Showing 201001 words to 204000 words out of 438336 words
ta shiga har ɗakinta ta sanya a ƙarƙashin gado amma ko gezau, bayan kuma Umma ta tabbatar mata idan har ta saka layun yarinyar nan ta kwanta a gadon bazata kwana a gidan ba sai dai gidan Ubanta. Kuma komai dare sai ta koma garinsu a ƙafa. Haka ta kwana zaman saurare amma har gari ya waye babu ko dogon motsi daya faru a gidan. Sai ma da farar safiya Halimen ta tashi ta damesu da aiki da waƙe-waƙenta na iskanci kai kace ita ɗin jikar barmani choge ce ko shata.
A fusace itama ta bar kitchen ɗin tana dakama mai aikinta tsawa....
💢🌟💢🌟💢
Suna akan hanya nufar gida Hayatu ke bashi labarin rikicin da Ummie tayi yau a gida na neman Samraah. Har falon ƙasa ta sakko yau tana riƙe duk wanda ta gani ta bisa da kallo, sai kuma ta girgiza kai ta saki wanda ta kama ɗin ta tafi na gaba. Bayan ta gama bin kowa bata ga wadda take neman ba sai kuma ta zauna ta sanya kuka. Abin yayi matuƙar bama kowa mamaki. Nima na koma amso kayan da zasuyi amfani da shi ne na tadda wannan drama. Da ƙyar na lallaɓata bayan na ambata mata sunan Aunt sai ta shiga gyaɗa kanta alamar dai tabbacin ita ɗin take nema. Lallashinta nayi tare da tabbatar mata zanje na kirawo mata ita sannan ta yarda ta koma saman. Shine dana kai musu kayan na samu abinci na kai mata taci na bata magungunanta. Tana kammala ci sai barci. Koda na koma bayan magrib ɗin nan na samu har lokacin tana barcin. Yaya abin nan yamun daɗi, da'alama Ummie ta fara samun lafiya, tunda har take iya banbance mai ƙyautata mata. Lallai Aunty Samraah alkairi ce a rayuwarmu. Lallai akwai hikima a cikin sanadin shigowarta rayuwarmu”.
Kamar yanda Hayatu yayi tsammani baice komai ba. Sai dai a bazata badan kar ace yayi ƙarya ba sai yaga kamar yayi murmushi. Amma dai baya ce ba, tunda ba gani yay ƙuru-ƙuru ba kasancewar fuskarsa na gefe.
Shiru ya samu gidan da alama kowa ya kwanta, maimakon wucewa nasa sashen duk da yunwa da gajiyar dake addabarsa sai ya nufi sashen Ummie. Daki-daki yake bin ko'ina da kallon tsaff, gaba ɗaya sashen ya canja yanzu akoda yaushe cikin ƙamshi da tsafta yake. Duk da a yanzu falon farko ne kawai mai kujeru, amma sauran duk an kwashe komai tunda Samraah tayi magana. Duk da a ɗari-ɗari yake bai dakata ba sai da ya dangane da bedroom ɗin da a yanzu yafi samunta. Sassanyar ajiyar zuciya ga sauke yana mai jingina da bango da lunshe idanunsa sannan ya buɗe a kanta. Barci take har yanzu, sai kuloli masu ƙyau ata gefenta alamar abincine a ciki, yasan wanda Hayatun ne ya kawo, dan haka ya ƙarasa a hankali cikin takun sanyin jiki ya bubbuɗe kulolin. Lafiyayyen abincine da ko ba'a faɗa ba yasan Falak ce ta yisa duk da tana fama da kanta itama. Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da iska mai nauyi daga bakinsa. Sai kuma ya maida komai ya rufe ya koma bakin katifar ya zauna. Blanket ɗin data ɗan zazzame ya gyara mata, a hankali ya kai hannu ya gyara mata hularta da ita ta zame. Sosai ya zuba mata idanunsa da suka kaɗa sosai. Daka gani kasan kukan zuci yake yi. Ya jima zaune a ɗakin duk da uban barcin da yake ji har kusan gabannin asuba ciwon kai ya takura masa sosai sannan ya miƙe........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_______
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
_______
.......Tsaff sashen nasa yake an gyara komai tamkar koman bai faru ba. Yasan aikin Mama Balki ne wannan. Dan hatta bedsheet ɗin saman gadonsa da blanket an canja su da wani fari tass mai ƙyau da masifar laushi. Bathroom ya shiga, can ma ɗin dai an tsaftacesa. Sai kawai yayi wanka tare da ɗauro alwala ya fito. Sai da ya fara gabatar da shafa'i da wutri sannan ya kwanta dan barci sosai ke cin idanunsa ga ciwon kai da baya raba ɗayan biyu a dalilin zaman sashen Ummie da yayi ne. Dan lafiya lau suka shigo gidan sai gajiya dake damunsa. Yana kwanciya kuwa barci mai nauyi yayi awon gaba da shi...
Da asuba makarar da yayi ce ya sashi yin salla a ɗakinsa ya sake kwanciya. Barci ne mai nauyi ya ɗaukesa har ya manta ma safiya ce ba dare ba. Duk da kuwa shi da wahala kaga yana barcin safe ko rana. To inama yaga wannan lokacin kullum abubuwa sun ma kansa yawa. Idan har kagansa yini guda a gida yana hutawa lallai ba lafiya ba. Ko kuma akwai wani ƙwaƙwƙwaran dalili. Dan ko nan ta samu ya gudo dan ya huta baka rabashi da laptop ko tab a hannu yana harkokinsa.
Cikin barci sautin knocking ɗin ƙofa ya addabesa. Dole ya buɗe idanunsa yana mai karanto addu'a. Sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya miƙe zaune cike da takaicin wanda ke damun nasa. Agogo ya kalla goma da wasu mintuna na safe. Yaɗan furzar da iska kaɗan tare da zuro clean ƙafafunsa ƙasa. Nan ɗin ma sai da yaja wasu sakanni sannan ya ɗauki remote ya danna ƙofar ta buɗe kanta. Paah ne ya shigo, dan haka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Good morning”.
Amsa masa Paah ɗin yay da, “Morning dear, ka tashi lafiya?”.
“Alhamdullah”.
“To masha ALLAH. Dama Baba ne yazo tun ɗazun, da yace kar a tashe ka harka tashi da kanka, sai kuma ga baƙi munyi da ga human right, wai sunzo ne akan case ɗin yarinyar nan. Bamu san wanene yaje ya sanar musu ba a gidan nan. Muhammad wai miya kaika aikata al'amarin nan? Bayan nasan wannan ba halinka bane ba. Baka aikata a waje ba sai a cikin gida, haba Muhammad da mahaifiyarka na cikin lafiyarta mi kake zato”.
Komai Maash bai ce ba har Paah ya gama maganarsa. Cikin ɓacin rai ya juya ya fita yana mai bashi umarnin fitowa yanzun nan ana jiransa kada ya ɓata musu lokaci. Da kallo kawai ya bishi na tsawon mintuna har biyu, kafin ya furzar da nannauyar iska ya miƙe. Bathroom ya nufa, bai wuce mintuna biyar ba ya fito. Ba tare daya canja pyjamas ɗin jikinsa ba ya zura bedroom slippers ɗinsa masu taushi farare tas kamar pyjamas ɗin nasa ya fito. Baiyi zaton a falonsa suke ba. Dan haka yay ɗan turus yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Gaba ɗaya manyan gidan ne sai baƙi fuska mata biyu da maza biyu. Ɗauke idanunsa yay cike da basarwa, a dakile ya furta, “Good morning”. Yana kaiwa cikin kujera da ke gefen Baba prof alamar shi aka barma wajen zaman dama. Duk da dai kowa ya samu nasa gurin kasancewar falon bawai kujeru bakwai bane ba kawai. Yanda ya tsuke bakinsa da ga gaisuwar farko kowa ya fahimci jam'i yayi. Kuma bazai sake wata ba. Harara Hajiya Mammah ta watsa masa. Hakama Hajiya ƙarama sai da ta ɗan cija lips. Maman Malika ce kawai tayi ɗan murmushi da faɗin, “Awwab babu dai wata matsala ko?”.
Kansa ya jinjina mata. Sai kuma a hankali ya ɗan motsa lips ɗinsa ya ce, “Alhamdullah Mamy”.
Da fara'a itama ta ce, “Alhamdullahi mun gode ALLAH. ALLAH kuma ya kiyaye gaba”.
Baba prof, Paah, Uncle Abdullahi suka amsa da amin. Duk da dai fuskokinsu babu walwala suma. Kallonsa Baba prof yayi kamar mai nazari, kafin ya masa nuni da baƙin fuskar yana faɗin, “Baƙine daga human right. Wai sun zo ne akan case ɗin yarinya da akai raping anan gidan. Sunyi-sunyi da ita tun jiya wai ta faɗa musu amma taƙi. Shiyyasa suka zo domin ganawa da kai, suna son a basu izinin yin bincike akan case ɗin”.
Shiru babu alamar Maash zai amsa kamar ba da shi Baba prof ɗin ke magana. Dan tun kallo ɗaya da yayma mutanen bai sake ba. A yanzu ɗin ma da yaji bayanin komai daga baba prof ɗin bai kallesun ba bai kuma tanka ba sai da ya mula dan kansa. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita a wulaƙance ya kallesu a karo na biyu. Cike da gizagonsa ya furta, “Ko zan iya sanin mai kai report ɗin?”.
Kallon juna sukayi, sai kuma cikin ƙarfin hali namijin dake facing Maash ɗin ya furta, “Ranka ya daɗe wannan ai sirri ne bama buɗesa. Duk wanda ya kawo mana report akan wani case yana da cikakkiyar kariya a garemu tako wace fuska. Amma idan munyi kuskuren shigowa bada izini ba ayi mana afuwa. Muna akan aikinmu ne”.
Kamar bazai tanka ba dan har sai da kowa ya zuba masa ido a falon, sai kuma ya yunƙura ya miƙe yana faɗin, “Okay tunda har kuka fahimci hakan da kanku ina fatan zaku gane hanyar da kuka shigo. Dan bana buƙatar fitowa na sameku koda a gate ɗin gidan nan ne”. Daga haka yay wucewarsa cike da takunsa na izza.
Duk binsa sukai da kallo, sai da Baba prof ya katse yanayin cikin wayancewa ya saki murmushi da faɗin, “Kufa yi haƙuri, shima tun jiya ransa a ɓace yake da faruwar al'amarin. Wani dalili ne ma daya ɗan gitta yasa bai ɗauki mataki ba. Amma na tabbatar tunda har kuka zo nan da kansa zai nemeku idan ya huce. Maybe shigowar karan tsaye da kukayi mana ne ya tunzurashi. Amma in har komai ya dai-daita ni da kaina zan nemo ku in sha ALLAH”.
Badan sun gamsu da bayanin Baba prof ɗin ba suka miƙe. Sai dai sun tabbatar da yanda suka karanci tsagwaron rashin mutunci a fuskar Maash ɗin to lallai idan har ya dawo ya same sun komai zai iya faruwa. Har gate Baba prof yay musu rakkiya yana ƙara basu haƙuri. Sai da ya ga fitar motarsu sannan ya dawo. Zama suka sake yi jugum-jugum amma babu alamar Maash zai sake fitowa. Hajiya Mammah ce ta katse zaman shirun nasu da faɗin bara ta sake kiran Maash ɗin. Amma sai Baba prof ya dakatar fa ita akan ta barsa yana son yanzu shi yaje asibiti yaga yarinyar kafin su san ta hanyar da zasu ɓullo ma al'amarin. Sam bata so haka ba, sai dai ganin sauran duk sun bada goyon baya yasa ta yin shiru....
Maash kam daga falon hanyar da zata sadashi da sashen Ummie ya nufa. Ya samu sashen na sabon ƙamshi alamar an masa gyara. Sosai yayi mamakin waye kuma? Tunda yasan ita tana asibiti. Yana shiga yaci karo da mama Balki na shirin fitowa. Cikin kasa ɓoye mamakinsa ya ce, “Mama kece?”.
Murmushi tayi cike da kulawa ta ce, “Eh Alhaji ƙarami. Ai mutuniyar taka ce tun asuba data farka take ta roƙona nazo na duba mata Ummie, tasan maybe bata ci abinci ba. Harda kukanta. Dan haka ina yin sallar asuba gari yay haske nai shirin tahowa sai kuma ga Hayatu ma yaje kai abinci shine na biyosa ya kawoni. Gata nan har ma taci abinci tasha magani barci ya ɗauke ta. Sauri nake kuma na koma can asibitin yanzu dan zata iya ƙin shiga ruwan zafin dana bar mata itama”.
Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya. Sai kuma a hankali da silent voice ɗin nan nasa ya furta, “ALLAH ya saka da alkairi Mama”.
“Amin Alhaji ƙarami ai yiwa kaine. Bismillah ka shiga, Bara naje Hayatu na jirana zai maida ni”.
Shiga yay ita kuma ta fice. Ya jima a ɗakin yana kallon Ummie har sai da kansa ya fara juya masa sannan ya fito. Da gaske sauƙi ya fara samuwa. Dan inda dane a yanda ya shigo ɗin nan komai barcin da take yi saita tashi kansa. Amma kalla jiya yafi zaman awa biyu amma harya fita bata ko motsa ba sai shine da ciwon kai ya addaba. Sashensa ya koma batare daya bi takan su Paah dake a falo ba. Yay wankansa ya shirya tsaff da shi. Bayan ya gama fesa turarurtukansa masu ƙamshi da tsada kala kusan biyar, shiyyasa ba'a gane ainahin turaren da yake amfani da shi yay zaman saka takalmi. Wayarsa da akai kira ɗazun bai ɗauka ba ya duba. MD ɗin companyn sa ne na Kano. Kiransa yay back, dan yasan akan maganar Musaddiq ne. Cike da girmamawa baturen mutumin ya gaishesa da ga can. Kafin ya ɗora masa bayani akan komai na Musaddiq ɗin ya kammala. Zuwa next week zai biyo jirgi zuwa nan Lagos daga nan sai ya wuce. Kamar yanda ya saba amsa wayarsa bata wuce ɗaya biyu koda zakuyi maganar awa ne ya amsa masa da “Okay” kawai ya yanke wayar. Daga haka ya ƙarasa shirinsa ya fito.
Hayatu da Tj kawai ya samu a falon suna jiransa. Bai zauna ba da ga tsayen ya amsa gaisuwarsu yana mai ɗan kallon agogon hannunsa mai shegen tsada da ƙyau. Sai kuma a hankali ya furta, “Let's go”. Duk miƙewa sukayi, yana gaba suna binsa a baya, sai ma Hayatu ne dake ɗan masa bayani daya shafesu dan akan kasuwanci ne har suka iso gaban motocin da aka gama shiryawa domin fitar tasa. A tare guards ɗinsa da sauran ma'aikatan gidan suka dinga kawo gaisuwa da jajanta abinda ya faru, tare da masa addu'ar kariya daga sharrin duk wani abun sharri. A karo na farko ya ɗan saki gajeren murmushi tare da haɗe hannuwansa a waje guda alamar ya gode. Kamar ko yaushe yana baya TJ na mazaunin driver Hayatu a gefensa. Sai motar guards ɗinsa guda biyu ata gaba da baya su suna tsakkiya.
Sam yawo da guards ɗin nan ba sonshi yake ba. Sai dai baida wani zaɓin daya wuce hakan saboda yanayin ƙasar tamu balle shi mai yawan maƙiya da masoya. Yasha tsallake tarko da aka shirya halaka rayuwarsa. Ana kusan ƙarshe ne da har ya samu harbi gab da shirin buɗe Companynsa na kano har aka harbesa, ALLAH dai ya taƙaita wahala harbin ya samesa a gefen kafaɗarsa ta hagu, daga nan ne Hayatu ya dage akan fitarsu da Guards ɗin.
Tsaiwar motocin ya sashi kauda tunanin ya ɗago, ganin asibiti ya sashi ɗan kallon Hayatu daya buɗe masa ƙofa. Murmushi Hayatun yayi yana duƙar da kai da sosa ƙeya. Komai baice masa ba face ɗan girgiza kansa kawai ya zuro ƙafafunsa ya fito. Ciki suka nufa batare da ya lura da motocin su Paah ba, amma shi Hayatu sarai ya gansu dan tsakanin isowar tasu da tasu ma ƴan mintuna ne.........✍️
To Masha ALLAH. Barkan mu da dawowa, ku tayani addu'ar dagewa na gama book ɗin nan kafin salla😀🥰
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_
_______
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
____________
......A ɓangaren su Paah kuwa isowarsu kenan asibitin suma. Ba kuma su san da su Maash a bayansu ba. Kai tsaye suka nufi cikin ɗakin bisa rakkiyar Mama Balki da sukai kira a waya. A tsorace cikin damuwa ta musu jagora dan bata san dami suka zo ba. Sai dai babu yanda zatayi dole tabi umarninsu. Sauƙin ma taga akwai Baba prof a tare da su. Sun shigo Samraah na zaune a kan gadon jingine da filo tana shan tea ɗin da Mama Balki ta haɗa mata a hankali. Fes take dan har tayi wanka saboda gashin ruwan zafi da Mama Balki tai mata bisa umarnin likitan.