Showing 210001 words to 213000 words out of 438336 words
Hajiya Ƙarama kuma? Idan na fahimta dai Hajiya Ƙarama na waya da Madam ne a farko, matar data ɗakko Samraah daga Abuja zuwa Lagos. Tab ɗin babbar magana. Ashe ita ɗin musulma ce shine tai ridda. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Anya wannan duniya kuwa. ALLAH mun tuba badan halinmu ba😭🙏._
__________________
*_THREE DAYS LATER_*
Kwanaki uku kenan da faruwar komai. Sam Maash yaƙi yarda ya zauna da family ɗin nasa akan batun Samraah. Dan haka ran kowa a matuƙar ɓace yake. Amma shi ko'a jikinsa sai manna musu hauka kawai yake. Dan gaba ɗaya ma ya maida hankalinsa ne akan binciken yanda akai containers ɗin companyn sa suka ɗiba yara da wiwi saɓanin lodin kayan abinci. Dan suna shirin tunkarar Mr Paul ne da ƙarfinsu a court saboda sun shigar da ƙara ne kafin shi bisa shawarar lawyers ɗinsu.
Ta gefe kuma ga jikin Ummie da ya rikice. Ga kuma Samraah dake asibiti har yanzu ba'a sallamota ba itama, sai dai wata irin kulawa take samu ta musamman da tattali a wajen Hajiya ƙarama har Mama Balki ta fara shan jinin jikinta. Sai dai abinda Mama Balki bata sani ba ita kanta Samraah nazartar Hajiya ƙarama take sannu a hankali. Gefe kuma tana kaima ALLAH kukanta. Koda labari Mama Balki bata sanar mata da ciwon Ummie ba sai yau da Falak tai kiran wayar Mama Balkin, a lokacin ita kuma ta ɗan fita dan haka Samraah ta ɗaga. Har yanzu basu taɓa haɗuwa da Falak ba sai dai tana cin abincin gidanta kullum. Bata da lafiya ne tana fama da tsohon ciki shiyyasa bata zo tama dubata ba, sai dai sun gaisa ta waya har kusan sau uku. Yanzun ma sun gaisa cike da kulawa ma juna tamkar dama can sun san junan nasu, kafin Samraah ta sanar mata Mama ta ɗan fita ne, amma idan ta dawo zata faɗa mata sai ta ƙara kira.
Daga can Falak tai murmushi da faɗin, “Okay ba damuwa ALLAH ya ƙara lafiya, dama zanji ko yaya jikin Ummie ne dan na kira Yaya Hayat ashe garin sauri yama bar phone ɗin a gida, gashi yanda ya fita a hargitse duk na kasa nutsuwa”.
Ɗan jimmm nayi zuciyata na bugawa da sauri-sauri jin ta ambaci Ummie, da ƙyar na iya tambayarta “Ummien Maash Mansion? Wani abu ne ya sameta?”.
Batare data fahimci kan tambayar ba cikin damuwa muryarta na rawa ta ce, “Eh ita, kin san kwana biyun nan jikin nata duk babu daɗi, to yau dai da alama ya tsananta ne dan shima Yaya Hayat a rikice ya fita TJ ya kirashi. Wlhy ina tausayawa Ummie, da ace inada wata babbar dama akan baiwar ALLAHr nan abinda zan farayi shine tsayawa akan samun lafiyarta, amma muna gani an hanamu taimakonta. Wanda keda ƙarfin yin hakan kuma an kulle masa tunani gaba ɗaya, dan wlhy da ace Yaya Awwab basu shiga tsakaninsa da lafiyar baiwar ALLAHr nan ba da kowama yaci ubansa, ai sun san shi ɗin ba kanwar lasa bane har Baba prof ɗin da Paah ba iya tankwarashi suke ba. Amma ba komai ALLAH yana nan, watarana sai labari”.
Tuni ma ni ba fahimtar zantukanta nake da ƙyau ba, rawa sosai jikina ke mun, ga hawaye suna bala'in gudu a saman fuskata. Ashe shiyyasa duk jiya bai zo asibitin ba, yau ma haka. Ko Hayatu mai ƙoƙarin zuwa sama da sau uku yana kawo musu abubuwa jiya sai dare ya shigo ya duba ta. Abinci ma TJ ne ke kawowa. Amma Maash tun daren shekaran jiya da zai tafi take cemasa ya dinga duba mata Ummie da bata abinci bai sake zuwa ba, harta ƙullacesa ma ita da, da tunanin ya gama cin moriyat ganga zai yada kwautrnta, ashe abinda ke faruwa kenan...
“Ya subahanallah Samraah! Wani abu ke miki ciwo ne? Ko tashi kikayi da ƙarfi kika fama ciwon?”.
Mama Balki ce mai maganar nan a rikice. Ɗagowa nayi ina kuka mai tsanani dan shashshekar da nake tasa har fisga numfashina keyi. Lallashina Mama Balki ta shiga yi tare da bani ruwa tace nasha. Da ƙyar na amsa nai maƙwarwa uku, jikinta ta jawoni ta rungume, hakan sai ya taimaka min wajen samun nutsuwa na fara sassauta kukan. Kaina na a saman cinyarta tana shafa gashina ta ce, “Samraah”.
Cikin dasashjiyar muryata na amsa mata da, “Na'am Mama”.
“Mike faruwa?”.
Da ƙyar na iya danne kukan dake taho min na ce, “Mama Ummie. Ashe bata da lafiya amma shine babu wanda ya sanar min”.
Iska ta ɗan furzar cikin damuwa. Kafin ta ce, “Waye ta faɗa miki?”.
“Falak”.
Na bata amsa ina sharce hawaye.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
___________
......Kanta ta girgiza da faɗin, “Ni ban san sai yaushe bakin Falak zai iya dinga koyon shiru ba. Kiyi haƙuri an ɓoye miki ne saboda kema ga yanayin da kike ciki. Shekaran jiya ne Alhaji ƙarami ya shiga yana ƙoƙarin bata abinci shine fa kawai jikin ya rikice. Ta jimasa ciwo sosai a hannu da ƙyar aka iya fiddoshi a ɗakin, daga nan duk wanda ya shiga da duka take korosa, to yau kuma sai ta yanke jiki ta faɗi saboda kwana biyun nan bata ci bata sha rashin abinci jikinta yayi week. Amma ki kwantar da hankalinki zuwa yanzu sun ce Alhamdullah komai ya dai-daita. Dan Hayatu ma ya tabbatar min tana barci saboda drip ɗin da aketa ƙara mata.”
Duk da na ɗan ji nutsuwa sai da na sake sharce hawaye, ɗan shiru mukayi kafin a hankali nace, “Mama”.
Da kulawa ta amsa min da, “Na'am Samraah”.
“Mama a yanzu sai nake ganin kamar shi yafi dacewa ma abinda ke tare da shi ya rabu da shi kafin a samu nutsuwar yima Ummie magani. Duk da dai wani abu ya jima yana damuna. Yanzu duk kuɗinsa ace gidan nan babu cctv camaras tako ina?”.
“Tabbas gaskiya kika faɗa Samraah. Sai dai mun kwatanta hakan muma bai yiwu ba, a dalilin tsanar magani da Alhaji ƙarami yayi tun yana ƙaraminsa. Ko yaya ruwa ya surka wlhy bazai sha miki shi ba koda da kala ne. Shiyyasa yin maganinsa keda matuƙar wahala. Gashi kuma shi ba'a zaune yake ba waje ɗaya, duk yanda muka so fara bashi koda ruwan addu'a ne sai kiga abin ya zama shiririta. Ina da tabbacin kuma wanda ke wannan aikin kullum cikin sabuntashi suke bawai sun koma sun kwanta bane suma. Maganar camara kuwa ai Alhaji ƙarami yasha sakawa amma sai a wayi gari duk an ciresu. Har ɓoyayyar camara an saka a gidan nan amma kamar abin maita wlhy sai da aka cireta. Hakan na nufin koma su waye a biye suke, shiyyasa ma kikaga ina sake jin tsoron al'amarin gidan nan da mutanensa. Dan idan bana jikinka ba banga wanda zai dinga maka wannan bita da ƙullin ba a nesa da kai”.
Baki na buɗe zanyi magana sai naji kamar amalar motsin tsayawar mutum a ƙofa. Shiru nayi bance komai ba, sai kuma kamar ance na ɗaga ido na hango inuwa ta jikin window. Magana Mama zatayi na wayance ina mai zame kaina da ga cinyarta na ce, “Mama barci nake ji. Dan ALLAH idan Nurse ɗin nan tazo kice bana son allurar nan ni nama warke karki bari tamun”.
Kallon mamaki da naga Mama namun yasa nai mata nuni da window da ido. Tuni ta ɗauki haske kasancewar dama a ankare take. Itama sai ta wayance ta shiga ƴar dariya da faɗin, “Ja'ira ai allurar nan sai an kaita har ƙarshe, bari ma Hajiya tazo zance ta sake ƙara miki kwana biyu kiyi digir dake yanda zamu koma gida da ƙarfinki”.
Shagwaɓa na shiga mata da faɗin ni bana so. Itako tana dariya. Daga haka mukayi shiru. Kwanciya nayi zuciyata na faman kai-kawo. Tabbas lokaci yayi fa dazan dawo hankalina. Dan na fahimci in har shi bai fita a halin da suke sanyashi ba baiwar ALLAHr nan bazata taɓa samun ingantaccen lafiya ba. Domin sauƙi yana samuwa a gareta, sai dai yanayin kwan-gaba kwan-baya da ake fuskanta yasa al'amarin ke taɓarɓarewa. Idan kuwa har za'a iya hana cctv camaras zama lafiya to lallai waɗan nan mutanen ba ƙaramin shiri sukai ba. Suma kuma suna buƙatar a shirya musu yanda ya kamata. Dan dole wayo al'amarin yake buƙata da hikima kamar yanda suma suke komai ta cikin basira”. Wannan tunane-tunanen da hawayen da suka kasa barin idanuna ne suka haifar min da zazzaɓi mai zafi, gashi naƙi gayama Mama har bayan sallar isha'i. Dan da ƙyar ma nayi alwala saboda sanyin da nake ji. Ina idarwa na haye gado na kwanta tare da duƙunƙunewa cikin bargo. Sosai na gaji da zaman asibitin nan, fatana kawai ALLAH yasa yazo dan shine kawai zaisa a sallameni. Yan gidansu dai dama babu wanda ya sake zuwa sai Hajiya ƙarama da nake gani, ita kam kullum ne sai ma tazo sama da sau uku, sai daga baya na fahimci ai dan asibitinta ne shiyyasa itama muke yawan ganintan.....
🩸🌟🩸
Sosai damuwar halin da Ummie ke ciki a kwana biyun nan yasa bai sake waiwayen asibitin ba. Duk da kuwa wani sashe na hankalinsa na'a can ɗin. Sai dai rashin isashen lafiya shima dana lokaci ta sashi baiyi wani yinƙuri ba. Yau kuma zafi da ƙuncin da gidan ya masa matuƙa ya sashi ɗan kimtsawa bayan ya dawo sallar isha'i. Tun la'asar ya kora Hayatu gida dan haka shi kaɗaine a sashen sai Laalah da TJ dake leƙowa akai-akai duba shi shi da Shu'aibu amintaccen guard ɗinsa. Tsaff ya fito yana zuba mayataccen ƙamshin nan nasa tamkar ba dare ba. Tj da Shu'aibu na ganinsa suka miƙe da sauri, hakama sauran ma'aikatan gidan sai gaisuwa suke miƙawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan kwana biyun nan miskilawan ne a kusa. Da ga shi sai TJ da Shu'aibu sukai fitar dan hana sauran guards ɗin binsu yayi. Tj ke driving Shu'aibu a gefensa. Shi kuma yana baya zaune idanunsa akan wayarsa yana daƙila. Kicin-kicin fuskar nan take babu alamar ya taɓa sanin minene ma dariya.
Cike da girmamawa TJ ya ce, “Boss ina muka nufa?”.
Shiru bashi da niyyar amsawa. Sai da ya mula dan kansa ya furta, “Hospital”.
Cike da girmamawa TJ ɗin ya amsa masa tare da ɗaukar hanya. Har sun gota wani bakery yace TJ ɗin ya dakata. Tuna duk lokacin da zasu je asibitin tare da Hayatu sai ya sa an tsaya ya sayi wasu abubuwan ya sashi cewa a dakatan. Shima TJ ɗin tun bai furta ba ya fahimci abinda yake nufi tunda dai koda yaushe da shi ake zuwa asibitin shima. Fita yayi zuwa cikin bakery ɗin batare daya amshi wani kuɗi ba, dan boss ya wuce fiye da haka a wajensu ai. Bai wani jima ba ya fito ɗauke da ledoji masu ƙyau har guda uku. Booth ya buɗe ya sakasu sannan ya dawo cikin motar. Zuwa yanzu ba wayar yake daƙila ba kansa ya kwantar a jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Koda suka iso ma sai da ya ja kusan mintuna biyu tamkar mai nazarin ta yanda zai shiga cikin asibitin sannan ya fito. Yana gaba cikin takun nan nashi na ƙasaita da isa su TJ na biye da shi. Babu yawaitar mutane har ma ma'aikatan jefi-jefi ne. Ko kallon wanda suke a reseption ɗin kuwa baiyi ba yayi wucewarsa. Sai su TJ ne suka gaishesu. Suko suka bishi da kallo tamkar wasu tsoffin mayu. Sai faman washe bakuna suke yau gasu ga Maash, mutumin da yafi kuɗi wahalar gani a Nigeria. Dama wasu a abokan aikinsu sun sanar musu da zuwansa a kwana biyun nan, sai dai su basu taɓa cin karo da shi ba sai yau ɗin...
Har yanzu duƙunƙune nake a cikin bargo ina rawar sanyi dan zazzaɓi nake ji sosai. Ga hawayen damuwa da halin da Ummie ke ciki sun kasa tsayawa a idanuna. Ita mama Balki ta ɗauka nayi barci ne, dan haka ta maida hankalinta a kallon tv tana sauraren wa'azin malam Ali isa fantami da aka saka a African tv3. Knocking ƙofa da akayi a hankali kamar abin dole ya sata rage ƙarar tvn, shiru kamar baza'a sake ba sai kuma aka ƙara. Miƙewa tayi zuwa jikin ƙofar tana tambayar waye? Jin ba'a amsa ba ta buɗe. Ni dai duk ina jinsu amma da yake har kaina na'a cikin bargo ba ganin komai nake ba.
Murnar da naji tana yi da ambaton sunan Alhaji Ƙarami ya sanya gabana faɗuwa. Sai ko ga mayataccen ƙamshinsa ya gama isowa har cikin hancina. Wasu muryoyi biyu naji suna gaisheta da tambayarta mai jiki. Na gane muryar driver ɗinsa. Ɗayan ne dai ban gane waye ba amma nasan ba hayatu bane ba. Sai da naji alamun fitarsu da rufe ƙofa sannan shima naji muryarsa a daƙilen nan can ƙasa-ƙasa kamar abin dole yana gaida Mama. Ita ko da kulawa take amsa masa da tambayarsa jikinsa da kuma na Ummie. Nan ɗin ma da ƙyar ya amsa itama yana tambayarta ya mai jiki. Itako da fara'a ta ce masa, “A jiki da sauƙi sosai. Yau ne ma ta so birkicewa saboda samun labarin jikin Ummie daya motsa da tayi. Dan har bayan sallar magriba ɗin nan tana shartar hawaye sai da na ɗan mata nasiha sannan tai shiru, inaga shine ma dalilin kwanciyar da wuri sai kuma barci ya ɗauke ta. Banji yace komai ba, sai dai haka kawai na dinga jin kaifin idanunsa a jikina. Shiru ɗakin na kusan minti ɗaya sai kuma naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa. A zatonta shine ya fita, dan haka cike da shagwaɓa na janye bargon daga saman fuskata zanyi magana da Mama. Zuuuu naji jinina na falfala uban gudu ta cikin jijiyoyina tsabar shock ɗin cin karo da abinda nai zaton shi ya fita. Da sauri na kauda kaina na sake maida fuskata cikin bargon.
A bazata naji alamar an zauna a kusa da ni, Ji nai na sake daburcewa kamar zan fasa ihu, amma sai na dake tare da yin luff a cikin bargon ina addu'ar ALLAH yasa kada yace sai na buɗe kaina........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_
......Shiru ɗakin har na fara murna. Kusan mintuna uku muna a haka babu motsin komai sai naji yayi ɗan gyaran murya. Idanuna na sake rumtsewa da ƙarfi batare da na yarda na motsa ɗin ba dai. Sake yi yayi, nan ma naƙi na motsa, sai da yay ta uku sai kuma a hankali ya ɗaura da faɗin,
“Dama Ummie c....”
A zabure na yaye bargon gaba ɗayansa. Na ware dukan girman idanuna a kansa. Lips ɗina na rawa a marairaice na ce, “Ummie mi?”. Maimakon amsa min sai kafe cikin idanuna yayi da nasa cat eyes ɗin masu matuƙar girma da yalwar gashi. Wani irin tashi tsigar jikina tayi, sai kif-kif kawai nake faman yi da idanu. Sai faman kokawa nake da numfashina dake seizing.
“Stubborn girl”.
Nakasashiyar muryarsa ta daki cikin kunnena duk da kuwa cikin low voice yayi ta, badan ma idanuna na akansa ba babu yanda za'ai na jisa dan pinkish lips ɗinsa ne kawai suka motsa a hankali. Kamar wata sakarai na jujjuya masa kaina a hankali. Motsa lips ɗina dake ƴar rawa na shiga yi, da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi ya sa mu Um mie?” a rarrabe ina rissinar da idanuna da suka ciko da hawaye. Dan duk yanda na ƙudirci masa tsiwa ko kallon cikin idanunsa nayi magana sai naji sam na gagara yin hakan. Mutum ne mai masifar kwar jini da cika wuri. ALLAH ya azurtashi da wani irin girma a gaban