Showing 393001 words to 396000 words out of 438336 words
kuma muna biye da shi har cikin shagon.
Bayan ya mana bayanin kayan lefen Yaya Musaddiq da Fahad zamu haɗa da wasu kuma daban aunty Falaq ke tambayarsa “Wai Yayana fa? Tunda muka iso bamu ganshi ba”.
Cikin ɗan shafa kai ya ce, “Ai wlhy yama bar Dubai ɗin nan awa ɗaya data wuce. Amma dai zai dawo kafin mu wuce dan tare da shi zamu wuce Nigeria. Jinai hawayen da nake ƙoƙarin riƙewa sun zubo min, da sauri na kauda kaina gefe na share su. Komai ban ce musu akan batun nasa ba, suma kamar sun fahimci yanayina sai suka bar maganar muka fara abinda ya kawo mu. Yin komai nake zuciyata babu daɗi, yanzu na yarda da batun mutane da kance da zarar ka samu ciki mazan nan sun bar batunka, musamman masu kuɗin nan sunfi bama dukiyarsu muhimmanci fiye da matansu. Banda ma wulaƙanci irin na mutumin nan, ina cikin wannan halin ya raboni da ƙasata cikin gaggawa babu shiri, nazo kuma inda yake yana garin bawai baya nan ba, amma bai nema inda nake ba balle ya kira yaji yaya muka iso, bai kuma zo inda nake ba bayan ya gama uzirin da yake ya sake taka jirgi ma yabar ƙasar. Harga ALLAH na tsani wulaƙanci, ni mace ce mai son kulawa. Bawai dukiya da samun duk abinda nake so ne matsalata ba. Ina buƙatar tattali a koda yaushe da nuna damuwa ga abokin rayuwata, idan kuma abinda ya kamata na fahimta ne a fahimtar dani zanyi uziri. Munyi siyayya sosai, gajiyar da jikina ya nuna yasa Yaya Hayat yace mu bari haka sai gobe in ALLAH ya kaimu. Muna zuwa gida kobi takan abubuwan daya saya mana na ci banyi ba na wuce ɗaki na kwanta. Sai da aunty Falaq taga ban fito ba ta biyoni da shi. Ƙin motsawa nayi sai ta ɗauka barci nakeyi harda gyaramin blanket ta fita. Shigowarta biyu ina mata haka, daga ƙarshe dai ta haƙura ta kawo min duk abinda zan buƙata ta tafi itama ta kwanta. Har cikin dare sosai ina kallon waya da tunanin zai kirani ya bani haƙuri da faɗa min uzirinsa, amma shiru. Sai kawai na sanya kuka. Sai da nayi mai isata sannan na tashi zuwa bathroom nai wanka na fito, daurewa nayi naci abinda Aunty Falaq ta ajiye min dan yunwa nake ji sosai. Ina kammalawa na ɗauki wayar kamar zan kirashi wata zuciyar dai ta gargaɗeni na ajiye na kwanta. Sai kuma dai na ɗauka na kira shin har sau biyu ba'a ɗaga ba. Haushine ya sake ƙuleni na ajiye wayar..
Washe gari ma har mukai shirin sake fita babu kiransa. Na kai ƙololuwar shiga ɓacin rai musamman lokacin da muke tafiya a mota da naji Hayat na waya da shi. Wato nice mara amfani kenan. Shike nan zan nunama mutumin nan na haifu nima. A ranar muka gama sayyar duka. Yaya Musaddiq da Fahad set uku-uku na akwatina. Sai kuma set huɗu daban da bamu san kona waye ba. Sai muma muka ɗauki abinda muke so ko nace Aunty Falaq da Yaya Hayat suka zaɓa mana ni takaici yasa ma komai baya birgeni. Tun aranar sukam kayan aka wuce da su Nigeria. Mu kuma Yaya Hayat ya tafi damu yawo. Ni sam ba daɗin yawon nake ji ba. Nadai dake ne kawai ban nuna musu koda a fuska ba.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_Ina miƙa saƙon ta'aziyya ta ga ƴan uwa masoyan mu dake ƙoƙarin bibiyarmu ta rasa ƴar uwarmu da mukayi RAHAMA NALELE. Ya rabbi ka gafarta mata, ka yafe mata kurakuranta, kasa kabari ya zama wajen hutu a gareta, da iyayemu baki ɗaya. ALLAH ya raya abinda ta bari ka albarkaci rayuwarsu. Ka bama iyayenta da ƴan uwanta haƙurin rashinta da mu baki ɗaya. Ida tamu tazo muma ALLAH kasa mu cika da imani. Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, duk wanda yake ji a ransa ta taɓa masa ba daidai ba ko wani kuskure da ita bama tasan ta masan ba ko akan sani muna roƙonsa ya yafe mata. Ko sau ɗaya ne kuma a matsayinki na masoyiyar mu dan ALLAH ki mata addu'a a cikin sallarki, idan kin samu dama kiyi sadaka da fatan yaje gareta koda kaɗan ne 😭🙏. ALLAH ya gafarta mana baki ɗaya._
........Yau ɗin ma a gajiyen muka dawo, dan ni harda ma ɗan guntun zazzaɓi na. Shayi kawai nasha na tafi na kwanta na barsu anan falo. Haka na tashi har washe gari zazzaɓin na damuna. Ban gaya musu ba, sai aunty Falaq ce data ɗan fahimci kamar bana jin daɗin take tambayata. Murmushi kawai naɗan mata da bata amsa da, “Kawai dai yanayin ne Aunty”.
“Uhm yanayi, ko kuma Baby na ne dai? Ko Yayana ake kewa”.
Murmushi kawai nayi yanzun ma ina ƙoƙarin kai fruit ɗin da ta yanka min sukai ƙyau a cikin bowl baki na. Dai-dai nan Yaya Hayat yay sallama. Itace ta amsa idonta a ƙofa, ni kam a zuciya na amsa ina mai gyara zaman gyalen dana yafa saman kaina ya sakko min har kafaɗa. Bai shigo ba sai da tace, “Bismillah”.
Yana buɗe ƙofar ƙamshin turaren da ko'a barci nake najisa nasan na waye. Sai da zuciyata ta motsa. Amma na dake batare da na ɗago ba na cigaba da shan fruit ɗina. Yayinda Aunty Falaq ke masa sannu da zuwa da gaishesa. Amsa mata yay da kulawa, yana tambayar Awwab. Da girmamawa tace masa barci yake yi. Da ga haka ta miƙe ta nufi kitchen. Jin kaifin idanunsa a kaina yasa na kasa jurewa, kaɗan na ɗago sai na samu idon nasa ne kuwa a kaina. Yana sanye cikin wandon jeans navy blue da hi neck riga black data masa ƙyau sosai ta kuma kama masa jiki, sai black jacket ɗinsa a saman kafaɗarsa ya ratayeta da hannunsa. Cikin abinda bai fi sakan biyu na masa kallon ba a kaikaice ta yanda shi kansa bai zama lallai ya lura shi ɗin na kalla ba na maida kan Yaya Hayatu. Gaishesa nayi ya amsa min da kulawa yana tambayata gajiya nace Alhmdllh. A dai-dai nan Aunty Falaq ta fito da tray ta ajiye gabana, batare da tayi magana ba tabi bayan mijinta daya kama ƙarfen stairs zai haye. Tare suka haura, niko na cigaba da shan fruit ɗina kamar ban san da mutum a wajen ba, sai bayan kusan minti ɗaya da wucewarsu na ce, “Ina yini”.
A mamakina sai kawai naji an gittani an wuce batare da ya amsa ba. Ta gefen ido na bisa da kallo wani irin tuƙuƙi na riƙe maƙoshi na, ɗakin da nake kwana ya shige abinsa. Ƙofar na ɗan harara na cigaba da shan fruit ɗina. Sai dai me, gaba ɗaya kuma sai naji ya fita a raina. Dangwarar da bowl ɗin nayi na zame a kujerar na kwanta. Tun ina ƙirga mintuna zai fito harna koma lissafin rabin awa. Jinai zuciyata ta ƙara yin ƙunci, lallai mutumin nan ɗan wulaƙanci ne. Amma bari naga iya gudun ruwansa dai kafin na yanke masa hukunci. Minti talatin ta zama awa guda, sai ma barci ya kwasheni a wajen batare dana shirya ba....
Ransa a dagule ya dawo Dubai ɗin nan kamar yanda ya barta cikin ɓacin rai. Dan akwai kayansa daya kamata tun six days ago ace suna Nigeria kawai ake sanar masa wai an riƙesu a ƙasar Camaroon. Yayi iya ƙoƙarin sa ta hanyar waya dan ganin kayan sun isa saboda muhimmancinsu da mabuƙata kayan dake jira amma sai wani banza ke raina masa hankali. Gashi anan Dubai ɗin ma abu mai muhimmanci yake yi. Ga matarsa na hanyar tahowa. Duk da yaso ace da kansa yaje tararta hakan bai yiwu ba, dan yayi zaman meeting da wasu manyan ƴan kasuwa na duniya akan wasu matsaloli. Yana cikin meeting ɗin ya samu saƙo wai ana neman juyar da jirgin kayansa inda ya fito an hanashi ƙarasawa Nigeria. Dole yay excusing kansa daga wajen Meeting ɗin cikin abinda bai fi awa ɗaya ba yabar Dubai ya nufi Camaroon ɗin. Tunda yaje can bai huta ba, yanata faman kaiwa da komowa shi da lawyers nashi dan ƙulli ne babba ake neman masa da gwamnatin ƙasar. Sai a yau ya samu kansa kayan suka wuce Nigeria, ko tabbatar da tashin nasu baiyi ba ya fallo ya koma Dubai ɗin dan hankalinsa duk hana kanta. Shine ya iso da ɗokin ganinta amma ko ɗaga kai ta kallesa ma batai ba. Yaso mata uziri sai yaga kawai ta ɗago ta gaida Hayatu batare da shi ko ma kallonsa tayi ba. Wane kalar wulaƙanci ne hakan, matarsa, da ya ɗauka dukkan kansa ya bata da kowane irin matsayin girmamawa. Kai ina baya son raini kuma sam. Koda wani laifi ya mata ya kamata ta haɗiye a gaban koda Ummiensa ne sai sun keɓe ita da shi ta faɗa masa ko ta nuna fushin da shi, idan ba ban haƙuri ne zai bata, idan na ya fahimtar da ita ne zai yi ƙoƙarin hakan. Amma har yanzu bata san wanene shi ba.
Wankansa yayi ya haye gado yay kwanciyarsa. Dan kwana biyun nan sam baya ko isashen barci, ga wata yunwa da yake ji mai tsanani amma yafi buƙatar barcin dai first. Barcin kusan awa biyu yayi alerm ya tada shi, ganin lokacin salla yayi ya miƙe da ƙyar zuwa bathroom. Ruwa ya sake watsama jikinsa dan ya warware da ƙyau, yay alwala ya fito. Yana ƙoƙarin saka kaya ta shigo ɗakin, bai nuna yasan da shigowar tata ba kamar yanda itama ta nuna bata san da shi ba tai waucewarta bayi. Sai da ta shige ya zubama ƙofar cat eyes ɗinsa da suka sauya kala. Komai baice ba ya saka sallaya ya kabbara salla. Bayan ya idar tana daga gabansa tana tata ya ɗauka waya yay kira. Cikin harshen larabci yay magana da bata wuce ta sakan huɗu ba ya ajiye yana miƙewa. Bakin gadon ya koma ya zauna yana latsa wayar, mintuna kusan goma aka danna door bell ɗin gidan, tashi yay ya fita, babu jimawa ya dawo ɗauke da ƙyaƙyƙyawan kwando a hannu. Cikin set na kujerun da aka ƙawata bedroom ɗin dasu ya koma ya zauna, bayan ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, dan har yanzu tana a saman sallayar bata tashi ba. Abincin da aka kawo masa ya ɗan tsakura kaɗan ya ture...
Dai-dai nan na tashi daga zaman sallayar daya ishe ni. Veil ɗin kaina na warware, yanzun ma batare dana kala inda yake ba na nufi ƙofa zan fita amma sai na jita a rufe. Mamaki ya kamani dan nasan dana shigo dai ban kulle ba. Numfashi na ɗan furzar na koma kawai saman gadon nai kwanciyata. Ina kwance kamar mai barci sai dai idanuna ne kawai a lumshe naji alamar tsaiwar mutum a kaina. Sai ƙamshin turarensa daya cika min hanci matuƙa. Kamar zan share sai dai na buɗe idanun. A kansa na sauke su, ganin yanda ya wani kafe cikina da ido yasa na yamutse fuska. Kamar na balla masa harara sai dai na daure na sake maida idanun na rufe. A matuƙar mamaki naji saukar muryarsa a kaina wai yana da buƙata..
Kutumelecy ban taɓa sanin guy ɗin nan tantiri bane sai yau. Kasa jurewa nayi na buɗe idanuna a kansa jin ya kwanto gefe na. Sai kawai na yunƙura zan bar masa gadon. Ya maida ni ya kwantar. Ƙoƙarin turesa na shigayi sai dai ko gezau. Ƙarshe takaici yasa na sakar masa kuka. Amma hakan bai sakashi fasa abinda ya ambata ɗin ba. Sai dai duk yanda yaso ya samu haɗin kai daga gareni bai samu ba. Bai kuma fasa bina a cikin nutsuwa ba. Niko tunda ya barni sai na juya masa baya kawoi ina raira kuka. (Wato bily fushin mai ciki sai addu'a kawai, dan har cikin ƙasan raina haushinsa nake ji). Yanzun ma komai baice min ba ya ma tashi ya wuce bathroom abinsa. Aiko na sake hawa fummm...
Haka yayo wankansa ya fito, sai da ya kammala gyara jikinsa cikin bada umarni ya da dakewar nan tasa a daƙile ya furta, “Five thirty zamu wuce”. Daga haka yay ficewarsa. Yau na sake tabbatar da rayuwar aure haƙuri ce kawai. Duk kuma daɗinka da miji sai ya baka wannan maɗacin. Nima ji nake ƙasar kawai nake son bari, sai kawai na miƙe na gyara jikina na shirya. Sai da nai sallar la'asar na ƙarasa kimtsawa na fito duk da da sauran lokaci. Babu kowa a farlon sai television, na wuce na ɗauka ruwa na koma na zauna a kujera. A haka su Aunty Falaq suka fito suka sameni suma cikin shiri. Damuwata na haɗiye na ɗauka Awwab dake ƙusha ƙushin kuka. Batare da mun zauna ba duk da saura kusan mintuna arba'in Hayatu yace muje anzo ɗaukar mu. Nayi zaton shi yana waje, amma sai naga mu kaɗai ne muka shiga motar, koda muka iso airport ma babu shi, sai da muka shiga jirgi bayan cikar lokaci mun zauna sai gashi ya shigo shi da Juliet. Dama a wuya nake, ga shi kuma da wannan shegiyar ƙandararriyar baturiyar. Su duka ban kallesu ba, sai da ya zauna a kusa da ni cike da iyayi ta ce min, “Good evening” tana ranƙwafowa da tab a hannu wai zata nuna masa abu.”
Ai bamma san na buga mata wata tsawa ba cikin rufewar ido na furta, “Hy bar nan!!”.
Ba ita ba har shi uban gayyar sai da ya kalleni. Na watsa musu harara su duka yayinda ita jikinta ma ke rawa. A daburce ta shiga bani haƙuri da ƙoƙarin mun bayanin abu zata nuna masa mai muhimmanci. Nima sai na sake fusata na ce, “Okay bazaki tafin ba kenan ko?”.
Zata sake magana yay mata nuni data wuce. Sim-sim ta tafi har tana waigena. Na sake balla mata harara sai ta zabura da sauri ta ƙarasa ficewa a wajen. Ƙwafa nayi da faɗin, “Da ki tsaya mana. ALLAH da sai an fitar da ke a karye daga jirgin nan. Ki cigaba da shiga mun hanci karki fasa ramammiyan banza jiki duk ƙashi ko ƙyan kallo babu subi su nanewa mazan mutane da sunan aiki mayu”.
Gyaran murya ya ɗan yi. A fusace na juyo ina harararsa. Na ce, “Oh ko zaka shigar mata ne?”.
Kansa kawai ya ɗan jinjina min alamar a'a, idanunsa dake wani lullumshewa a kaina ƙyam. Cikin masifar dai nace, “Aida ka shigar mata duka zan iya daku”. Na ɗauke kaina nama kwanta ina wani buɗewa da ƙyau yanda zanji daɗi.
Ta gefen ido yake kallonta sai yaji abin ma ya koma bashi dariya. Ya dai dake baiyi ba, sai ya ɗan murmusa kaɗan da girgiza kansa yana ɗaukar tab ɗin gefensa ya shiga daddanawa, dan akwai abinda yake son bincika a google.......✍️
_😂 ALLAH sarki Yayanmu Sarkin haƙuri. Dangin Sam-G magana ta gaskiya ku sake mata karatun aure, mu bama son Hayaniya da raini😌._
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒐𝒖𝒓_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan