Showing 384001 words to 387000 words out of 438336 words

Chapter 129 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2240

na fahimci take-takensa so yake ya gudu dani gida wai hayaniya namun yawa ga babynsa.
Cikin gidan na koma aka cigaba da hotuna. Sai ga yara na shigowa da labarin wai mijin Samraah da ƙaninsa (Hayatu) nata rabon kuɗi wa matasa da magidantan anguwa a ƙofar gida. Kamar wasa ana haka sai ga Hafizzullah da sukai kira a waya shima ya shigo shi da Fahad suka farama matan cikin gidan rabo. Zo kaga gyuɗa, wasu ma kaina sukazo sunayin gyuɗar ana zuba min kirari. Humm kuɗi! Kuɗi! Jama'a kuɗi dabbane. Badai zance komai ba, na bama kowa damar ya auna a cikin ransa kawai....

Suna kam dai Alhamdullah, dan yayi matuƙar armashi fiye da zato da tsammani. Dan daga ƙarshe dai su Maash basu tafi ba sai da akai sallar magrib muka tafi tare akan gobe in sha ALLAHU zamu dawo a gaisa sosai gobe idan ALLAH ya kaimu Yaya Musaddiq ya shigo sai mu shiga gwarzo. Badan naso ba na bisu muka tafi. Ni da shi a mota ɗaya ina jikinsa inata faman fushi an hanani kwana. Nan ko jikina harda su zazzaɓi abinda na jima banyi ba. Nasan wannan hayaniyar ce da daƙunar dana sha wajen mutane. Gwaggo Gudidi harda bani tofi nasha wai maganin baki. Ni har dariya ta bani dan har ɗaga rigata tayi ta shafe cikin da shi. Kafin mu isa gida nayi barci, sai kawai jinai kamar an ɗaukeni ana tafiya dani, sanda nake buɗe ido har mun iso falo gasu Ummie da kowa sai kawai na fuske naƙi buɗe ido dan bazan iya yarda na haɗa ido da kowa ba a wannan yanayin wlhy. Sai da ya shiga ɗaki dani ya dire a saman gado na buɗe idanuna. Tsayawa kawai yay a rankwafen yana kallona cikina ido, irin dama kin tashin nan ashe kikai likimo.
Kaina na kauda gefe ina murguɗa masa baki. Sai ya saka hannu ya dawo da fuskar yanda take cikin ɗage gira da motsa lips kaɗan ya ce, “Naga wannan”.
Zanyi magana kawai ya rufen baki ruff da nashi. Daga haka salon wasan ya canja sai tsintar kaina nayi a ruwan wanka. Ai ban sake cewa komai ba dan nasan dai da gudunmawata akaje inda akaje ɗin....

Washe gari ɗan zazzaɓin dana tashi da shi yasa na tashi a kasalance. Da ƙyar na iya taimakawa Falaq da Ummie da Mama balki mukai break fast, duk da Yaya Hayat yace mu bari za'ai order muka ƙi, sai da muka kusa kammalawa sai kuma gashi an kawo daga gidan Sheikh ma. To baiyi yawa ba, tunda dama akwai guards da securitys ɗin gidan, sai hakan yasa abincin ma ya sake wadatar mu sosai. Sai da akai zaman ci wasu ma sun fara sannan mai gayya da aiki ya fito. Dan barcin daya hanamu yi jiya yay ramuwa da safen bayan sun dawo daga jogging shi da su Hayatu. Da kayan barci ya fito jikinsa alamar ma ko wanka baiyi ba. Kujerar kusa da ni Fahad ya ja masa ya zauna. Batare da ya kalla kowa ba yace “Ummie, Mama good morning”.
Da kulawa suka amsa masa. Yayinda muma muka shiga gaishesa. A fakaice ya amsa mana sau ɗaya ya ɗauka tea ɗin gabana ya fara sha. Ummie ce tai magana tana kallonsa. “A'a Muhammad ya zaka shanye mata tea, ba gashi zata haɗa maka ba.”
Cikin langaɓe kai da marairaice murya ya ce, “Ummie yunwa. Rabona da abinci fa tun jiya da dare”.
Kanta ya ɗan girgiza da faɗin, “Ai laifinka ne. Ace mutum bazaicin abinci ba sai yunwa ta cimasa ciki ta cinye. Shiyyasa gaka nan ko ɗan tumbin nan na matasa bakayi sai uban ƙirji kamar zaki. Ni Ulser ma nake tsoritar maka”.
“Humm Ummie ai ta jima da kamashi fa”.
Cewar Hayat cikin damuwa. Hararar Hayat ɗin ya ɗan yi da ɗaukar tea spoon ya jefa masa. Sai ko a saman kansa. Dafe wajen yay da faɗin, “Ummie shike nan ya fasa miki kan ɗa”. Yanda Hayatun yay maganar da yanda Ummie taima Maash ɗin daƙuwa da jifa masa tea spoon ɗin itama ya cafe yasa muka hau dariya. Sai da ya ɗan harare mu musamman su Fahad sannan muka gimtse. Sai Ummie da Mama ke kayarsu da su babu damar a hanasu dai. Haka dai muka ci abincin cike da nishaɗi, yaƙi yarda na zuba masa wani dole a plat ɗaya muka ci ni da shi. Duk da bama wani na kirki yaci ba, shine ya fara tashi wai ya ƙoshi. Duk lallaɓawar da Ummie ta masa sai ya marairaice wai a hakan ma yayi over feeding cikinsa zai fashe. Ni tausayi ma ya fara bani, na fara jin ya kamata likita ya dubashi ko hanjin nasa sun naɗe ne shin. Falo ya ɗan zauna har lokacin da muka fara kammalawa muma. Kafin ya tashi ya sake komawa bedroom ɗin namu. Muma bamu zauna a falon ba kowa ya tafi ɗakinsa domin kimtsawa. Dan Yaya Hayat yace fita zamuyi mu dukanmu....

💢🌟⭐🌟💢

“K yanzu kina ganin wannan kukan zai fisheki Jalilah? Tun fa jiya kike abu ɗaya bayan na kwana takwas da suka wuce. A gabanki kuma likita ya sanar mana idan fa baki nutsu ba zaki iya yanke jiki ki faɗi ƙarshe da paralysis ce.”
Hawayen da suka cika idon Mom ɗin ne suka sake sakkowa a guje. Bata iya ta share ba. Sai magana data farama mahaifiyarta muryarta na sarƙewa. “Umma yaya kike son nayi, miya rage mun idan ba kukan ba. Ki duba fa ki gani komai neman ƙwacewa yake yi kamar a mafarki. Mun gagara samun mahaifar shegiyar yarinyar can ƴar ƙauye amma tazo ta addabemu. Tsabar munafunci mun rasa a ina tsohuwar can takai ta bizne. Muna ji muna gani munga samu munga rashi. Bamu gama fita a wannan magagin ba sai ga wannan shegiyar yarinyar. Kiga fa, ƙamshinta ma kawai abin firgitarwar ne a garemu. Ki kalla lass ɗin jikinta wlhy irin na miliyoyin kuɗin nan ne. Sarƙarta ta diamond ne Umma. Diamond da muke ji a labari, dan Gara zinare kanzo hannayenmu koda na ƙaramin kuɗi. Umma handbag ɗinta da mayafi da takalmar ƙafarta ba kannanun kayan kuɗi bane. Ga ciki a jikinta, kiga yanda yaron nan ke mata kamar ita kaɗaice mace a duniya ko kunyar uwarsa baya ji kai tsaye yake nuna mata kulawa da tattali. Itama uwar kuma ko'a jikinta ko irin ɗan kishin nan na uwar miji babu a tattare da ita. Ƙamshin turarenta kawai ka shaƙa kasan irin na manyan turaren nan ne da talaka sai dai yaga hoton kwalayensu a net idan yay searching. Why Umma why hakan ta kasance ne? Umma Baby da Bibaa na naima tanaji da fatan irin wannan rayuwar ba sakaran yarinyar nan da ko hasken kirki na fata bata da shi ba. Ina ganin Mansoor yafi ƙarfinta ashe wanda ya takesa ya shanye ne zai maye gurbinsa. Umma taya hankalina zai kwanta ni ko sanin inda tawa ƴar take banyi ba ma. Ga Abbas na hannun ƴan sanda. Gaba ɗaya Imam bai damu damu ba yanzu. Yanda yake rawar jiki akan ƴaƴan nan da aka haifa masa sai ki ɗauka ba'a taɓa masa haihuwa a gidan nan ba. Umma wlhy ji nake kamar na kashe kaina na huta kawai da ganin wannan baƙin cikin. Wai waɗanda ke ƙasan ƙasan ƙafafuna, na fisu da komai na rayuwa a da sune suke kokawa da turareniyar hayewa can sama ƙololuwar ƙurewa suna shirya alamomin zubar da ni da mun ɗagawa. Kamar ni Jalilah Ummie. Ni ɗin nan dai Jalilarki......”
Kuka mai ƙarfi ya sake sarƙeta. Kamota Umma tayi jikinta ta rungume itama idanun nata cike da hawaye. Dan abinda ƴar tata ta faɗa duk gaskiya ne. Ita kanta dauriya kawai take ta manya amma jiya ko wani barcin kirki batayi ba saboda tunani da damuwa. Zuwan yarinyar nan Samraah ba ƙaramin hargitsa musu lissafi yayi ba. Ga lissafin Halime da basu gama ba. Ganin wanene ai nahin Maash ɗin a zahiri yau ba hoto ba, da yanda ya dinga ɓarin kuɗi kamar ba nemansu yake da wahala ba ya sa komai ya ƙwace mata ma. Ga yarinyar da ciki itama, idan ta haifi Namiji fa shike nan ta gama mallakar komai. Har zuwa yau da safe ta gagara komawa dai-dai yanda ya kamata........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_



*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._


......A tsare motocin da muke ciki suke tafiya saman titi tamkar an zana su. Duk ta inda muka gitta sai kaga idon mutane na binmu. Ni dai ina kwance a jikinsa ina game da waya yana kallona hannunsa a saman cikina yana shafawa. Jakin babangida da muka ɗan hau ya sa na cije baki da miƙewa zaune da ƙyau saboda motsin da cikina yaya babu shiri, ƙoƙarin tambayata yake lafiya ni kuma hankalina nakan mai agwalina dake bakin titi cike da barrow da idona ya hango min. Har mun ɗan gota nace ma TJ ya tsaya. Tsayawar kuwa yayi, ni kuma na kalla ogan nasa daya zuba min ido. Batare da damuwa ba na ce, “Ya Awwab Please bara na sayi Agwalima ɗin can”. Nai maganar ina zaro 1k a handbag ɗina. Ƙoƙarin buɗe ƙofar motar nake ya riƙo hannuna. A marairaice na juyo na kallesa kamar zanyi kuka. Baice komai ba ya ɗauke kansa tare da sakin hannuna ya buɗe side ɗin da yake ya fita. Cikin rawar jiki TJ ya fita shima yana faɗin ya bari ya sayo amma ya ɗaga masa hannu. Hakama Hayat da su Fahad ganin ya fito duk suka fito suma amma sai bai kalla kowa a cikinsu ba ya tsallaka wajen mai agwalima ɗin. Tashin bal, gaba ɗaya mutane sun zuba masa ido musamman ganin yanda yaje gaban mai agwalima ya tsaya. Shi kansa mai agwalima duk ya rikice dan duk wanda dai ya kalla wannan ɗan gayen yasan baiyi kalar shan abun titi irin wannan ba, barema wai agwalima. Hannu ya bama mai agwalima alamar busabaha. Jikinsa na rawa ya waro idanunsa waje zai ɓoye hannun, amma sai bai damuba ya riƙo hannun nasa shi kuma. Cikin dakewar nan tasa da silent voice ga hausa bai cika ba ya ce, “Ina son shi duka saka a leda”.
“Agwalima ɗin ranka ya daɗe?”.
Mai agwalima ya faɗa cikin waro idanunsa waje fiye da ɗazun. Cikin halin ko'in kula ya jinjina masa kai. Sake ruɗewa mai agwalima yayi ya shiga kwasheta yana zubawa a bako. Yayinda masu wayoyi aka samu abin ɗauka kasancewar wani ya ambaci sunan Maash ɗin a wajen. Yana gamawa ya laluba aljihun farar shaddarsa da yau ma Samraah ta dage sai ya saka ya zaro kuɗi. Bai wani damu da dubawa ba ya ajiyema mai agwalima ya ɗauka bako ɗin zai wuce. Cikin sauri TJ da Hayat, Fahad, Hafizzullah suka zo dan su amsa amma nan ma ya hanasu sai da ya kawota har mota ya saka a sit ɗin gaba ya cira guda biyu ya buɗe side da nake ya ɗauka roban ruwa ɗaya ni dai ina binsa da kallo kamar wata sakara ya wanke a gwalimar fes sannan ya miƙo min.
Kasa koda motsawa nayi, sai idanuna na ne da suka cika da hawaye ke binsa da kallo, ɗan duƙowa yay ya hure min idanun tare da kamo hannuna ya ɗaura a gwalimar sanan ya rufe murfin ya zagaya nasa side ya shiga. TJ na gama rufewa na faɗa jikinsa kawai na ƙanƙamesa hawayen da nake riƙewa na gangaro min. Ku gane bawai yayi abinda maza da yawa bazasu iya bane ba ko basu taɓa yi ba, kawai dole ne abin ya bani shock musamman da na sani kuma da kuke biye da labarin nan kuka sani Maash yayi makamancin hakan abun mamaki ne.
“Shagwaɓa ba”.
Naji saukar soft muryarsa cikin kunnena dai-dai yana ɗagoni zaune da ƙyau. Ɗagowa nai na kallesa idanuna na sake cika da hawayen zanyi magana. Kansa ya girgiza min tare da kai yatsarsa ya ɗauke hawayen. Sai kuma ya ɗago hannuna dake ɗauke da agwaliman ya ce, “Ya ake ci?”.
Murmushi na sakar masa ina ɗan langaɓe kai na ce, “Bafa ci ake ba sha, bari ka gani”.
Ban jira amsarsa ba na luguyguyta agwalima ɗin yay ruwa sannan na sha shi, wani irin lumshe idanu nayi dan jinai tamun daɗi fiye da koyaushe. Jin an riƙo hannuna yasa na buɗe idanun, kan bakinsa ya kai agwalimar dana sha ɗin shima ya sha. Da sauri ya saki hannun nawa yana dafe bakinsa. Cikin ɗan waro idanu na ce, “Miya faru?”.
“Tsami”.
Ya faɗa fuska a yamutse kamar zai fasa ihu.
Bamma san dariya ya kwace min ba. Sai da ya dungure min kai yana faɗin, “Mugunta ba”. Sannan na tsagaita. A haka muka iso gidan Abba. Tarba muka samu fiye data jiya. Dan yau iya danginmune kawai sai na Aunty Halima amaryar Abba dake shirin tafiya gida, dan har suyar namansu sun kusa kammalawa. Cike da farin ciki auta yazo ya ƙadandaneni harda kukansa yana faɗa min yayi missing ɗina, miyyasa na tafi na barsa Bibaa nata dukansa. Bata masa homework bata masa wanka. Murmushi nayi ina mai lallashinsa, na kalla Bibaa da tai sumar tsaye kawai tana kallonmu. Hannunta na kamo itama na rungumeta a jikina. A mamakin kowa sai kawai ta saki kuka da babu wanda yasan dalilinsa.
Haka dai bayan an nutsu a falon baƙi iya manyan damu aka gaggaisa ni da Falaq muka fito, dama su Fahad basu shigo ba suna ɗakin Yaya Musaddiq abinsu. Sashen Mom muka shiga gaisheta. Dan tunda ta fito taga mune ta koma. Tana kwance a kujera ta juya ma ƙofa baya. Koda muka gaisheta Ummanta ta amsa wai barci take. Dariyama abin ya bani ni kam. Dan na fahimci bata san na ganta ne kawai, alhalin sanda muke shigowa suka fito suma, daga baya ne suka koma dakin. Ban wani damu ba muka fito. Sashen Aunty Halima muka shiga. Nan ne kam muka baje anata shan hira har ƙanwar mijin Aunty Zakiyya da tai min ƙunshi biki tai mana ƙunshi ni da Aunty Falaq. Sai ga Hafizzullah ya shigo da waya a hannu ya nuna mana wai mutane sun yi video ɗazun wajen sayen agwalimar da Yaya Awwab yayi gashi nan yanata tranding anata comments. Ni abun ma sai ya bani mamaki irin wannan rashin aikinyi haka har ina. Kowa yaji da sabgar gidansa amma sun zauna damuwa da abinda bai shafesu ba. Wannan nunawa ta Hafiz tasa ƴan uwa da basu san abinda ke faruwa ba suma duk suka gani. Nanfa abokan wasa suka tasani da shaƙiyanci aunty Falaq na kare ni da Aunty Halima.
Sosai kasancewa a gidan Abba yau ta sakamu a farin ciki, bayan sallar azhar sai ga Yaya Musaddiq ya iso. Fahad da Hafizzullah sunje airport sun ɗakkosa. Sosai gidan ya sake rikicewa da farin ciki, sai lokacin ma nasan ashe su Yaya Awwab meeting sukayi akan batun auren Yaya Musaddiq ɗin. Shi Abba da bai san Yaya Musaddiq nada budurwa ba yace ya bashi Bibaa. Sai da Yaya Musaddiq ya iso aka tambayesa kafin a sanar masa batun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login