Showing 60001 words to 63000 words out of 438336 words
kallo, nasan kuma dalilin yin hakan, dan kan shower ɗin na ɓalle nabar ruwa nata zuba. Ka ɗan naga ya duƙa yana kai yatsansa biyu ƙasa ya dangwala, sai kuma naga yay saurin ajiye ledar abincin hannunsa ya nufi toilet ɗin da alama ruwan ne ya fara fitowa.
“Lafiya miya faru?”.
Na faɗa a hankali. Bai tanka min ba, bai kuma tsaya ba. Na saki murmushi ina tashi zaune. Bayansa na bi. Duƙe na samesa yana ƙoƙarin buɗe hanyar da ruwa ke fita gaba ɗaya da ɗayan hannunsa. Ɗayan kuma ya danne pipe ɗin shower ɗin ya cusa babban yatsarsa a ciki ya tsayar da ruwan. Sai dai duk da haka yana ɗan fita sii. Da wannan damar nai amfani nima na shigo ina faɗin, “Tun ɗazu nake kiranka dan ka duba amma baka amsamin ba.”
Kaɗan ya juyo ya kalleni sai kuma ya sake maida kansa ga abinda yake yi. Ni ko na duƙa kamar zan janye masa boket dana jiƙa kaya ciki na samu nasarar zare wayarsa. Da sauri na tusata cikin rigata. Na janye bokatin na fita abina. Sake komawa nai cikin katifar nai kwanciyata. Sai dai zuciyata sai faman gudu take a ƙirjina. ALLAH ALLAH nake ya zo ya fita kafin ya farga babu wayar tasa. Amma bai fiton ba sai kusan bayan minti goma. Batare daya kallan ba ya nufi hanyar fita. Cikin rawar jiki ina jin ya kulleni ta baya alamar ya tafi kenan. Na ciro wayar. Naji daɗin ganin babu password jiki, cikin rawar jiki data hannau na saka number Yaya Musaddiq na danna masa kira. Harta katse bai ɗauka ba. Hankalina ya sake tashi jikina har kakkarwa yake. Sake ƙoƙarin kira nake ina kallon ƙofar. Nan ma ta shiga amma har tana neman yankewa babu alamar za'a ɗauka. Nama gama sadaƙarwa dan idanuna har sun cika da hawaye sai ya ɗaga. A yanda yay sallama cikin wani yanayi na mutum mai damuwa yasa idanuna sun ciko da ƙwalla. Cikin rawar muryar alamar son sakin kuka na ce, “Yaya Musaddiq nice. Nice kandalarka. Dan ALLAH kuzo ku fiddani anan karna mutu. Yaya banda lafiya ciwo zai kasheni. Sun kawoni nan sun ɓoye kullum sai dai suyita bani abinci kawa.....”
Fittt naji an ƙwace wayar daga hannuna. Hannu ya ɗaga zai ɗauke fuskata da mari sai kuma miya tuna oho masa ya tsaya cak. Niko tsoron da naji na kar ya kai ƙaton hannunsa kaina ya sani dunƙilewa waje ɗaya na rumtse ido. Jin shiru banji saukar marin ba na buɗe idona. Dai-dai nan yake ƙoƙarin fita a ɗakin. Na taso kuwa da uban gudu na nufi ƙofar nima, ina gab da ƙarasawa ya datse da sauri. Zubewa nai a wajen na saki wani kalar kuka mai ban tausayi da cin zuciyar mai sauraro.. Ina a wajen ko cikakken minti biyu baiyi da fita ba sai gashi ya dawo cikin sassarfa. Jin saukar handkerchief kawai nai a saman face ɗina. Kamar waccan ranar nayi niyyar yunƙurin tashi amma abinda suka shaƙa min yaci ƙarfina. Kamar ƙyaftawar ido na sulale ƙasa, daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba kuma..
✨●●)(●●)(●●)(●●✨
Gaba ɗaya yanda Yaya Musaddiq da Mansoor suka rikice bama su fahimci wayar ya yanke ba. Dan suna tare ne a mota sanda Samraah ta kira wayar. Da farko hankalin Mansoor ba'a kan Musaddiq yake ba. Sai da yaga yayi wata shegiyar zabura yana ƙwala kiran sunan Samraah jikinsa har wani gab-gab yake na rawa sannan. Wayar shima ya fisga jikinsa na rawa yake faman kiran ta. Sake ƙarɓewa shima Yaya Musaddiq ɗin yayi. Duk sun rikice sun ruɗe, jin dai ɗif ɗin yayi yawa suka ɗan fara dawowa hankalinsu. Sai sannan suka fahimci wayarma ta yanke. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga rige-rigen sakkoma Yaya Musaddiq. Dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar ƙanwarsa. Mansoor ma dai idonsa cike yake da ƙwalla, cikin ƙarfin hali ya buɗe motar ya fita. A ɗan zabure Musaddiq ya figi wayarsa dai-dai sanda Mansoor ke fita a motar, dan tunawa da ya dace ma su kira d.c.o fa. Kiran nasa kuwa yayi, sai dai ba'a ɗagaba. Cikin tashi hankali ya cigaba da kira. Har 3 miscall, fita yay da sauri a mota. A jikin motar ya samu Mansoor jingine idonsa a lumshe. Cikin sauri-sauri yake faɗin, “Na kira d.c.o amma bai ɗagaba. Inaga ya kamata mu ƙarasa police station ɗin mu sanar masa”. Shima ɗan zaburar Mansoor yay, cikin alamar gamsuwa da zaburowa ya nufi motar yana faɗin, “Hakane yaya, wlhy ni kaina ma ya tushe na rasa mizan yi, amma bara na kira Yaya Attahir ya nemesa tunda abokinsa ne”.
Musaddiq ya gamsu da hakan, cikin ƙanƙanin lokaci Mansoor ya sanarma yayansa halin da ake ciki, kafin suma su ɗauki hanyar zuwa police station ɗin. Sosai Mansoor ke gudu, hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka iso station ɗin. Sun samu d.c.o baya nan ya fita sai dai Yaya Attahir ya kira Mansoor ya sanar masa yay magana da d.c.o ɗin ta waya, gashi nan zuwa ma su jirashi. Dole sukai zaman jiran dawowarsa duk a ƙage. Sai bayan kusan mintina sha biyar kuwa sai gashi ya dawo. Ganin yanda suke hankali a tashe ya buƙaci fara ganinsu. Suna gaya masa kamar yanda Attahir ya sanar masa tun a waya, shiyyasa ma ya katse abinda yake acan ya taho, ya amshi wayar Musaddiq tare da kiran yaronsa yace ya kwashe number ɗin yanzun nan ai masa tracing. Amsa yaron nasa yay ya kwashe number ɗin ya fita da hanzarinsa.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_
......A matuƙar hanzarce cikin tashin hankali yake bin umarnin ogan nasa. Ita daya shaƙama abu ya fara kinkima ya kai mota. Ya sake dawowa ya tattara duk abinda ya shafeta ya fita da su suma. Hatta kayan data jiƙa domin wankewa bai bari ba. Bedsheet da komai ya tattare katifa kawai ya bari a ɗakin. Cikin abinda bai wuce minti goma ba ya bar gidan da ita da komai nata. Cikin uban gudu ya nufi hanyar inda ogan nasa ya sashi maidata. Yayi nisa a tafiyarsa saƙo ya shigo masa. Sanin wayar da mutum ɗaya take da alaƙa ya sashi taka birki da sauri ya ɗan gangara gefen hanya. Titine da bai cika yawan kai kawon motoci ba saboda sabuwar anguwace sosai kuma a gefen gari ne ma. Idanu ya waro matuƙa sakamakon ganin saƙon da ogan nasa ya turo masa, tare da sauri ɓalle murfin wayar kasancewar ƙarama ce dama ya cire batteryn shima ya zare layin. Karyashi yay huɗu yay cilli da shi yana mai kwanciya akan steering ɗin da sauke nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yayi kusa minti biyu a haka sannan ya ɗago. Samraah dake kwance a baya tamkar gunkiya ya kalla, cikin cije baki ya ɗauke kansa. Motar yay ƙoƙarin sake tadawa akai knocking glass. Da wani irin bala'in sauri ya kalla gefen nasa, dan motar tinted glass ne da ita shiyyasa. Yasan wanda yake ta wajen bai ganinsa, amma shi yana ganinsa. Ganin kamar babu wani alamun kasancewar sa jami'in tsaro ya sashi sauke gilashin a hankali. Matashin saurayi da bai wuce sa'ansa ba ya ɗan sake duƙowa da faɗin, “Barka oga. Badai wata matsala bace ba ko?”.
Murmushi yay shima cikin sauri ya ce, “Barkanmu. A'a babu komai na ɗan tsaya amsa kiran waya ne kawai. Nama gama yanzu zan wuce”.
“A to masha ALLAH, dama ina tunanin ko akwai matsala ne. ALLAH ya tsare hanya”.
Godiya ya masa yana ƙoƙarin maida gilashin kawai yaga an buɗe murfin gefensa an shigo. Da sauri ya juyo nan ɗin. Mutum ne garjejen gaske gashi cikin baƙaƙen kaya kamar shi. Sai dai wannan yasan ko'a mafarki sukai wasan kokawa ɗagashi zai dingayi yana nanawa da ƙasa. Amma cikin dauriya ya ce, “Malam lafiya kuwa?”.
“Itace ta kawo haka”.
Mutumin ya faɗa a gadarance. Sai kuma ya sa hannu ya zare key ɗin motar yana faɗin, “Fita ka koma baya”.
“Na koma baya kamar ya? Ni da motata ka shigo min babu wani neman excuse kace kuma na fita na koma baya. To kai a wa kuma?”.
Uffan mutumin baice da shi ba. Sai ma ɗora masa bindigar daya zaro a jikinsa yay a saman cikinsa. Da sauri saurayin ya kalla bindigar, cikin son ɓoye tashin hankalinsa amma yana ta son bayyana kansa ya ce, “Malam miye kuma na bindiga anan?”.
Shi dai bai tanka masa ba. Sai ma ƙoƙarin saƙala yatsarsa yake akan kunamar bindiga ɗin, shima sai kawai ya buɗe motar ya fita zuciyarsa na wata irin bugawa da sauri. Turus yayi jikinsa na tsuma ganin zuƙa-zuƙan motoci har biyu baƙaƙe wulik, ga Samraah ana ƙoƙarin sakawa a ɗaya. Sai garadan maza har uku irin wanda ya titsiyesa a mota tsaitsaye da bindigu suma. Yana ji yana gani haka ya shiga bayan motar dan dolensa, saboda babu makami ko ɗaya a tare da shi. Kodama akwai ai sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Sannan waɗan nan kam sunfi ƙarfinsa, dan yama riga ya sadaƙar kawai jami'an tsaro ne su ɗin.
Shima abu suka shaƙa masa, a take ya sulale sai barci. Daga haka bai sake sanin a wace duniya yake ba sai farkawa yay ya gansa a inda bai taɓa sani ba. Dan ɗaki guda shima aka ajiyesa shi kaɗai. A yanzu kam hankalinsa ya fara tashi ƙololuwa. Dan ya fahimci ba ƴan sanda bane ba. To ko ogan nasa ne yasa akai masa haka? Amma mizaisa yay hakan kuma?. (Ka nema ɓata masa aiki mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya ayyana masa. Kansa ya dafe da ƙyar, dan gaba ɗaya jikinsa yay masa nauyi. Jin kamar jiri na ɗibarsa ya ɗan zame ya sake kwanciya yana mai lumshe idanunsa...
(✿(✿(✿)(✿)✿)✿)
A ɓangaren su Yaya Musaddiq kam anyi traicing number da Samraah tai kiransa an kuma gano inda suke. A take babu ɓata lokaci d.c.o ya shirya mutanensa. Duk yanda yaso su Mansoor su zauna sun dage da roƙon son binsu, ya fahimci koda ya hanasu zasu iya binsu a baya, hakan kuma akwai haɗari dan haka ya haƙura aka fita har dasu. Sunyi tafiya baifi ta mintuna uku ba layin ya yanke. Da sauri yaron d.c.o ya sanar masa.
“Oga akwai matsala fa. Da alama sun farga damu dan layin ya daina aiki. Hakan na nufin an ciresa a wayane, dan da yana kan wayar ko kasheta sukai zamu same su”.
Shima hankalin d.c.o ya tashi, amma sai ya dake shi cikin bada umarni ya ce, “Ku ƙarasa har inda layin ya dakata da aiki”.
“Okay sir”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Su Mansoor basu san halin da ake ciki ba. Dan suna a ɗayar motar ne. Gashi kuma an cigaba da tafiya kamar yanda aka faro. Cikin abinda bai gaza mintuna talatin da biyu ba suka iso dai-dai wajen, dan gefen gari ne sosai. Sun sami mota kaɗai, amma babu alamar mutum. A take duk suka fito, sauran da basu san mike faruwa ba duk sun zagaye mota da bindiga. Wanda dai yake kamar ogan tafiyar ne ya sake kiran d.c.o ya sanar masa cewar gafa mota sun samu, sai dai basu sani ba koda mutum a ciki ko babu. Nan ma umarnin bincikawa ya basu, dan haka suka fara aikinsu, sai dai an hana Mansoor da Musaddiq zuwa kusa da motar duk da yanda suke a zalame.
Cikin kulawa da ƙwarewar aiki aka buɗe motar, sai dai me babu kowa a ciki sai kayan Samraah harda jiƙaƙƙun nan na botiki, sun cigaba da bincike motar tako ina, har suka samu nasarar ganin layin wayar a gefen titin an karyasa. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga kwaranyoma Musaddiq, hakama Mansoor ya duƙar da kansa jikin motar ƴan sandan kawai da alama shima dai kukan yake yi. Dan ba sai an faɗa musu ba komai ya tabbatar musu da mutanen nan sun sake samun nasarar tserewa da Samraah kuma.
Komai an tattara har motar aka wuce da su station. Wasu a cikin ƴan sandan kuma suka watsu a wajen ta cikin jejin har ma da cikin ƙauye dake ata wajen bisa umarnin d.c.o. Dan yana zargin wanda suka ɗauke tan ko dai sun shiga jejin, ko kuma sun shiga cikin ƙauyen domin tsira tunda har aka samu motarsu anan. Sauran ƴan sandan da suka wuce station nata ƙoƙarin kwantarma da su Musaddiq hankali. Dan a take sun nema bayanai daga companyn layin wayar da Samraah tai kiran Musaddiq. Za'a binciki dukan abinda akai da layin a kwanakin da suka gabata. Kai tunma daga randa aka sayesa. D.c.o ya tabbatar musu da in sha ALLAHU za'a dace tanan. Badan dai sun gamsu ba suka haƙura suka tafi, dan bayanan sai zuwa gobe za'a samesu...
(✿(✿(✿)✿)✿)
Tunda na farka daga nannauyan barcin dana kasa tuna lokacin farawarsa rufin ɗakin da nake kwance kawai nake iya kallo. Rufine dake tabbatar da ba'a ƙaramin gida nake ba. Dan yanayinsa da fentin bangon ɗakin kawai ya isa ya tabbatar da haka. Na jima a hakan kafin na motsa da ƙyar. Saman gado nake, tabbas hakan ne, na ayyana a raina cikin tabbatarwa da kaina. Komawa nai na sake kwantawa batare dana ƙarasa tashin ba. A take komai ya shiga dawo min dalla-dalla. Na zare wayar wanda ke gadina na kira Yaya Musaddiq, bayan ya ƙwace ya shaƙa min abu, daga haka ban sake sanin komai ba. Kenan dai ɗakkoni yay daga can gidan ya maidoni nan saboda gudun tonan asirinsa. Hakan na nufin babu rana balle watan komawa ga zuri'ata. A hankali wasu hawaye suka shiga silalo min masu zafi. Yau saura kwanaki takwas aurena, na tabbata duk hankalin wani masoyina ba'a kwance yake ba zuwa yanzu. Musamman Yaya Musaddiq, Mansoor, Hafizzullah... Wani murɗawa da marata tai ya katse min dukan tunani na. Faɗuwa gabana yay, Dan kuwa lallai lokacin prioud ɗina ne. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Aiko akwai matsala, idan na kasance a wannan halin anan waye zai kula dani? Dan ba ƙaramar wahala nake sha ba har sai an mun allura, wani lokacin ma ai allurar taƙi sauka. Shiyyasa har shan magani nake a ɓoye dan kar jinin yazo. Abinka daba uwa ba balle ta gani ta kwaɓa, sai babu wanda yasan ina hakan har yanzu, kuma na jima inayin hakan, dan ko yanzu kusan watana na biyar kenan banyi ba saboda bana wasa da maganin a duk sanda nasan kwanakin period ɗina sun gabato, yanzu ma da ace akwai shan kawai zanyi shike nan bazai zo ɗin ba. Jin yaɗan lafa min na sake buɗe idanuna tare da yunƙurawa da ƙyar na tashi zaune. Ɗakine babba, sai dai babu komai a cikinsa sai iya katifar da nake kai, ashe ba gado bane, irin ƙatuwar katifar nan ce irin wadda ba'a sakawa a gado. A hankali na miƙe da ƙyar, windows ɗin ɗakin nabi na lalleƙa, sai dai bana iya gane komai sai dai ina iya jiyo magana mutane ƙasa-ƙasa. Hakan yasa na nufi inda nake ƙyautata zaton ƙoface. Bugawa na shigayi babu ji babu gani ina kuka. Sosai nake ma ƙofar bugun hauka da nasan dolene ya damesu. Amma ƴan iskan nan kamar kurame, ga wani irin murɗi da marata kemun na azaba, tun ina ƙarfin hali har na sulale ƙasa jikin ƙofar na zube. Tuni nayi sharkaf da zufa na azaba, ga jikina dake rawa, sai kuma uban kuka da nake ina kiran sunan ALLAH da fatan Yaya Musaddiq ya zo ya ɗaukan.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_
.......Dukkanin bayanan da d.c.o ya buƙata an kawo daga companyn layin wayar mutumin. Dan haka yay zaman dubawa daki-daki. Sabon layi ne, an kuma buɗesa wata ɗaya daya gabata. Sai dai ba'a taɓa waya da kowa da shi ba sai number Yaya Musaddiq da Samraah ta kira. Sai kuma number ɗaya jal da sakwanni kawai aka dinga tura masa da ita. Dukannin sakwanin kuma a gajarce ne. Babu kuma wata ma'anar da za'a fahimcesu sai su da suka yi abinsu. A yanda kuma sakwannin suke kamar babu sanayya tsakanin wanda ke amfani da layin da mai tura saƙon da alamu suka tabbatar shine ya saka akai kidnapping Samraah ɗin. Abin ya tsayama d.c.o a zuciya. Amma dai ya sake bada number da ake tura saƙon