Showing 399001 words to 402000 words out of 438336 words
da shi. Hoto na masa a gurguje ya fice dan kiran su Uncle Abdullahi yaƙi daina shigowa. Yana fita nima nai nawa shirin inata faman sakin murmushi. Na yarda kam mata da miji sai ALLAH. Duk iya ƙololuwar fushin da za'a ɗauka da juna sai kaga na lokaci ne, da zarar an huce kuma an manta shike nan...
A gurguje Please 🥺.
★★
Alhamdullah bayan sallar juma'a ɗunbin al'ummar MANZON ALLAH suka shaida ɗaurin auren Yaya Musaddiq da amaryarsa Ruƙayya. Yaya Fahad da Bahijja. Ɗaurin aurene da ya tara manyan mutane ƙasar da wajenta, ƴan siyasa, sarakuna, ƴan kasuwa daga ƙasashe daban-daban. Wasu ma dai suna Lagos suna jiranmu zasu halarci dinner ne. Shugaban ƙasa da kansa ya halarci wannan aure (Amma fa shugaban ƙasa Ramadhan nake nufi🤪). Ko garin Kano yasan yau ana ɗaurin auren masu hannu da manda. ALLAH sarki Paah ma da jiki ya fara sauƙi yazo, sai da za'a ɗaura aure Maash ya gansa. Tunda suka haɗa ido da Maash yay ƙasa da kansa bai yarda sun sake ba. Sai Maash ɗin ne ya danne zuciyarsa ya gaishesa da girmamawa. Bai kuma tambayesa yaya jiki ba. Uncle Abdullahi dai shi yay waliccin Fahad, Kawu Lurwanu kuma na Yaya Musaddiq. Bayan ɗaura aure aka ɗunguma ƙaton Hall ɗin da aka tanada domin ƙwarya-ƙwaryar liyafar da su Hayatu suka shirya domin ciyar da baƙinsu abinci. Anci kuwa ansha kowa ya godema ALLAH. Yayinda mu ma anan muketa namu hidima. Mansoor da Attahir da suma next week nasu bikin da Dad ɗinsu sun halarci ɗaurin auren. Bayan kammala cin abinci manyan baƙi suka fara kaucewa. Na jirgi na nufur airport na mota na nufar masauki, wasu kuma Lagos ma suke wucewa tun yau ɗin kasancewar can akai musu masauki.
Sai bayan la'asar anguna suka shigo mana da manyan yayye. Ummie ta rungume Fahad tana hawaye, kowa yasan na farin ciki ne. Shima dai hawayen yake yi, mutane da yawa na tayasu. Koda ta sakesa Yaya Awwab dake tsaye kawai yana kallonsu shima ta kamo ta rungume tana mai sanya musu albarka. Daga haka akai hotuna, Paah dai bai zo gidan ba sai su Kawu Abdullahi. Dama matarsa da Malika suna nan tun jiya, Hajiya Mammah ce dai sai yau tazo a ɗarare, itama Hajiya Mama tana nan yau kwana biyu ita da duka yaranta. ALLAH sarki Ummie, ta dake zuciyarta komai daya shafi uba su take sakkowa gaba, tun Hajiya Mammah na nuƙu-nuƙu dai harta fara ɗan warewa. Ana hotuna Ummie na maƙale da ni da Aunty Falaq. Babu ko kunya shima uban gayya ya rungumeni aka mana, harda inda yake sumbatar goshina, hannunsa kuwa na saman cikina ko'a jikinsa.
Bayan kammala hotuna anan muka ɗunguma can gidan Abba kuma. Cikin namu ƴan uwan da gayyar dangi. Nan ɗin ma dai anyi hotuna na kece raini, Mom dai taƙi ko fitowa. Tanama bedroom babu wanda zai ce yazo wajen bikin nan ya ganta daga jiya zuwa yau. Ita dai Bibaa da taga babu sarki sai ALLAH saita ware abinta cikin dangi. Auta kam yana nane da Yaya Musaddiq.
Sai da aka ɗakko amarya Yaya Musaddiq sannan aka ɗakko ta Fahad, gida ne mai ƙyau da tsari aka kai amaren su duka anan anguwar da muke. Yaya Musaddiq a can sama, Fahad anan ƙasa. Duk da ba zama zasuyi ba su duka kowa yasan haka duka iyayen amaren sunma yaransu jere gwargwadon ƙarfinsu. Babu shiri daga gidan amaren na fito a ƙafa saboda babu wani nisa na koma gida. Dan ji nake kamar zan zube dan gajiya. Aiko ban nema kowa ba na shige nai wanka da ƙyar na kwanta. Bamma san lokacin da Yaya Awwab ya dawo gidan ba, sai cikin dare da yunwa ta sakani farkawa na gansa........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒊𝒙_
........Washe gari tun safe wasu aka wuce Lagos da su, dan jirage uku na Maash aikin jigilar ɗaukar mutane sukayi🤪. Su Ummie suna cikin masu tafiyar farko, ni dai da Aunty Falaq da amare da angwayensu sai namu mazan dole sai yamma. Dan Fahad ya buɗe aiki. Babu ɗaya ƙafa a daren ya maida Bahijja amaryar gaske. Baiwar ALLAH tana ta ɓarzar kuka. Babu shiri Ruƙayya ta kirani tace nazo akwai matsala ta rasa yanda zatai da Bahijja itama duk ta firgice. A lokacin ina jikin nawa angon, cikin mamaki yake tambayar lafiya dan na roƙesa zanje can.
Abinda ta gaya min na faɗa masa. Zai kira wayar Fahad dan shi bai ma fahimci komai ba na dakatar da shi. “Yaya karka kirashi, bafa wani abin tada hankali bane ba.”
“Kamar ya kada a kira shi, kika sani ko wani shirmen ya aikata. Kin san fa Fahad baya jin magana”.
Dariyama ni abin ya bani, na ce, “Ai wannan karon rashin jin nashi na manyanta ne. Kawai inaga ya angwance ne fa”.
Idanu sosai Maash ɗin ya zaro da faɗin, “Samrh! Anya yaron nan nada hankali? Ya bari a gama bikin mana”.
Dariya kawai na shiga yi. “Kai yaya mutum da matarsa. Nidai yanzu bara naje...” bamma gama rufe baki ba sai ga kiran Fahad ɗin ya shigo min. Muryarsa a sanyaye ya ce, “Aunty dan ALLAH kizo yanzu. Amma kada ki faɗama kowa nan zaki zo har Yaya Please. Wlhy ina cikin matsala”.
Dakewa nayi ina ƙoƙarin danne dariya nace masa gani nan kada ya damu. Koda na yanke kiran sai Yaya Awwab da duk ke jinmu yay ƙwafa kawai. Ni dai na ɗan taɓe baki da faɗin, “Idan ma dai babu batun kwanciya asibiti da ɗinke-ɗinke irin na wasu ai da sauƙi. Shi yayi da ƙyau”.
Harara ya zubo min kamar zai cinyeni da idanu. Na fita abina ina dariya dan nasan ya gane da shi nake dai....
Sosai Bahijja ta bani tausayi, kai maza dai duk sai abarsu. Ita kanta Ruƙayya duk tayi laƙe-laƙe. Haka na taimaka mata da ruwan zafi tanata faman kuka. Dole Yaya Musaddiq ya samo mana wata Nurse ƴar anguwar mu ta dubata. Alhamdullah dai tace ɗan ƙarin data samu baida yawa. Adai kula da shigarta ruwan zafi sosai wajen zai haɗe da kansa. Ta kuma bata magunguna. Ban baro gidan ba sai da taci abinci tasha maganin ta kwanta. Na fito na samu Fahad a falo ya zabga tagumi. Dariya nayi a zuciyata. Amma a zahiri fuskata a dake na ce, “Ta samu barci, ni bari naje na samu Yayanka dan dole tafiyar mu ta koma sai ko zuwa six ne. Idan ta tashi ka kula da ita ta shiga ruwan zafi yanda ya kamata”.
Kansa dake ƙasa ya jinjina min, kafin murya a sanyaye ya ce, “Amma aunty babu matsala ko?”.
Hararsa nayi. Ya sake duƙar da kai yana sosa ƙeya.
“A yanzu dai babu, amma idan ka kuma batare data warke ba akwai. Ka kuma san duk yanda zaka lallasheta ta nutsu kar Ummie ko yayanka su fahimta, kaga dai wajen taro za'a shiga. In ba hakaba kai da su ne ni babu ruwana kaga tafiyata. Sai na shigo anjima”. Daga haka nai ficewata. A ƙofar gida na samu Maash jikin mota yana waya. Na ɗan tsaya ina masa kallon mamaki har ya kammala ya katse.
“Lafiya kuwa na ganka anan? Ba barci kace zakayi ba?”.
Fuska ya ɗan yamutse, “Na kuma kasa tunda kika fito. Idan akwai matsala inaga ki fito da yarinyar nan muje asibiti”.
“No babu wata matsala fa. Ai shi bai jawo magana da yawa ba kamar wasu”.
“Suwa kenan?”.
Ya faɗa yana wani bina da kallo a dake. Kafaɗa na ɗan ɗage da taɓe baki na ce, “Ni dai ai ban faɗi suna ba a zancena ba ko”.
“Kin san ALLAH yarinyar nan kina shiga mun hanci kwana biyun nan, amma zan kamaki ne. Zaki san ni kika tasa a gaba”.
Dariya nayi da faɗin, “Oh oh kaji tsargar kai. My Lion kaji na ambaci sunanka a maganata. To kodai kaima haka kayi ne?”.
“Zo muje sai na faɗa miki yanda nayi ni, dan har farkawa nayi aka ɗinke”. Yay maganar yana ƙoƙarin cafkoni. Da sauri na zille ina dariya nai hanyar gida. Tsaye yay kawai hannayensa duka biyu riƙe da ƙugunsa yana kallona harna buɗe gate zan shige. Sai da na saka ƙafata ɗaya na ɗan leƙo kaina na masa gwalo na ida shigewa ina murmushi. Kusan karo mukaci da Aunty Falaq a ƙofar falo.
“Ke kuma daga ina haka?”.
Dariya na saki da nuna mata gate. Nace, “Daga gidan amare. Na leka nemanki da zan fita naga kuna tare da Yaya Hayat a baya shine na wuce. Yayanki ne ya jiƙa aiki”.
Idanu ta zaro sosai da faɗin, “Wanne daga ciki?”.
Dariya na sake kwashewa da shi da kai bakina saitin kunnen ta na raɗa mata. Ta riƙe baki tana dariya da fadin, “Kai ALLAH ya shirya Yaya Fahad wlhy. Shi babu ɗan kawaici mu ƴan biki mu tafi sannan. Muje ni dama nemanki nake fa Aunty Maijidda ce ta kirani yanzun”.
“Okay muje to”.
🏃A gurguje Please 🥺.
🌿🌿🌿🌿🌿
Bamu bar Kano ba sai shida na yamma. Abinka da jirgi mun isa akan lokaci, dan Alhamdullah sallar magriba ma a gida ta mana. Mansion fa yayi masifar cika ta ban mamaki. A hakama wasu suna hotels. Na ɗan ji sanyi ganin sashenmu babu wannan hayaniyar. Dan sai da ma ya buɗe sannan muka shiga. Bamufi mintuna biyar ba Ummie ta shigo ta samemu a falo dan bamu kai ga haurawa sama ba. Mun gaisheta cikin girmamawa. Ta amsa mana da kulawa tana tambayata babu dai damuwa ko? Babu inda ke mun ciwo kuma.. Nace mata eh babu komai.
Sosai na waro idanu waje jin wai harda mu fa a wannan dinner. Dan Uncle Abdullahi ya dage akan dole mu kasance cikin anguna da amare tunda mu a namu bikin babu abinda akayi. Abubuwan da suka faru kuma Yaya Awwab bai taɓa magana ba ya kamata a wannan gaɓar duniya ta sake tabbatar da aurenmu.
A marairaice na ce, “Amma Ummie ALLAH ai shine shaida. Idan ta mutane zamu bi ko UBANGIJI bazamu bautamawa ba yanda ya kamata. Kawai a barsu su cigaba da shirmensu watarana sa gane da kansu. Bayanin da Abba yay musu kuma a wancan karon mutane da yawa sun fahimta”.
“Hakane Daughter. Amma ku fahimci zancen Abdullahi nakan gaskiya. Anji duk wancan ta wadatar, amma watarana ake gudu musamman ga masu tasowa da su bamu san wazai iya rarrabe musu gaskiyar ba. Sannan yaranku nan gaba wani zai iya amfani da wannan damar ya saka musu ruɗani a zukatansu”.
“Hakane Ummie”.
Na faɗa a sanyaye kaina a ƙasa. Jin shiru uban gayyar bai taka ba na ɗan ɗago na kallesa. Itama Ummie shi take kallon. Itace ta katse shirun namu da faɗin, “Muhammad bakace komai ba”.
“Ummie toni mizance tunda kun gama magana. Duk hukuncin da kuka yanke ai dai-dai ne. Kawai dai kamar yanda ta faɗa ne maganar mutane ba abin biyewa bace. Tunda mu mun san kammu fine”.
“Duk da hakan dai kawai ku shirya. Ga kayan da zaku saka can a ɗakinta an ajiye muku. Mai kwalliya zata zo ta mata”.
Da sauri ya ce, “No Ummie abar batun kwalliyar nan. Kayan ma idan basu min ba zan iya canjawa”.
“Kai kuma ka sani wannan uban ƴan kishin tsiya”.
Ta faɗa tana miƙewa ta fice abinta. Shiru da ga ni har shi babu wanda yay magana. Sai ma wani kicin-kicin da yay da fuska alamar sam baya ra'ayin abin kawai yayi biyayya ne. Nasan dama bazai masa ba shiyyasa naso tun farko Ummie ta fahimta. Gudun karma ya juye bala'in a kai a sai na miƙe kawai ina faɗin, Bara nayi fitsari” na gudu abina. Nafi minti talatin da shiga sannan ya shigo. Ina kwance a gado kawai ina ƙullawa da kwancewa. Nasan mutumin nan da kishi kada ayi abun nan ya zame min baya da ƙura. Box ɗin da kayan ke ciki dako motsasu banyi a inda suke ba ya ɗauka ya shiga buɗewa. Sai da ya fito da kayan ciki tas ya gama kallonsu kafin ya zubesu a saman gadon ya kai zaune yana wani shafar fuska da furzar da huci mai ƙarfi.
Shiru kusan na minti ɗaya kafin cikin sanyi nace, “Uhmm Yaya Awwab kodai kawai nacema Ummie banda lafiya. Nasan hakan zai sa tace nai zamana. Kaga shike nan an rabu lafiya”.
Shiru kamar bazai tanka min ba sai kuma ya juyo ya kallani. Sai da ya ɗan lumshe ido ya buɗesu a cikin nawan kafin ya sake furzar da numfashi a slowly. Fuskarsa a yamutse ya ce, “Bayan ta tambayeki kince lafiya kike. Kawai ki tashi ki shirya ɗin”. Daga haka ya tashi ya fita abinsa..........✍️
🏃🏃Mufa mun wuce airport. Wanda bai shirya ba sai ya taho a mota babu ruwana. Bikin Fahad guda ai sai mun zubar😂🤣🤣🤣.
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
......Ajiyar zuciya kawai na sauke nima na tashin. Sai da na fara yin wanka nazo nai sallar isha'i sannan na hau shiri. Lass ne ko material zan kirashi bamma sani ba nikam. Amma yayi masifar haɗuwa. Ga wani uban stones work yasha na musamman. Rigace doguwa har ƙasa fitet datai bala'in bin jikina ta fito da matashin cikina ɗas hannunta dogo sosai. Sai akai wani shegen flay jacket data sauka ta rufe har mazaunaina ta gaba kuma ta ɗan gota cikina ta yanda ba'a ganinsa sam. Sosai pitch and black color ɗin lass ɗin ya fita da fitarsa ta haƙiƙa. Ɗinkin kuma ya sake ƙawatashi. Tunda ya hana mai kwalliya dole ni na zauna naima kaina ɗan light makeup da na tabbatar yama fi wancan da za'a canja min kamanni. Dan nan a ainahina nake komai cif-cif. Ɗan ƙwalin kaina ɗauri daya sake ƙawata kwalliyar sannan na saka jacket ɗin da ɗan turare kaɗan na saka sauran tarkacen ƴan