Showing 381001 words to 384000 words out of 438336 words
duk zanyi maganinku. Bari mu dawo zan faɗa masa duk abinda kukace a motar nan”.
Da sauri har hada baki suke wajen bani haƙuri. Falaq dai nata dariya...
Mun iso anguwarmu lafiya. Ban san nayi kewarta ba sai da muka shigo cikinta. Komai yana a yanda na barsa. Ɗan cigaban da aka samu a shekara ɗaya da wasu watanni da bana nan ba wasu masu yawa bane. Murmushi kawai nake saki har motocinmi uku sukai parking a ƙofar gidan Abba. Ta farko data bayanmu duk guards ɗinsa ne. Sai mu a motar tsakkiya fara tass dako makaho ya laluba yasan an sayeta da kuɗaɗe masu tsokar gaske. Tunda muka shigo anguwar aketa kallonmu. Barema cikin layinmu wasu har biyowa sukai suga su wanene a ciki. Kafin Hafiz da Fahad su fita guards ɗin har sun fito. Sune suka buɗe mana ni da Falaq, kamar yanda suka buɗema Fahad da Hafizzullah........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
......Jinai ma hawaye na neman cika mun ido. Amma haka na daure na dake abina dan yanzu fa ba da bace. Matar Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash nake. Amsar handbag ɗina guard ɗin ɓangaren da nake yayi da sauri, yayinda ni kuma na saka little Awwab a kafaɗa na zuro ƙafata dake sanye cikin takalmi mai ƙarancin tudu silver sai sheƙi yake, ya wani masifar haska ƴar ƙafata da tai cas a ciki. Cike da ƙasaitar da ban san ta fara bin jinina irin ta matan manya🤪 ba na fito. Ni kaina a yanda nai action ɗin fitowar nasan nayi barazana a wajen Bily. Dan a take shock ɗin mutane da yawa ya bayyana saman fuskokinsu. Aunty Zakiyya dake tsaye tare da wasu mata da alama rakosu tayi kota tarosu ce tai wani masifar zabura da ƙwala kiran sunana cike da farin ciki tazo ta haɗa ni da little ta rungume. Kafin kace mi yara sun fara cillawa da gudu cikin gida suna faɗin ga Samraah. Ya ALLAH da ƙyar muka samu shiga cikin gidan. Hafizzullah riƙe da handbag ɗina daya amsa hannun guard ɗin nan. Mu huɗun duk muka shiga har Fahad. Cikin lokaci kaɗan gida ya yamutse, na ɗaki nata fitowa. Ni dai ina rungume jikin Gwaggo Gudidi da itama ta fito. Hango Mom da tai kamar mutuwar tsaye yasa na saki Gwaggo Gudidin na nufeta na rungume. Dan harga ALLAH wani irin kewarta nake ji, na yarda da batun masu iya magana da sukance sabo akewa kuka ba mutuwa ba. Farin cikin da nake ciki da ƴan uwa da suka lulluɓeni yasa sam bamma fahimci halin da Mom ɗin ke ciki ba. Da ƙyar aka sarara min saboda Gwaggo Abu datai maganar su barni na zauna bani kaɗai bace ina fama da kaina sai jagwalgwala ni suke. Kai tsaye kowa ya fahimci inda ta dosa, dan koba'a fada ba duk mai hankali ya ganni yasan inada ciki. Anan tsakar gida muka zauna a tabarma dan na samu damar gaisawa da kowa. Ƴan uwan, maƙwafta dama yara nan fa aka shiga gaisuwa. Yayinda yaran keta shigowa da kayayyaki. Ashe Hayatu ne ya lodosu a motar bisa umarnin uban gidan nashi batare da saninmu ba. Cike da shaƙiyanci abokan wasa ke tambayar wai cikina wata nawa ne. Harararsu kawai na dinga yi naƙi faɗa, da naga zasu takura min ma sai na gabatar musu da aunty Falaq. Ai ko nan take aka koma murnar ganin ƴar uwa, dan akwai dangin ɓangaren babanmu da yawa da sukazo daga Gwarzo kasancewar dai akwai zuminci a tsakaninsu da dangin mahaifiyar tamu su Abba. Sai kuma aka koma koke-koken yima iyayenmu addu'a. Kiran sallar azhar ya taimakemu muka samu sararawar mutane. Sashen Mom da ban sake gani ba tunda na rungumeta ɗazun muka shiga. Babu mutane sosai dan wai bata gayyaci kowa ba. Hasalima tun ɗazun tana ɗaki ihun zuwane ya sa ta fito har mutane suka ganta a yau ɗin. Zaune muka sameta ta zabga tagumi. Zama nai kusa da ita na sake rungumeta. Koba komai dai ita muke ma kallon uwa dan itace ta rainemu. Sai da na ɗan jima a jikinta sannan na ɗago cike da kulawa da girmamawa na gaisheta. Muryarta na rawa ta amsa min, ban damu ba na tambayarta ina su auta naga banga kowa ba sai ita kaɗai sai Ummanta da itama na gaisar. Umman tata ke sanar min ai sun ɗan fita ne. Kaina na jinjina da faɗin, “Mom bari muyi salla yau akwai labari, so nake ki bani labarin duk abinda akayi bana nan nayi kewarku sosai. Hanun Aunty Falaq naja muka wuce tsohon ɗakina dan Little Awwab na hannun su Gwaggo an goyesa, su Hafizzullah kam tuni sukai gaba abinsu. Mun ɗauro alwala zamu fara salla Aunty Falaq ke faɗin, “Sis... Matar nan kamar batai murna da ganinki ba. Da fa muka shigo kamar kuka take”.
Murmushi na mata da faɗin, “Kai aunty maybe na murnar ganinmu ne. Kin san fa itace ta riƙemu”.
Humm kawai tace badan ta yarda ba ta kabbara sallarta. Nima sai na kabbara tawan. Bayan mun idar na ciro wayata a jaka dake ruri. Ganin Yaya Awwab ke mun video call da sauri na ɗaga. Tar-tar kuwa ya fito akan screen ɗin kamar na taɓashi na kama. Ganinsa zaune kamar a bedroom yasa na ɗan waro idanu. A shagwaɓe na ce, “Salla fa?”.
Sai da ya ɗan kalla agogon hannunsa tare da lumshe idanun ya buɗesu a kaina sannan ya motsa lips ɗinsa ya furta, “Yanzu kikayi naki ke kenan?”.
Kai na jinjina masa. Shima ɗan taɓe bakinsa yay da jinjina kansa ya ce, “Yayi. A ina kike nan?”. Back camara na maida na haska masa ɗakin kaf sannan na maida ta gaba fuskata da murmushi na ce, “Tsohon ɗakina ne munyi salla da aunty Falaq”.
Zaune ya tashi da ƙyau yana faɗin, “Sake haskawa na gani”. Babu musu na tashi tsaye ina haska masa da nuna masa wardrob ɗina na bango ni da su auta, inda nake ƙwana. Harma da wasu abubuwa nawa da har yanzu ba'a fita dasu a ɗakin ba. Maido da camaran nai kaina ina murmushi, shima sai ya murmusa da silent muryar nan tashi ya furta, “Ɗakin matar Maash ya ƙayatar da ni, zanso wataran nima nayi barci a cikinsa tana jikina”.
Sosai na waro idanuna, sai kuma na kalla inda Aunty Falaq take. Wayam ta fita, na ɗan sauke ajiyar numfashi da kallonsa. Gira ya ɗan ɗaga min alamar miye ɗin nan. Nima sai na tura masa baki na ce, “Aunty Falaq fa na nan, a gidan namu kuma zaka kwana harma na kwanta a jikinka”.
“To minene? Kuma zan ƙi magana da Matana saboda Falaq na nan? Yanzu dai yashe zaku taho. Ina buƙatar ɗumin matata”.
“Kai Yaya ko awa biyu fa bamu yi a gidan nan ba. Bammaga Abba ba? Kuma su Ummie zasu zo idan anyi la'asar. Kai bazaka zo ba?”.
Shima fuska ya ɓata, da ƴar shagwaɓa ya ce, “My Tiger ana ga ƙura kina ga yaƙi, ni mizan zo nayi taron mata, sai gobe in sha ALLAHU zamu zo mu duka gaida Abba sai muga babys.”
“To Please mu kwana nan. Kagafa ƴan uwa duk suna nan sunzo da yawa musamman ƴan gwarzo. Ga shi duk basu san Falaq ba”.
Kai ya girgiza min alamar a'a yana lumshe idanunsa. Idanuna cike da ƙwalla na ce, “Miyasa?”.
Kamar bazai ce komai ba sai kuma a hankali ya furta, “Sabida mijin Samrh bazai iya barci ba sai da Matarsa a jikinsa”.
“Kaida kake tafiyanka fa sai ma kai sati ban ganka ba”.
Murmushi ya ɗan yi kawai yana kallona hannayensa harɗe a ƙirjinsa. Ganin yaƙi magana na sake tura baki da faɗin, “Shike nan amma fasa hiran da kai, kuma namayi yaji yau anan zan kwana”. Na katse kiran. Nayi hakan ne saboda shigowar su aunty Zakiyya da suka kasa haƙuri. Dole na biye musu muka fita. Babu su Mom a falon yanzu, dan haka muka fice tsakar gidan dake ta sake cika da ƴan suna. Sashen amaryar Abba muka shiga mai jego kenan. Haka kawai naji tamun a rai, gashi dama bazamu wuce sa'anni ba. Daga ita har ƴan uwanta sai haba-haba suke damu. An zagayemu da kayan ciye-ciye kamar mune kaɗai baƙin sunan. Yara na hannunmu Masha ALLAH daga gani dai sun kwaso ƙyawunta. Muna a sashen Abba da Kawu Jafaru da abokansa suka shigo. Shima kasa ɓoye farin cikinsa yayi, babu kunya ya dinga yima abokansa bayanin ga ƴarsa dake aure a Lagos tazo. Tuni sun ɗau haske. Niko da Falaq munata gaidasu da girmamawa. Anan muke jin ai walima zasuyi, nima sai na sanar masa ai Yaya Awwab ɗin ma na zuwa idan anyi la'asar harda mahaifiyarsa. Kasa rufuwa bakin Abba yay dan farin ciki. Ganin yanda yake ta farin cikin na ɗauka waya na turama Yaya Awwab ɗin roƙon dan ALLAH ya biyo su Ummie.
Sam banyi tunanin zai zo ɗin ba. Bayan la'asar gida ya gama cika matuƙa mun zama abin kallo tako ina sai ƙusƙus mata suke da nuna ni, ta wajema anata shirin fara walima wasu ma har sunje sun zazzauna sai ga wasu zuƙa-zuƙan motocin har huɗu. Biyu dai na guards ɗinsa ne da suka rakomu ɗazun suka koma. Biyu kuma ɗaya Ummie ce da Mama balki da uwargidan Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain ce. Sai ɗayar Tj da Hayatu a gaba, uban tafiya a baya. Ina da ga bakin gate muna magana da wasu ƴan islamiyyar mu da aka kaima labarin zuwana dake nan layinmu sun zo tabbatar wa na ɗan rakosu akan gobe zamu haɗu yau taro yasa bazamu gaisa da ƙyau ba motocin suka tsaya. A take kallo ya koma kansu kamar sanda muma muka iso. Number motocin yasa na gane nashi ne, sai nai tunanin su Ummie ne kawai. Su na nufa cike da murmushi zan tarbi su Ummie sai kawai aka buɗe masa. Fitowarsa ta saka mutane da yawa ambaton Masha ALLAH. Dole nima na tsaya cak ina kallonsa kallo irin na mamaki. Dan sanye yake da bugaggiyar shadda data ji ɗinki ɗan ubansu da yay masifar zauna masa a jiki tamkar dan shi kaɗai aka halicci shadda a duniya (Tofa namu mazan fa🤔😏) ga wani arnen takalmi da hula daya murza a sama. Yana masifaffen ƙamshin nan nasa daya mamaye wajen gaba ɗaya yama danne namu. Karo na farko dana ganshi sanye da manyan kaya a rayuwata. Kullum daga suit sai ƙananu kawai. Gira ya ɗan ɗage min da kashe ido ɗaya cike da salon nan nasa na isa da ƙasaita. Sai kuma yamun alamar wai nazo garesa. Kafaɗa na maƙe masa da nufar Ummie na rungume. Hannu biyu ta riƙeni itama tana murmushin da masa daƙuwa dan kowa a wajen kasancewar idanu na kanmu yaga abinda ya faru a tsakanin namu. Kansa ya ɗan rissinar da kai hannu ya shafo wuyansa. Tuni kuwa waje ya fara ɗaukar ƙusƙus. Yayinda su Abba suka taso cike da farin cikin tarbar babban mutum irinsa kuma surukinsa. Yanda yake ƙoƙarin girmama iyayena sosai yake ƙara saka min ƙaunarsa da kgirmansa a zuciyata. Nima sai naja su Ummie muka shiga cikin gidan da tuni har an kai musu labarin mijina da iyayensa ne suka zo. Shigowar su Ummie ya saka gidan ɗaukar tsitt, kowa na yaba sunan UBANGIJI a ransa. Dan duk wanda ya kalla Ummie yaga cikakkiyar baturiya a kayan hausawa. A falon Mom Gwaggo Gudidi sukai musu masauki. Babu wani alamar wulakanta kowa ga Ummie. Kowa yazo cikin girmamawa da mutuntawa take gaishesa. Kamar yanda suma suke mata gaisuwa irin ta girmamawa.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_
.......Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama shirya musu abincin suna kala-kala a farlon Mom ɗin data fito ta gaishesu cikin dauriya da dakewa. Da alama dai mahaifiyarta ta kwakwkwafeta ne. Dan kallo ɗaya zaka mata ka fahimci a susuce take. Bare ma ganin su Ummie ta sake firgicewa. Bata ma ida susucewa ba sai da Maash suka shigo shi da Hayat da Abba har cikin gidan a falon da muke na sashen nata. Da ga can tsakar gida Abba yabar bakin kowa buɗe dan kai tsaye ya sanar musu wannan mijin Samraah ne, wannan kuma Falaq. Anan kuma tsabar neman magana irin na Yaya Awwab Ummie ta bani Babys na miƙa musu kawai ya haɗa da hannuna ya riƙe yaƙi kuma saki dole na kai duƙunne gabansa hannayena da nashi tallafe da Babys ya ɗaura saman cinyarsa a haka. Niko ina ta duƙunne a gabansa like na dafa gwiyawunsa. Cikin ɗan iskan salon kallon nan nashi dake kashe min jiki ya kallan fuskarsa da ɗan murmushi muryarsa very soft da kowa baya ji sai ni ya furta, “Kamar ace namu ne ko My helf”.
Tamkar zan nutse dan kunya, danni gani nake kowa na jinsa na marairaice masa fuska. Cikin magana ƙasa-ƙasa na ce, “Yaya Awwab su Abba fa da Ummie, ka saki min hannu na tashi Please”. Ɗagowa ya ɗan yi da alama shima dai ya shagala da mantawa da su ɗin, fiiii ya ɗan kalla kowa sai kuma ya dawo da kallonsa kaina. Cikin sake maida muryarsa Low ya ce, “Ya Rabba. My tiger dama bamu kaɗai bane?”.
Hararsa na ɗan yi, sai kuma nai ƙoƙarin janye hannayena dan nama fara gajiya da durƙuson. Ina samu na zaresu na miƙe a wajen batare dana kalla kowa ba. Kamar munafuka sum-sum na koma kusa da Mama balki na zauna kaina a ƙasa. Har aka gaisa aka gama ban sake kallon kowa ba. Sai da Abba yace nazo na amshi yaran a hannunsa zasu tashi sannan na miƙe dan dole. Koda naje sai ya bani ɗaya wai na bari zai tayani da ɗaya. Ya zanyi dole na bisa a yanda yake so muka fito a falon dan na ƙara fahimtar yana matuƙar son yara. Kamar an saita sai ga su Fahad da mai hoto. Ai kawai taremu sukai mu tsaya a mana hoto a haka. Yau dai naga takaina, dan dole na tsaya aka ɗaɗɗala mu babu ko kunyar taron mata dake cike da gidan nan ga su Abba Yaya Awwab ya rungumeni ni da Babys ɗin aka mana hoton nan. Ina samu wani ya amsa na nufi fecewa a wajen amma ya damƙe hannuna dole a haka muka fito har ƙofar gida. Sai da yaga matasan anguwa da abokan Abba dama magidantan sun zagaye motarsa sannan ya barni na koma ciki badan yaso ba. Naji daɗin hakan dan