Showing 423001 words to 426000 words out of 438336 words
farga da su. Miƙa musu Babyn yay yana tambayar Nurse ɗin matarsa fa. Cike da girmamawa ta sanar masa itama tana cikin ƙoshin lafiya. Suna kammala gyarata ma zai iya ganinta. Daga haka ta karɓi Babyn a hannun su Nasreen ta koma da shi ciki. Shi kuma ya ciro waya ya koma gefe. Paah ya fara kira ya sanar mawa. Dan zuwa yanzu kam tsakaninsu Alhamdullah, suna waya ko yaushe da mahaifinsu. Sun kuma cire komai a ransu hatta sauran dangin baban nasu suna kira. Farin cikin da Paah ɗin ke ciki har babu misali, haka ya yanke wayar yana murmushi yay kiran Ummie itama. Sai akai Sa'a suna tare da Mama balki da Mammi ma. Aiko suma dai can suka kaure da murna. Daga haka yay kiran Abba sannan Yaya Musaddiq da Hayatu sai su Fahad. Shi kansa yanda kowa ke farin ciki da zuwan Babyn tasa sai yake jin farin cikinsa na ƙara nunkuwa. Bare kuma da aka fito da Samraah zuwa ɗakin hutu. Bai ko ɗaga musu ƙafa ba yabi bayansu. Haka dole suka fito suka barsa suna dariya. Dan tuni ya rungume kayarsa yana bata kisses tako ina da sanya mata albarka.
Ban iya nace masa komai ba dan barcine sosai a idanuna saboda alluran da sukai min. Tun ina jinsa da ƙyau har na koma sama-sama barcin ma yay awan gaba da ni. Sai da nai barcin awa takwas cif sannan na farka. A lokacin kam baby na kusa da ni itama tana barcinta hankali kwance. Sai Nasreen a gefe zaune cikin kujera tana danna waya. Ta na ganin na motsa ta taso inda nake tana mun sannu. Kaina kawai na iya jinjina mata da tambayarta Yaya Awwab. Bakinta yama kasa rufuwa ta ce yanzu ya fita tarbo baƙi airport shi da driver. Sunzo da ga Nigeria. Nayi mamaki, su waye ya taso haka kuma tun daga Nigeria, muda ya kamata muyi shirin wucewa kuma tunda ALLAH ya ƙaddara anan zan haihu. Nurses ɗin ta kira min, suka taimaka min na ƙara gyara jikina, sai lokacin naga Baby. Idanu kawai na zuba mata hawaye na sakko min. Ni Samraah Abdul-wahab Gwarzo, Sam-G ce yau da ƴa ta mutum matsayin mallakina, tare da mijin da ban taɓa mafarkin samu ba a rayuwata. Dan ban taɓa koda kwatance tunanin Maash zai iya zama mijina ba. Tabbas tun a ganin farko dana masa jikin Magazine naji wani abu a raina game da shi, shiyayasa ma na dinga ƙoƙarin kushesa dan kar abinda najin yay tasiri a zuciyata. Saboda ina gani Mansoor ne kawai ya cancanta a lokacin, babu ma wani abu wanda zai tabbata makamancin abinda ƙasan zuciyata ya ke ji. Ashe shi UBANGIJI ya gama nasa tsarin. Ƙaddara ta jima da rubutuwa a cikin littafi. Sosai na rungumeta ina mai sake godiya ga UBANGIJI daya azurtani da wannan ƙyauta. A hankali na furta, “Ina neman miki tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa. ALLAH ya raya mana ke, ya albarkaci rayuwarki, ya sa ki zame mana ɗiya abar alfahari, yasa ki amfanar da kanki da addininmu da zuri'armu da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). ALLAH ya hanaki aikata shirka, ALLAH ya hanaki aikata zina, ALLAH ya hanaki aikata Maɗigo, ALLAH ya hanaki aikata sata, ALLAH ya hanaki cutar da kowa, ALLAH ya hanaki shaye-shaye da dukkan miyagun ayyuka. ALLAH ya tsarkake zuciyarki ya wadata ta da imani da tsoronsa, da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) mara yankewa ke da ƙanneki masu zuwa idan hakan na cikin ƙaddararmu”
“Amin ya rabbi ALJANNAR DUNIYA TA”. Aka amsa min daga baƙin ƙofa. Idanuna dake lumshe na buɗe, shi ɗin ne dai tsaye kamar yanda na sani kodan muryarsa data ratsani da kuma ƙamshinsa da sai yanzu na farga. Takowa yay a hankali zuwa garemu. Ya zauna kusa da ni yana mai rungumoni jikinsa ni da ita. Sai kuma ya kaimin kisses a wuya tare da raɗa min a cikin kunne, “Madalla da samun Uwar ƴaƴa ta gari abin alfahari miji da ƴaƴanta. Sannu da ƙoƙari Samrh. ALLAH yay miki albarka”.
“Amin tare da kai mijina. ALLAH ya bamu ikon bata tarbiyya kamar yanda iyayenmu suka bamu”.
Da Amin nan ma ya amsa. Kafin ya sanar min Ummie, Mama Balki, Paah, Baba, sai Mammi sun iso suna gida. Cikin zaro idanu waje na ce, “Kai My hot muda ya kamata ace mune zamu tafi mu samesu ma yanzu. Amma shine ka barsu suka wahala suka taho”.
“Sunce bazasu iya haƙuri bane ba. Yanzu haka ma da ƙyar na samu suka wuce gida nace musu za'a sallameki yanzu tunda sunce dakin farka ne. Kuma lokacin da suka tabbatar zaki iya farkawar har ya gota. Little Ummu tazo da farin jini”.
Murmushi kawai nayi ina mai girgiza kaina. Haka ya taimaka min shi da Nasreen muka kimtsa. Da taimakon Nurse ɗin nan mukaje mota. Suna mana addu'a da fatan alkairi muka wuce muka tafi. Mun samu iyayen namu kam zaune sunƙi ko cin abincin da aka taresu da shi suna jiran isowarmu. Ai motarmu na shiga suka firfito. Tun a haraban gidan suka tarbemu. Ummie ta rungumeni tana hawaye da sanya min albarka. Yayinda Baby na can hannun su Paah suma suna sanya min albarka da mata addu'a. A haka muka shiga cikin gidan. Dandanan fa tsohuwa Mammi da tazo da guzirinta na kayan wanka ta fiddo ta bama Mama Bilki akan a ɗora. Haka kuwa akayi, dandanan aka dafa Mama Balki tai mun cikakken wankan jego ina shagwaɓa ina wash tana lallaɓani. Yayinda tsohuwa da kanta ta sulluɓe baby tas ita kuma. Kafin kace mi mu duka an shiryamu tsaf. Ummie kuma ta dama min kunun kanwa da duk suka taho da kayansu, sai gasashen naman rago da yaji haɗi na musamman 😋🥱 sai uban ƙamshi gidan yake yi. Aka kuma baɗesa da yajin daddawa da suka taho da abinsu dai. Haka Ummie ta zauna cikin kulawa ta sakanni a gaba naci naman nasha kunun wai kuma sai ga tea, aiko na fara mata kuka wlhy na ƙoshi. Dole aka barni haka. Sai lokacin na samu mukai gaisuwa da su. Sunata ƙara jerama Baby addu'a da ni kaina. Kasancewar su a tare da ni ta ƙara min farin ciki da walwala. Haka mukai shirin kwanciya cike da kulawarsu. Baby dake barci tun ɗazun ta farka. Haka aka tsareni nai feeding ɗinta dan sunce yunwa ce. Na dai sha zafi, to amma yaya na iya tunda muma haka iyayenmu sukai haƙuri da mu a lokacin tamu haihuwar da rainon. Ga kiran waya tako ina shigowa yake kamar wayata zata tashi aiki. Kowa ya kira ɗaga masa nake. Dan masoyi na gaskiya ne ma zai tayaka farin ciki idan abin farin cikin ya sameka. Ya kuma tayaka kuka idan na jajen ya sameka. Nasha mamakin ganin harda Hajiya Mammah a masu kira, cike da farin cikinta kuma tanatama Baby Addu'a kuma dan tuni hotunanta sun kai garesu. Hakama Maman Malika da Malikar duk sun kirani. Suma zuwa gobe in sha ALLAHU sun ce suna tafe. Ƴan Kano ma harda wanda bamma yi zato ko tsammanin suna da number ta ba duk sun kira. Aunty Halime ce ke sanar min da aka faɗama Mom na haihu kuka wai ta fashe da shi. Gata babu isashshiyar lafiya. Kullum bakinta nakan Baby yanzu. Duk ta bushe ta lalace a tsaye. Ummanta kuwa wajen neme-nemen asirinsu taje mai mashin ya kadata a hanyar wani ƙauye ta karya ƙafa har waje biyu. Cinya da gwiwa. An ɗaura baiyi ba aka sake har sau uku. Ga ƙafar nan tana neman zame mata jangwam. Dole sai ƙanwar Mom ɗin ce tazo tana kula da ita. Ita Mom ɗin taƙi wai abarta ta kanta takeyi. Abinda ya dameta shi ya dameta. Umman tata dai har ranta ya ɓaci taita kuka akan furucin Mom ɗin tana ja mata ALLAH ya isa da faɗin ai duk ta dalilinta ne komai ya faru da yaƴanta, amma shine zata mata sakayya da halin ko'in kula........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
.......Washe gari su Maman Malika da Hajiya Mammah suka iso suma. Hakan sai ya sake bani mamaki. Na tambayesa wai ba gida zamu tafi ba. Dan ina jin kunyar tambayar su Ummie. Shine yake sanar min ai batun tafiya babu shi. Babu mai kwasarma yarinyarsa sanyin jirgi. Za'ai suna anan kawai. Hankalina ya tashi, ta ina zan yarda da hakan. Idan shi danginsa na da ƙarfin tahowa nan ni kuma nawa fa? Ai ni za'a cuta kenan. Bamu ƙarasa maganar ba ya fita saboda kiran da akai masa a waya. Dama ya shigo ne mu gaisa da safen nan bayan Mama Balki ta mun wanka Mammi tama Baby. Da wannan damuwar na yini a rai dan bai dawo gidan ba har su Hajiya Mammah suka iso. Ummie ce ta ɗan lura da yanayina shine take tambayata mike damuna. Har nayi niyyar ɓoye mata sai naga bayan ita inada wata uwar ne. Sai kawai na fito na sanar mata ina hawaye. Murmushi tayi da rungumeni, cike da kulawa ta ce, “Karki tada hankalinki kinji yarinyata. Nima ina bayansa, dan ba baby kawai ba koke bazan yarda kisha iskar nan ba. So nake ki samu jego mai ƙyau da kulawa. Shiyayasa ma muka taho nan. Tunda kuma kikaji ya faɗa nasan yanada nashi shirin shima a ƙasa. Dan yanzu haka bamu jima dayin waya da Gwaggo Gudidi ba ma. ALLAH ya ƙaddara anan ɗin za'a haihu, sai kawai ayi haƙuri a ƙarasa komai”
Kaina na jinjina mata ina godiya. Daga haka muka cigaba da sabgogin mu. Bai dawo gidan ba sai dare. Koda ya shigo muka gaisa ban masa maganar ba. Sai ma zancen isowar su Yaya Musaddiq da Hayat gobe idan ALLAH ya kaimu yay min. Tare da nuna min wasu kaya wai idan ina son su zasu taho dasu ne. Idan kuma bana so su barsu kawai. Cikin farin ciki na sanar masa ni komai ransa ya biya masa yayi basai ya bi takaina ba. Daga haka mukai ƴar hira yana rungume da ƴarsa sai da Ummie tazo ta korashi. Dan tare da Mama balki muke kwana anan.
Washe gari kamar yanda ya faɗa da yamma sosai sai ga ƴan China sun iso. Basufi awa biyu ba sai ga kuma ƴan Spain suma. Hafizzullah, da Fahad da Bahijja. Aiko gida ya sake kacemewa. Dan har ma ya fara mana kaɗan. Sai da aka buɗe na kusa da mu ban taɓa sanin nashi bane ba sai yau. Ina dai ta ganin gidan a rufe koda yaushe sai nayi tunanin masu shi banan suke zama bane maybe zuwa suke time to time yin hutu kawai. Wannan taron ya sa naji a raina dama ya shirya abinsa fa. Dan tabbas-tabbas a haka yaso al'amarin ya kasance. Shiyayasa ya dinga min wayo da su Ummie ɗin kansu wai sai na shiga watan haihuwa saboda doctor yace ina son kulawarsa. Kai ya Awwab sai a barsa dai kawai. Yanda kowa kenan nan da Baby nece lallai kam naga haihuwar dangi. Dan daga Fahad har Yaya Musaddiq, aunty Falaq da Yaya Hayatu uban kayan da sukazo da shi na baby sai kawai nai tagumi ina kallonsu. Bayan ma anan shi uban gayyar ya loda wasu, saboda har ɗaki an haɗa mata. A ɓoye kam sai da nayi kuka Bily, dan sai nake jin kamar soyayyar ma ta mana yawa.
Mammi dai ta kafa ta tsare, duk abinda ake mun na jegon nan irin na mutanen da ne. Tsohuwar nan da uban guzirinta ta taho na kayayyakin itatuwa. Ga Hajiya Mammah nata ƙoƙarin ganin ta goge laifinta, sai dai fa masifar tana nan, wannan kam sai haƙuri dan kowa yasan halittarta ce. Itama Aunty Mama a yau ta iso da nata yaran. Sai fa aka sake kacamewa. Jikina duk ya fara yin sanyi, ƴan uwana uku ne fa sai matar Yaya Musaddiq a cikin duk wannan taron. Ina zaune a ɗaki nayi tagumi na saka Baby da nake feeding gaba da kallo ya shigo da sallamarsa. Ganin yanda ya tasamu gaba da kallo idanunsa ƙyam a kammu yasa naji kunya, janyeta nai na gyara jikina na miƙa masa ita. Ɗan murmushi yay da faɗin, “Oh baki so naga kina mun feeding Mamana?”.
Nima murmushin nayi ina ɗan girgiza kai, na ce, “Kai yaya kunya kuma. Kawai dai naga baka ganta bane tun safe shiyayasa. Ka dawo lafiya?”.
“Alhamdullahi, kuyi haƙuri na kasa baku attention ɗina yanda ya kamata. Ni kaina ina son ko yini ɗaya nai a gidan ayi jegon da ni amma uziri yamun yawa”.
Cikin ƴar dariya na ce, “Namiji kuma da jego? Kayi harkokinka mu zamu maka jegon”.
“Kin tabbata?”.
Na jinjina masa kai alamar tabbatarwar. Murmushi yay shima tare da ɗan jamun hanci. Sai kuma ya ɗan bata fuska da faɗin, “Duk sun saka min ke kinyi duhu. Nace ma Ummie a daina miki amfani da wannan ruwan zafin ga wani traditional medicins a ciki dani ko kallonsu ma bana son yi amma Ummie tace babu ruwana. Kema baƙya so ko?”.
Fuska na marairaice masa ina kwanciya a jikinsa da faɗin, “Yaya bawai fa ina sha bane ba. Kuma suna da amfani sosai. Duhun nan kuma wanka da ruwan zafi ne yasa ba wani abu ba. Zamu washe ne. Ni yanzu ma ba wannan ba, wai taro zakayi ne naga invition card a hannun su Hafizzullah?”.
“Eh mana, ALLAH zai mun ƙyautar nan ne ban nuna farin cikina ba. Banyi na aure ba fa, dan ina kishin Matata. Wannan kuma ya kamata nayi dan kowa yasan Maash ya zama Baba shima”. Ya ƙare maganar da kashe min ido ɗaya. Murmushi kawai nayi da faɗin, “ALLAH to ya taimaka. Amma a ƙasan raina ina jin damuwar babu nawa dangin sosai a cikin sabgar. Ya jima a ɗakin sosai yau kam Hajiya Mammah tazo ta korashi. Ni saima suke ban dariya. Duk yanda suke tunanin rashin kunyar Yaya Awwab yana kuma fa da kawaici. Duk abinda kuma yasan zan cutu yana matuƙar ƙoƙarin kauda masa ido koda yana a buƙace da shi, dan ni kaina nasan a takure zai kasance a tsakanin nan. Amma idan bashine yaso ka fahimta ba bazai taɓa nunawa ba. Washe gari na tashi sukuku dan sabgogin bikin suna sun kankama a ƙasar da ba tamu ba. Sai kawai gasu Hafizzullah da Fahad suna shigo da kaya. Da mamaki nake kallonsu saboda a lokacin na fito zan nunama Aunty Falaq abu a kitchen basu ganshi ba. Ga Nasreen sun fita ita da yaran Aunty Mama kasuwa. Gaba ɗaya sai na saki baki da hanci da idanu ina kallon masu shigowar. Abba ne kan gaba. Sai Gwaggo Gudidi da aunty Halime Aunty Zakiyya a bayanta ɗauke da Babyn aunty Haline ɗaya. Sai Mom a ƙarshe Bibaa da Auta biye da su, sai Matar Kawu Musa da ta Kawu Sabi'u da Aunty Magajiya. Na zata sun ƙare sai ga Adda matar Uncle Sulaiman da yaranta sai Mamin su Mansoor da ƙannen su Mansoor ɗin biyu da matansu, sai uwargidan Sheikh, maman Bahijja kenan. (Ikon ALLAH, sai kace ba daga wata ƙasa zuwa wata bane)