Showing 315001 words to 318000 words out of 438336 words

Chapter 106 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2153

tashi su wuce Hayatu ya ce, “No Yaya ba'a haka ba. Sai Ummie ta kimtsa ku bani awa uku kawai.” baima saurari amsar Maash ɗin ba ya fice. Kamar ko yanda ya buƙata awanni ukun ma basu gama cika ba sai gashi da duk kayayyakin da Ummie ɗin ta saka. Kawo kayan ya saka Maash haɗa sabon plan shima. Dan haka yay kiran Sheikh da ya sauka Lagos babu jimawa yay masa bayinin akan Fahad. Dan yana fatan yanda yake jin sakawai game da ɗan uwan nasa a yanzu babu wannan ƙiyayyar shima ta kasance hakan. Kuma ko shi abin bai sakesa ba ya san ko akan Ummie da Samraah zai iya yin duk abinda suke so. Sai gashi kuwa komai ya tafi musu dai-dai a ƙanƙanin lokaci Fahad ya haye dokin da suka azashi....
Ummie taso ganin Samraah kafin shigarsu Maash Mansion amma Maash ɗin ya lallaɓata akan tayi haƙuri, akwai dalilin da yasa baya son su haɗu a yanzu dan zata iya shiga shock ɗin da matsala zata iya afkuwa. Dole ita tana buƙatar a bita mataki-mataki yanda komai zai zo mata da sauƙi. Amma ya mata alƙawarin yanda zata kwana a maash Mansion itama Samraah a ciki zata kwana in sha ALLAHU yau.. wannan ne ya bata ƙarfin gwiwar haƙuri suka tafi...
Rikicin daya ɓarke acan babban falon gidan da kowa yay cirko-cirko yana kallon Fahad dake garzaza tsiya da rantsuwar idan har basu fiddo masa Yayansa da Ummiensa da Paah da Samraah da Hayatu da su Mama Balki da Falaq kamar yanda suka fiddosu shi da Hafizzullah ba. Ya rantse da ALLAH yau sai kowa ya kwana da zanen yarbawa a fuskarsa kafin da safe yasa a kwashesu zuwa police station gaba ɗayansu yasa basu ko ji motsin shigowar motar su Maash ɗin gidan ba. Tun a main perlor suke jiyo hargagin Fahad. Wani irin makirin murmushi Maash ya saki yana mai lumshe idonsa baby har yanzu na'a hannunsa ya kwantar da shi a kafaɗarsa ya riƙe Ummie da hannunsa na dama. Mama Balki ce ta fara shiga da sallama mai ɗan ƙarfi. Hakan yayi dai-dai da juyowar Fahad yana nuna Baba prof dake tsaye kawai zufa ta gama jiƙesa dan kalaman Fahad wani masifar ratsashi suke, ballema yanzu da yake nunasa da takobin yana faɗin, “Wlhy da kai zan fara Baba. Dan ma su san da gaske nake yi babu ruwana da kai ka haifi Paah zaneka zanyi da takobin nan tsaf da zanen yarbaw.....” yay ɗiff ya gagara ƙarasawa yana kallon Mama Balkin kamar yanda take kallonsa tana murmushi. Baki ya motsa zaiyi magana sai kuma ga Hayatu, kafin yace tak Falak ta shigo da sallama itama. Ya yunƙura zai nufesu kamar yanda Hajiya Mama da Maman Malika suka yunƙura suma sai ga mai gayya da aiki Muhammad Awwab El-Mu'azz Adams riƙe da hannun Ummie ga abu dake a kafaɗarsa dake tabbatar da Baby kuma.
Yanda kuka san an saka remote an tsaida Film ɗin dake tsaka da aiki haka kowa ya tsaya cak a yanda yake. Musamman Hajiya ƙarama da Baba prof. Yayinda karyayyen harshen nan na UMMIE daya rangaɗa sallama ya ratsa kunnen kowa tamkar yanda sautin kiran salla kan ratsa kunnen mai barci a bazata. Karo na farko Baba prof ya wani zabura ya manne da bango. Hajiya ƙarama ma tai baya tana mai sakin handbag ɗin hannunta zuciyarta na wani girgiza a cikin ƙirjinta. Hajiya Mammah dai baki ta saki da waro idanu waje gaba ɗaya. Haka Maman Malika sai da ta ɗan ja baya.. Fahad kuwa wani kalar suɓucewa takobin hannunsa tayi tare da ƙafafunsa ya tafi ƙasa ragwafff ya dire gwiyawunsa a ƙasa tamkar irin tsohon raƙumin nan daya galabaita a tsakkiyar sahara... Yaran kam da su ganin Hajiya Babba cikin ado kuma tana sallama ne ya hargitsasu duk sai suka cure waje guda suka ƙanƙame juna. Dan tuni an gama cusa musu zancen Hajiya Babba mahaigakciya ce tuburan da zata iya kisa ba kuma lallai ta warke ba...
Da wani kalar sassarfa Ummie ta ƙarasa ga Fahad, tarosa tayi gaba ɗayansa dan neman rasa numfashi yake tsabar firgita. Wani irin ƙanƙamesa tayi a jikinta cikin matuƙar dakiya ta furta, “Oh my sweet Auta don't fall down” dan tayi alkawarin bazata sake barin maƙiya suka gazawarta ba. Ina Fahad fa ya shiɗe farin ciki ko firgici sun sakashi suma. Hayatu ne yay saurin ɗakko ruwa ya kawo. Ɗago Fahad ɗin yayi daga jikin Ummie da nauyinsa ya sata zama dole ya shafa masa ruwan. Nannauyan numfashi ya kawo mai azabar ƙarfi. Sai kuma ya kalla Hayatun da Maash dake tsaye a kansa. Muryarsa na rawa hawaye na kwarara ya ce, “Yaya mafarki nayi Ummie ta warke harta shigo ta ganni na ganta fa. Dan ALLAH miyyasa kuka tadani ku barni na koma ko magana muyi da ita”. Ya faɗa yana sake rumtse ido.
“Ba mafarki bane kiddo. Da gaske ne buɗe idonka”.
Tamkar matsoraci jikin Fahad ya fara rawa, hatta idanunsa mar-mar sukeyi yana buɗesu a hankali har ya buɗe gaba ɗaya kan ƙyaƙyƙyawar fuskar UMMIE da ke kallonsa tana hawaye itama. Hannunsa dake rawa ya shiga ɗagawa a hankali a hankali har ya isa saman fuskarsa ya ɗora. Da sauri ya janye tamkar wanda ya dafa wuta. Sai kuma ya miƙe zaune daram ta sake kai hannun yana kallonta yana hawaye. Caraf ta riƙe hannun tare da ɗorawa saman fuskar tata ta ƙanƙame. Sai ga hawayen da taketa riƙewa sun zubo sharrrr. Wani irin firgitattacen ihun da faɗin “Ohhhh Myyyyy Goooood!!!” Fahad ya fasa yana rungumeta gaba ɗayanta sai kuma ya fashe da kuka.
A hankali Maash ya kauda kansa gafe na tsawon minti ɗaya kafin ya maidosa kansu. Hayatu ya miƙama Babyn sannan ya kai duƙe a slowly tamkar wanda baya so ya ɗago Fahad daga jikin Ummie. Miƙar da su yay tsaye su duka ya kama fuskar Fahad da hannu biyu ya fara share masa hawayen da yatsunsa manya yana wani ɗan jujjuya masa kansa”.
Jikinsa kawai Fahad ya faɗa suka wani ƙanƙame juna da iyakar ƙarfin ƙwanji. Cikin kuka Fahad ya ce, “Yaya dan ALLAH da gaske UMMIE ta samu lafiya? Da gaske ba mafarki nake ba kamar yanda na saba?”.
Ɗagoshi Maash ɗin yayi ya tsurama fuskarsa ido. Sai kuma ya sakar masa wani shegen murmushi daya kusan ɓaro zukatan wasu tare da motsa lips ɗinsa kaɗan, cikin silent voice ɗin nan tashi ya furta, “Ba barci kake ba Kiddo. Ummien ce a gabanka da lafiyarta. Dan haka ga saƙo ka faɗama MAƘIYA GASKIYA!!!” ya ɗan ɗaga sautinsa anan ta yanda kowa sai da ya jisa. “Su fara gudu, gudu na ceton rayukansu. Gudu na cigaba da bizne abinda suka shuka. Idan ba haka ba. Bayan ka musu zanen Yarabawa. Ni Muhammad Awwab El-Mu'azz nayi musu alƙawarin sai nayi gunduwa-gunduwa da kowanne gaɓa ta jikinsu ta yanda ba za'a iya iya banbance kowanne ɓangare na halittar su ba!!!”.
Tamkar wani abun shirin Film kawai Fahad ya bushe da wani ɗan iskan dariya. Sai da yay mai isarsa kafin ya kalla yayan nasa. Cike da jin sabuwar izza ya ce, “My sweetheart yayana. Idan ka fatattaka namansu. Na maka alƙawarin siyo ƙatuwar tukunya da ƙatin iccen nan na dahuwan naman raƙumi, na bama Aunty Samraah ta mana DABGENSU mu baje a ƙaton tray UMMIE da MAMA su dinga bamu a baki muna taunawa da korawa da ruwan kamfanin MAASHHHHHHH”.
Dariya abin ya bama Falaq. Tako kasa haɗiyewa ta fara ƙyalkyatawa. Sai kawai Hajiya Mama da itama abin ya birgeta ta shiga yin dariyar. Ai kawai sai su Mama da Hayatu da Maman Malika suka hau tayasu. Gogan kan sai ya wani lumshe idanu kawai yana mai tura hannayensa duk biyu a cikin aljihu. Da wannan damar Hajiya Mama da Maman Malika suka sami damar tahowa rungume Ummie. Tsabar makirci sai itama Hajiya ƙarama ta taho da gudu tana kuka zata rungume Ummien wai. Ajiyar zuciya Hajiya Mammah ma ta saki tana sakkowa. Ganin hakan yasa su Azizat fara sakkowa daga upstairs da suka maƙale a guje suma duk da bawani saninsu Ummie ɗin tayi ba duk suna ƙananu sosai, sai ɗan sanda ta samu lafiyar nan lokacin kuma ba'a tare suke ba. Suma duk nufar rungumetan sukayi. Amma mi duk kafin su isa gareta sai kawai Fahad yasha gaban kowa ya tare ta. Cak duk suka tsaya suna kallonsa kamar yanda shima yake kallonsu cikin wani irin ɗage kan rainin waye da girgiza hannu ya ce, “Inaa ai babu mai taɓa Ummie a gidan har sai anyi searching”. Yana gama faɗa yaja hannun Ummie yay hanyar sashen Maash da ita dake ta cikin falo yana wani kalar takun buɗewa daka gani kaga tsageran matashin zamani mai shirin a mutu ko ai rai🤣😂.
Shi kansa Maash a wannan gaɓar sai da yay gajeren murmushin da kowa zai iya gani a kan fuskarsa yana mai ɗan girgiza kan kaɗan. Batare da yace ma kowa komai ba yay ma Falaq nuni da hanya ita da mama Balki. Gaba kuwa sukayi ya bisu a baya bayan ya juya ya kalla Baba prof cikin ido ya sakar masa murmushi, ya sake juyawa ga Hajiya ƙarama ita kuma ya mata wani shegen kallon da su duka sai da suka nema zubewa ƙasa. Cikin nashi takun bajintar shima yay gaba. Yayinda falo yake tsitt har yanzu tamkar an jera gunkunaye. Kowa da abinda yake rayama zuciyarsa.
Rawar da ƙafafun Baba prof keyi yana shirin zubewa a ƙasa ya maidosa hayyacinsa daga sumar tsaye da yayi sakamakon kallo da murmushin da Maash ya masa. Yay taga-taga zai faɗi sai da Hayatu ya taroshi yana faɗin faɗin, “Subahanallahi Baba”.
Cikin wani irin jan numfashi dake shirin ƙwace masa a hankali ya ce, “Kaini na zauna Hayatu zaunar da ni.”
Babu musu Hayatu ya kamashi har kan kujerar dake kallon ta Hajiya ƙarama da itama ta kai zaune sakamakon jirin dake neman yarda ita ya zaunar. Sai kawai ya ƙara yin shakaff a kujerar dan kaɗan ya rage zawayin dake ƙoƙarin ɓarke mas ya samu ƙofar fara tsirarowa.........✍️

(😂😂😂😂Baba prof sannu kaji, abin tausayi wlhy🥱🥱🥱).



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒇𝒐𝒖𝒓_


.......Shigowar Uncle Abdullahi gidan da labari ya kaimawane ta dawo da kowa a hayyacinsa. Sai tarin da ya sarƙe Baba prof. Su duka su kansa sukayi, banda Hajiya ƙarama data samu hanyar hayewa sama. Kallon kallo sukaima juna ita da Hajiya Rubayya da har yanzu ke tsaye tana kallon komai. Sai kawai suka sakima juna murmushi. Cikin rawar murya Hajiya ƙarama dan ita kaɗai tasan halin da take ciki itama ta ce, “Ki tattara su Falilah subar gidan nan zuwa gobe bayan kowa yasan wacece Nafisa”.
“An gama ranki ya daɗe”.
Hajiya Rubayya ta faɗa cikin kashe ido tana sakin wani makirin murmushi. Gaba Hajiya ƙarama tayi zuwa sashensu. Sai da ta tabbatar ta dannama ƙofar key kafin ta wurgar da bag ɗinta bayan ta ciro wayarta. Kira ta dannama Commando, yana ɗagawa bata jira cewarsa ba cikin bushewar zuciya ta furta, “Wasa ya canja gaba ɗaya. Dole ne a mutu har liman. Uwar tafiya ta dawo hayyacinta, yanzu kam kan mai uwa da wabi kawai. Ka canjama Mu'azz wajen zama a daren nan. Shi kaɗai ne makamin mu a yanzu”.
Tana gama faɗa ta yanke wayar. Jannifer ta kira, itama tana ɗagawa tace, “Bana son kuskure. Idan har naga kiranki ya zama Mu'azz da Commondo na a hannunki ne”. Wayar ta wani irin jefa saman gado. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya ta kuma fashe da kuka duk a lokaci ɗaya, tamkar itama dai kan nata ya fara taɓuwa.

Hajiya Lawisa sorry woohoo😂😂🤣🥱.


✨✨✨✨

Commondo ya jima zaune da waya a hannu shi bai ajiye ba shi bai motsa ba. Dan shi kansa ba ƙaramin dukan zuciyarsa zancen Hajiya Ƙarama ɗin yay ba. Yanzun nan fa yake ganin text message ɗin wani yaronsa da tun ɗazun ya turo masa kasancewarsa da Hajiya ƙarama yasa bai lura ba. A saƙon yana sanar masa cewar ya gano inda Mahaifiyar Maash take. Har ya tura masa address yanzu haka shirin da yake kenan na zuwa su ƙwamusota ransa fari ƙal zai fara aiwatar da nasa plans shima. Kansa ya girgiza, dan haka kawai yaji kamar bai yarda da batun Hajiya ƙarama ɗin ba. Wayar ya fara daddanawa, yana zuwa kan sunan da yake nema ya danna mata kira.
Siyama da tun ɗazun take a bayan window laɓe ita da wasu ma'aikatan gidan mabanbanta suna kallon komai dake faruwa dan tun isowar su Maash duk wanda idonsa ya gansu bai zauna ba ya biyo saboda son tabbatar da Hajiya Babba ɗin ce ko watace ke musu gizo wayarta ta hau tsuwwa. Da sauri tabar wajen ganin Commondo ne. Sai da ta shige cikin garden sosai sannan ta ɗaga tana mai maida muryarta can ƙasa ta ce “Boss”.
“Siyama mike faruwa a gidan nan?”.
“Hummm! Boss ai komai ma ya faru ko nace yana kan faruwa. Jira nake kawai akai ƙarshen Film ɗin na kiraka na baka bayani.....” tsaf ta zayyane masa komai fiye da yanda Hajiya Ƙarama ta sanar masa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Mutuniyarka ta haye sama kamar zata zube. Dan numfashinta ma kamar siezing yake. Kakansu ɗin nan da yau na ɗaura alamar tambaya a kansa gashi nan za'a wuce da shi gida naji suna kiran likitansa”.
Murmushi Commondo yayi, dan yasan Siyama bata san komai akan Baba prof ba. Ya turata jikin Paah ne domin ɗaukar fansa da sanya masa ido akan duk wani motsin Hajiya ƙarama. Tunaninsa ya katse tare da yin gyaran murya. Sannan ya ce, “Zamanki ya kusa ƙarewa a gidan nan. Sai dai ki saka min ido akan Lawisa sosai-sosai a tsakanin nan. Koda tari tayi na sani”.
“An gama Boss”. Ta faɗa cike da girmamawa. Dan commondo ya cancanci fiye da komai a wajenta. Ya taimaketa a lokacin da kowa ya ƙyamacesu akaƙi taimakonsu ita da mahaifiyarta. Ita kaɗai ta tashi gaban uwarta batare da sanin kowa a danginta ba da mahaifinta. Tunda tai girma tayi wayo takan tambayi mamanta ina babanta saboda ganin sauran yaran da iyayensu ke haya a gidan da suke duk suna da Baba. Maman tata bata bata amsa. Sannu-sannu idan faɗa ya haɗata da yara sai a dinga zaginta da kiran mamarta karuwa ita kuma ƴar shege. Tun abin baya mata zafi harya fara. Ta dinga tsare mamarta tana kuka amma bata cewa da ita uffan. Daga ƙarshe ma suka bar gidan. A anguwar da suka koma ɗin ma komai bai canja ba, dan nan ɗin ma dai Hausawa ne. Tasha kama mata a lokuta da dama na gulmar mamanta akan ita munafukar karuwa ce. Kullum tana nuna ita ta ALLAH ce sai dare yayi ta fita aikata aikin ta. Tun abin baya mata tasiri har itama ta fara tsarguwa da fara sakama Maman nata ido. Sai dai hakan ya gagara dan barci na hanata rawar gaban hantsi. Tunda tai wayo bata iya wuce takwas na dare batai barci ba, takan kuma rasa dalilin hakan. Sai daga bayan nan data duƙufa bincike ta gano Maman nata ce ke bata abinda ke sakata barci ashe a cikin wata FURAR ƙaddara data sabar mata sha tun tana yarinya. Dan haka tafa canja taku itama. Furar ta fara sayowa tana ɓoyewa a duk sanda Mamanta ta bata wadda keda maganin sai ta ƙi sha ta canja da wadda ta sayo ta ɓoye waccan. Haka zatai likimo har Maman tata ta gama shirinta cikin ƙazamar shiga irin ta karuwan dare ta zabga hijjab har ƙasa sannan ta fita. Randa ta fara gani tayi kuka sosai, daga baya ma sai ta sha furar nan barci dole ya ɗauketa. Sai da sukai haka da mamanta fin sati sannan a cikon kwana na takwas tabi bayanta. Hankalinta yay mummunan tashi da abinda ta gani, dan tabbas Mamanta Karuwa ce. Karuwarma ƙazamar karuwa da ake nema ta gaba da baya. Kaɗan ya rage a ranar Siyama bata bar duniya ba. Dan har jiyya ta kwanta na wasu kwanaki. Bata da aiki sai kuka. Ko kallon Mamanta bata ƙaunar yi. Kwatsam a washe garin da aka sallameta asibiti sai ga Mamanta an kawo jage-jage da jini wai wata ta soketa da kwalba a club. Duk yanda taso barinta zuciyarta bata yarje mata hakan ba. Haka ta rungumeta tana kuka da roƙon a taimaka mata. Amma mi kaf anguwar babu wanda ya taimaketan sai Commondo. Shi ya saka yaransa suka ɗauki Mamanta aka kai asibiti, ya biya kuɗin komai harna gado. Tsahon sati uku da tai a asibitin nan har nauyin abincinsu shiya ɗauka. Sai dai me tunda suka dawo gida sai sabon ciwo

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login