Showing 270001 words to 273000 words out of 438336 words

Chapter 91 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2135

da tafiyata caraf aka cafke hannuna. Ƙin juyawa nai na kallesa. Sai dai ban ƙwace hannuna ba daga riƙon da yay min. Munfi sakan goma a haka shi bai sakeni ba shi baice komai ba. Jinai wani takaici ya sake kume mun zuciya, sai nai ƙoƙarin jan hannun nawa. Sake riƙeni yay da ƙyau, tare da matsoni jikinsa ya juyoni gaba ɗaya na muna fuskantar juna. Ban yarda na kallesa ba, ban kuma ce da shi komai ba. Sai kawai ya ƙarasa jawoni jikin nasa ya rungume. A kusan tare ni da shi muka saki ajiyar zukata, kafin ya dagoni fuskata a cikin tafukan hannunsa duka biyu.
“Yau ba magana ne?”.
Ya faɗa da soft murya kuma can ƙasa da ni kaina dan yana a kusa dani ne na jisa. Ban kallensan ba, ban kuma ce komai ba sai kafaɗa dana maƙe masa.
“Oh! Why?”.
Sai da na ɗan murguɗa baki sannan nace, “Ai kaima baka yi ba”.
“Uhhmyim. Dan banyi ba sai kema ba zakiyi ba?”.
Kaina na jinjina masa alamar eh.
“Humm Aku na ta zama kurma kenan yau?”.
“Ni dai ba Aku bane”.
“To miye? Banan kike cika mana kunni da surutu ba ke a dole ƴar jarida”.
Farr nai da idanuna, tare da ɗan jujjuyasu, sannan na ɗan murguɗa baki na ce, “Kaima ai shaida ne tunda na karya maka record. Ko nayi ƙarya”. Na ƙare maganar ina waro masa idanuna sosai.
Maimakon ya tanka sai kawai ya saki murmushi, tare da kissing idanun nawa. Kunya ce ta kamani kuma. Dan haka nayi yunƙurin kwace fuskata amma yaƙi barina. Dole na haƙura amma na rufe idanuna naƙi yarda na sake kallonsa. Sai dai kuma shi ina cigaba da jin tasirin idanunsa a kaina sosai. Ganin bashi da niyyar barina a shagwaɓe na ce, “Gashi can za'a shiga salla fa”.
Tamkar wanda na dawo a hayyacinsa ya furzar da wani irin nannauyan numfashi. Sai kuma ya saki mun fuska a hankali. Jin kamar ba hanyar fita yayi ba na buɗe idanuna. Sai na hangosa zai shige bathroom. Mamaki hakan ya bani, sai dai bance komai ba na tsaya a wajen, babu jimawa kuwa sai gashi ya fito da alama alwala ya ɗauro. Har ya gittani zai wuce sai kuma ya ɗan dawo baya. Dawowar tasa ya sani ɗagowa na kallesa. Dai-dai da ya kawo fuskarsa gab da tawa, dan haka a bazata naji saukar sumba a saman goshina. Kafin ma nayi wani yunƙuri ya fice a binsa. Bamma san sanda na saki murmushi ba da kai hannu na shafi lips ɗina da goshina a hankali. Kasan raina kuma ina dariyar al'awar da ya sake, wato mutumin nan ja... Humm bari dai nayi shiru kada danginsa su min ca..

(Kin taimaki kanki kuwa, dan ba barinki zamuyi ba😎😌.)

Fitowarsa ya saka su TJ masu jagorantar companyn nan dake shigo da kwalayen kayan aikinsu rissinawa suna gaishesa. Kallonsu kawai yake batare daya amsa musu ba. Dan haka Shu'aibu ya fara masa bayanin cewa Hayatu ne ya turo companyn ya kuma kira su akan su sami Aunty ta basu izinin shiga da kayan. Shine yanzu da zata shiga suka sanar mata ta basu izini.. maimakon ya amsa musu bayanin da sukai masan sai ya ɗauke kai tamkar ma bai ji bayanin ba. Takunsa ya cigaba dayi cike da bajinta da mazantaka. Sai da yaje gaf da fita a daƙilen nan nasa ya furta, “Ina fatan dai kunyi salla? Su kuma aikinsu ya koma ta back door”.
Daga haka ya ficewarsa. Sanin basuyin ba ya sasu ajiye aiki suka bar wanda ba musulmai ba. Amma kamar yanda yay umarnin komawarsu ta back door sai suka kulle ƙofar tanan nan falo suka koma ta can ƙofar baya ta kitchen ɗin.....

❤️‍🔥❤️‍🔥💦❤️‍🔥❤️‍🔥

Jigatuwa iya jigatuwa Baby tayi, dan bata tashi farkawa ba sai a hannu Doctors. Su kansu likitocin ma firgitata sukayi. Dan daga ganinsu kaga irin manyan gawurtattun ƴan iskan turawan nan da akafi gani a cikin films matsayin criminals. Illahirin jikinsu ne tattoo baƙi da jaa. Ga wasu irin yan iskan abubuwa kamar stones sun manna a fuska harda haƙora babu ƙyan gani. Sun kuma irin zama ɓarka-ɓarka ɗin nan saboda workout. Idanunsu kam harda kwalli ga ƴan kunne. Kai tako ina dai basu da ƙyan gani. Tana ji tana gani sukai treatment ɗinta. Ba wannan ya tada mata hankali kawai ba. Sai da nishi ya isheta ta waiga ta gefenta kasancewar ko iya zama batayi sai kwance rigingine sai kawai tayi tozali da mijin nata na aikata irin abinda ya aikata da ita da ɗaya daga cikin yan iskan dake a kanta matsayin likitoci. Wani irin uhun tashin hankali ta saki. Sai dai a mamakinta ko'a jikinsu kamarma basu jita ba harkokin gabansu suke, sai wasunsu ne ma da suka kwashe da dariya. Haka ta dinga musu ihun kuka tana zaginsu da Hausa da turanci, tare da tsine musu ta uwa ta uba tana kiransu ƴan wuta.
Oho ita tama san mi take faɗa, dan hatta turancin nata babu alamar suna ganewa. (A Nigeria kuma sune wayayyu ma'iya turanci😝🤣). Haka sukai kunnen uwar shegu da ita har suka gama hidimarsu sannan suka fice suka barta a ɗakin ita kaɗai sai mijin nata daya shiga wanka shi da ƙaton da suka gama aikata alfasha. Tana nan tana cigaba da cin kukanta suka fito riƙe da juna kamar wasu mata da miji. Sai kawai taji numfashinta ma na neman ɗaukewa. Dan duk iskancinta da ƙarancin rashin ilimi tasan wannan aiki ya ƙazanta........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_


.......Wato jama'a kuɗi! Kuɗi! Kuɗi!! Humm dole ma musha wahala akan kuɗi wlhy. Yo duk in kana son abu a rayuwarnan a yi maka shi tamkar ƙyaftawar idanu tofa lallai sai da kuɗi. Shiyyasa gasu nan sun zame mana masifar rayuwa. Talaka da baida su yafi kowa shan wahalar rayuwar. Karna dai cikaku da surutu. Ba komai ya sani muku sambatun nan ba sai da na fito ganin kitchen ɗin da aka shirya cikin abinda bai gaza awa uku ba. Tsaff an gama shirya duk wani abinda za'a buƙata a cikinsa kalar kitchen cabinet ɗin. Tuni ya canja kamar bashi ba a ɗazun tsurarsa sai cabinet. Ban sake tsinkewa ba sai da na shiga cikin store naga yanda aka ajiye wasu extra kayan aikin iri daban-daban. “Tab ɗin, ALLAH dai ya gafarta mana to. Ya bama kowa halalinsa ya kuma bamu tsahon ran mora da neman lahirarmu a cikin duniyarmu”.
Na fito inata ƙara jinjina al'amarin na sameshi a falon da alama shigowarsa kenan. Dan tun fita massalaci sallar la'asar bai dawo ba sai yanzu da ake shirin gab da magriba. Cike da ɗauki na ƙarasa inda yake na zauna ta kujerar gefen. Duk da kunyar yanda ya wani zuba min idanunsa nake yi haka na fuske abina.
“Hummm Yaa Awwab kaga kuwa yanda suka maida kitchen ɗin nan? Tab ɗin jan aljannar duniya. ALLAH yanda kasan mutum ya koma can ya saka gado kawai ace canne ɗakinsa. Gaskiya mutanen nan sun iya aiki tabb”.
“Shi kuma wannan bakin ya iya surutu”.
Ya faɗa yana wani lumshe idanu da buɗewa tamkar wanda ya sha yay marisa. Ɓata fuska nayi tare da tunzura bakin na ce, “Namayi fushi, dama ka samu nake baka labari ko”. Na tashi fuuu zan gudu. Ji nai kawai an fisgoni, sai gani daɓar a saman cinyarsa. Ƙoƙarin ƙwace kaina na shiga yi ina kukan taɓara da faɗin, “Ni ka barni babu ruwana da kai. Kowa yay sabgarsa, ni wajen Ummiena ma zan koma”.
Tsam ya matseni a jikinsa yana mai cusa fuskarsa a gefen wuyana. Yayinda numfashinsa ke shiga cikin kunnena da sautin dan murmushinsa. Ban fasa yunƙurin sauka a jikin nasa ba har sai da ya ɗan cizar min kunne, gaba ɗayana na naɗe masa jiki tare da sakin ƴar ƙara, a shagwaɓe na ce, “Wayyo Ummie King zai cire min kunni. ALLAH ni bazan yarda ba sai na rama cizona”. Na faɗa ina mai hayewa jikin nasa gaba ɗaya nima na shiga kokawar laluben kunnensa ni a dole saina ciza..
“Oh my god, yarinyar nan baki son zaman lafiya sam”. Ya faɗa kamar zai saki kuka yana kare kunnensa duka biyu da hannayensa. Oho bamma nuna na jisa ba, na shiga cigaba da ƙoƙarin zame hannunsa da hannu ɗaya, ɗayan na kaisa gefen cikinsa ina mintsina. Hannunsa ɗaya dake a saman kunnen ya cire yana ƙoƙarin buge nawa dake mintsininsa. Ai ko sai na samu caraf na cafke kunnen. Kaɗan na ciza amma mutumin nan ya wani saki ƴar ƙara da faɗin, “Ouchhh! Ummie kunnina, tiger ta ciresa”.
Sosai na ƙyalkyale da dariya. Na yunƙura zan gudu ina faɗin, “Sai tsoro ga jan faɗa”. Caraf ya riƙoni yana ɓata fuska. Marairaice tawa fuskar nayi kamar zanyi kuka na ce, “Ayya Yaa Awwab ayya!. Nifa ƴar ƙararrama ce kar kace zaka rama”. Harara ya zuba min yana sake ɓata fuska da murza kunnensa da hannu alamar har yanzu yana masa zafi ko kuma shagwaɓa ce ta motsa abinka da Ajebota. Ganin yanda ya zuba min idanunsan nan na maguna kamar zai cinyeni da su, ga fuskarsa babu alamar fara'a ya sani sake narairaicewa. “Na tub...”
“Shii!!!” ya katseni yana sake ƙanƙance idanun da shanyesu kamar mai jin barci. Sai kuma ya ɗan yamutse fuskar da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Sai fa na rama”.
“Mi ɗin?”.
Na faɗa cikin waro idanuna. Hararata ya ɗan yi, da sake matso da fuskata gab da tashi, sosai na sake waro idanun da marairaice fuska zanyi magana a hankali ya wani irin sauke small pinkish lips ɗinsa a kan nawa. A salon daya cafka lips ɗin nawa yasa bamma san na ƙanƙamesa ba.....
“Yau na shiga uku! Mizan gani haka ni Nafisatu Adams”.
A bazata muka ji saukar muryar Hajiya Mammah a saman kammu. Kici-kicin ƙwace kaina na shiga yi duk da shi bashi da niyyar yin hakan kuma sarai yaji abinda naji. Amma bawan ALLAHn nan sai ya wani sake matseni da komawa wani irin salo na taƙadarin namiji da sam babu ɓarɓashin kunya tattare da idanunsa. Ina jin ta sake saka salati har muryarta na rawa...

Ba muryar Hajiya Mammah ba hatta jikinta rawa yake yi. Ba komai ya firgitata ba sai ganin ko kallo bata ishi Maash ɗin ba ma. Sai ma wani sabon salan iskanci da yake yi a jikin Samraah ɗin. Duk da iskancin ɗan iska akwai a inda idan akai wani iskancin shi da kansa kunyar kansa da kansa yake. Dan haka Hajiya Mammah taga abinda zai tsiyayar mata da idanun ganinta batama san lokacin da tai wufff ta fice waje ba jikinta na ɓari, mamaki ma take wai yaushe Maash ɗin yay irin wannan fitsarewar ne? Dama yaron nan bayan iya wulaƙanci da raini ma mutane tantirin ɗan hau ne?. Ai ko baiji kumyar kansa ba ya tuna ita ɗin yayar ubansa take fa... Fuuu-fuuuu take wucewa kamar wadda ake controlling da remote. Ko kallon masu gaisheta batayi ta afka ɗakinta ta kulle kanta. Jingina tayi da murfin ƙofar tana sauke numfashi a gwagwgwame. Ita wannan yaron zaima tantiranci haka? Daga ta nuna masa hanya shike nan abu na neman zama bala'i. Tayi barazana wa hukuma amma ko'a jikinsa ma. Hasalima sai ya bita yana gasa mata magana. (Yi baga yarinyar ba ma ɗazun ta gasa miki) wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata. Tab ɗin jan, babbar magana ɗan sanda yaga gawar soja. Shin ko dai bayan abin farko ya faru yaron nan zuwa yay ya zagaye aka ɗaura masa aure da yarinyar nan? Yo inba auren ba taya za'ai ma wai a dinga wannan kwamacalar ne haka. Ko ƴar iskar yarinyar nan dai dama ta saba da harkar nan ita ke ƙara kanainayesa. Ko kuma ta masa barazana idan bai cigaba da mata ba zata tona shi. Kai yafa kamata su dawo cikin hankalinsu...
Laluben waya ta shiga yi, cikin Sa'a kuwa ta samota a aljihun doguwar rigarta. Har rawa jikinta yake wajen son kiran Baba prof. Sai dai har ta yanke ba'a ɗaga ba. Kiran ta sake yi nan ma shiru. Sai kawai ta tura masa saƙo tasan dai idan ya gani zai kirata. Daga haka taja ƙafafunta da ƙyar zuwa kan sofa ta zauna ta zabga tagumi. Iskancin Maash na mata kai-kawo a cikin idanu da ba shegiyar yarinyar nan mai kama da afiruwa.....

🌿✨🌿✨🌿

Ram jami'an tsaron Dubai sukayi da Mansoor batare da bashi damar yin wata magana ba wai sai a office. Duk yanda yake son kare kansa da tabbatar musu gaskiyar al'amari sunƙi saurarensa. Sai ma tabbatar masa da sukai duk da abinda ya faɗa shine zai zama hujja garesa a wajen alƙali a court. Yana ji yana gani kuwa suka sakayashi a cikin cell cikin manyan criminals.. Abin kamar wani wasa sai gashi kusan sati uku shi ba'a kaisa court ɗin ba, ba kuma a yarda an samar masa da lawyer ba. Sun kuma hanashi neman kowa a waya dan dama sun amshe tasa a hannunsu. Sannan ko buga wayar cikin station da suke da ita sun hanashi wannan damar. Ganin tun komai zai iya zama labari amma ya gagara zaman ya fara tada ma Mansoor hankalinsa. Ance duk wanda yabar gida gida zai barsa, to lallai hakance ta fara faruwa da al'amarin sa. Dan kuwa gadai shi cikin masifar rayuwa da yake kallonta ba komai ba a farko amma rashin wani nashi da zai san halin da yake ciki na neman dulmiya rayuwarsa a masifar da babu wanda yasan iya ina zata tsaya kuma. Iyaye ba wasa ba, ko da ɗan iska zaka zama idan da albarkar iyaye wlhy kafin cin ribar iskancin (🤷idan har masuyi na ganin akwai ribar a ciki fa kenan. Dan kar ace Bilyn Abdull tace iskancin akwai riba da albarkar iyaye bance ba😂😵). A ranar cikarsa wata guda suka fara kaisa kotu, musawar da yay a zama na farko da dagewa akan shi bai aikata abinda ake tuhumarsa da shi ba yasa aka ɗage Shari'a aka miƙashi ajiya prison. Cikin amincin UBANGIJI a wannan zama wata baiwar ALLAH ƴar Nigeria taci karo da shiri'ar. Haka kawai tun a ganin Mansoor ɗin ta fahimci lallai akwai lauje cikin naɗi, sannan kishin juna na baƙin fatar da kasancewarsa ɗan ƙasarta ya sata shiga da fita har sai da ta samu damar ganinsa a prison ɗin bayan kwana biyar. Da yake akwai ilimi sai da ta samu nasarar yin hakan.....

💞⭐💞⭐💞

Duk yanda naso kuɓuta daga hannunsa a wannan gaɓar bai bani wannan damar ba sam. Sosai hankalina ya tashi da tsoron kar wani ya sake shigowa ya samemu a wannan halin kamar yanda Hajiya Mammah ɗin tayi. Amma bawan ALLAHn nan ko'a kwalar rigarsa bidirinsa yake yi. Sai da yayi yanda yake so sanan ya barni tare da rungumeni tsam-tsam a jikinsa. Duk da nima riƙen nake da shi fatana ya sakeni na sauka a jikin nasa. Amma bashi da niyyar hakan. Da ƙyar nayi ƙarfin halin fisgo furucin dake bakina na furta, “Yaya Hajiya Mammah fa”.
Ya jima shiru babu alamar yama ji mina faɗa, dan har na fidda rai da samun amsa ko samun damar barina sai naji a hankali ya fara sassauta min riƙon. Sai da na fara murnar zan samu dama na tashi sai naji muryarsa da tai matuƙar shaƙewa can ƙasan maƙoshi a cikin kunnena.
“Waye ita?”.
Tsabar mamakin mutumin nan bamma san na manta da wata aba kunya ba na ɗago manyan idanuna da suka gama shigewa ciki suka canja launi na zuba masa. Cikin suɓutar baki na ce, “Hajiya Mammah ɗin?”.
Fuskarsa a yamutse ya ɗaga min kai alamar eh. (Mutumin nan zai kasheni da halinsa) na faɗa a zuciyata ina mai ƙura masa ido. A zahiri kam sai na yunƙura kawai zan sauka daga jikinsa. Amma sai ya hana hakan, sai ma a ɗan kausashe da daƙilalliyar muryar nan tasa da ke fita so silent ya furta, “Idan kika tashi ALLAH sai na ɗauke ki naje da ke har cikin ɗakin barcinta na miki abinda yafi wanda ta gani ɗin. Idan kuma baki yarda ba bissmillah”.
Sosai na saki baki da hanci da idanu dama gangar jiki duka ina kallonsa uwa wata saƙago. Yako wani kashe min ido ɗaya da shegen salonsa na manyan shegun yara da suka gogu da sanin duniya. Ni sai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login