yarinyar tayi sake shiga masa rai take. Ga alkairin data kawo masa har gadon barcinsa na ƙara sakashi jin ƙaunarta mai tsanani da kimarta harma da mutuncin iyayenta. Shagala a lallashin Halime yasa bai san lokacin da Mom ta bar buga ƙofar ba ma. Yana samu tayi barci ya tashi yayi shirin massalaci ya fita sallar asuba. Da yakan bari gari yay haske sannan ya dawo gida. Amma yau ana idarwa ya dawo gidan. Wajen Halime ya koma sai da ya tadata tayi salla ya bata shayi tasha da magani tana masa taɓara yana lallashi, bayan ta koma barci sannan ya sauke ajiyar zuciya ya fito. Ɗakin ya rufe mata ya nufi ɗakin da Gwaggo Gudidi ta kwana suka gaisa. Acan ya samu Musaddiq wajen Gwaggo suna hirarsu hankali kwance. Dan haka ya zauna ana hirar da shi. Anan ne yake jin wai Musaddiq ɗin ya samu aiki a companyn Maash na ƙera motoci. Kusan satinsa uku kenan ma yana zuwa. A yanzu haka ma company ya masa alƙawarin turashi ƙarin karatu ƙasar Chaina. Gaba ɗaya sai yaji kunya ta rufesa. Yay ƙasa da kansa kawai yanata jinjinawa.
Daga Musaddiq har Gwaggo Gudidi sun fahimci kunya ta rufe Abba, dan haka Musaddiq ya saki zancen ya kama wani. Itama sai Gwaggon ta koma masa nasiha akan kada ya biyema Mom duk haukan da take a gidan kodan darajarsa matsayin namiji uba da kuma yaƴansu. Ya mata alƙawarin in sha ALLAHU bazai biye mata ba. Daga nan suka ɗan ƙara taɓa hira ya tashi ya fita zuwa ɗakin Mom ɗin.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login