Showing 324001 words to 327000 words out of 438336 words

Chapter 109 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2246

yaje? Ya bashi amsa da “Gidan ne fa babu lafiya. Kunama ta harbi har mutum biyar gasu can an wuce asibiti da su.”
“Ikon ALLAH kunama kuma a gidan nan? Dawa-dawa?”.
“Wlhy nima abin yaban mamaki. Hajiya Mammah da wata mata baƙuwa sai budurwar nan mai iyayin tsiya mai kama da sadakar yalla da kuma wadda ka saka ranar ta kawo mana abinci baƙar nan da Mamanta ita tama suma”.
Dukansu ya gane su, idan ka cire baƙuwar da bai san wacece ba. Haka kawai sai baiji komai a ransa ba ya ce, “ALLAH ya ƙyauta” kawai ya tashi ya shige toilet. Alwala yayo shima dan yanzu ya dage ta tashi sallar dare saboda Hafizzullah da ya ga yanayi. Dan Hafiz akwai ibada gaskiya. Training ne kuma daya samu daga Yaya Musaddiq tun yana ƙaraminsa. Dan tun sanda ya fara wasa da salla ganin Mom nayi da yaranta Musaddiq ya dage a kansa har sai da yaga ya dawo hankalinsa. Daga nan kuma abin ya shigesa sosai bai sake sakaci ba sai ma Alhmdllh....

💢✨💢✨💢

Masu iya magana kance rana dubu ta ɓarawo ɗaya rak take zama ta mai kaya. Tabbas hakanne ta faru a daren yau da mutane guda biyu da yaransu. Dan jami'an tsaro sun samu nasarar cafke Commondo da yaransa biyu. Sai Madam Jannifer da yaranta huɗu harda dattijuwar tsohuwar nan ta gidanta Mama. Su dukansu kuma an cafkesu ne a lokacin da suke shiga gidan da suka ɓoye Paah batare da shi Commondo ya san da zuwan su Jannifer ba. Amma su su Jannifer sun san da zuwansa dan sun mayi shirin ƙwamushesa ne shima bisa umarnin Hajiya ƙarama. Sai dai basu san an saka tarko a gidan ba tun yammaci sakamakon bayanin da Maash ya bama su Isma'il akan inda su Commondo ɗin suka kai Paah.
Gaba ɗayansu hankalinsu ya matuƙar tashi. Duk da dai shi Commondo yana ganin kamar duk iya ma miza'ayi zuwa safiya sai Baba prof ya fitar da shi. Itama dai Jannifer ɗin tana da ɗan nata hope ɗin na ganin manyan ƙwarin da take huɗɗa da su zasu fitar da ita zuwa gobe. Yaransu ne dai hankalinsu ke matuƙar tashe musamman yaran Jannifer da irin haka bai taɓa faruwa da su ba. Wasu ma a cikinsu kuka sukeyi. Abinda kuma ya sake ɗaga musu hankali da akaje station ɗin da su gaba ɗayansu rarrabasu akayi babu wanda aka haɗa da ɗan uwansa...

Kai tsaye asibiti aka wuce da Paah duk da babu wani rauni a jikinsa. Sai dai yunwa ta galabaitashi dan ko sun bashi abinci baya wani ci sosai sakamakon azababben yajin da suke cika masa. Gashi yana da urlser. Taimakon gaggawa aka shiga bashi, sai dai ba'a sanar da kowa a gidansu ba kasancewar dare ya riga yayi. Garama Isma'il ya turama Maash text message sai dai shi kuma hankalinsa bai kai ba dan lokacin kam yana wani tsagin daban kuma. Da safe suka tashi da tashin hankalin yanayin Samraah. Sai da doctor ta dawo duba jikin Samraah da azhar suke jin ai su Hajiya Mammah na asibitinsu an kaisu jiya da dare kunama ta harbesu. Musamman ma Hajiya ƙarama har yanzu tana cikin azaba. Tana tsaka da musu wannan bayani aka kirata wai tazo asibiti akwai matsala ga Baba prof an kai shima kunamu sun masa kaca-kaca da harbi har a saman kansa. Yanzu ma'aikatan gidansa suke kawosa...
A firgice tama su Ummie bayani ta fice akan tana zuwa. Abin mamaki Maash ko tari baiyi ba sai ma hayewarsa yay sama kamar ma bai ji mi aka faɗa ba........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_


.......Da kallo kawai su Ummie suka bisa har ya ɓacewa ganinsu. Uwa uwa ce koda kuwa sakarai ce. Dan a take kan Ummie ya kawo mata haske. A zuciyarta ta raya (Anya ba Muhammad bane?) Sarai tafa sanshi idan aka masa sai ya rama. Wannan halin nasa tun yana mitsitsinsa yana matuƙar damunta. Tasha masa addu'ar ALLAH ya yaye masa shi. Ganin ya lafa daga baya sai tayi tunani ai ya barsa gaba ɗaya. Ashe-ashe.
Falaq ce ta fara ƙyaƙykyalewa da dariya da faɗin, “ALLAH yaja kwana Yayana”.
Kallonta duk sukayi, ta ɗauke kanta kamar ba ita tai maganar ba. A take itama Mama kanta ya kawo haske. Lallai kam zata iya yiwuwa Awwab ɗin ne. Wato ya rama musu abinda ya faru da su. Kai jama'a wannan hatsabibin yaro sai a barshi. Itama dai sai da ta murmusa. Hafiz da Fahad basu fahimci komai ba. Dan haka sukabi Falaq suna mata nacin tambaya. Cikin raɗa ta faɗa musu komai da abinda ta fahimta. Idanu Hafiz ya waro, yana haɗa 1+1 a ransa. Eh lallai biri yayi kama da mutum. Idan ba haka ba tayaya kunamar sai selecting mutanen data harba harda ma wanda bai kwana a gidan ba. Wato Maash abin tsoro ne. Dariyar Fahad ta maido Hafizzullah hayyacinsa. Sai kawai shima ya fara dariyar suka tafa.. ita Falaq ma sai ta koma ƴar kallo, dan ta kula sun fita iya shege...
Sai da sukai mai isarsa Hafizzullah ke faɗin, “Ya Fahad anya kuwa ba yarinyar nan bace tai aikin nan? Dan lokacin da ake fita da su gidan nan na ganta tana dariya acan baya laɓe”.
Cikin zaro idanu waje Fahad ya ce, “Kuttt wace yarinya?”.
“Kamar Bahijja naji suna kiranta cikin masu aikin nan”.
Salati Fahad yasa kafin yaja hannun Hafizzullah suka fita. Kai tsaye sashen masu aiki suka nufa. Karo na farko kenan tun zuwan Hafizzullah ya shigo nan ɗin, iyakarsu sashen su Mama Balki. Shi kansa Fahad ɗin zai iya rantsuwar bai fi sau biyu ya taɓa shiga ba. Cikin sa'a ma suna buɗe ƙaramin gate ɗin sashen suka hangota tana shanya kaya da alama wanki tayi sai raira ƴan wakoƙinta take. Kiran da Fahad ɗin ya mata yasa ta ɗan juyo a firgice, sai kuma duk ta daburce dan ya tsuke fuska hakama Hafizzullah. “Biyomu”. Ya faɗa murya a dake yaja hannun Hafiz suka juya. Gaba ɗaya sai ta ƙara rikicewa. Haka tabi bayansu hawaye na taruwa mata a ido. Itafa tana shakkar Ya Awwab sosai saboda baya wasa da yara. Amma wannan Ya Fahad ɗin tafi tsoronsa barema yanda yake cewa zai ma mutane yankan rago.
Ganin sun nufi sashen Fahad ɗin ta sake ruɗewa. Dogarewa tai ƙoƙarin yi a bakin ƙofa Fahad ya daka mata tsawa. Ai babu shiri ta shigo tana hawayen da take dannewa. Ƙasa ta durƙushe daga ɗan bakin ƙofa. Yanda duk take a ruɗe dariya ke bala'in cinsu. Amma duk suka danne Fahad ya ɗakko takobinsa ya ajiye. Murya a dake ya ce, “Kece kika sakama ƴan gidan nan kunamu jiya ko?”.
A wani mugun firgice ta ɗago tana zabga salati kamar tsohuwa. Zata fara rantse-rantse ya zaro takobin a cikin kufanta. Hafiz ya kalla ya ce, “Broth rufe min ƙofar falon nan ka riƙe min ita idan bata faɗa ba saina cire mata harshe.”
“Lahhhh ina ha illahu.... Ni Bahijja na shiga uku. Dan ALLAH Uncle Fahad kar muyi haka da kai.”
“Idan baki son muyi hakan faɗa min yanda akai kunama taje jikinsu?”.
Kuka Bahijja take sosai dan ta shiga tsaka mai wuya. Tunda take abubuwanta a gidan nan wani bai taɓa kamata ba sai yau. Bata son faɗa amma tana tsoron Fahad ɗin nan. Ganin dai Hafiz ya rufe ƙofar falo ta ƙara sakin kuka da faɗin, “Wlhy ni ce. Na sakama Hajiya ƙarama a kayan barcinta data ajiye saman gado ne tana wanka. Na saka biyu a aljihun wando biyu a aljuhunan rigar. Shine shine na laɓe, to bata fara cizonta ba sai bayan kusan mintuna goma, su kuma sauran taimakonta suka zo yi suka sami rabonsu....”
Kafinma ta kai ƙarshe Fahad ya bushe da dariya. Ganin haka itama sai kawai ta fara dariyar saboda tuno yanda Hajiya ƙarama ta dinga yin ƙaramin disko. Cikin dariya Fahad ya nuna Bahijja yana faɗin, “Yarinyar nan ALLAH ke muguwa ce. Ina kika samo kunama da bata cijeki ba?”.
Sai da ta ɗan sosa kanta sannan tace, “Ai nasha magani. Na kuma ramawa su Uumie ne ranar da suka sa ta cijesu”.
“Oh woow! Aiko nima dole a bani maganin nan kodan irin wannan ranar. Fantastic”.
Haka dai sukaita nishaɗin su ita dai Bahijja ma sai ta zama ƴar kallo....

★★★

Zuwan likitan Ummie yasa bata nema Maash dan taji gaskiyar magana ba. Ga zancen cikin nan na Samraah ya ɗaukaka farin cikinta yau matuƙa. Kasancewar suna mata allura tasha magungunanta sai barci yau ma hakanne. Doctor kuma ya sake tayata murna da in sha ALLAHU bai wuce ya ƙara shan magunguna na watanni uku zuwa huɗu ba abubuwanta su dai-daita. Abinda yasa ma zai kai haka saboda an jima ana mata allurorin da suka so jawo mata babbar matsala. Sai dai Alhamdullah komai zai zama labari. Shima bazai basu bayanai bane saboda akwai abinda yake shiri kan likitocin da suka kula da ita ɗin ta bayan fage. Sai ya kammala bincikensa sannan zai mata cikakken bayani. Ummie ta gamsu, ba kuma ta matsa da sai taji ɗin ba. Barci ne ma ya rinjayeta har doctor ɗin suka ƙarasa abinda suke suka fice bata sani ba kuma....

❤️🤍❤️🤍❤️

Ban tashi farkawa ba sai gabannin azhar. Yana kwance a kusa da ni da alama shima barcin ne ya kwashesa. Nauyayyun idanuna kawai na zuba masa tsahon lokaci, kafin na sauke ajiyar zuciya da kai ɗayan hannuna saman tattausan gashin kumatunsa na shafo. Janyewa nayi ƙoƙarin yi ya riƙe hannun tare da buɗe idanunsa a hankali ya saukesu kaina. Idanu muka zubama juna cikin wani bahagon yanayi kafin ya lumshe nasa tare da matso da fuskarsa daf dani har hancinanmu na gogar juna.
“Kin ta shi?”.
Ya faɗa yana ɗaura hannunsa akan wuyana. Idanuna na ɗan lumshe masa na buɗe alamar eh.
“Mike ciwo yanzu?”.
Kaina na ɗan girgiza masa alamar babu. Numfashi ya ɗan sauke da sumbatar lips ɗina kaɗan, sai kuma ya janye hannunsa dake saman wuyana ya maida saman cikina. Yanzun ma da raɗa ya ce, “My Baby fa?”.
Hannunsa na ɗan mintsina cikin tura baki na ce, “Ni ban santa ba”.
“Jealous ba?”.
Yay maganar da ɗan goga hancinsa kan nawa.
“Ba wani jealous nima ai Ummie na na sona. Ga kuma Mama”.
“Kidai tsaya a Ummien taki banda ƙwacen Mamana. Dan kin san ita ɗin tawace ni kaɗai. Falaq ma sammata nake”.
Murmushi nayi a karo na farko. Na ce, “Yaya!”.
“Uhhmyim My Tiger”.
“Har yanzu ba'a san inda Paah yake ba? Ina ka shige duk wannan dambarwar baka zo ba sai daga baya?”.
Shiru ya ɗan yi kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya buɗe idanunsa yana kallona. Yayinda hannunsa ke saman fuskata yana shafa gashin girata da yatsarsa babba. Muryarsa can ƙasan maƙoshi ya furta, “Paah dama nasan a inda yake, na barsu ne kawai naga iya gudun ruwansu Samrh”.
Idanu sosai na waro da faɗin, “Yaya da gaske?”.
Kansa kawai ya jinjina min.
Murmushi nayi tare da sumbatar mitsitsin bakinsa kaɗan, ina ƙoƙarin janyewa ya riƙe lips ɗin nawa da nashi. Sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so sannan ya barni. Muryarsa a shaƙe cikin kunnena ya furta, “Kema kina buƙatar mijinki ba?”.
Maimakon na bashi amsa sai kawai na shige jikinsa na rungumeshi dan kunya maganar tashi ta bani, shi ba ruwansa kai tsayensa yake magana ba kwana-kwana. Sosai ya riƙeni shima batare da ya sake cewa komai ba. Daga haka ɗakin yay shiru tsawon lokaci tamkar barcin muka koma amma duk idonmu biyu. Kiran salla ya sakashi sauke ajiyar zuciya, tare da ɗagani a hankali zai gyara min kwanciya na yunƙura nima. Sai kawai ya zaunar dani na jingina jikinsa. Yanda ya tsareni da kallo yasa na kasa kallonsa ni. Sai naji ya ɗan furzar da numfashi. Sauka yay tare da ɗagani cak a gadon. Fuskata a marairaice na ce, “Nifa ina iyawa”.
Komai baice dani ba har sai da muka shiga ciki bayin ya direni a bathtub sannan ya kamo jaw ɗina. Ɗago idanuna nai nima ina kallonsa. Yanda yake wani bina da narkakken kallo yasa tsigar jikina tashi, har sai da na sauke ajiyar zuciya a hankali. Shima iska ya ɗan furzar kaɗan, tare da furta, “In dai ina cikin gidan nan kin daina komai sai kula da ni shima a be.....” da sauri na kai hannuna saman bakinsa na rufe. Janyewa yay yana murmushi.
“Kin san mizan faɗa ne kika wani rufen baki”.
Bakina na ɗan tura nima da faɗin, “Nidai ba ruwana. Ga abinda nake son ka faɗa min ka tafi wanda ba'a sakaka ba”.
“ALLAH yarinyar nan kin lalace. Toni mi nace zan faɗa kike neman fassara min zance?”.
Kaina na juyar ina murguɗa baki na ce, “Ni dai ba ruwana”.
Murmushi ya sake saki mai ƙayatarwa da kai hannunsa saman cikina ya shafa. A mamakina sai jinai ya ce, “My blood kada kiyi rashin jin Ammien ki kinji”.
Harararsa nayi nima na ɗora hannuna saman cikin na ce, “My blood kada kayi miskilancin Dadaan ka kaji”.
Dariya muka saki a tare, ya dunguremin kai. Nima hancinsa naja da alama mun manta a bayi muke........✍️

(Nima dai na fara tunanin kun manta a bayin kuke🏃🏃🏃🤣).


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_



.......“Wai kai lado yau mike damunka ne? Motsi kaɗan sai ka wani kwashe da dariya. Kai ko damunka abinda ya faru da oga kamar baiyi ba ma. Alhalin idan binciken inda aka samo kunamu aka zo yi wlhy kai zasu kama tunda kaine ka kwana da shi”.
Dariya wanda aka kira lado ya sake kecewa da ita, sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Bazaka gane ba Hamisu. Wlhy ko kaine zakai dariyar da tafi tawa ma. Ka koga wani gigitaccen ihu da Yallaɓai yayi, ai ni nasha kallo. Da gudu fa ya fito falo ya kwaɓe wandon sai ɗan panti. Hannunsa kan jikinsa ya damƙe yana rabga ihu. Badan Kuka ya taimaka ya rufe ƙofaba da har tsakar gidan nan zai fito a haka hhhhhh!!!!” ya ƙara kwashewa da dariya. Da ƙyar ya cigaba da faɗin, “Kama-kama mukayi da Kuku wajen kamashi amma ina sai rawar disko dansa yake. Ashe bawan ALLAH abune goma da ashirin ya ishe shi. Kunama a wando, kunama a cikin hula ga wata a ƙafa tana bashi wuta. Haka dai muka dannesa muka cire panti da ƙyar shegiyar ta manne kuwa tanata aikin da aka sakata. Shiyyasa jikinsa fa ya kumbura tunkan a bar gidan nan sai bargo aka lulluɓa masa. Bakaga har mukaje asibiti dubasa da alama babu wandon ba hhhhhh!!! ALLAH alhakinmu ne anƙi bamu albashinmu, ALLAH yay ma wanda yasa kunamar nan albarka hhhhhhhh!!!!”.
Duk yanda Hamisu yaso ƙin biyewa lado hakan ya gagara. Shima sai da ya shiga kwasar dariyar.....

Baba prof ashe haka abubuwa Suka kasance harda rawar disko dansa😝😝, Sai munzo dubiya dai to, ALLAH yasa sannan ka fara saka wando😂🏃🏃🏃.

⭐✨⭐✨⭐

Kusan lokaci ɗaya Ummie da Samraah zamuce sun farka. Wanka ta farayi dan in dai tai barcin nan sai ta jita Alhamdullah jikin kuma yay mata sakayau. Kasancewar Mama Balki na yawan shigowa dubata sai ta kawo mata abinci ganin ta tashi. Bata wani zauna

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login