Showing 279001 words to 282000 words out of 438336 words
screen ɗin laptop ɗin da yake dubawa ya haske masa fuska ya sani shagala kallonsa. Tun inayi a sace har na tafi direct abuna na shagala sosai. Ko kaɗan banyi tunanin hankalinsa na'a wajena ba, dan yanda yay serious a daƙilar computer ɗin ko kaine zaka ɗauka baya tare da duniyar mutane, sai kawai a bazata naji cikin silent voice ɗin sa ya furta, “Kina buƙatar wani abu ne?”.
Kaina na kauda, kamar bazance da shi komai ba dan naji kunya. Sai kuma na fuske nima ƙasa-ƙasa na furta, “Ba zamuje gida ba?”.
Cak ya tsaya da abinda yake yi, sai kuma ya ɗan ɗago ya kallan. Rissinar da nawa idanun nayi ina wasa da yatsun hannuna. Shima sai ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda yake yi. Sai da ya mula dan kansa a taƙaice ya furta, “Next tomorrow”.
Da sauri na ɗago tare da gwalalo idanu waje. Na ce, “Zamu tafi? Ummie fa?”. Ɗan dakatawa ya sake yi, sai kuma ya cigaba da aikinsa batare daya tanka min ba. (Tab ɗin, aiko bazan iya zama anan har jibi banga Ummie ba. Sai dai kai ka zauna) na ayyana a zuciyata ina miƙewa. Bayin na koma na saka rigar barcin nan daya bani sai na lulluɓo gyalena dana shiga da shi. Fitowa nai na haye gadon abina tare da jan bargo na shige ciki. Addu'ar barci nayi dan shi nake ji sosai, duk da wani gefe na zuciyata duk gana akan can gidan saboda Ummie, sai dai idan na tuna Mama nan ga Fahad sai naji sanyi a raina. A haka barci mai nauyi ya kwasheni ban san sanda ya baro latse-latsen nashi ba yazo ya kwanta....
🌿🌿🌿🌿
Idan ma tace abin duniya bai isheta ba a ɗan tsakanin nan wlhy tayi ƙarya. Tama rasa ina zata kama. Gaba ɗaya haushin Rubayya take ji, shiyaysa ma ta daina amsa mata waya a kwana biyun nan. Tunda ita ta bata shawarar da gashi nan ta rubza a ciki. Anya kuwa bazata tafi plan bi b ba. Shegen yaro sai jarabebben taurin kai. Ga wannan ƴar iskar yarinya sheɗaniya sun nuna mata hanya itama tana neman zame musu ƙalliƙalallah. Dolene ma ta ɗauki mataki akan yarinyar nan itama. Amma sai plan ɗin ta ya gama kankama. Shima Fahad tunda ya fara koyon tsagerancin ɗan uwan nasa zata gyara masa zama. Dole ne fa itace kaɗai zatai mulkin Maash Mansion. Kuma dole Awwab ya auri Azizat ta hakane kawai zata cigaba da mallakar kowa na gidan. Koda wataran ALLAH ya bama Ummu-Hidaya lafiya bata isa jaa da ita ba tunda dai a yanzu Maash shine mai dukiyar.
Murmushi ta saki har haƙoranta na bayyana. Cike da izza ta furta, “Baba tunda ku bazaku iya komai ba kuna tsironsa, ni Nafisatu bint Adams zan ƙwatama kaina abinda ku kanku anan gaba sai naso ku samu. Dan ɗaya bayan ɗayanku sai na maida muku murtani wlhy. Musamman ma Mu'azz. Sai na tabbatar masa da ni suka haifama Awwab shi da Ummu-Hidaya. Badai ni ya ɗagama murya ba, hahahahaha sai ka koma ƙasan ƙafafuna kuwa muje zuwa”. Ta wani miƙe tana juyi kamar ƙaramar yarinya..
Ni sai ma abin ya bani dariya😂😜.
💓🪴💓🪴💓
Washe gari kamar yanda Maash ya bama Hayatu umarni akan gyaran sashensa bisa shawarar Samraah sai ko gashi da companyn da zai yi aikin. Bayan sun shiga sun dudduba ko ina da gwadawa aka shiga fitar da komai da ba'a buƙata. Bedroom ɗin Maash ɗin ne kawai ba'a taɓa ba sai kitchen da akama gyara jiya. Aikin bai tsaya anan ba harda sashen Fahad shima. Sai da suka kammala kwashe komai aka fitar tsakar gida sannan suka fara aikin fenti da canja wasu abubuwan duk da kuwa babu abinda gidan yayi, amma abinka da masu kuɗi, a duk sanda za'ai sabon gyara ana ƙoƙarin ya tafi da irin wannan zamanin ne ko tsarin kayan da za'a canja ɗin. Mutanen gida basu san mike faruwa ba sai gani sukai kawai anan aiki. Yayinda ake maida kayan sashen Maash ɗin sashen su Mama Balki dan kayan sabbine ko shekara basuyi ba. Kawai dai anso ciresun ne saboda ba'a matsalar kuɗin canjawar. Wannan abu ya sake harzuƙa zuciyar Hajiya Mammah, harta gagara haƙuri sai da ta tsare Hayatu da masifa dan duk shekara biyu ko ɗaya da rabi ita ake bama kwangilar canja kayan gidan, duk da dai ta karɓi hakan ne da ƙarfin tsiya dan da Hayatun ne. Sai kuma abinda taso za'a sakama kowa iyakaci ta tambayi kalar da kake son kawai. Sai gashi wannan karon taga ana aikin kuma ko shekara batai da canja kayan ba. Abin ma takaicin banda nasu sashen. Komai Hayatu baice da ita ba, sai da yaga azabar tayi yawa ya sanar mata umarnin boss ne. Shi nashi kawai tsayawa kan masu aikin.
Sake tunzurata zancen yayi, take ta hau neman layina Maash. Sai dai switch off. Wani irin tuƙuƙi taji yana sake turnuƙeta. Ita a ganinta taya za'a hau canja kaya yanzu bayan ga biki na tahowa, dan tana nan akan bakanta yanda Baba yace nan da wata ɗaya za'ai bikin Maash da Azizat babu fashi sai hakan ta tabbata. Shiyyasa ma zata ƙulla plan b domin masa ɗaurin goro shi da kowa na gidan. Fuuuu ta nufi sashen su Paah. Yana zaune dan yana kallon wani program da alama yau bazai fita office ba ta shigo. Kallonta kawai ya tsaya yi har sai da ta iso gabansa sannan ya ɗauke kansa tare da gaisheta a fisge. Dan wannan ɗabi'ar Tata ta shigama mutane ba sallama na ƙona masa zuciya. Ya tabbatar idan bata fasa ba wataran sai taga abinda zai dameta wlhy. Yanda yay mata ɗin yasa ranta sake ɓaci, a take ta balbalesa da masifa akan laifin Maash kamar wani ɗanta ba ƙani ba. Ƙanin ma fa sako bawai na can-can nesa ba. Banda ma ta raina masa wayo a yanzu duk wanda ya kalleta ta kallesa baza'a taɓa cewa ta girmesan ba saboda shi namiji ne. Amma bai sani ba ko wannan linda-lindar jikin nata ne ke kwasarta tana ganinta shirum kamar matar sarkin yarabawa. Karan farko da ya fara manna mata hauka har taci jarabarta ta tsire bai tanka mata ba. Sai Hajiya ƙarama ce data fito da shirin fita asibiti ta ke bata baki. Bata kulata ba, hakan kuma ba sabon abu bane ba. Dan tun tana ma amarya basa shiri, duk da kuwa da farko farkon auren babu wata matsala saboda Hajiya Mammah na murna amma Ummie kishiya, kasancewar a lokacin akoda yaushe cikin saka ran zata warke suke. Sai dai a dalilin wani abu da su suka san tsakaninsu ya saka su ƴar walle-walle. Duk da kuwa ita Hajiya ƙarama taƙi nuna akwai matsala kowa laifin Hajiya Mammah kawai take gani da tunanin itace tama Hajiya Ƙaramar koma minene.
Rai ɓace Paah ya tashi ya bar mata falon. Ai ko sai ta hayayyaƙo masa harda shan gabansa tana daka masa tsawa. Ai ko shima ya daka matan cikin matuƙar fusata da hargagin da bai taɓa koda kwatanta mata ba ya nunata da yatsa tare da faɗin, “Addah! Leave me alone!. Get out of my side kafin na nuna miki ainahin true color ɗina wlhy. Kin isheni! Kin isheni!!. Haba wai ƴaƴana sune kaɗai ƴaƴa a family ɗin nan da kullum dai sai ance sunyi-sunyi. Musamman Muhammad bashi da wani filin shaƙar iska mai daɗi a gidan nan. Kullum cikin wahalar nema da kai kawo yake na ganin ya ƙyautata rayuwarmu da ingantata amma bazamu masa addu'a ba mu gode masa sai zaman lissafa kurakuransa. Kuskuren ma daba kuskure ba dai Muhammad. Yanzu ki duba Fahad tunda ya iso gidan nan wlhy ko kallo ban ishesa ba. Yama nuna gaba ɗaya bai san dani a cikin gidan nan ba. Shekara nawa ban gansa ba, ko naje ƙasar da yake guduwa yake baya barin ma mu haɗu sam. Shi kansa Muhammad idan bai so ba sai ya shafe wata biyu ban gansa ba kuma yana cikin ƙasar koma cikin gidan. Miyyasa wai bazaku tausaya min bane ku barni da damuwata. Shin da halin da uwar ƴaƴana data zama sanadin rufin asirina da ku zan ji ko da fitinarki Addah?!!. Ke wane kalar iskanci ne yaranki basayi kin ma taɓa nuna kin san suna yi ɗin. Please! Mind your business and leave me alone!!!!”.
Ya wuce abinsa fuuu cikin bedroom. Ba Hajiya Mammah da Paah yayima ihun ba. Hatta da Hajiya ƙarama sumar tsaye tayi. Dan abune da bai taɓa kwatanta faruwa ba a gidan koda a mafarki. Mu'azz na ɗaga murya ma wani. Kai kai koda ƴan aiki bata taɓa ji ba. Shi mutum ne mai shiru-shiru, dan zata iya cewa ma rashin magana kamar a wajensa Awwab ya gado shi. Sannan shima wani lokacin akwai miskilanci, dan in bai gadama ba sukan iya gaɓar sati biyar ita da shi wlhy bata ishesa koda kwallo ba. Sai dai ita ta gaji ta sauka. Amma jiba yau ya koma kamar wani mafaraucin zaki..
Ido suka haɗa da Hajiya Mammah data suma a tsayen itama. Sai kawai ta wani balla mata uwar harara tai gaba abinta.. sai kawai murmushi ya suɓucema Hajiya ƙaramar batare data shirya ba. Wayar dake hannunta ta kalla, sai kuma ta kwashe da dariya, tare da shiga WhatsApp ta turama Baba prof recoding ɗin da tayi na duk abinda ya faru. Tana turawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta koma cikin ɗaki dan ga fasa fita aiki kuma. Sai taga ƙarshen wasan........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_
.......Koda kiran salla ya farkar da mu da asuba nayi mamaki. Sai daga baya na fahimci daga wayarsa ne ya saita hakan. Tashi yay ya shiga bayi. Bayan ya fito ya kabbara salla nima sai na shiga domin gyara jikina na kuma yo wanka. Sai dai ƙasan raina ina cikin damuwar kayan sakawa. Koda na fito sai da na gyara gadon sannan na zauna. Wayarsa na ɗauka na duba naga ko akwai app na Alkur'ani. Nayi sa'ar samu kuwa, dan haka nayi zaman yin karatu, shi kuma da alama azkar yake yi dan yana dai zaune a inda yay sallar idanunsa a lumshe ya jingina bayansa da kujerar wajen. Mun jima a hakan har sai da gari yay haske sosai ya miƙe, nima sai na ajiye wayar batare dana kallesa ba kaina a ƙasa na gaishesa.
“Kin tashi lafiya?”.
Ya amsa min a taƙaice. Numfashi na ɗan sauke a hankali ni ma nace masa, “Alhamdullah”. Fita yay, ni kuma na ɗan sauke ajiyar zuciya. Ina a wajen zaune babu jimawa sai gashi ya dawo riƙe da wata ƴar ƙaramar bag mai shegen ƙyau. Kusa da ni ya ajiye batare da yayi magana ba ya wuce bathroom. Da kallo kawai na bisa har sai da ya shiga na ɗauka jakar na buɗe. Abinda ko nayi tunanin ganin ne wato kaya. Har cikin raina naji sanyi, dan haka na miƙe a gurguje na shirya cikin doguwar rigan mai ƙyau sosai. Yana fitowa ɗaure da towel kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, har ya kammala shiryawa ban sake maimaitawa ba. Sai da yazo har inda nake ya kama hannuna sannan na ɗago na kallesa. Da ido yay min nunin na tashi, ban musa ba na miƙe, sai dai a raina ina mamakinsa. Gurin jiya muka fito, ganin da nai masa na yau sai naji ya sake ƙayatar da ni. Gamu a gaɓar ruwa yanzu kam al'amarin zabbirgewa da ƙayatarwa, sai dai bata inda muka baro bane nan ɗin ma babu kowa shiru sai kukan tsuntsaye. Bamma san na saki murmushi ba. Ganin yana kallona nayi ƙoƙarin ɗauke kaina ina gimtse abina. Nima gwara ai na koya irin halin nashi Aita zaman kuramen kawai. Ƙayataccen breakfast ɗin da aka shirya mana mukai zaman ci. Koma nace naci, dan shikam ma tsakurar komai yake kamar abin dole. Na fahimci sam baya son abinci, ya dai fi ganewa kayan ƙwalam ɗin nan da maƙulashe...
Ana kiran wayarsa ya tashi a wajen, can ya koma ya tsaya. Ban tsaya jiransa ba na ƙarasa cin abincin na tashi. Ciki na koma ban jima ba na dawo. Na samu ya gama wayar, ma'aikatan jirgin ma na tattare kwanikan da mukaci abincin. Kallona naga yayi kamar mai nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da maidawa kan wayarsa dage vibration dan shi sam baka jin ƙara a duk wayoyinsa.
“A ƙaraso da su”.
Kawai yace yana mai yanke wayar. Mamaki ne ya kamani, na kalla gabas da yamma kudu da arewa naga dai a tsakiyar jajeji muke sai ruwa. To ta'ina ma wani zai samu damar zuwa nan ya same mu. Bari dai naga ikon ALLAH. Aiko na gani, dan ba'a cika minti biyu ba sai ga ma'aikacin jirgin ya shigo bayansa da mutane guda uku. Ɗaya babban mutum ne mai cikar kamala da mutumtaka. Ni sai ma naga kamar nasan fuskar. Sai matashin saurayi da bazai wuce sa'an Hayat ba, shi kansa saurayin kamanninsa da Bahijja sosai ya mugun jan hankakina. Sai dai na cije kawai na kame kaina, sai Hayatu dake biye da su. Araina nace (bindin Maash kenan). Ganin Maash ɗin ya miƙe cike da girmamawa yana ma dattijon barka da zuwa da kiransa da Abbah yasa nima suna zama na gaishesa cikin girmamawa kaina a ƙasa. Sosai yake murmushi, kafin cikin jinjina kai ya ce, “Masha ALLAH, abu yayi ƙyau Muhammad Awwab. ALLAH kaine abin godiya, ALLAH ya ƙarama wannan aure albarka”.
A mamakina murmushi naga yayi yana ɗan rissinar da kai alamar jin nauyi, nace (tofa, dama akwai wanda Maash kejin kunya a duniya ashe). Gaisuwar da saurayin nan ya mun cike da girmamawa ta katse min tunani na. Na amsa masa shima ina ɗan murmushi. Muka kuma gaisa da Hayatu na tambayesa aunty Falaq yace tana lafiya.
“Samrh!”.
“Na'am”.
Na ɗago ina amsawa da ɗan kallonsa. Inda dattijon nan yake ya ɗan kalla, tare da sake maido idanunsa a kaina ya ce, “Wannan shine Malamina kuma kamar Abbana. Shiyya fara koyar da ni ilimin addini kamar yanda ya koyar da kakana mahaifin Ummie kenan da ALLAH yayma rasuwa tare da Baba. Shine kuma ya amsar min walliccin aurenki. Nasan dan da wahala ace baki san wannan fuskar ba. Dan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain ba Nigeria ba a Africa ma sananne ne”.
(Haba no wander nifa nace nasan fuskar nan) a zahiri kuma sai na jin jina kaina da sake rissinawa na ce, “Sannu da zuwa Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana masu albarka”.
“Amin ya rabbi ɗiyata. ALLAH yay miki albarka. ALLAH kuma ya jiƙan mahaifinki Abdul-wahab da rahama. Mutumin kirki mai gaskiya da riƙon amana. Mai sadaukarwa. Ina fata da addu'ar ALLAH ya gadar da ƙyawawan halayensa ga ku zuri'arsa. Dan masu iya magana kance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Nayima mahaifinki ƙyaƙyƙyawan sani gaskiya. Har takai ina jin kunyarku matsayin zuri'ar daya tafi ya bari da ya kasance bamu taɓa bibiya ba har sai a gaɓar da UBANGIJI ya zartar da ikonsa. Amma tabbas nasha yin hasashe a kanki a duk lokacin dana ganki a tv. Saboda iyalan gidana na bin program ɗin da kike gabatarwa. Tun ina faɗa da yawan kallon tashar har dai na nutsu nima naga abinda suke kallon a wata rana. Amfanin shirin da hikimar iya zance da ALLAH ya baki yaja hankalina matuƙa. Sai kuma a raina nake jin kamar na taɓa saninki amma a ina shine na manta. Har dai randa Muhammad ya kirani da bayani akan rikicin aurenki da hukuncin kawunki. Kasancewar yana faɗin min wadda yay hira da ita a Alheri tv yasa na gano kece. Abinda yay matuƙar sake ɗaukar hankalina kuma hoton da ya tura min na ɗan uwanki dake tsananin kama da mahaifinku, kema ashe jininsa nake gani a jikinki shiyyasa nake ganin kamar na sanki. Dan haka na buƙaci yazo ya sameni. Mun tattauna sosai akan abinda bamu tabbatar ba, a take nan ya saka aka masa bincike aka kuma tabbatar mana ke ɗin jinin Abdul-wahab ce. Madalla da ƙyaƙyƙyawan tsiron alkairi. ALLAH ya gafartama Abdul-wahab Gwarzo”.
Sosai nake kuka. Yayinda Malam ya cigaba da zabgama Baba addu'a har ma da kakan Maash ɗin. Maash na amsawa da Amin, dan Hayatu da saurayin nan suna can gefe sun bamu wuri. Nima dai ina amsawar sai dai kuka yaci ƙarfina. A hankali naji saukar hannunsa saman nawa kasancewar muna zaune ne a kusa da juna. Na kuma ɗan dafe kujera da hannun, ina sharar hawaye da ɗayan. Sosai ya runtse hannun cikin nashi tare da ɗan murzawa alamar lallashi. Sai kuma ya zato tissue a cikin kwalinsa dake saman Centre table ɗin kujerun wajen ya miƙa min. Ban musa masa ba na amsa. Hawayen na share, sai kuma ya miƙa min ruwa. Nan ɗin ma amsa