Showing 186001 words to 189000 words out of 438336 words
aunty akan batun kuɗi. Mace ce mai son ace ita itace. Shiyyasa ko'a sutura bata saka ƙarama. Koda bazaka saya mata ba tasan buga-bugar da zatayi ta samarwa kanta. Hakan yasa ma kuke yawan samun matsala da ita. Dan idan ban manta ba har ƙararta kasha kaiwa gida akan wannan halin nata na idan taga abu a wajen wane sai da tayisa itama hankalinta ke kwanciya tun ma baka da komai. To awannan gaɓar ma bikin Mansoor take hari. Ta riga ta gayyato ƙawayenta ƴan ƙarya irinta da matan oganninka na wajen aiki, gashi kai kuma ka kwafsa mata kaƙi yarda da duk tsare-tsaren sharholiyar da muka tsara, ka kuma ce bazaka bata ko sisi ba. Haka shima Mansoor yaƙi. Attahir ne ma ya ɗan biye mata ya bata 1mil yace ta ƙara dana wajenta tayi haƙuri. Dan haka jin wannan batun video da maganar Attahir ta kawo mata wuta a cikin kai.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_
.......A ranar daƙyar ta iya barci kamar yanda ta faɗa min, washe gari tunda farar safiya tai kirana. Da farko kwana-kwana nima ta dinga min, sai da na nuna mata ta fito kawai a mutum muyi magana tasan dai ni mai rufa mata asiri ce sannan ta buɗe min komai. Koni zancen nata ya girgizani gaskiya. Bakomai yasa hakan ba sai jin batun Maash. Dan ni nasan wani abu kaɗan daga Maash ɗin sakamakon mijina yaronsa ne. Saboda a Companynin sa na Abayoyi dake anan Dubai yake aiki. Na buƙaci nima ta ɗan bani lokaci nayi tunani, ta roƙeni karna wuce yinin yau to.
Banko wuce yinin ba, dan ta hanyar mijina na ɗan ƙara bincika halin Maash da ƙarfin ikonsa. Amsar daya bani akan cewa Maash mutum ne murɗaɗɗe, sannan yana da zafi sosai. Amma da wahala ka masa abu a farko ya maida hankali a kanka. Sai idan ka cigaba da aikatawar ne, idan har fa ya maka gargaɗi na farko baya sake na biyu sai hukunci. Wannan amsa tashi ta bani ƙwarin gwiwa, dan koba komai dai mu ai bama fata bayan na farko mu sake, yo inama zamu sake ganinsa. Wannan ɗin ma rabonmu ne ALLAH ya kawo mana har gida. Husnah ta jima tana son Mansoor amma yaƙi saurarenta, aunty kuma taƙi ƙarfafa al'amarin duk da ta sani, dan haka kawai naga ai wannan wata hanya ce ta samun cikar burina, sannan nima dai dani za'a ci kuɗin. Kai tsaye nai kiran aunty muka tattauna da tsara yanda komai ya kamata ya tafi, tare da bada sharaɗin in fa har akaci nasara a 500mil inada kaso biyu. Ma'ana inada 200mil kenan. Aunty ta nuna min bazai yiwu ba, sai dai na amshi 100mil nayi haƙuri, tunda nasan abinda ke gabanta ai. Kai tsaye na fito mata a mutum. (Aunty ke tayaya kike tunanin auren Mansoor da yarinyar nan zai kuma kasance? Mufa zamu amshi kuɗin nan ne a hannun Maash da sunanta, idan ma har ya bibiya ita zai saka a kama. Sai dai auren Mansoor ya koma kan Husnah tunda dama ba'ayi invetion ba wai ko baki gane ba). Da sauri ta amsa min da hakane fa Sakeena. Wlhy kaina duk ya cure. Yanzu dai a daren nan zan samo video daga wayar Mansoor. Ke kuma sai ki samo mana Number Maash a wayarki. Na amsa mata da karta damu, kafin ma na samar da Number zan saka a fara aika masa saƙon barazana gidansa dan akwai wani yaron mijina dake tare da Maash ɗin kuma ya san sabon gidan nasa...
🌛❤️🌜
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso guesthouse ɗinsa. Gidane daya amsa suna gida sai dai bashi da girma sosai. Amma a ƙyau da tsaruwa ba'a magana. Dan yanda akai kusan rabin gidan da gilashi dolene ya ɗauki hankalin mai kallo. Ga wata green ciyawa da aka malala a harabar gidan aka ratsa lafiyayyen baƙin kwalta da mota zata iya bi kawai kota tsaya. Sai furanni da ƙamshinsu ya cika gidan da kukan tsuntsaye. Babu wani hayaniya, dan anguwar ma shiru ce sai uban karunuka ata waje duk da kuwa akwai securitys da baka isa ka shigoba sai da izininsu. Cikin girmamawa security ɗin daya wangale musu gate da remote ke ɗaga musu hannu, koda ya maida ya rufe motocin ya biyo. Dai-dai Hayatu na buɗema Maash mota ya iso wajen. Sannu da zuwa da gaisuwar girmamawa yake jerama ubangidan nasa. Maash dake ƙoƙarin fitowa hannu kawai ya ɗaga masa. Kafin bayan ya gama fitowa a motar a taƙaice ya furta, “How are you Semuel?”.
“I am fine Sir”. Samuel ya faɗa cike da zumuɗi. Ga bakinsa washe kamar gonar auduga. Dan ya jima baiga boss ɗin ba kasancewar kwana biyu bai shigo nan ɗin ba. Tamkar wani mai mulki haka yake tafe cikin takun mazantaka da rashin hayaniya guards ɗin nasa da su Hayatu harma da TJ da Samuel biye da shi. Hayatu ne ta ɗan gefensa amma ya zartashi a taku ke masa magana ƙasa-ƙasa. Shiko yana tafiya tamkar bada shi ɗin yake ba. Dan inda yake ajiye ƙafa kawai yake kallo. Da sauri wanda ke tsaye a bakin ƙofar shiga wajen ya wangale musu ƙofar shima tare da risinawa kwasar gaisuwa wajen boss. Hannu shima kawai ya ɗaga masa. Babu alamar damuwa a tare da shi alamar dai duk wanda ke tare da shi yasan ɗabi'unsa, da girmamawa ya cigaba da faɗin, “Sir ya iso tun kusan awa ɗaya. Kamar yanda ka bada umarni securitys basu barshi ya shigo da mota ba. Kuma da yaronsa biyu aka barshi ya shigo kawai.”
“Good job” ya faɗa a taƙaice yana tura kai ciki. Dan shima tun shigowarsu anguwar yaga motocin Minister ɗin tare da yaransa da aka dinkare a waje. Da ga shi sai Hayatu da TJ sai amintaccen guard ɗinsa Shu'aibu suka shiga. Kallo ɗaya yayima Minister da ya gama cika da takaici ya ɗauke kansa. Babu wani alamun damuwa ko nadamar shanyasa da yayi ya ƙarasa kujera ɗaya tal data banbanta da duk kujerun dake a haɗaɗɗen falon ya zauna. Wani shegen zaman ƙasaita da gadara yayi, yayinda Shu'aibu ya koma bayansa ya tsaya kamar saƙago. TJ ya ajiye kayan dake hannunsa a stool ɗin gefen kujerar na sashen damarsa. Hayatu kuma yakai zaune a ɗaya daga kujerun falon ta gefen kusa da shi. Bakin Minister daya miƙe domin girmamawa a washe kamar bashine ke faman tsinema Maash ɗin ba a zuciya. Amma kuma dama birgar ta bayan idoce kawai. A kallon ido cikin ido ko ganawar fuska da fuska Maash tamkar lu'u-lu'un narkakken ɗanyen zinare yake a cikin idanunsu. Duk da ƙarancin shekarun nan nasa shi fa takalmin ƙarfe ne baya takuwa a yanda kaso. To kaɗan daga aikinsa yace bazaiyi business ɗin da kai ba. Kuma babu ubanda ya isa yace komai, idan kuma kace zaka kona wajen wani saboda ka saɓa da Maash, to ka tabbata kuwa babu mai saurarenka kuma koda a ƙetaren ƙasar ne. Sai da ya tabbatar Maash ɗin ya gama zama sannan ya miƙa masa hannu cikin murmushi. Amma mi, sai Maash ɗin yaƙi bashi nasa, a maimakon hakan ma sai ya haɗe hannayensa biyu a daƙile alamar ya amsa masa. Shiko minister sai faman murmushin yaƙe yake dan abinda Maash ɗin yayi ya baƙanta masa zuciya, dan gaisuwar ma shine yayi Maash ya amsa a taƙaice. Bai nuna ya damu ba, dan lallaɓawa yake kasancewar ya jima yana neman alfarmar wannan zaman amma abin ya gagara, dan kusan wata biyu kenan. Yanzun ma da ƙyar sai da ya biyo ta wasu hanyoyin yaran Maash ɗin sannan ya dace. “Ranka ya daɗe ai kusan 1hour kenan da isowarmu”. Ya faɗa cikin son nuna an shanyasu a wayance. Kamar Maash ɗin bazai tanka ba dan hankalinsa nakan wayar hannunsa da yake daƙila, kusan minti ɗaya har ma Minister ya fidda rai da samun amsa sai tsine mar yake a zuciya a daƙilen nan ya furta, “10:30 ne ƙa'idar zuwana nan dama”.
Yawu mai nauyi Minister ya haɗiye yana jinjina kai da washe baki, “Hakane kuma gaskiya. Hakan ma na gode.”
Maash ɗin baice komai ba, sai ajiye wayar yay gefensa ya ɗan ɗago ya zubama Minister cat eyes ɗinsa masu kaifi da ƙarfin gani. “Zamu iya fara abinda ya zaunar damu dan banda lokaci”. Ya furta ƙasa-ƙasa batare daya janye idanun ba kuma. Ji Minister yay duk kamar ya daburce. Cikin sarƙewar harshe da in inar da bai san daga ina tazo masa ba ya fara magana yana kaɗa kai kamar tsohon jandala gwaja na ƙadangare.
“Yes! Yes mizai hana. Bussines ne dama nake son mu ƙulla ranka ya daɗe, na turoma PA ɗinka kuma dukkan bayanai na. Motoci nake son a shigo min dasu kamar guda dubu biyu, idan babu damuwa bana son su wuce wata biyar. Dan nayima yarona alƙawari bana son na saɓa. Sai dai za'amin alfarmar biyan kaso ɗaya bisa biyun kuɗin daga nan zuwa ƙarshen shekara zan sake bada kaso ɗaya kasan al'amarin namu harkar gwamnati tasa fidda kuɗi kai tsaye zai iya jawo mana matsala, next shekara a wata biyar ɗin farko sai na ƙarasa biya harma da ƙarin wasu kuɗaɗe a sama. Amin alfarmar nan dan ALLAH badan ni ba badan na isa ba. Idan kuma kana buƙatar kaya sai muyi gishiri na baka manda a shirye nake”
Shiru babu alamar Maash zai amsa saima cigaba da kallonsa yake wani ƙasa-ƙasa batare da yasan kallon na hargitsa jinin minister ɗin bane. Hayatu daya fahimci Maash bazaice komai bane ya fuskanci ministar a karo na farko. Kansa tsaye ya furta, “Sir amma na gaya maka akwai ƙa'idoji sosai, sannan mu bama bada bashi kai tsaye sai kabi dukan ƙa'ijin mu. Bazai kuma yiwu ka bamu kuɗi ɗaya bisa biyu ba mu kawo maka kaya. Ƙa'idarmu zaka bada biyu bisa uku ne, tare da takardun kadarorinka na adadin sauran kuɗinmu dake kanka, lauyanka da namu su saka hannu muma mu saka. Mune kuma zamu baka lokacin biya, sannan bama buƙatar kuɗin ruwanka, zamu sakama kayanmu iya ribar da muke buƙata ta cinikayya kawai wannan kuma sirrinmu ne. A sunayen motocin daka bada kuma akwai waɗanda dokar ƙasa ta hana shigo da su kwata-kwata. Mu kuma bama ƙimma doka biyayya saboda duk wanda zai mu'amalance mu dolene muma yabi tamu dokar, idan ya kauce kuma ya rage nasa. Da farko dai fara karanta wannan sune dokokinmu da sharɗin ƙulla kasuwanci damu first. Ƙa'idarmu kuma gani ɗaya ake mana, dan daga wannan zaman boss bazai sake zama da kai ba face to face. Idan ka shirya daga nan har zuwa 3 lokcinka ne”.
Tuni fuskar ministar na ƙoƙarin canja yanayi, amma dai yana ƙoƙarin hana bayyanar hakan. Takardar da Hayatun ya taso ya ajiye masa a saman table ɗin gabansa ya ɗauka. Da sauri ya ɗago ya kalla Maash ɗin da yay biris da su, dan idanunsa ma a lumshe suke kamar namai barci. Sai dai makirin tsaff yake kallon Minister da su har yanzu. “Amma ranka ya daɗe yaya haka? Sannan nace inada kaya a hannu ko yanzu zan iya baku su muyi ciniki nima”.
“Tsarin kenan?”. Ya faɗa a yanda yake alamar kunnesa dai na'a kansu.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_
.....Baki Minister ya buɗe zai sake magana Hayatu ya taresa da faɗin, “Ranka ya daɗe bama canjawa a yanda muke. Zaɓi biyune kawai yarda matsayin amincewa, ko haƙura ka nema wasu kuyi business ɗin kawai mu bamu da damuwa, sannan bama buƙatar wasu kayanka mu nan dan duk abinda muke nema mun san inda muke samunsa”.
Wani mugun yawu minister ya sake haɗiyewa. Ji yake kamar ya zaro bindigar jikinsa ya fasa kan Maash ɗin da shegen PA ɗin nasa ma kowa ya huta. Sai dai hakan bashi yiwuwa, dan Maash na zama ya zaro tasa bindigar ya ajiye ta yanda kowa yake ganinta ƙuru-ƙuru, idan girma ne da cika aiki kuma tafi tashi a komai. Ashe girman kai da wulaƙancin yaron nan da ake faɗa masa ma ya wuce duk hakan. Yaro ƙarami da bai wuce sa'an ƴaƴan cikinsu ba sai gara rayukansu yake akan tituna saboda ya tara dukiyar da ba'asan tayaya tai tashin hauhawar gwauron zabi cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Gashi ya mamaye komai sai da shi a manyan Business ɗin ƙasar da ada sune masu juyasu a yanda suka so. Dolene ma suyi maganin terror ɗin yaron nan da sam babu tsoro ko shakkar kowa a cikin idanunsa shege mai ido a tsakar kai. Wata fitinar zasu ƙullo masa ta yanda ko allura bai isa sake sarrafawa ya siyar a ƙasar ba cikin daɗin rai. Dan tsalle target ɗin su na farko akan ƙin ko ganin Bussines ɗin daya zo masa da shi bashi ke nuna zasu barsa bane, akwai plan A har zuwa Z da suka tsara a kansa....
Kallon agogo da Maash yayi ya saka Hayatu daya san abinda yake nufi faɗin, “Sir kowane irin lokaci boss zai iya barin wajen nan mi ka yanke?”.
Firgigit Minister ya dawo hayyacinsa. Murmushi danne ɓacin rai ya saki da faɗin, “Shike nan na amince ɗin”.
“Okay zamu iya fara ciniki, lawyer ɗin mu na hanyar zuwa nan ɗin. Muna fatan tare kake da naka kai ma?”.
“Eh muna tare, yana can waje inda securitys suka ce su tsaya.”
Kai hayatu ya jinjina kawai yana rubuce-rubuce a file ɗin hannunsa. Kafin ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyi huɗu daya zube a gefensa, danne-danne yayi tare da miƙewa cikin girmamawa zuwa gaban Maash. Amsa Maash ɗin yayi batare da yace komai ba. Sai da ya kai wayar kunnensa cikin bada umarni ya furta “Lawyer ɗinsa ya ƙaraso”. Daga haka ya miƙama Hayatu wayar. Amsa Hayatu yayi shi kuma ya ajiye masa file ɗin hannunsa a stool ɗin gefensa....
Ƙarfe kusan uku suka dawo gidan, a matuƙar gajiye ya shigo, ga kansa na masa ciwo sosai na hargagin da surutun da Minister ya sashi yi. Dama sun sauke Hayatu gida, shi da TJ ne kawai da guards ɗinsa suka ƙaraso nan. Kai tsaye ya wuce bedroom, ya bar Tj na ƙoƙarin kashe sauran abubuwan dake kunne a falon. Kamar yanda ya saba kansa tsaye ya buɗe ƙofar ɗakin nasa ya shiga da sallama ciki-ciki yana ƙoƙarin zame jacket ɗinsa. A kan Laalah idonsa ya fara sauka. Har zai fara fusata tunda ba barinsa yake ya shigo masa nan ya kwanta ba sai kuma idonsa ya sauka a kanta. (Ya ALLAH) ya faɗa acan ƙasan ransa. Dan wlhy shaf yama manta ya barta anan ɗin. Sosai ta wani lafe can jikin fuskar gadon alamar a tsorace tai barcin saboda Laalah. Saletaf da handcuffs daya saka mata kuma na nan duka. Wani irin murza goshin yayi. Sai kuma yaja sirrin tsaki a ɗan kausashe da nuna harzuƙa ya furta, “Laalah get up!”. Zumbur kuwa karen ya miƙe shege da kunnen maciji dan barci yake fa. Amma tun motsa ƙofar ya wani tada kunnuwa sama alamar saurare, da alama kuma tunda bai miƙe ba tun farko ya gane ubangidan nasa ne ya dawo. Ƙofar ya buɗe masa kawai ya ce, “Go and sleep, goodnight thanks”. Bindi karen ya kaɗa masa ya fita abinsa shi kuma ya maida ƙofar ya rufe tare da ƙarasa cillar da jacket ɗin daya cire ɗin saman sofa. Gaban gadon ya ƙarasa tare da lalubar aljihunsa ya ciro keys ɗin Handcuffs ɗin ya cire mata daga hannayenta, dama bai wani matse ba, sai dai hannunta bazai iya fita ba. Kamar wadda ke a ido biyu kuwa ta wani sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sosai da ya saka shi ɗan kallonta. Idanun ya zuba mata kusan sakan goma kafin ya kai hannun a hankali ya shiga ɗaye saletaf ɗin a hankali, da yaga zata motsa sai ya dakata. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta koma sai ya cigaba. A haka ya gama cirewa duka. Aiko ta wani turo lips dinta gaba da suka sake zama jazur suka tsuke sosai kamar an gyara mata su ne da gayya. Sai lokacin yaga sawun hawaye da suka bushe alamar an dai ci kuka.
(Trouble Maker ). Ya faɗa a ransa yana kauda kansa da barin wajen. Ta riga ta juya kwanciyar tata zuwa jikin fuskar gado, dole ya koma ta