Showing 309001 words to 312000 words out of 438336 words

Chapter 104 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2895

Wayarsa ya ɗauka yana miƙewa da faɗin, “Abdullahi bamuga ta zama ba muje ko”.
Miƙewa Uncle Abdullahi yayi yana faɗin, “Baba bara na ɗan canja kaya” ya nufi hanyar sashensu, yayinda Hajiya ƙarama ta saki murmushi dan ta gane wayo ne kawai ya sashi barin gidan. Duk da kuwa wanda aka lissafa ɗin duk bai san inda suke ba. Amma jin za'a buɗe Maash yake son zuwa ya nemo mafita....

Uncle Abdullahi na shiga bedroom ɗinsa ya ɗakko wata ƴar ƙaramar waya. Kunnawa yayi sannan yay kira. Ana ɗagawa. Daga can cikin bada umarni ya ce, “Ku saki yaran nan daga nan zuwa awa ɗaya da kwata. Sai dai ku tabbatar basa a hayyacinsu”. Daga haka ya yanke wayar yana wani makirin murmushi. Kasheta yay gaba ɗaya ya maida inda ya ɗakkota sannan ya canja kayan ya fita kamar bashi ba...

Bashi kaɗai ba, a ɓangaren Hajiya ƙarama ma a hargitse ta wuce ɗakinta. Kira ta dannama Commando. Yana ɗagawa zai fara mata surutun banza a tsawace ta ce, “Akwai matsala fa. Mun manta wayar nan duk mun taɓata da hannayenmu kafin a jefar da ita, sannan bamu kasheta ba. Yanzu ƴan sanda sun samo wayar kuma shirinsu shine bibiyar sayin yatsun mutane uku da suka gani a jiki. Kaga kuwa akwai nashi, nawa, naka. Ga shi wannan tsinannen tsohon yace a fara da nan gidan kuma nasan danni yayi haka. Sai dai da yake bani da hakkin matsiyaci yanzu ake sanar ma Mashi'a ana ƙoƙarin buɗe gidan Awwab ashe sakawa yay aka yanke masa wutar gida da network da duk wani abinda zai iya tabbatar da yana a gidan sannan yasa jami'an tsaro suka zagaye gidan kamar dai yanda ya taɓa sawa akama Shamsu. Shine ya wayance da wai bai kamata Awwab ya dawo babu iyayensa babu Fahad ba. Kaji makiri fa, nasan neman mafita ya tafi dan in har aka samu Maash a gidan nan ya kuma fito a yau kashinsa ya gama bushewa”.
Ƴar dariya commondo ya saki daga can da faɗin, “Cakwakiya kenan. Yanzu yaya za'ayi to?”.
“Ya kamata dai musan mafita kam. Dan in ba hakaba tofa wasan zai canja salo in har Awwab ya fito. Kai dai kasan halin mutumin nan kansa kawai ya sani. Duk kuma yanda zai yi yaga ya fidda kansa a wannan gaɓar zai yi ɗin tunda babu wata alama data tabbatar da shine ya ƙulla duk wannan harmutsin jiya zuwa yau ɗin. Shi kuma Awwab ba kanwar lasa bane ba”
“Ya kamata kizo ki sameni. Dan bamuga ta zama ba.”
Daga haka ya yanke kiran.....

💢⭐💢⭐💢

Alhamdullah jikin Abba yayi sauƙi, ƴan Gwarzo da labarin komai ya sama suma ta ɓangaren su Gwaggo Gudidi da ɓangaren mahaifin su Samraah ɗin su kawu Musa kenan duk sun shigo ganinsa. Basuyi ƙasa a gwiwa ba kuma suka haɗa community zuwa gidan Sheikh Muhammad bin Khalipha Al-Hussain. Sai dai basu sami ganinsa ba ance ya wuce Lagos. Haka dole suka haƙura suka koma gidan Abba da shima aka sallama. Sun sake zaman meeting kan zuwa can Lagos ɗin. Dan har yanzu basu san halin da Samraah take ciki ba su. Sun kira no bata shiga, an kira ta Hafizzullah duk ba'a samu. Ga Musaddiq da yaga komai a Media yanata faman kiransu cikin tashin hankali. Dan har yana tabbatar musu da shifa zai dawo gida. Sai da sukaita tausarsa dai....

A yayin da su suke cikin wannan damuwa da tashin hankali ita Mom ranta fari ƙal. Sai ma siɗaɗewa tai tabar gidan zuwa gidan Ummanta. Cike da nishaɗi sukaita tattauna batun. Duk da zaka iya fahimtar tsantsar hassadar su a cikin zancen game da jin wai Samraah Maash ta aura. Sai da suka gama ƙulle-ƙullen sharrinsu sannan suka koma kan tattauna batun Baby dake matuƙar ɗaga musu hankali. Abu kamar wasa kwanaki nata sake tafiya. Bata ba mijin nata babu batun zuwa makarsu bayan sun gama baje gari da zance. Dan su har yanzu hankalinsu bai fara basu akwai babbar matsala ba, balle su fara ƙoƙarin neman ahalin mijin baby ɗin. Bata jima ba ta koma gida tunda ta baro shi cike da mutane. Sai Halime baiwar ALLAH dake ta fama da kanta keta hidima da su ga hidimar Abba shima. Dan ma su Aunty Zakiyya na tayata.....

💓💓💓💓

A guje ɗaya daga cikin securitys ɗin ƙofa yazo yana sanar ma su Hajiya Mama dake cikin gida duk da ita tana ma ƙoƙarin wucewa duba jikin Samraah ne ita da yaranta. Haka itama Hajiya ƙarama ta fito ne zata wuce wajen commondo amma da shirin asibiti kamar can ɗin ta nufa.
Yanda jikinsa ke rawa ya gagara iya cewa komai ya saka Hajiya Mammah daka masa tsawa. Da ƙyar ya iya nutsuwar shaƙar numfashi da fesarwa sannan ya sanar musu ga wata mota ta ajiye su Fahad a ƙofar layin nan. Yanzu nan securitys ɗin farkon layi suka kawosu wasu kuma sunbi mai motar. Kafin ya gama rufe baki ma'aikatan gidan suka shigo ɗauke da su Fahad da ke cikin yanayin barci. A saman kujeru aka shinfiɗar da su, hakan yasa kowa yin cirko-cirko kawai ana kallonsu. Musamman ma Hafizzullah da Hajiya Mama ta zubama ido. Sai zuwa can tai ƙarfin halin tambayar shi wanene?. Maman Malika ce ta bata amsa da bayani gamsashe. Murmushi ta saki tana mai jinjina kanta.. Sai kuma ta juya ta zaro waya tai kiran Baba prof. Kamar wanda ya daburce ya shiga amsa mata harshe a cuɗe, ita harma yanda ya ruɗe ɗin yaso bata mamaki. Amma dai batace komai ba.

Babu jimawa kuwa sai gashi ya iso. Dai-dai nan suma ƴan sandan nan suka dawo. Su kansu sunyi mamakin dawo da su Fahad ɗin, duk da dai su dama ba'a ma san ainahin abinda ya faru da su ba. Tunda aka fara dambarwar nan babu su a gidan. Hajiya ƙarama ce ta dubasu domin tabbatar da lafiyarsu.
Yanda ta ɗago tana wani jijjiga kai ya sakasu zuba mata ido. Cikin nuna damuwa ta ce, “Babu abinda ya samesu da alama ma shaye-shaye sukayo.”
“Shaye-shaye?!!”.
Kusan atare kowa na falon ya faɗa. Sai da taji zuciyarta tayi wani irin tsargawa amma ta dake tace eh. Masifa Hajiya Mammah ta fara akan Hafizzullah ne ya koya ma Fahad to, dan Fahad dai baya shaye-shaye duk sun san da wannan. Babu wanda ya iya cewa komai a falon. Sai Baba prof dake a cikin ruɗani. Sai kuma Uncle Abdullahi daya kafe Hajiya ƙarama da kallon mamaki. Dan a wannan gaɓar dai shi shaidane tayi ƙarya.. Ma'aikatan gidan aka kira suka ɗaukesu suka maida sashen Fahad ɗin, daga haka kowa ya kama gabansa tunda su ana ganin babu wata matsala a tattare da su sunje sun shawo kayan maye ne........✍️


Uhhmmm Uncle Abdullahi??? To bance dai komai ba🤔🏃


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_


........A hankali na dinga buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi, ɗakin na fara bi da kallo. Take komai ya shiga dawo min dalla-dalla. Ciki harda abinda ya faru a daren jiya. Waige-waige na fara yi, sai dai babu ko alamar wanda nake son ganin, sai ƴar sandar nan kaɗai zaune a kujerar gaban gadon da nake tanata zabga game a waya. Wani irin rauni naji zuciyata tayi, dan na fahimci tabbas nayi mafarki ne a daren jiya kenan. A cikin mafarki Maash ya kawo min ziyara harda shayar dani shayi mai daɗi. Hakan na nufin koda bama tare zukatanmu na tare. Idanun kawai na maida na kulle, sai da na ɗan sake jimawa a hakan kafin na yunƙura na tashi zaune. Dai-dai nan Nurse ta shigo. Da sauri tayo kaina batare data damu da ƴar sandar nan ba. Zanyi salla nace mata. Babu ko musu ta kamani zuwa bayi. Ita ta taimaka min nayi al'awar ta sake fito da ni. Ganin bazan iya tasowa ba ina ganin jiri tace nayi sallar a zaune. A zaunen kuwa nayi ta, ina idarwa na zame a wajen na kwanta dan babu abinda kuma nake buƙata yau sama da waje mai sanyin. Dai-dai nan Alaja ɗin nan data ɗakkoni daga hannun Madam Jannifer wadda Mama ta sanar min autar su Paah ce ta shigo da sallama. Likita biye da ita sai wasu yara masu ƙyau sosai daka gansu kaga ƴan hutu. Wani kalar faɗuwa gabana yayi, babu shiri na zabura na tashi tsaye. Da sauri doctor ɗin ta kamani ta zaunar a bakin gadon tana faɗin, “Please calm down kada ki ruɗar da kanki. Dan yanzu yin wani babban yunƙuri a gareki haɗari ne..
Murmushi itama Alaja ɗin tai mun, tare da zama a kusa da ni ta rungumoni jikinta. “Cool dawn my Daughter cool down.”
Sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya. Zancen Yaya Awwab na wancan ranar na dawo min akan batun shine ya sakata ta ɗakkoni ai da ga gidan Madam Jannifer. Gaisheta nayi, ta amsa min da kulawa, tare da tambayata jikina. Na tabbatar mata da Alhamdullah. Suma yaran suka gaisheni. Amsa musu nayi, tare da miƙa musu hannu cikin ƙarfin hali ina murmushi. Babu musu kuwa duk suka zo gareni.. sai da taga suna neman haye min jiki ta dakatar da su. Baki suka dinga turawa cikin shagwaɓa. Ni sai ma suka bani dariya dan su duka sun kai kusan 12years da 10years. Amma Abinka da rainon madara.
Hajiya Mama da kanta ta bani abinci naci, doctor ta shigo ta dubani ta bar Nurse ta bani magunguna sannan suka fita. Duk yanda naso daurewa na kasa. Sai da na tambayeta Ummie na lafiya, sannan anga Paah. Aunty Falaq kuma ta haihu?.
Sai da tayi ɗan jim kafin ta saki murmushi da faɗin, “Everyting Alhamdullah daughter. Yanzu ki kwanta ki huta, idan kika samu lafiya duk zaki ji komai, za kuma ki gansu.”
Kaina na ɗan jinjina mata kawai. Ina son tambayar ta Maash ko ya kira waya amma ina jin kunya. Dan ban san yanda zata fassara al'amarin ba tunda koba komai matsayin suruka take a wajena. Haka na haƙura na kwanta ina mai lumshe idanuna....

💢⭐💢⭐💢

Gaba ɗaya komai ya ida daburcewa Baba prof.. suna isa gida yace driver ɗinsa ya biyosa dan tun a can Maash Mansion suka rabu da Uncle Abdullahi. Ya turashi wani waje akan shima zai je wani waje. Cikin rawar jiki kuwa ya bisa har falo. Wasu azababbun maruka har huɗu ya dinga sakar masa. Kafin ya shaƙe mas wuya ya buga kansa da bango. Wahalalliyar ƙara ya saki jikinsa na rawa. Sai da prof yaga numfashinsa na barazanar barin jikinsa sannan ya wancakalar da shi gefe aiko ya faɗa akan hannunsa ji kake ɓasss alamar karaya. Wata ƙarar ya sake saki da ko fita batayi, sai ga zufa na wanke masa jiki. Babu ko tausayi a idanun Baba prof ɗin ya take hannun daya karye ɗin tare da duƙowa kansa ya sake shaƙar wuyarsa ya ce, “Ya akai waɗan can yaran suka fito??”.
“Wlhy! Wlhy ban sani ba yallaɓai. Na rantse da ALLAH inda kace na kaisu can na kaisu. Kuma ko daren jiya na kai musu abinci. Yau ne kawai ina shirin fita da safen nan zuwa wajensu kace min zamu fita shine na bari akan sai in mun dawo naje ɗin. Amma wlhy ban san tayaya akai hakan ba. Ban san wanene ya fito da su ba, babu kuma wanda na saka ya tayani aikin balle nace wani yaci amanata”.
Sake falleshi da mari yayi. Ya mutsika hannun da ƙafa har sai da ya saki fitsari. Cikin azababbiyar murya ya ce, “Idan baka faɗa da arziƙi ba zaka faɗa ta tsiya ai dan ubanka. Sai kayi dana sanin sani na”. Ya ƙare maganar yana kai waya kunnesa. “Commondo ka sameni yanzun nan a gida”.....

Kallon Hajiya ƙarama da ke tsaye Commondo yayi, cikin taɓe baki kasancewar taji komai ta ce, “Wannan wawan fa ya fara haukacewa wlhy. Jeka dai ka jiyo mana mike faruwa zan jiraka. Dan nina a haukacen nake. Dolene fa yau muyi wani motsi”.
Kamar Commondo zaiyi magana sai kuma ya fasa. Miƙewa yay yana murmushi, sai kuma ya kai mata runguma ta kauce tana harararsa. Dariya ya kwashe da ita yana ajiye karan sigarin hannunsa a ɗan bowl ɗin daya tarasu da yawa ya fice. Raka bayansa tayi da harara itama tana kaiwa zaune. Wayarta dake ringing ta ciro a jaka tana kaiwa kunnenta. Bayan sun gaisa ta ce, “Jannifer ki kasance cikin shiri fa, da zarar na tura miki text ko na kiraki ku shiga gidan. Dan ina gama jin cikin wawan nan shima yanzu aikinmu zai fara”.
“Baki da matsala hajjaju na. A yanzu haka na shirya tsaff ni da yarana”. Jannifer ta faɗa daga can cike da nishaɗi. Wayar Hajiya ƙarama ta yanke itama tana murmushi. Dan ita kaɗai tasan nata plans ɗin, daga Commondo har Prof a tafin hannunta suke.....

A ɓangaren Commondo yana isa ya samu Baba prof cikin bikitaccen yanayi, ga driver ɗinsa kwance a tsakkiyar falon hannu ya kumbura sosai, bawan ALLAH har yayi sumar wahala. Kallo ɗaya commondo yay masa ya ɗauke kansa. Kan Baba prof ya maida yana mai faɗin, “Ranka ya daɗe gani”.
Wata irin iska mai masifar nauyi baba prof ya furzar. Kafin cikin shaƙaƙƙiyar murya ya ce, “Commondo akwai matsala. Wannan wawan ya jiƙa mana aiki ɗaya”.
“Aiki? Wanne kenan a ciki ranka ya dade?”.
Kallon Commondo ɗin yay da juyayyun idanunsa ya furta, “Yaran nan sun kuɓuta. Fahad da ƙanin yarinyar nan”.
“What?!!”.
Commondo ya faɗa yana wani miƙewa. Dan shi kansa yanada babban target akan Fahad a daren yau. Dan tunda Prof ɗin ya sanar masa suna a hannunsa sune farkon plan nashi. Hannu baba prof ɗin ya yarfar shima cikin zafin rai ya ce, “Wai mike shirin faruwa ne? Tabbas ana bibiyar bayanmu”.
“Yallaɓai waye zai bibiyi bayanmu amma? Kafa ce Maash yana ƙarƙashin ikonka shi da jarababben PA ɗin nan nashi. Yarinyar nan tana asibiti a ƙarƙashin kulawar likita da jami'an tsaro. To kodai Mahaifiyar Maash ɗin ce? Dan tabbas ina ji a jikina matar nan ta samu lafiya......”
“Nooooooooo!!!! Bazai yiwu ba Commondo bazai yiwu Ummu-Hidaya ta taɓa samun lafiya ba har sai idan nine naso hakan. Kuma zanyi hakanne a gaɓar dana shimfiɗe gawawwakin yaranta biyu a gabanta na durƙusar da ita bisa gwiyawunta ta damƙa min dukiyar da tai min gadara a kanta sannan, dan banaso Ummu-Hidaya ta mutu yanzu. Sai ta wulaƙanta, ta rasa inuwaf raɓawa taji sanyi. Idan har kuma wani ya bata wannan inuwar wlhy sai ta gwamci GARA RANA DA ITA...”
Kai kawai Commondo ya jinjina masa, sai kuma cikin sauke numfashi ya ce, “Banƙi ta takaba oga. Amma yakamata fa zuwa yanzu mufara tunani irin na mutane guda biyu. Idan ba haka ba taya akai ta gane hanyar da zasu gudu a ranar? Sannan da suka gudun shi wanda ya taimakesu wanene shi?. Oga akwaifa tufƙa da warwara a al'amarin nan na wannan karon. Anya kuwa? Anya Maash bai baka ƙafa ba? Ka kuwa tabbatar guy ɗin nan zai yarda ya faɗi ƙasa irin haka da sauri. Maash ba ba wawa bane kansa na aiki fiye da gudun sakannin agogo. Ina baka shawarar kayi bincike shin da gaske ne har yanzu Maash na'a gidan can? Hakama PA ɗinsa. Idan har mun samu wannan tabbacin to dolene a cikin yaranka bayan Maash akwai wanda yasan wani abu kuwa. Ko kuma dole mu yarda Ummu-Hidaya ta samu lafiya. Dan kowowar su Fahad gida kam akwai ayar tambaya akai....”
Kasa magana Baba prof yay, sai idanu da ya tsurama Commondo tamkar mai nazarin zantukansa. Jirin dake neman yadda shi ƙasa ya sashi kaiwa zaune. Hannunsa har rawa yake wajen ƙoƙarin ɗaukar wayarsa. Danne-danne ya shiga yi tare da kai wayar kan kunensa. Sai dai layin ɗaya kira yaƙi shiga. Sake gwadawa yay har sau fiye da goma amma bata tafiya. Kallon Commondo ɗin yayi cikin ɗan rikicewa.
Kafin ma yay magana Commondo ya ce, “Miya faru? Waka kira?”.
“Zain bin Abideen. Kuma layinsa yaƙi shiga. Dole ne nai shirin tafiya Dubai daren yau da sunan duba jikin Awwab”.
“Shawara mai ƙyau sir”.
Commondo ya faɗa cike

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login