Showing 432001 words to 435000 words out of 438336 words
kenan. Da dare aka shirya zuwa dinner, anan ne kam dole suka tafi tare da mu. Dinner tayi ƙyau sosai, sunyi bajinta dangin ango suma. An gabatar damu a matsayin dangin mahaifiyar su, dan haka muka buɗe bakunan bags muka zuba liƙi muka fiddasu kunya. Daga nan za'a wuce da amare ɗakinsu. Dan su biyar ne cif. Akwai sauran ƙannensu da suke uba ɗaya suma. Kawai sai me bawan ALLAH ya gudu da ni hotel. Hankalina ya tashi dan na zata inda har su Paah da su Abba suke ne. Sai na samu ashe wani yaje ya kama ba inda akai musu masauki ba. Dana dage banzan shiga ba ɗaukata yay camak yay ciki dani, a ɗakin kuma ya hanani ƙwaƙwƙwaran motsi sai da yay min biji-biji da har sai da nayi kuka. Dan dole na shiga ruwan zafi sosai inajin kamar na masa ALLAH ya isa a zuciyata na dai danne. Koda ba fito daga bayin ban kulashi ba na hau shirin komawa can gidan, dan nasan dai an riga an kai amare yanzu. Amma sai ya ƙi kulani ma yamayi kwanciyarsa. Dama Heedaya na wajen Ummie. Kuka na fara masa amma ya shareni, haka dole na haƙura muka kwana anan. Washe garin ma bai maida ni ba sai yamma lis. Na je su Aunty Falaq suka tasani gaba da tsokana. Sai da nai musu bore suka barni. A daren ranar shi da tawagarsa suka bar ƙasar, mu kuma muka ƙarasa shagalin bikin washen gari. Sai lokacin nake jin ashe an maida auren Hajiya Mammah ɗin da Baban su Azizat jiya. Na tayasu murna gaskiya. Dan rabuwar kan iyaye damuwace.
Muma a cikon kwana uku da gama biki muka koma Nigeria. Babu zama Ummie tai mana shirin na musamman bayan kwana biyu kowacce ta nufi mijinta. Mukaje kowacce kuma ta tadda nata sabon ɓacin rai. Da dai aka hau saman kuma sai aka dawo aka shirya kamar komai bai faru ba. Lamarin mata da miji sai ALLAH ai daman. ALLAH ya ƙara mana haƙurin zama da juna.. A wannan yanin ne kuma wani gagarumin cigaba ya tasoma Yaya Awwab. Planing ne na tsawon shekaru da yake yi sai yanzu ALLAH ya kawo iyaka. Haka ya kwashemu zuwa ƙasar saudia. Watanmu biyu a can har su Ummie suka zo suma suka samemu akai shagalin tare da su. Bayan munyi aikin Hajji muka wuce da su Dubai. Can ma zasu kwana biyu dan Paah na can yana wani aiki shima. A wannan ɗan tsakanin aka saka bikin Bibaa. Zuwa Nigeria ya kamamu dole kenan. Dama shi Yaya Musaddiq bai koma China ba tun haihuwar Aunty Ruƙayya. Akwai abinda yake yi mai muhimmanci a Nigeria ɗin sai ya kammala zasu koma dan yanzu ya kammala karatun nasa sai wasu courses da zai yi sai kuma Business da Yaya Awwab ya ɗaurashi a kai. Dan yanzu Yaya Musaddiq ɗin bana da bane ba. Ya zama komai Alhmdllh, ba nauyin iyalinsa kawai ba na ƴan uwa da yawa ma yanzu a kansa yake. Dai-dai gwargwado yana kamantawa. Sannan komai na gidan Abba yanzu ya koma kansa. Ya zama tauraro uba a cikin zuri'armu.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
......Hidimar bikin Bibaa yayi dai-dai da haihuwar Bahijja da kuma sake haihuwar Aunty Falaq. Ta sake sulluɓo mana baby boy, yayinda Bahijja tai baby girl itama. Haka fa muka rankaya sai Nigeria. Sai da aka fara shan shagalin suna a Lagos da kusan sati ɗaya mun gyagije gajiya sannan muka ɗunguma zuwa Kano harda masu jegon. Sosai Mom bata da lafiya. Dan komai na fanin uwa Aunty Halime kema Bibaa, fannin Uba Yaya Musaddiq duk da Mom ɗin da Bibaa ɗin na nuna basa ra'ayin hakan. Babu wanda yabi takan su dan al'amarin Mom na bama kowa tsoro. Matar nada taurin zuciya matuƙa da girmama ƙiyayya. Ita har yanzu taƙi yarda nagaba yayi gaba fa.
Muna isa muka sake maida biki namu dole kuma aka sakar mana. To itama dai mijin Bibaa ɗin sai a hankali. Dan ɗan kwalta ne irinta acan suka haɗu a tazubar ɗin su. Saboda a yanzu kam tsiyar da Bibaa ke tsulawa tacema Baby bata iya komai ba a sanda tai nata yayin. To koma dai miye tunda sun zaɓi zaman aure ai sai a taya musu suje can su ƙarata. Haka dai aka ɗaura aure muka sha dinner ta ƴan kwalta. Ango da kansa ya wuce da amarya gidansa. Mu sai muka koma gida. Sai washe gari mukaga gidan amarya. Gida dai na haya ne kuma ita ta kama da kanta. Kayan cikinsa kuma mune muka zuba su. Dama kuma bai mata lefe ba. ALLAH na tuba sadakin ma da yaya. To mudai munyi walima muka kamo gabanmu. Inda a daren Yaya Awwab ya kirani da sabon tashin hankali ko farin ciki zamu ce oho. Ya tabbatar min an gano inda mijin Baby yake. Ya kuma fahimci an ganosa yanzu haka ya sami issues mai ƙarfi cewar ya ɗakko Baby ya taho Nigeria da ita. Dan haka koda yaushe zamu iya ganinsu. Rasa dawa zanyi maganar nai. Sai kawai naja bakina nai shiru. Amma gaba ɗaya na kasa zaune na kasa tsaye nikam. Har safiyar washe gari kunnena a waje. Dan muna gidan Abba ɗin har yanzu. Dangi ma na Gwarzo duk basu wuce ba dan yanzu suna da ƴancinsu a gidan. Kwatsam bayan sallar la'asar mukaji hayaniya da iface-iface a cikin layi. Tun muna tunanin daga ina har dai muka fahimci anan gab da mune. Sai ga Hafizzullah ya shigo da gudu ya ɗauki taɓarya zai fita. Riƙeshi mukai muna tuhumarsa. Shiko yana fiffisgewa cikin fushi da faɗin mu sakesa. Wlhy da hannunsa zai kashe mutumin can. Tashi hankalinmu yay matuƙa dan bamu san wane mutum bane. Da ƙyar muka turashi ɗakinsa muka rufe. Yanata faman jijjiga ƙofa yana kuka da mana magiyar mu buɗesa. Bamu buɗesan ba mundai fita muma. Sai muka samu matasan anguwa sun ma wani jina-jina a kwance da alama ma baya numfashi sam. Tacan cefe ɗaya kamar mutum a kwance an lulluɓe da abu. Ga wari babu daɗi masu kallo nata toshe hanci. Wasu ma na kuka. Furucin makwafciyarmu da fasa kukan Baby data ambata yasa mukai wajen. Jikin Mom da itama ta taƙarƙara ta fito har ɓari yake wajen yaye mayafin da aka sakama Baby. Ai sai ta fasa gigitacciyar ƙara kawai ta zube a wajen sumammiya. Hankalinmu ya sake tashi muma dai muka isa wajen. Tabbas Baby ce kuwa ta rame matuƙa tamkar skeleton, sai idanu ɓulu-ɓulu babu ƙyan gani. Jikinta duk wasu irin ƙuraje, abin tashin hankali tsutsotsi sunata fitowa ta kamar bayanta. Ai dole aka maidata aka lulluɓe da sauri. Dai-dai nan jami'an tsaro suka zo. Mutumin da akaima kaca-kaca da jini suka ɗauka. Sai lokacin naji wasu na faɗin ai mijin Baby ɗinne. Kuma da alama ya mutu ma. Ashe zuwa yay kawai babu tausayi babu imani ya jefar da ita a ƙofar gidan tare da wurga uban kudi a kanta zai taka mota ya tafi matasan anguwa suka riƙeshi. Akaje wani shago akai kiran Hafizzullah. Ai yana zuwa yaga Baby da bayanin da akai masa ya kama jibgarsa. To yanzu Hafizzullah ɗin bana da bane. Ya zama cikakken saurayi ga ƙarfe yana ɗagawa duk ya wani buɗe. Ganin irin dukan da yake masa suma matasan anguwa suka tayashi. Ganin haka ya shiga ɗakko taɓarya wai sai kwankwatsesa. Shine fa har muka farga.
Ana barin wajen da shi Hafizzullah ɗin na fitowa da alama ɓalle ƙofar yayi. Da ƙyar aka daddanesa ana bashi haƙuri da tabbatar masa ƴan sanda sun ɗaukesa da alama ma ya mutu. ALLAH sarki ɗan uwa, sai kawai ya zube a wajen yana kuka kamar yanda yaga munayi. A haka Abba da Yaya Musaddiq da aka kira a waya suka iso. Sai shima Abba kawai ya shiga kukan jikinsa na rawa har yana neman faɗuwa. ALLAH dai ya kiyaye Yaya Musaddiq ya riƙeshi. Ganin mutane nata sake cika wajen aka shiga da Mom da Baby da ke bin mutane kawai da idanu. Babu wanda zai san Baby a baya ya yarda itace wannan a yanzu. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ya rabbi kasa mu gama da rayuwa lafiya. An sakama Mom ruwa ta farfaɗo, yayinda dole aka rufe gida fa aka hana kowa shigowa. Kuka Mom take na fitar hankali daban tausayi. Faɗi take ta cuci kanta, bazata yafema mutumin nan ba. Ummanta ta cuceta, ta zalunceta data ɗaurata akan wannan mummunar rayuwa. Ita inama ta mutu ta huta. Tana wannan sambatun akaga Baby dake hawaye itama na ƙoƙarin yin magana. Dole aka shiru tare da tsawatar ma Mom domin saurarenta. Dan Muryar bata fita da ƙyau.
Cikin jan numfashi da ƙyar irin na mai kuka ta ce, “Mom ba Umma ce ta cutar da ke ba kece kika cutar da kanki sannan muma kika cutar damu. Dan ko tantama banayi alhakin su Samraah ne da Abba ke bibiyarmu. Kin sha sakama Abba kayan asiri a gaban idonmu cikin abinci ko ruwa ko ƙofar shigowa gida amma bamu taɓa sanar masa ko hanaki ba domin bama mahaifinmu kariya. Kin sha yima su Yaya Musaddiq asiri dan su koma ƙasan mu. Kin sa Abba ya cinye dukiyarsu ta gado, dan hatta gidan nan da muke ciki ainahin gidansu kika saka ya sayar ya siyamana wannan. Kin hana Abba ya sakasu a makaranta mai ƙyau. Shi Yaya Musaddiq ma daga secondary bai cigaba ba. Kullum fatanki ALLAH ya bama Samraah mijin da zai wahalar da ita, talaka, hatsabibi shaiɗani koma a mata cikin shege a titi. Kina hanasu abinci, duk wanda yazo domin taimakonsu sai kin rabashi da gidan nan. Daga ƙarshe ƙwaɗayinki ya sakaki haɗani aure da wannan mitumin da sam baya jin tsoron ALLAH. Tun a zuwan farko kuka baɗesa da asiri ke da Umma wai a riƙeshi da ƙyau saboda ya muku alƙawarin zuwa Saudiyya. Bakuyi bincike a kansa ba kuka hana Abba yayi kika aura min shi kuna murna. Ga sakamakon hakannan, ya kaini wata ƙasa yana luwaɗi da ni, abokansa nayi. Idan ban yarda ba su dakeni su ɗauri suyi ta ƙarfin tsiya. Ba kuma mutum ɗaya ba su da yawa. Wani lokacin har suma nake dan wala suna ciyar dani abinci mara ƙyau. Suna shan magani domin kare kansu daga cututtuka amma ni basa bani. A haka na fara ciwo. Yau wannan gobe wancan har aka tabbatar musu da na kamu da ƙanjamau da ciwon hanta dana ƙoda. Hakan ma kamar daɗi yay musu. Sai suka daina min komai suna saka karnukansu nayi da ni a madadinsu......” kuka sosai ya sarƙeta. Muma kukan mukeyi, sai da tayi sosai ta cigaba da faɗin, haka zasu ɗaureni subama karnuka ni suyi amfani dani, har ciwon jikina ya fara bayyana ƙuraje suka fara fitomin. Ga tsutsotsi ta gabana da bayana. Shine yace zai maidoni gida dan ya bama iyayena kuɗin da suke ƙwaɗayi a wajensa gasu ya samu dani fiye da yanda yay fata. Dan burinsa ya cika na mallakar kuɗaɗe masu nauyi, samoni ya zame masa alkairi har an bashi muƙami a ƙungiya. Mom ki dubeni, miya rage mun, mi kuma ya rage banda jiran ranar mutuwa ta. Ni kaina nafi son na Mutu, bana son wannan duniyar Mom bana son ta. Inama ace baya zata dawo, dana goge abubuwa da yawa a rayuwata. Inama ace nice ke Samraah. Gaki nan kinyi aurenki, da alama ma har kin haihu dan Babyn hannunki na kama da Maash sosai. Babban tashin hankali na ƙilama makomata wutace, dan faɗar ALLAH ce wutar masu aikata abinda akai shekara kusan biyu anayi dani daban take. Kaicon na, kaiconki Mom, kaico da samun uwa irinki Mom. ALLAH ya isa tsakanina da ke bazan yafe miki ba ke da mahaifiyarki. Indai inada hakki a kanku ALLAH yay gaggawar saka min......”
Kuka ya sake sarƙeta. Yayinda Mom damu duk muke kukan, sai dai tari ya sarƙe Mom ɗin ta fara aman jini. Tun yana fita iya baki ya koma harta hanci. Sai kuma al'amari ya rikice. Ai babu shiri aka kwashesu ita da Baby ɗin sai asibiti. Da ƙyar aka amshi baby, dan gaskiya al'amarin ta akwai tashin hankali ga duk mai imani. Ai dole shima Abba aka bashi gado. Muna cikin wannan tashin hankalin kuma sai ga jami'an tsaro wai sunzo kama Hafizzullah ance shine ya kashe mijin Baby ɗin. Sake tashi hankalinmu yayi, shiko ko gezau ya bisu yana kuma tabbatar musu ko yanzu aka kawo gawar mijin Baby gabansa sai ya sake mata raga-raga.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
.......Hankalinmu ya kasu kaso biyu. Ga Hafizzullah a station ga Mom ga Baby ga kuma Abba duk a asibiti. ALLAH dai ya taimakemu Yaya Awwab ya iso ƙasar a ranar. Ai jikinsa kawai na faɗa ina kuka. Ya rungumeni yana lallashi ta sigar shafa min bayana. Mun jima a haka kafin ya shiga ɗakin da Abba yake. Yafi mintuna talatin sannan ya fito. Shi da Yaya Musaddiq da Yaya Hayatu sai wani da ban sani ba suka fita. Kusan awa guda suka sake dawowa da police suka shiga ɗakin da Baby take. Sun ɗan jima suka sake dai fitowa. Mudai duk bamu san abinda ke faruwa ba. Dan har aka turo driver ya maidamu gida basu sake dawowa ba. Badan mun so ba muka koma, sai dai ba gidan Abba ba. Kusan sha biyu na dare ina zaune wanka ma na kasa na zuba tagumi Heedaya data gaji da tsalle-tsalenta tai barci na gefena ita da Awwab baban nasu ya shigo. Da sauri na miƙe ina hawaye da tambayarsa ina Hafiz?. Maimakon amsa min sai kawai ya jawoni jikinsa ya rungume tsam. Kuka na sake fashemasa da shi.
A hankali ya fara hura min iska a kunnena, sai kuma cikin raɗa ya furta, “Calm down My Tiger. Mun amsoshi gashi can ma yana cin abinci wajen Falaq. Kema kin san ina gari, Musaddiq na nan, ga Hayatu bazamu bar Auta ya kwana can ba. Balle ma Yayansa Fahad ya iso yaje ya gwada musu halin nasa saboda harkar law ya karanta aikin ne kawai baida ra'ayin yi. Ko a wata ƙasa aka kama Hafiz sai ya kwana gidansu balle Nigeria ma kasarmu da muke da dukkan alfarma da karfi. Ni abinda yay min yayi dai-dai an rage mugun irin dan mutumin nan in ba kashesan akai ba yanda ya yaddata yay niyyar guduwa wani wajen zai sake tafiya ya yaudari wata itama yaje yayo mata hakan ya dawo da ita. ALLAH dai ya kare mana zuri'a. Kuɗi sun sa komai bawa na wannan zamanin zai iya aikatawa, sannan mata da yawa suna jefa kansu a irin wannan rayuwar saboda kwaɗayin auren mai kuɗi. Kaga mace tana maka tallan kanta babu kunya babu tsoron ALLAH a tattare da ita. Basu san dukiya daban ba, ƙyaƙyƙyawar rayuwa daban. Sannan ba kowace dukiya bace