Showing 147001 words to 150000 words out of 438336 words

Chapter 50 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2261

saka hannu...

Ina fita na saki murmushin farin ciki. Yau dai na samu wayar yin magana da ƴan uwana. Duk da ko a da da nayi niyya zanyi hakan dan su Bahijja duk akwai waya a hannunsu. Abinda yasa ban taɓa ara ba saboda bana buƙatar kowa yasan sirrina. Farin cikin waya ya mantar dani wani batun aikin Hajiya Mammah. Dan amaimakon kitchen daya kamata na koma ficewata nayi daga sashen baki ɗaya ko su Azizat dake zaune acan rukunin ƙarshe na kujeru bana tunanin sun ma ganni. Ban nufi sashen mu ba na wuce garden ɗin gidan. Tsabar wuce wuri kuma maimakon babban garden sai na shige ƙaramin da akace nasa dan na samesa a buɗe da'alama aikin gyarashi akayi saboda kayan aiki dana gani an tule. Can na shige kusan ƙarshe duk dan dai na samu wajen ɓuya nai wayar a tsanake. Kaina tsaye na sake danna kiran layin Yaya Musaddiq. Sai dai harta katse bai ɗaga ba sai da na sake kira na biyu. Hayaniyar da naji ya sani faɗin, “Yaya ya nake jin hayaniya ko kana kasuwa ne?”.
Maimakon amsa ƴar dariya yayi da cewa, “Har kin gama darun?”.
“Kai Yaya ni har wani daru ne da ni?”.
“Sosai kuwa Kandalata. Ai ke naki ma na musamman ne.”
Karon farko na saki dariya, sai kuma na shiga gaishesa da girmamawa. Ya amsa min da kulawa tare da tambayar lafiyata da kuma jiyyar da nayi. Na amsa masa da Alhamdullah, tare da tambayarsa mi ake a gidan naji hayaniya. Kansa tsaye ya ce, “Mamarki akema kishiya”.
Da mamaki nace, “Mamata kuma Yaya? Wa kenan?”.
“Mom mana. Abba ne ya ƙara aure”.
Tuni na miƙe daga zaunen da nake dan mamaki, sai kuma na shiga ƙyalƙyala dariya. “Wai dan ALLAH yaya da gaske kake ko wasa? Mom fa akaima kishiya? Ta yaya Abba ya samu wannan ƙwarin gwiwar haka? A ina kuma ya samo matar?”.
Tsaf Yaya Musaddiq ya kwashe labari ya bani, tun daga zuwan Halime gidan har kawo yau da suke jiran isowar amarya batare da Mom ta sani ba. Tsabar farin ciki bamma san lokacin dana rangaɗa ghuɗa ba. Sai da Yaya yace min, “Ƙaniyarki kandala” sannan na bari ina dariya. Haka kawai nake jin raina fes da wannan al'amari. Dai-dai nan sautin muryar aunty Zakiyya data rangaɗa sallama ya ratsa kunnuwana. Bayan sun gama magana da Yaya Musaddiq yake cemata gani a waya. Amsa tayi cike da zumuɗi muka gaisa, kafin cikin raunin murya da lallashi ta ce, “Samraah shike nan kuma babu kira duk kinsa hankalinmu ya kasa kwanciya?”.
Murmushi nayi hawaye na cika min ido. Muryata na rawa na ce, “Aunty bani da waya ne. Kuma kuma kun sallamani ga wanda ban ko sani ba kamar bani da kowa a duniya”.
“Haba Samraah, shin bazamu iya haƙuri da karɓar ƙaddara ba a duk lokacin da tazo mana? A maimakon tada hankali a ganina godiya ya kamata muyima UBANGIJI dan a maimakon tozarcin da akaso ganinmu a ciki alkairi ne ke lulluɓe da mutuncin mu. Samraah kiyi haƙuri dan ALLAH, ki karɓa da hannu biyu sai ALLAH ya sauƙaƙa komai a yanda ba kowa yay zato ba. A kowace daƙiƙa ta rayuwa kuma kina ranmu. Kawai dan bamu san ta yanda zamu sameki bane ba”.
Babu daɗi kalamanta suke sake saka ni. Dan haka na sake raunana murya, “Aunty kina nufin maganar da wannan mutumin ya faɗa da Yaya gaskiya ce? Da shi aka ɗaura min aure, kuma aka kawo ni garesa? Shike nan kuma kun barmasa ni?”.
Ƴar dariya tayi, cikin wasa ta ce,.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚_

_________

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG



https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

_____________

........“Ya zamu bar masa ke. Sai dai ya ɗauki rabi ya bar mana rabi. Ke dai ki kwantar da hankalinki kinji. In sha ALLAHU ni da Musaddiq muna nan tafe har inda kike. Dama a tunaninmu idan kinji sauƙi zai dawo mana dake gida ne shiyyasa. To amma uzirin daya kawo akan zaman naku anan yanzu dole a haƙura har sanda ya kawoki da kansa ɗin. Ni dai kawai roƙona ki kwantar mana da hankalinki, ki mance da Mansoor kamar yanda mahaifiyarsa ta buƙata, ALLAH shine shaidar mu ba laifinmu bane sune sukaƙimu. Dan a ranar ɗaurin aurenku mahaifiyarsa da kanta tazo tace sun fasa ɗanta bazai aureki ba saboda ba'a san mi aka aikata miki ba da akai kidnapping ɗinki. Babu yanda su Kawu Musa basu lallasheta ba har gwaji sukace aje ai miki amma fir matar nan taƙi sai ma cin mutunci da gori data shiga musu. Suko sun san mutuncin kansu ai, dan haka suka janye suka bama wannan bawan ALLAHn ke dan su mutuntaki da mu kammu. Dan inba hakaba wannan mugun baƙin fentin da sukai miki zaita bibiyar rayuwarki ne harma mijin ya gagara gareki a gaba”.
Sosai maganganun aunty Zakiyya suka ratsa min jiki. Mamaki da al'ajabin mahaifiyar Mansoor ya tsaya min a zuciyata. Harna kasa daurewa na ce, “Amma Aunty shi yaya akai yasanni yazo neman aurena? Ko su kawun sun sanshi ne su?”.
“To ni dai bazance ba gaskiya. Amma dai kamar naji ance shine yazo yace yana son aurenkin da kansa. Ki dai tambayi Gwaggo tasan komai kuma nasan zata sanar miki. Ko kuma shi mijin naki ki tambayesa ai bazai ƙi sanar miki ba”.
Shiru nai tsahon lokaci na kasa cewa komai. Sai kuma can na ce, “Okay Aunty in sha ALLAHU zan tambayesa”.
Nasiha suma suka min cikin lallashi ita da Yaya Musaddiq. Bayan munyi sallama na jima zaune a garden ɗin ina tunani kafin na miƙe na koma sashenmu bayan na kashe wayar na sakata a jikina. Ina shiga Aunty Sadiy ta shigo wai naje Hajiya Mammah na kirana. Idanu na ɗan waro dan harga ALLAH nama manta da batunta...

A ɗarare na tafi amsa kiran nata, sai dai cikin sa'a ina zuwa na samu wai tana da baƙuwa sun ma fita yanzun nan. Ajiyar zuciya na sauke na juya na koma ina godema ALLAH. Dan dana sameta ban san mi zance ba wajen kare kaina.

✨★✨★✨

Da ƙyar aka samu Mom ta farfaɗo. Tana kuwa farfaɗowar wasan ya koma sabo. Dan tuni Ummanta da su Baby da basa gidan sun dawo harma da wasu ƴan uwanta. Faɗa ne mai ƙarfin gaske ya ɓarke tsakanin dangin Mom da ita kanta da dangin Abba. Dan dangin amarya su dai ƴan kallo suka zama. Sai dai kuma ransu ko ɗar balle gezau akan ƴarsu bazata iya zama ba. Sai ma murna suke da rahamar da UBANGIJI yay mata na samun wannan danƙareren gida a matsayin gidan aurenta. Itama ɗin dai Halimen ko'a kwalar rigarta. Yo ita wane kalar masifa da bala'i ne bata gani a wajen Innarta ba. Sannan faɗan kishi babu irin wanda ba'ayi a gidansu. Dan kaf matan kawunanta ba su ɗaɗɗaya bane Innace ma kawai ita kaɗai a wajen Baba. Amma sauran daga mai mata uku sai mai biyu harma da mai huɗu. Kuma haka ake shan cakwakiya a gidansu gashi gidan yawa. Ita dariya ma abinda ke faruwa ke bata. Sai da Hajiya Asabe ta ƙwaɓeta daga yanda take kwasar dariya tana leƙe ta window sannan ta nutsu.

Shi dai Abba ma tuni ya fita ya bar musu gidan bisa umarnin Gwaggo Gudidi. Haka aka ci uwar sabada mata anguwa nata shigowa. Masu yima Mom dariya da ALLAH ya ƙara sunfi yawa. Dan har a cikin ƙawayen nata wasu abin ya musu daɗi. Ummanta ce data fahimci al'amarin fa shiryayye ne dan dangin Abba sun kafa sun tsare yasa ta janye Mom ɗin suka shige ɗaki. Ba'a sake ganinta ba har kusan goma na dare sai ga likita wai yazo zai dubata hawan jininta ya tashi. Babu wanda yabi takan batun kowa ya cigaba da sabgarsa. Sai ita da ƴaƴanta da Ummanta ke ƙulle-ƙullensu can a sashenta su kaɗai.

Har washe gari daga ɓangaren Mom dai babu daɗi, gashi Abba yaƙi shiga inda take tun dubatan da yaje yay na farko bai sake zuwa ba, dan yana shiga ta sake birkicewa harda shaƙeshi tana kuka da faɗin sai ta kasheshi sai dai duk su rasa. Har ita zai tozarta yama kishiya, to wlhy ya sani ya ɗakko bala'i da masifar da bazata taɓa ƙarewa ba har sai cikin abu uku ɗaya ya faru. Kodai ta kashesa, ko kuma ya saki yarinyar a yau danginta su koma inda suka fito da ita, ko kuma idan ita ta mutu. Kuma koda ta mutu yace zai sake aure sai ta dinga masa fatalwa. Abin nata kamar wasa ya nema zama babba, dan da ƙyar aka fiddo Abba a ɗakin tana neman murɗe masa jikinsa ALLAH dai ya taƙaita masa wahala akwai babbar riga tare da shi.
Su dai ƴan uwansa da dangin amarya sabgar gabansu suke hankali kwance dan basu san mike faruwa a cikin ba sai da su Gwaggo Gudidi suka fito da Abba ne suke jin komai. Aiko fa kowa ya shiga ALLAH wadarai da wannan baƙin hali na Mom, daga nan kowa ya sake ɗaura ɗammara a kanta. Dan a ranar dangin amarya sukai walima tare da rabon kayan gararsu cikin bajinta da aka san katsinawa da ita a wajen rabo. Al'amarin ya ƙayatar da kowa a dangin Abban, sun kuma yaba da ƙoƙarin mutanen. Ana yin sallar azhar motocin da zasu maidasu gida suka kwashesu aka bar amarya Halime na kwasar kuka. Sai da su Aunty Zakiyya suka jata ɗaki suna lallashi. Daga ƙarshe ma dai su suka cigaba da zama da ita suna ɗebe mata kewa har washe gari da suma kowa yay haramar kama gabansa bayan sun kimtsa gidan. Har kuma sannan babu wanda yaga idon Mom. Sai dai duk sun fahimci akwai abinda suke ƙullawa ita da uwarta dan sai shigi da fici Ummar tata keyi a kwana biyun nan, saboda rashin sanin ciwon kai a gidan take kwana itama har a yau da bikin ya tashi. Ƴan Gwarzo ma sun rigata wucewa. Ganin bata ma da niyyar tafiya ne yasa Gwaggo Gudidi itama ta fasa tafiya a yau duk da dai dama wasu a dangin sun kawo shawarar Gwaggon ta ɗan zauna har gidan ya dai-daita gudun kar'a cutar da yarinyar mutane. Kowa kuma ya gamsu da shawarar dan haka Gwaggon tai zamanta. Sai hakan kuma yayima Abban daɗi shima. Dan dama yana tunanin ta yanda zai fita yabar Halime daga ita sai Mom ɗin a gidan har sai ya gama saita gidan...

💦💥💦💥💦

Kwanaki biyar kenan da faruwar dukan da naci a sashen Hajiya Babba. Alhamdullah jikina yayi sauki, dan hatta ciwon da taji min ma ya warke sarai sai tabo. Tun wannan ranar ban sake gigin komawa ba duk da hankalina na'a kanta. Haka shima uban gayyar ban sake ganinsa a gidan ba. Sai ma a bakin Mama Balki nake jin wai yayi tafiya ai tun a washe garin faruwar al'amarin da dare. Ranar da Hajiya Mammah ta aikani sashensa kai masa coffee kenan harna taho masa da waya. Bakina kawai na taɓe na cigaba da harkar gabana, dan damuwar data daman daban, duk da kuwa tana da alaƙa da shi. Sosai ina buƙatar zama dashi a wannan gaɓar, dan ina son jin yanda akai har ya je gidanmu ya nema aurena. Ai abin da mamaki, dan Mansoor mahaifiyarsa ta hanashi aurena shi kuma ace yaje ya auran bayan babu wata alaƙa data alaƙanta tsakanina da shi bayan ta kidnapping ɗina da yayi da hira da nai da shi a station ɗinmu...
Zuwa yanzu aikina ya koma sashen Hajiya Mammah, nice kullum mai mata gyaran sashenta safe da yamma. Da farko dai abinda na fara fahimta ga halayyar matar shine nuna isa da mulki. Na biyu shegen kallon raini na ƙurillar tsiya kamar zata cinyeka da idanu. Sai masifa komai kayi sai ta maka jaraba kamar itace ta halicceka. Shiyyasa idan na tashi kafin ma ta tashi a barci na gama gyara ko'ina nabar sashen, sai kamar 11 sai na koma na gyara mata bedroom lokacin ta fito. Yau ma kamar kullum da wuri na kammala aikin nawa, sai dai ina ƙoƙarin sauka dawn stairs na jiyo kamar sautin kuka na fitowa ta sashen Hajiya Babba. Tsamm nayi da raina kusan mintuna uku, jin dai da gaske tanan ɗin ne bamma san lokacin dana juya cikin sauri da sassarfa ba. Idanuna a rufe na faɗa sashen batare dana tuna da wahalar dana sha a hannunta kwana biyar da suka wuce ba. Ganin key a ƙofar ya sani murɗawa na afka ido rufe, jikina har rawa yake jin sautin kukanta da yanda take ambaton kiran sunan “Muhammad” dan zuwa yanzu na fahimci Maash kadai suke kira Muhammad a gidan ita da Paah. Zubewa nai a inda take zaune can karƙashin ƙafar bene ta cure jikinta waje guda fuskarta cikin ƙafafunta.
“Ummi miya sameki? Baki da lafiya?”. Na faɗa cikin rawar murya ina kamo hannayenta dake ɗauke da sayin ɗauri har yanzu amma duk ciwukan sun warke. A mamakina sai naga ta ɗago a hankali. Yanda idanunta suka kumbura sukai jaa sosai ya sake tayar min da hankali. Ga hawaye face-face da fuskar tata. Sai kawai nima na fashe da kuka tare da faɗawa a jikinta. Tsamm ta rungumeni itama tana ƙara fashewa da kukan da cigaba da magana cikin sambatu. “Muhammad ciwo, kaina ciwo zai fashe Muhammad. Ga jikina ƙaiƙayi yake min. Muhammad ina jin yunwa”.
Kuka na sake fashewa da shi ina mai ɗagowa a jikin nata. Amma sai ta hanani tashi ta sake matseni sosai. Duk da zafin da nake ji ban sake yinƙurin tashin ba. Tsahon mintuna biyar muna a haka har na fara numfashi da ƙyar. Sai kuma ta sakeni ta dafe kanta da riƙe cikinta. Zumbur na miƙe jikina na rawa, ga hawaye sun kasa tsaya min, “Kiyi haƙuri Ummie ki daina kuka dan ALLAH, yunwa kike ji ko?, Zakici abinci na kawo miki?”.
A mamakina kai ta ɗaga min tare da kamo hannuna ta ɗaura a saman cikinta hawaye na sharara ta shiga jujjuya min kanta. Ta ce, “Yunwa Muhammad yunwa”.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_


.......Da sauri na jinjina mata kai ina ƙoƙarin miƙewa. “To Ummie in sha ALLAHU yanzu zan kawo miki abinci bani ɗan lokaci ƙalilan.” ban jira amsawarta ba na tashi na fita a guje dan nasan bama amsawar zatai ba. A falonta na farko naci karo da wasu mata guda uku sabbin fuska daban sani ba a gidan. Nayi mamaki dan ɗazun ban gansu ba, ko kuma ban lura dasu bane oho. Takan kowa banbi ba a cikinsu nafice zuwa downstairs na afka kitchen, ganin an gama komai har an gyara kitchen ɗin ma fito dining, komai an shirya na breakfast, sai dai babu kowa a kai dan sai sun gama barcin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login