Showing 30001 words to 33000 words out of 438336 words

Chapter 11 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2145

ne yake hakan, sai ko Ammie. Volume ɗin tvn ya sassauta tare da canja tasha zuwa inda yasan yafi yawan kallo a irin wannan lokacin. Tasha ce ta addini, sai dai suna gabatar da duka programs ɗin su ne da turanci, hatta da wa'azi kuwa........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_


.......Gyaran murya ya ɗan yi idonsa akan Tijjani. Cikin sauri Tijjani da idonsa ke akan tv ya maido hankalinsa garesa. Kafin ma yace wani abu cikin muryar nan tashi kamar ta rowa ya taresa da faɗin, “Ina za'a samu abinci mai tsafta?”.
Cikin girmamawa Tijjani ya ce, “Ranka ya daɗe akwai gidajen abinci masu inganci dake tsaftace abincinsu sosai a garin Kano. Harma da masuyi a cikin gidaje sai dai kawai ai order suna da masu delivery da zasu iya kawo maka har inda kake, ko aje a amso”.
“Good. Sai ka samo duka gidan. Ka tambayi kowa abinda yake buƙata”
“In sha ALLAHU yanzu kuwa ranka ya daɗe”.
Bai sake cewa komai ba ya maida idonsa a television dan an fara gabatar da program ɗin da yay zaman kalla. Hayatu ne ya miƙawa TJ kuɗi masu yawa. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Nidai jallop rice da ƙirjin kaza nake so.”
Dariya TJ yayi ƙasa-ƙasa yana ƙumshe baki dan karta fito. Sai kuma yayma Hayatu nuni da ogan nasu da ido. Kai Hayatu ya jinjina masa yana sake gyara nutsuwarsa da maida hankalisa garesa ya ce, “Sir za'a karɓo maka kaima ko?”. Shiru kamar bazai tanka ba, dan yamayi biris tamkar baiji ba. Sai kuma batare da ya kallesu ba ya ɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai shegen ƙyau. Ya ɗan yamutsa fuska da jan siririn tsaki. “In dai bazai jima ba a samo min tuwon semo.. miyan kuka”. A tare suka amsa da girmamawa. TJ ya fita da hanzarinsa dan sun san baya cin abincin dare late, wani lokacin ma bai fiya ci ba. Yau ma suna ƙyautata zaton dan baici komai bane tun black tea ɗin safe. Haka yake abinci bai damesa ba, shiyyasa ga shi nan ko kaɗan baida wani tunbi, jikin ma badan yana haye-hayen waɗan nan tarkacen machines ɗin na motsa jikin zamani ba da zai kasance ne falen-felan.
TJ na ficewa Hayatu ya katse tunaninsa tare da matsowa inda yake. Da ga tsayen da yake kamar soja ya ɗan rissina yana fito da flash da ga aljihunsa da faɗin, “Sir ga cctv footage ɗin an samo”. Juyowa yay ya ɗan kalli Hayatu ɗin a yanayin jin daɗin hakan. Sai dai kuma ko kaɗan fuskarsa bata nuna komai ba tana nan a ɗaurenta tamau. Kujera ya nunama Hayatu. Zama yay yana ɗaukar laptop dake a Centre table ajiye ya saka flash ɗin jiki. Kafin ya miƙe yaje har gabansa batare da yayi playing video ɗin ba. Ajiye masa yay a stool ɗin daya jawo a hankali gabansa sosai. Sannan ya zauna a saman carpet kusa da ƙafafunsa yana shiga inda folders ɗin videon suke. Duk zubama screen ɗin laptop ɗin ido sukai. Cikin ƙwarewar aiki Hayatu ya zaluƙo video ɗin sashen da abin ya faru, tare da dai-daita lokacin da komai ya faru sai dai baiyi playing ba ya ɗan ɗago ya kallesa.
A hankali ya furta, “Kunna”.
Kunnawar yayi. Ko'ina ya fara nuna shiru babu kowa babu motsin komai. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai ga Samraah na bubbuɗe ƙofifi bayan ta fito da ga wani lungu da suka san restrooms na ma'aikatane a wajen. Yanda take taɓa ƙofofin tana ɓata fuska kamar zatai kuka zai baka tabbacin ta ɓata ne. Can cikin takaici ta fincike face mask ɗin fuskarta. Ƙyaƙyƙyawar fuskarta da babu zanen komai na kwalliya ta bayyana. Hayatu dai ya gagara haƙuri sai da ya furta “Masha ALLAH” a hankali. Dan ko makaho ya laluba fuskar Samraah yasan yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, duk dama eyeglasses ɗinta har lokacin yana a idanunta shi bata cire ba. Isowarta ƙofar da suke ciki ya sanya Hayatu waro idanu sosai, sai dai bai iya cewa komai ba. Ta buɗe ta ɗan leƙa. Sai kuma tai baya a rikice alamar akwai abinda ta gani. Wayarta data zaro tai danne-danne ta kanga tabbacin video take musu yasa Hayatu kasa haƙuri ya furta, “What! Sir itace kenan?”.
Bai samu amsa ba, dan ogan nasa ko motsi baiyi ba har sai da ya kai ƙarshe. Fitowarsa, tsintar nurse mask. Har cigaba da video da Samraah tayi sanda suke fita da gawar mutumin. Cikin ƙanƙanin lokaci Hayatu ya gama haɗa uban gumi kamar wanda ke a filin kokawa. Shi kam duk da a birkice take video ɗin yaga matuƙar ƙarfin halin yarinyar nan. Motsin da ogansa yayi yasa hankalinsa dawowa jikinsa. Ya ɗan ɗago ya kallesa. Sai da gabansa ya faɗi ganin yanda cat eyes ɗinsa suka canja launi. Dan gaba ɗaya gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama ƴar siririya exactly yanda na mage suke komawa idan suna a cikin haske. Batare da ko kallon Umar ɗin ya sake yi ba ya miƙe ya fara tafiya. Sai da yaje gab da ƙofar bedroom ɗinsa sannan cikin dakiyar muryar dake tabbatar da ransa a ɓace yake ya furta, “A nemota duk inda take. A cigaba da bin duk wani motsinta daga nan zuwa sati biyu”.
“An gama Sir. Amma in baka manta ba ka bata damar yin hira da kai ma”. Hayatu ya faɗa cikin tsumar jiki. Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shigewa da yake yi kamar mai nazari, sai kuma batare da ya juyo ba ya furta “Zanyi tunani akan hakan”.
Buɗe baki Hayatu yay zai sake magana cikin nuna gamsuwa, sai dai harma ya riga yay shigewarsa shi. Hayatu ya rabga tagumi tare da faɗin, “Tab ƙyaƙyƙyawa kin shiga uku wlhy, bama ke ba duk zuri'arki kin sakasu a masifa. Ke miya kaiki shiga gonar da bataki ba. Aikata wannan aikin da ba'a sakaki ba, karanbaninki ya ɗebeki shiga fadar sarkin aljanu. Dan oga ALJANI ne irin ifiritan nan.” yana cikin wannan sambatun nasa TJ ya shigo da ledoji masu ƙyau an musu tambarin gidan abinci. Firgigit Hayatu ya dawo hayyacinsa tare da gyara yanayinsa. TJ da ma bai wani lura da halin da yake a ciki ba ya ajiye masa tasa ledar sannan ya ajiye wata a Centre table yana faɗin, “Wannan tuwon oga ne. Shi na tsaya ma sai da akayisa yanzu-yanzu gashi nan da zafinsa yanda zai masa daɗin ci.”
“Ai wannan tuwon mawuyacine ya samu shiga kuma yanzu”.
Idanu TJ ya waro a rikice ya furta, “Na shigangaɗi Hayatu badai na makara ba? Wlhy babu tuwonne amma matar tace zatayi da sauri tana da miya. Ni kuma naga tunda yace yana buƙatarsa yana so ne shiyyasa nace tayi da sauri...”
“Kai ka kwantar da hankalinka badan ka daɗe bane ba kawai dai wani abunne daban ya ɓata masa rai. Amma bari na gwada faɗa masa ka dawo mugani”.
Ajiyar zuciya TJ ya saki, duk da kuwa yanayinsa bai warware ba. Dan in har ogan nasu na cikin ɓacin rai ko damuwa suma sukan shiga matuka saboda yanda suka ɗauki al'amarinsa da matuƙar muhimmanci a rayuwarsu. Tashi Hayatu yay ya nufi hanyar bedroom ɗin nasa, sai da yay jimm a tsaye bakin ƙofar kafin yay knocking a ɗarare. Ko motsi ba'aiba, bai gajiyaba ya sake yi tare da sallama. Nan ma anja kusan minti ɗaya kafin ya amsa masa a daƙile. Sake nutsuwa Hayatu yay kafin cikin dauriya ya ce, “Kayi haƙuri Sir, dama TJ ne ya dawo, a kawo maka abincin nan ne”.
“No! I'm okay”.
Shiru Hayatu yay cikin nuna damuwa ƙarara a fuskarsa. Sai kuma ya sake raunana murya ya ce, “Please Sir, duk yau fa bakaci komai ba. Ko nace ma rabonka da abinci tun shekaran jiya a Lagos. Abu mafi saka Ummie damuwa a rayuwa shine ka kwana da yunwa. Dan ALLAH ko kaɗanne ka daure kaci, saboda nasan duk da bata tare damu zata ji a jikinta kamar yanda ta saba”.
Wani irin cizar lips yay da ga zaunen da yake a bakin gadon hannunsa dafe da kansa. Hayatu ya matuƙar sanin lagonsa a rayuwa. Dan shine kaɗai yake iya bi da shi fiye da kowa bayan mahaifiyarsa. Hakan kuma nada alaƙa da sanin da yay masa tun ƙuruciya. Duk da dai shi ya girmi Hayatun da kusan shekara biyar ma, amma kasancewar sun tashi ne shi da iyayensa a cikin gidan kakansa da ya haifi Ummien sa yasa yay masa farin sani na gaske. Ya jima a gurin kamar bazai motsa ba sai kuma a daƙile ya furta, “Kawo nan”. Cikin sauri Hayatu yabar jikin ƙofar cike da farin ciki bawan ALLAHn kamar cikinsa zai kai. Babu jimawa kuwa sai gashi da tuwon. A can ya shirya masa shi saman table ɗin gaban sofa dake bedroom ɗin, har lokacin kuma yana a zaune bakin gadonsa hannunsa dafe da kansa. Yanayi ne dake nuna yana cikin zafin rai, dan Hayatu ya sanshi a rayuwa fiye da tunanin mai tunani. Ganin Hayatu ɗin baida niyyar fita yaja siririn tsaki yana ɗagowa, harararsa yayi da faɗin, “Ka tsaya gadi na ne sai naci ka gani?”.
Ƙasa Umar yayi da kai yana ɗan murmushi. Sai kuma ya rissina tare da faɗin, “Ayi haƙuri Sir”. Daga haka ya fice a ɗakin. Wani tsakin ya sake ja sannan ya miƙe zuwa gaban sofa ɗin ya zauna. Hatta ruwan wanke hannu Hayatu ya tanadar masa. A nutsensa cikin yanayinsa na rashin gaggawa akan komai ya fara cin tuwon dan yana son tuwo sosai saboda fevorite food ɗin Ummien sa ne, ada sanda yana yaro idan tayi tace sai yaci yakan zauna yayta kuka shi bazaici miyan daddawa mai wari ba. Amma bayan wani lokaci da rayuwa ta canja kanta zuwa abinda bai taɓa mafarkin riska ba a cikinta sai ya maida tuwon fovorite nashi shima. Yaci kusan rabin malmala ɗaya ya ajiye duk da kuwa tuwon ya masa matuƙar daɗi, sai dai bai cika son cin abinci late haka ba. Shiru ya ɗan yi zaune a wajen kafin ya tashi zuwa toilet. Brush yayi da sake gyara jikinsa ya fito. Ya samu Hayatu har ya shigo ya tattare komai harda sakama ɗakin freshener ya ƙara dai-daita masa ac. Komai baice ba ya rage kayansa zuwa na barci, sai dai maimakon kwanciyar zama ya sake yi a sofar yana ƙoƙarin kunna laptop ɗinsa, dan yana son ƙarasa harƙallar wani business ɗinsa kafin ya kwanta. Dai dai kuma mi hakan kamar neman gagararsa yake. Dan tunda ya kunna ya gagara danna ko keyboard ɗaya tunaninsa ma neman tafiya yake wani sashe daban. Da ga ƙarshe dai ya ture laptop ɗin gefe ya ɗauki wayarsa. Wata number da aka saka Dude ya nemo tare da danna kira.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)


_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_

......Kusan lokaci ɗaya muka iso garejin da Mansoor. Dan haka babu ɓata lokaci muka nufi cikin motarsa, dan nan ɗin zaifi mana zama sirri fiye da ko'ina saboda abinda zamu tattauna ɗin. Gaba Yaya Musaddiq ya shiga ni kuma baya. Sun gaisa da Mansoor cikin mutunta juna kamar yanda suka saba nima na gaishesa. Amsawa yay idanunsa a kaina ta cikin mirror.
“Ya kamata ki huta da kukan nan Samraah. Sai kace kece kika aikata laifin nan. Kinga kuwa yanda idanunki suka koɗe”. Mansoor ne yay maganar cikin nuna damuwa matuƙa. Yaya Musaddiq dake saurarensa ya ce, “Ai ita haka take bata bin al'amarin rayuwa a hankali ka ganta nan. So take sai ta jama kanta wani ciwon muma ta sake sakamu a wata damuwar sannan”.
Idanuna na cikowa da hawaye na ce, “Kuyi haƙuri Yaya ba haka bane. Wlhy na kasa mantawane da ganin gawar kawai. Amma in sha ALLAHU bazan ƙara ba”.
“ALLAH yasa hakan” Yaya Musaddiq ya faɗa. Yayinda Mansoor yaja numfashi ya fesar tare da amsawa da Amin. Idanuna na share tare da ƙoƙarin yin magana wayar Mansoor ta shiga ruri. Tamkar an saita sai tawama ta fara. Kusan a lokaci ɗaya duk muka kai hannu domin ɗauka. Sai kuma muka kalli juna tare da sake ɗagowa duk muka kalli Yaya dake tambayar mu “Lafiya kuwa?”.
“Daga office ne”. Mansoor ya bashi amsa yana ƙoƙarin kai wayar kunnesa. Nima dai tuni nakai tawa tare da yin sallama. MD ne ya amsa daga can, batare daya bi takan gaisuwata ba ya ce, “I'am Sorry Samraah muna son ganinki a office yanzu Please”.
“Yallaɓai lafiya kuwa?”. Na faɗa da sauri hankali a ɗan tashe.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Kinga kwantar da hankalinki ba wata damuwa bace. Mun samu baƙuncin babban baƙone mai matuƙar muhimmanci da muka daɗe muna fata. Ya kuma ce da ke kaɗai yake son ayi hira da shi”.
“Ni kuma oga? Duk mutanen dake a gidan sai yace sai ni. Wanene haka da ƙarfin halin nan? Sai kace wani abin cin rabo. Ya kamata Ku faɗa masa ba sashin da nake aiki ba kenan”.
“Humm Samraah Please mana. Dan ALLAH ki shirya kawai ga driver na nan ma na aiko gidanku ya ɗaukeki a motata”.
Sake tashi hankalina yayi, sai dai kafin nayi magana oga ya yanke kiran. Sagale nai kawai ina kallon wayar kamar wata gunki. Wane irin baƙone da zai tada hankalin oga har haka. Sannan kuma ma yace ni yake so nai hira da shi. “Kodai mutumin nan ne?”. Na faɗa a zahiri batare da nasan maganar ta suɓuce min ba. Atare Yaya Musaddiq da Mansoor da shima yay zororo alamar kiran da akai masa nada nasaba da nawan suka juyo suna kallona.
Yaya Musaddiq ne yay ƙarfin halin cewa “Wane mutumi?”. Firgigit na dawo hayyacina. Dan na fahimci zancen zucini ne ya fito fili. Idanuna ne suka cicciko da ƙwalla. Cikin rawar murya na zayyane musu komai da MD yace min. Mansoor ne yay saurin faɗin “Tabbas akwai alamar tambaya. Dan nima akan abinda suka kirani kenan. Amma ina ganin ki kwantar da hankalinki bari muƙarasa office ɗin domin ganin wanene ɗin ko kuwa Yaya Musaddiq?”.
“Tabbas shawararka yayi Mansoor. Tunda akan aikine bai kamata ayi sakaciba kam. Kuje idan kun dawo ma ƙarasa maganar in sha ALLAH. Nima zuwa lokacin na ɗan ƙara yin nazari.”
Mansoor ne kawai ya iya amsa masa. Nikam sai binsu da kallo kawai nakeyi. Yaya Musaddiq ya fita yana buɗe baya yace na fito na dawo gaban. Ganin banda niyyar hakan ya buɗe ya kamo hannuna ya fiddoni ya maida gaban. Key kawai Mansoor yayma motar ya haura kan titi. Babu wanda ya iya sake yin magana a cikinmu. Kafin mu isa office ɗin kuma sai danno mana kira MD yake yana kuma sakawa amana. Da wasu kalar shegun zuƙa-zuƙan motoci na alfarma muka fara cin karo a harabar gidan. Sai mutane cikin baƙaƙen kaya tsatstsaye ƙiƙam kamar masu tsaron ƴan fashi. Mudai wucesu mukai muka shiga abinmu. Duk da lahadine mun samu ma'aikatanmu dake duty a wannan ranar dukansu. Harma da wadanda aka kira irinmu da ranar suna hutu suma kamar mu ɗin dai. Office ɗin MD muka wuce kamar yanda aka sanar damu yace muyi. Anan ɗin ma mun tadda mutane biyu irin waɗanda ke a haraba su biyu a jikin ƙofar. Matsa mana sukai muka shiga bayan Mansoor yayi knocking an bamu izinin shiga. Mun fara cin karo da ƙamshin turare mai armashi sosai. Sai sanyin ac a office ɗin kamar ba safiya ba. Wannan kuma ba halin MD bane zama cikin ac da ƙarfi haka.
Akan MD idanunmu suka fara sauka. Kafin dattijon dake zaune a kujerar kusa da shi cikin shigar ɗanyar shadda mai tsananin ƙyau da ɗaukar hankali sai maiƙo take da walwali. Ƙyaƙyƙyawane sosai baƙi ga dogon hanci da shiryayyen farin gashinsa daya ƙawata taswurar fuskar tasa. Gaishesa muka farayi kawunanmu a ƙasa. Dan tun shigowarmu ya zuba mana idanunsa manya farare yana murmushin bajinta. Yanzun ma da fara'ar ya amsa mana. Sai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login