Showing 282001 words to 285000 words out of 438336 words

Chapter 95 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2226

nayi na sha kaɗan na ajiye. Sai da na ɗan samu nutsuwa kafin Malam ya cigaba da faɗin, “Samraah kinyi ƙoƙarin, ALLAH ya saka miki da alkairinsa. Mijinki yana min duk bayani akan kula da mahaifiyarsa. Tare da cigaban da ake samu yanzu sosai. Waɗan nan halayyar sune halayen mace ta gari. Sune irin halayen da kowane namiji zai so samu ga matarsa koda kuwa akwai wani special abu da yafi so ga mace. Ki cigaba da yanda kika fara kar ki canja kinji. Kema in sha ALLAHU ALLAH zai kula dake. Ba kuma zai taɓa taɓar dake a ƙarƙashin ƙafafuwan ƙasƙantattu ba masu bijirema gaskiya”.
“In sha ALLAHU Abba Nagode sosai. ALLAH ya ƙara rahama da jin ƙai a gareka.”.
“Amin ya rabbi ɗiyata, tare dake da zuri'armu baki ɗaya. Akwai magunguna da nazo da shi da ruwan addu'a duk suna a motarku. Idan kun koma gida sai a cigaba da yimata amfani da su. Hatta kuma zaku iya sha da amfani da su ɗin ba komai bane, har a girki kina saka muku musamman ruwan addu'ar zaki iya abinci da shi. Sai kuma a ƙara dagewa da addu'a da sadaƙa. Kiyaye dokin ALLAH, kiyaye hakkokin mutane. Azkar, karatun Alkur'ani. In sha ALLAHU muna fatan nasara a wannan gaɓar. Sannan Bahijja ta sanar min dukkan abinda ya faru a ɗazun akan Fahad, shima kar ai wasa dan abinda ke jikinsa a yanzu yafi na ɗan uwansa ƙarfi sosai gaskiya, dolene zai fishi zafi da son ayima duk wacce za'ai. Jarabawa ce ALLAH ya bamu ikon cinye wa baki ɗaya”.
Sosai nayi mamakin jin sunan Bahijja a bakinsa. Amma dai na daure na amsa da “Amin ya rabbi. ALLAH ya tabbatar Abba. In sha ALLAHU shima komai zai tafi dai-dai”. Na faɗa fuskata cike da murmushi. Shima murmushin ya min tare da faɗin, “Kina mamakin nace Bahijja ko?”.
Kaina dake a ƙasa na jinjina ina murmushi. Shima sai ya sake murmusawa. Tare da nuna saurayin da suke tare da Hayatu. “Wancan yarona ne shima. Sunansa Hameed. Yayane ga Bahijja mamansu ɗaya. Mijinki shine ya kawo Bahijja gidan nan domin yimana wani aiki, kuma Alhamdullah ana cin nasara. Sai dai itama ban sanar mata ke ɗin matar Yayan nasu bace ba.”
Kasa daurewa nayi sai da na ɗago na kalla Maash da hankalinsa gaba ɗaya ke a kan wayarsa yana daƙila. Mamakin duniya ya kasheni, amma sai bance komai ba na sake maida hankalina kan malam da fuskarsa ke a ƙawance da Murmushi. Ya ce, “Karki damu, a hankali zaki fahimci komai. Dan gidan nan naku sai mijin naki ne ya iya musu ai. ALLAH dai ya shiryar camu”.
“Amin” na amsa masa a hankali, ina sake mamakin mutumin nan. Tabbas na yarda shi ɗin yafi Aljani taƙadaranci kamar yanda Hayatu ya taɓa faɗa min...

Daga haka suka cigaba da tattaunawa da Maash, a tattaunawar tasu ne na fahimci shima Hameed ɗin an kawosa ne yin wani aiki a asibitin da Hajiya ƙarama ke aiki. Abin ya bani mamaki, sai dai ban iya saka musu baki ba tunda zancensu ne. Amma wai abu dana taɓa ji a asibitin nan sanda nake jiyya sai Sosai wannan zama ya jamu lokaci mai tsayi, dan sallar Azhar ce ta tashemu........✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5


......Malam shine ya ja musu sallar azhar a cikin jirgin. Maash da malam ɗin sun sake sabon zama da ga shi sai malam ɗin daya jasu har zuwa la'asar, kai da kaga zaman zaka san abu mai muhimmanci suke tattaunawa, nan ma ya jagorancesu sallar la'asar sannan suka tafi. Ni lokacin ma ina ɗaki kwance ya kirani mukai sallama. Bayan tafiyarsu na zata muma zamu wuce sai naga wasa farin girki. Dan kuwa zama daram mai naƙuda ta samu katifa. Haka ina ji ina gani muka sake kwana a cikin jirgin nan dake ta faman shawagi kawai a cikin ruwa. Daren ranar ɗin ma dai bai ƙyaleni ba nasha jagwalgwala har sai da nayi laushi a hannunsa. Kai jama'a mutum ina ma prioud ɗin ban tsira ba. Kamar yanda ya faɗa kuwa washe garin cikarmu kwana biyun gabanin magrib muka bar cikin jirgin. Sai kuma naji du kamar kar mu wuce. Dan rayuwa a cikin jirgin nan rayuwace mai tsayawa a zuciya da bazamu taɓa mantawa da ita ba da ga ni har shi. Ga wata shaƙuwa ta musamman data shiga tsakanina da shi. Duk da kuwa yana nan da halinsa da kuka sani na rashin son magana babu abinda ya canja. Wani lokacin ma idan na gaji da shirun nasa sai na ɗauka wayarsa naita game abina. Dan zuwa nai na dinga ɗakkosu a play store iri-iri. Wani lokacin ma ina a jikinsa zanta abina yana kallona. Kokuma yana aikinsa a computer ni kuma ina game ɗina ko kallon films tunda ga datan banza. Yo ta banza mana tunda shi koyaushe data ɗinsa a buɗe yake.
A motar da mukazo dai muka koma. Sai dai maimakon gida ma wani wajen yay dani. Ganin ƙaton companyn da muka zo ya sani tambayarsa ina ne nan. Bai bani amsa ba sai da ya gama shan ƙamshinsa ya ce, “Na Ummie ne. Shine ta fara ginawa”.
“Woow Masha ALLAH”. Na faɗa tare da cigaba da yaba haɗuwar companyn da girmansa. Har ciki muka shiga a office ɗin dana fahimci nashi ne. Dan babu kowa sai masu gadi a ciki da waje. Kujera ya nuna min shi kuma ya shiga bayi, koda ya fito ficewa yay da alama zaije massalaci. Ina jin ya kulleni ta baya. Ban damu ba na miƙe ina bin hotunan saman desk ɗinsa da kallo. Kusan biyar duk shi da Ummie ne da Paah da wani da aka rufema fuska da wani emoji kwalliya. Mamaki ya kamani na ɗan kware ɗaya sai naga fuskar Fahad. Murmushi kawai nayi tare da jin tausayinsu. Dan masifa ma ace a hoto ma basa son ganin juna. Duk inda fuskar Fahad take ya rufeta. Da ga shi sai Paah da Ummie sai wani ƙyaƙyƙyawan baturen dattijo dake tsananin kammani da Ummie da shi kansa Maash ɗin daya ɗan ɗebe wasu abubuwan da ƙyaƙyƙyawar mace baka. Tabbas wannan shine Ibrahim (Alonso) kenan, ita kuma macen Rabi'ah. A take naji ƙaunar dattijon ya shiga raina yayinda na shagala a kallon Rabi'ah, wlhy ji nake kamar na san fuskar nan. Addu'ar samun rahama na musu tare da mahaifina sannan na maida hotunan a yanda suke na koma na zauna inata son tuno a inda na san fuskar Mama Rabi'ah. Zamana baifi minti biyu ba ya dawo. Zama yay tare da ɗaukar wayarsa dake vibration tun ɗazun ya kai kunne.
“Office”.
Kawai ya faɗa yana mai yanke wayar. Ɗan juyowa yay ya kallan, sai kuma ya ɗauke kansa tare da nuna min wani ƙofa ya ce, “Jeki ciki”.
Kamar zanyi magana sai kuma na fasa. Mikewa nai na nufi inda ya nuna ɗin, a cikin raina ina mitar ALLAH ko'a jikin ƙofa ne sai na maƙe naga wanda zai shigo. Ai ko hakan nayi, ina maƙe a jikin ƙofar ina kallo da ido ɗaya ta ɗan wajen nan mai kamar camara. Saurayine matashi ya shigo, sai dai fuskarsa kusan a rufe take da hirami, sai gilashi daya rufe idanunsa tas ba'a iya ganin komai. Idan ka gansa saika ɗauka baida gaskiya. Cike da girmamawa ya rissina ya gaishesa. Ina kallo ya amsa masa da alamun jinjina kai. Sai kuma ya nuna masa kujera. Zama yayi, tare da yaye hiramin ya cire gilashin. Ban sanshi ba, bamma taɓa ganinsa ba. Oho su suka sani wannan kuma. Ganin bazan iya jin abinda zasu faɗa ba na ɗan buɗe ƙofar kaɗan. Dai-dai nan ko saurayin ya miƙa masa wani abu kamar yana faɗin,
“Alhamdullahi Sir, naci nasarar ganin fuskar ɗaya daga cikin masu zuwa gidan da ɓoyayyar fuska. Sai kuma ita Hajiya Nafisa kwana biyun nan tana yawan zuwa gidan gaskiya. Guy ɗin nan mai suna Commondo da muka bibiya kwanaki shima kwana biyu nan yana zuwa akai-akai gidan. Sauran baƙin kuma da suka ɗan zazzo duk akwai sunayensu da fuskokinsu anan zaka gani. A jiya tattaunawasu da commondo ya bada damar a bibiyar masa brothers ɗin wata yarinya da suke zargin tana anan cikin Mansion ɗinka kamar mai something suna Samraah. Wadda naji Hajiya Nafisa ma tazo da batunta. Sai ita mai ɓoyayyar fuska data bayyana itama tazo da batunta. Kamar dai itace ya bada umarnin a kashe a asibiti ranar.”
Shiru Maash ɗin bai ce komai ba. Har kusan mintuna biyar kafin ya buɗe baki da ƙyar ya furta, “Ya akai ka fito kai yanzu?”.
“Baya gida tun around 11am ya fita. Amma dai akwai abinda yake ƙullawa gaskiya, sai dai bai faɗi komai ba akan shirin dan an sanar masa kun fita a gida tun shekaran jiya, lokacin suna tare da ita matar nan yace zai yi wani abu amma itama yaƙi sanar mata, amma a randa kuka fitan aka sanar masa. Jiya ma bai yini a gidan ba, yau ma gashi kusan hakan”.
“Kai mi kake tunanin yana shiryawa?”. Ya faɗa a daƙile.
“Eh gaskiya bazan ce ba kai tsaye. Amma dai ina hasashen koma minene tabbas zai iya shafarka. Dan haka ma na saka abu a jikin driver ɗinsa. Idan har an dace bai farga ba ya cire to zamu iya ganin wani abu koda ba duka ba ta nan. Sai dai gaskiya Sir ya kamata ka ƙara ninka tsaro a mansion. Dan shirin nan na musamman ne kuma daɗaɗɗen shiri kamar yanda Jaga ya faɗa. Sannan har yanzu kowa ba abin yarda bane a gidan nan. Ita kanta yarinyar da suke magana na fahimci a al'amarin nata akwai lauje cikin naɗi, musamman yanda naga al'amarinta na ɗaga musu hankali matuƙa, dan a nasu bincike sun gane tana da aure, amma sun gagara binciko ainahin mijin nata. Shiyyasa nake ga muma kamar ya kamata mu binciko ita ɗin wacece kafin su su binciko”.
“No wannan ba aikinka bane. Yanzu abinda nake so da kai shine. Ka tabbatar Hameed ya samu karɓuwa a wajensa hundred percent ta yanda samun aiki a asibitin bazai masa wahala ba. Akwai yarinya mai suna...” ya ɗan yi shiru alamar tunani. “Oh na manta. Ka kira Bahijja zata faɗa maka. Ina son kama oganka bayani ya kamata daga nan zuwa sati biyu. Kaima bazan sake ganinka ba sai nan da four to five weeks haka. Dan zan yi tafiya gobe in sha ALLAH”.
“Ba komai Sir, ALLAH ya kaimu. In sha ALLAHU kuma komai zai cigaba da tafiya fiye da yanda muke fata. Zan kuma sanarma oga saƙonka in sha ALLAHU. Komai da kake buƙata zaka gansa a flash ɗin nan ga kuma bayanai a file ɗin shima oga na bashi copy ɗin komai”.
Hannu naga ya bashi, sukai musabaha wancan ɗin ya fice. Kasa motsawa nayi a wajen. Dan tunda suka fara magana komai ke mun kai-kawo a zuciya..
“Idan kin gama laɓen ki fito”.
A bazata matuƙar bazata na ji saukar furucinsa tsakiyar kaina. Sosai na waro idanu waje. Tare da dafe ƙirji na kallesa. Yana zaune a yanda yake. (Kambu, yaya akai ya san ina laɓen? Ka jimun aljani) na ayyana a zuciyata. A zahiri kam sai na tunzura baki ina danne kunyar da naji na fito. Hankalinsa na akan file ɗin da aka kawo masa, dan haka na ɗan hararesa da murguɗa baki kaɗan. Har zan zauna gefe sai wata zuciyar ta ƙwaɓeni zama kusa da shi kodan naga mike a file ɗin. Sai dai me, ina zaman naci karo da hoton Hajiya ƙarama da shima ya ƙurama ido...
“What!?”.
Na faɗa cikin tsananin mamaki ina mai kai hannu na amshi hoton. Bai motsa ba, bai kuma ce dani komai ba. Sai da na ƙarema hoton kallo ciki da bayansa na sake tabbatar dai da ita ɗin ake maganar sannan na kallesa. Sosai naga jijiyoyin kansa sun wani irin tashi, yanayinda gaba ɗaya ya sauya. File ɗin na zame gaba ɗaya daga jikinsa nima nawa jikin na rawa na shiga dubawa daki-daki.
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”. Na faɗa wani irin abu mai nauyi namun kai-kawo. “Tabbas biri yayi kama da mutum. Dama matar nan tana a cikin suspect ɗina a gidan, ashe kuwa. Amma Yaya abinda ban gane ba wane Baba prof ake magana? Wlhy kaina ya kulle gaba ɗaya, zuciyata bugawa take da ƙarfi”.
Shiru bashi da niyyar motsawa tsahon lokaci. Sai kuma ya ɗago a hankali ya kalleni. Sake firgita nayi zuciyar tawa na ƙara ƙarfin gudu da ganin idanunsa da sukai wani kalar masifar juyewa. Gaba ɗaya sun koma golden kai kace irin gawurtattun zakunan nan ne da suka addabi jeji tako wacce kusurwa. Ga wani irin tsananin fusata dake nuna ainahin stubborn Maash ɗin nan da bai san komai bace rashin mutunci. Rawar jikina ƙaruwa tayi, na shiga girgiza masa kaina hawaye na cika min ido. “Please Yaya ka daina kallona idanunka tsoro nake ji”. Shaaa hawayen da nake maƙalewar suka zubo. A hankali yay wani luuu da idanun, sai kuma ya miƙe murya a matuƙar shaƙe ya ce, “Les't go”.
Kasa tashin nayi dan har sai da yaje ƙofa kafin na miƙe jikina na rawa ina sharar hawaye. Har muka isa motar ma kukan nake, gaba ɗaya komai ya ƙwace mun. Sam bana son yarda Baba prof ɗin su ake nufi ya ce a kasheni. Idan fa har shine shima akwai lauje cikin naɗi a tattare da al'amarinsa kenan. Kai mun shiga uku wannan duniya to waya kamata mu YARDA da shi?. Waye zamu YARDA MASOYINMU ne na gaskiya? Wai kenan da gaske anzo zamanin da zakama mutun ALKAIRI ya maida maka da SHARRI ke nan? Da gaske ne maganar malamin nan da yace wannan al'ummar na wannan gaɓar tamu sune MAFI SHARRIN AL'UMMA?. Mu zauna mu auna mana. Wlhy da wahala, matuƙar wahala a yanzu ka ƙyautatama mutum biyar ka samu ɗaya ƙwaƙwƙwara za dai maido maka da ALKAIRI. Mai ɗan sauƙi a ciki ne sanda ka masa zai nuna jin daɗin yimasan da kayi zuwa anjima ya manta. Wani ma kana bashi, bakinsa a washe a gabanka yana matsawa ya zageka da nuna ai dole ma kayi masan. Haba mutane why! Why! Why! Mukafi buƙatar yima WUTA tanadin kammu tun a duniya saɓanin ALJANNA. Why muka fi yarda da rayuwa da ruɓaɓɓiyar ZUCIYA saɓanin tsarkakakkiya?. Ni gaba ɗaya ma zuciyata ta cure waje ɗaya........✍️


_To adai ji tsoron ALLAH kar a samu naman salla a manta dani🥱_.


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


*_Masha ALLAH, Barkanmu da salla. ALLAH ya maimaita mana da rai da lafiya. Mahajjata ALLAH ya karɓi abadu da mu da mukai tamu anan 😀. ALLAH yasa muma baɗi iyanzu muna can. Har yanzu dai banga naman salla ya fara sauka ba. A dingayi ana rage rowa fa🌚🌚._*



.......Ganin uban gudun da yake damu da magribar ALLAH ya sani sassauta kukana na share hawayena. Matsowa nayi a hankali ta jikinsa na dafa hannunsa dake a saman steering. Cikin shaƙewar muryar da nake ƙoƙarin controlling na ce, “Please yaya kayi haƙuri. Ban san ainahin mi kake bincike ba, amma ina ji a raina yana da alaƙa da Ummie tunda naga maganar Fahad ya shigo ciki. Dan ALLAH kayi haƙuri zuciyarka ta sauka karka shiga gida da wannan fuskar, yaƙin sunƙuru ai suƙunrun ake masa. Sannan kaike na koya min dabarun zama da maƙiyi”
Na ƙare maganar da kwantowa jikinsa na lumshe ido. A hankali ya fara sassauta gudun kuwa, jin mun tsaya yasa na buɗe idanuna. A hankali na ɗago na kallesa sai kuma na kalla inda muke. Gefen titi ne kawai, nima sai na sauke ajiyar zuciyar. Goran ruwan dake saman cinyata wadda ɗaya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login