Showing 348001 words to 351000 words out of 438336 words

Chapter 117 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2252

rikicin a kanta da Hajiya Rubayyar. Dai dai nan Hajiya ƙarama ke fitowa da alamun bata cikin nutsuwarta ko wadda ke cikin wani yanayi. Dan duk tayi wani firingai-firingai kamar wadda bata samu isasshen barci.
Ƙoƙarin magana Hajiya Rubayya tai mata amma sai ta wani ɗauke kai. Wata muguwar ashariya Hajiya Rubayya ɗin ta lailayo, sai dai kafin ta dire securitys ɗin sunyi waje da ita. Baki ta taɓe kawai ta juya ta koma. Babu wanda hankalinsa ke kanta sai ni. Dan haka na sakama yanayin nata ayar tambaya. Cikin sauke numfashi na maida kallona ga Hajiya Mammah da aka rasa wanda zai ƙarasa gareta, sai ihu take abin tausayi. Sai naji kawai na sake girmama rashin mutuncin Ya Awwab ɗin, amma dai maybe yana da dalilin karyatan. Karo na farko Azizat da ƴar uwarta suka bani tausayi, dan sun haɗe kai can gefe suna faman kuka. Hakama Hajiya Mama hawaye take yi, da alama abinda ƴar uwar tata ke aikatawa ya ɗimautata kamar yanda ya ɗimauta kowa. Ummie da Paah da Mama Balki dake can gefe na kalla suma. Sai naga Ummie ta juya ta koma abinta, shima Paah ya take mata baya. Mama Balki kam babu wani alamun razani a fuskarta da alama tasan abinda Hajiya Mammah ɗin ke aikatawa tuni.
Jiki a sanyaye na kalla Hayatu. Na ce, “Yaya Hayat ko za'a kaita asibiti ne dai. Kaga hannun har ya fara kumbura”.
Ɗan jimm yay kamar mai tunani, sai kuma ya jinjina kai da faɗin, “Boss ya iya ɗori, ko dai kije ki lallaɓashi ko zai ɗorata, dan yanzu dare yayi ɗaya saura fa”.
Cikin mamaki na ce, “Yaya Awwab wai kake nufi?”.
Kai tsaye ya jinjina min kai alamar eh. Ajiyar zuciya na ɗan sauke da kallon Fahad da Hafizzullah dake latsa waya hankalinsu kwance suma. Sai bance komai ba na fita kawai ina addu'ar ALLAH ya sa a dace ɗin yazo yay ɗorin tunda dama shine ya karya...


Sosai nasha mamakin samunsa zaune a falon ƙasa hannayensa duk biyu dafe da kansa. Gefensa na dama Paah ne zaune, haggu Ummie. Suma dai sunyi jugum-jugum. Juyawa nai da nufin komawa Ummie ta kirani. Dole na ƙarasa garesu kaina a ƙasa na durƙusa a gabanta. Hannuna ta kamo cikin mata, dole na ɗago na ɗan kalleta. Da ido tai min muni da shi. Sai na waro idanuna cikin marairaicewa. Kanta ta girgiza min tana sake lumshe idanunta alamar kar naji komai naje. Babu yanda na iya dole na rarrafa gaban nasa, kamar mai jin tsoro na ɗora duka hannayena biyu a saman nashi da ya dafe kai da su. Shiru babu alamar zai motsa ko nuna yasan da zamana. Sai naji na sake jin shakkar tasa. A marairaice na juya na kalla Ummie. Sake jinjina min kai tai cikin ƙarfafa gwiwa. Sai kuma ta miƙe, shima Paah miƙewar yay suka bar falon.
Na ɗan ji sauƙi kaɗan dan ina jin kunyarsu. Dan haka na daure da rawar murya na ce, “Yaya Awwab!”.
Shiru. Na saka faɗin, “My Lion!”. Nan ma shiru, ban gajiya ba na ce, “My hot please mana. Kayi haƙuri dan ALLAH kaje ka duba mata hannun kafa karyata. Bai kamata ba ko yaya ita ɗin uwa ce. Bai kuma zama lallai gaskiya bane abinda matar can ta faɗa, kama sani ko sharri aka ƙulla mata. Bai kamata mu yanke mata hukunci batare da wani bincike ba......”
“Samrh leave me alone and get out of here!!”.
Har tsakkiyar raina naji tsawar nan. Amma na dake na sake buɗe baki zanyi magana ya sake daka min tsawar.
“I say leave!!”.
Takaici yasa na saki masa kuka, miye nawa daga roƙon alfarma irin wannan tsawa haka kamar wata dabba. Abunka da mai ciki zuciya a kusa. Tsabar taurin kan mutumin nan har naci kukana na tsire bai kulanin ba. Bamma san lokacin dana tashi a fusace nabar wajen ba ina jin kamar zuciyata zata fashe. To irin wannan wulaƙanci har ina dan ALLAH. Idan ya gadama kar yaje ya ɗorata ai yayar babansa ce sunfi kusa. Haba bana son taurin kai wlhy. Ɗakina nai shigewata na kulle kaina ban kuma sake bi takansa ba. Wanka nayi nai kwanciyata sai zazzaɓin nawa na fama yay mun rijif kuwa. Da ga haka na koma takaina nima.......

*_WASHE GARI_*

Washe gari safiyar suna. Daga tashi sallar asuba da nayita da ƙyar na sauka ƙasa. Can ɗakin da Aunty Falaq take naje na kwanta dan zazzaɓi ne sosai a jikina. Tambayar duniya tamun na ganina anan da asubar nan nace mata ba komai anan kawai nake son kwanciya. ganin yanda nake rawar sanyi dole ta bar ni. Sai ma blanket data ƙara min. Kamar kuma yanda yake ga al'adar bahaushe an raɗama baby suna a masallacin nan Mansion Muhammad Awwab. Sama-sama naji su Fahad sun leƙo suna faɗama Aunty Falaq ɗin. Kasancewar basu shigo ba yasa basu san ina ciki ba. Sau biyu ina tashi yin amai kafin barci mai nauyi ya ɗaukeni. Na roƙeta kuma kada ta gayama kowa karma ta faɗama kowa ina a ɗakin.
Shaƙiyancin da take min yasa na fahimci ita tana fassara yo yajin nawa zuwa nan da wani abune daban. Sai kawai na barta a hakan ne wai ina gudun Ya Awwab. Harda cemin itama farkon cikin nan haka ta dinga yi, sai da ya shiga wata uku sannan. Ni dai ban kulata ba....

★ A sauran ɓangarori kam kowa ya tashi da shirinsa a yau ɗin. Baba prof, Hajiya ƙarama, Maash da muƙarrabansa. Sai su Fahad masu shagalin suna. Hajiya Mammah dai yau babu kanta. Dan Maash dai bai ɗorata ba a daren nan aka kaita asibiti, sai sune sukai mata ɗorin. Tsabar fitina kuma tace a sallameta zataje gida tai jiyya. Basu ƙi hakan ba suka sallamota. Wajen ƙarfe goma drivern ta da Maman Malika datai mata rakkiya suka dawo. Zuwa lokacin gida ya fara ɗaukar harama dan masu tsara decorretion a cikin garden har sun fara aikinsu.
Dai-dai lokacin da su Hajiya Mammah ke dawowa Hajiya ƙarama ce daga can ta ɗakin da gen ɗin gidan yake da wani matashin saurayi dake aiki a gidan Baba prof matsayin mai shara da goge-goge. Wani ɗan akwati mai ƙyau ta buɗe tare da nuna masa cikin akwatin. Ƙaramar kwalbace ɗauke da ruwan allura sai syringe a gefenta. Fuskarta ƙawace da murmushi ta ce, “Kaga wannan allurar ita zakaje ka masa yanzu da gaggawa kafin giyar ta sake sa. Ka tabbatar a kan jijiya ka masa ita. Kada kai min wasa da abun nan. Idan ba haka ba, kaima kasan mizan iya yi Labaran”.
“Babu abinda zai faru maa, dan har video ma zan miki ko kuma na kiraki ta WhatsApp video call dan ki tabbatar”.
“Hakan ma idan kayi babu laifi, zan fiyin farin ciki ma.” tai maganar tana bashi akwatin. Da hannu biyu ya amsa ya saka aljihu, sai kuma ya gyara hiramin kansa da ƙyau ya fice. Sai da ya fita da fin mintina goma sanan itama ta fice ranta fesss. Tana komawa ɗaki Marcel ta kira akan karfa suyi wasa. Dan ƙarfe huɗu za'a fara taron. Ya kamata ace zuwa ƙarfe biyu sun gama da batun DJ ɗin da aka ɗakko su su maye gurbinsa yaransa su iso da kayan kiɗan. Ya tabbatar mata komai sun gama tsarawa. Nan ma ta yanke wayar tana Murmushi. Cike da nishaɗi ta shirya ta fita saloon. Dan yau so take ta fito a hajiyarta.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒚-𝒐𝒏𝒆_


.......A ɓangaren Baba prof kam sai kusan sha ɗaya ya tashi saboda giyar da yasha. Zuwa lokacin yaron Hajiya ƙarama har ya zabga masa allura yama bar gidan dan ya gama nashi aikin kuma. Sai dai da yake ba take zata fara aiki ba, bai ji komai a jikinsa ba lokacin. Wanka yayi yay sallar asuba data suɓuce masa. Bayan ya idar break fast ya fara zaman yi sannan ya koma bedroom ɗin sa yay zaman yin waya da yaransa akan su kasance duk cikin shiri. Dan shi anayin azhar zai wuce Mansion. Suma sun tabbatar masa da komai done. Lokaci kawai suke jira. Amintaccen guard ɗinsa ya kira ya dinga kwasar kayyakin da yay packeging a daren jiya yana kaiwa mota. Sai da ya gama lodesu tsaf sannan ya faɗa masa inda zai kai masa su. Guard ɗin na wucewa yay kiran ma'aikatan gidan. Albashi ya babasu tare da sanar musu zaiyi tafiya, amma sai nan da gobe ko jibi. Su cigaba da kula da gida kamar yanda suka saba. Sun amsa masa da gurmamawa tare da addu'oin dawowa lafiya sannan ya sallamesu. Isma'il nakomawa kitchen ya turama Maash da Uncle Abdullahi dukkan bayanin. Shima ya fara shirya inasa-inasa dan yau ne aikinsa zai ƙare a gidan. Zai ma riga Baba prof fita...

★★★

Har ƙarƙashin zuciyarsa kewarta yake ji. Amma girman kai bazai barsa zuwa ya nemeta ba. Sosai yaji zafin damunsa da tayi jiya akan Hajiya Mammah. Har ma tana faɗa masa wai sharri akai mata bayan ga komai a bayyane gaban kowa akayi. Shi ya tsani aitama abu kwana-kwana bayan kuma ansan gaskiya ce a bayyane. Gefe kuma dama zuciyar ƴan mazan a tunkushe take. Dan ya gama samun dukkan bayanai ta kowanne ɓangare game da shirin Baba prof da Hajiya ƙarama tun a daren jiya. Hasalima bayan barowarsa karya Hajiya Mammah yana shiga sashensa aka kira wayarsa. Dukkan shirin Baba prof aka sanar masa. Dan haka hankalinsa ya tashi ya kai zaune cikin kujera shine ita kuma Samraah tazo ta damesa da wani batun Hajiya Mammah can. Yau kuma da safe aka bashi dukkan bayanan Hajiya ƙarama itama. Hatta da allurar data bayar akama Baba prof ya sani. Shi kuma a yanda yake jin zafin Baba prof ɗin baiga dalilin da zai sa ya hana ai masa allurar ba. Ai Hajiya ƙaramar ce dai-dai da shi. Suci kansu su sha baƙin ruwa. Makashin maza ai dama maza ne ke kasheshi.
A ɓangarensa shima ya gama dukkan shiri da team ɗin sa da kuma su Uncle Abdullahi matsayin jami'in tsaro. Bai so wannan taron suna zai kasance a haka ba. Amma babu yanda zai yi dole sai an kai ga hakan dan ya gaji shi kansa. Yafi buƙatar komai ya fito ya kwashi iyalansa subar ƙasar nan suje su hutama ransu ko matarsa tayi rainon cikin nan cikin salama. Ummie ta huta daga gwagwarmayar da ga sha...
Jin bazai iya daurewa ba kasancewar yasan a irin wannan lokacin tana a halin ciwo yasa ya nufi ɗakin nata, sai dai ya samu wayam babu ita. Amma dukkan alamu sun nuna anan ɗin ta kwana. Ransa ne ya ƙara ɓaci da tunanin ina ta tafi kuma. Dan har Bathroom ɗin ta ya duba amma babu ita. Ƙasa ya sakko ɗakin su Ummie nan ma babu ita, sai ma Paah ne kawai ke barci Ummie na bathroom alamar wanka take dan yaji motsin ruwa. Har zai nufi kitchen sai kuma ya fasa. Wayar Falaq yay kira a dake yace ta turo masa Samraah ɗin. Itako sai taji tsoro tace masa ai tana barci ne tun ɗazun. Ɓoyayyen numfashi ya sauke da yanke wayar kawai dan dama wayo yay mata dan ya tabbatar Samraah na wajentan. Daga haka ya sake haurawa saman a ransa yana raya sai ya hukuntata tunda har ta tafi inda bai aikata ba ta kwanta bayan ga ɗakinta ga nashi. Bata san dama yaji haushi rufe masa ƙofa da tai jiya ba. Sam baya son raini, dan shi abinda kawai ya ɗauki rufe ƙofan raini ne. Bai ƙara bi takanta ba yama shirya ya fita a gidan shi da Hayatu.....

✨✨✨✨

Kamar yanda zazzaɓin ya saba sakina gabanin azhar yau ma hakanne. Da ƙyar na tashi zuwa upstairs ɗin nai wanka nayi salla. Kasancewar Aunty Falaq ta faɗa min duk abinda ya faru har kiran da yay mata a waya yana nemana yasa bayan na shirya na nufi ɗakinsa. Kimtsashi na shiga yi duk da babu wani datti dan nawa dai an gyara, wannan aikin Mama Balki ne kullum takan zo da masu aiki su gyara ko'ina na sashen tana tsaye ɗakinsa ne kawai nake gyarawa ni dan babu mai shiga. Koda na kammala sai na ƙara ɗan jin ƙarfin jikin nawa. Komawa nai ɗakina na sake gyara jikina, dan sunan kamar wasa yanata tara mutane. Dangin Mama Balki sun zo suna sashensu, hakama na Baban su Hayatu da na mamansa. Saboda ma haka Aunty Falaq ta koma can babu wanda aka bari ya shigo nan sashen Ya Awwab ɗin. Ni kaina kwalliyar tawa sai naga ta burgeni, dan haka na tsaya ina kallon kaina a mirror harda yin hoto. Key na sakama ɗakinsa da nawa sannan na sakko dawn stairs. Na ɗan ji shock ɗin samunsa zaune a falon ƙasan shi da Ummie da Likitanta da Paah. Amma sai murmushin da Ummie tai min da miƙo min hannu alamar naje gareta ya sani sauke ajiyar zuciya. Yanda yay mun kallo ɗaya ya ɗauke kansa nima kallo ɗayan na masa na basar. Paah na fara gaidawa da girmamawa sannan Ummie dake riƙe da hannuna tana yaba kwalliyata. Batare dana kallesa ba shima nace masa ina yini sannan na gaida doctor ɗin shima. A haka Fahad ya shigo ya samemu likitan na cigaba da mana bayanin illar da aka so yima Ummie da alluran da aka dinga mata na birkita mata brain. Ya bata shawarar ƙoƙarin fidda abinda duk ke ranta koda ta hanyar faɗama wani ne, hakan zai sa nauyin da zuciyarta tayi ya ragu har ita brain ɗin ta samu rangwame. Haka dai ya dinga bayani dalla-dalla na matakan da za'a cigaba da bi domin tabbatuwar ingancin lafiyar Ummie ɗin. Tamkar an jeho Mama Balki sai gata ta shigo tana kuka. Mu duka duk miƙewa mukayi a razane. Ummie ta shiga tambayarta abinda ke faruwa. Da ƙyar cikin shaƙewar muryar kuka ta ce, “An ɗauke takwaran Alhaji ƙarami, an tare kuma ƴan Kano da akaje ɗakkowa airport kafin su ƙaras....”
Kiran wayar Maash da akayi ne ya katseta. Uncle Abdullahi ya gani ɓaro-ɓaro. Ɗagawa yay, kasancewar akwai bluetooth a kunnensa saurarensa kawai yake. Daga can a rikice Uncle Abdullahi yake magana. “Awwab tabbas akwai matsala. Dan sun canja wasan da ga yanda ka sani. Sai dai ban san daga cikinsu ta ɓangaren wa aka samu canjin ba”.
Komai Maash ƙin cewa yay sai yanke wayar da yayi kawai, ya wani fincike bluetooth ɗin kunensa yayi wurgi da shi. Gaba ɗaya kamaninsa sun canja jijiyoyin kansa sun mimmiƙe. Dai-dai nan Hayatu shima ya shigo a birkice yana tambayar Mama ina Falaq. Sake rikicewa mukai dan ita kanta Mama ma sai yanzu hankalinta ya kai. Cikin wani sabon tashin hankalin ta ce, “Ba kuna tare ba? Tun kiran da kai mata ai ta fito mafari kenan ma ta ajiye yaron.”
“Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Wlhy ban kira Falaq ba ni. Tun yaushe kenan akai kiran?”.
“Yau na shigesu ni Bilkisu. Wayarta fa na hannuna mun gama magana da Hafizzullah kiranka ya shigo na miƙa mata na tashi, bai fi minti ɗaya ba ta sameni da yaro a hannu tace kana kiranta shine ta bani shi ni kuma na miƙama Zaituna. Kwata-kwata bai fi mintuna talatin ba yanzu”.
“Hafizzullah! To shi yana ina?”. Na faɗa cikin kiɗima nima, dan sai yanzu hankalina ya kai kansa. Kuka na fashe musu da faɗin, “Na shiga uku, aunty Falaq, Hafizzullah, da Baby kenan duk aka tattare. Dama sun faɗa, ashe sakacin da suka ambata sunyi naƙin bibiyar zuri'ar baban mu suna wani sabon shirin. Shin minene mahaifinmu ya aikata haka mai zafi garesu shi da Abie? Mi suka aikata musu Umm.....” na kasa ƙarasawa saboda wani irin kuka daya taho min ga jiri na neman kwasata...
Rawa jikin Ummie ya farayi itama. Da kyar ta iya ɗaura hannunta akan kafaɗar Samraah dake wani irin kuka mai cin zuciya. Lips ɗin ta na kakkarwa ta ce, “Samraah mahaifin ku?”.
“Yes Ummie, sun faɗa sunyi sakaci da basu bibiyi suri'ar jirgin mota ba kamar yanda suka bibiyi ta Abie.”
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Kina nufin kema jinin Abdul-wahab ce?”.
Ɗagowa nai na kalleta, cikin kuka nace, “Ummie da ni da Hafizzullah da Yaya Musaddiq da Ya Awwab yakai ƙasar China karatu duk shi ya haifemu. Mu ƴan uwan aunty Falaq ne na jini”.
Sake rikicewa Ummie tai ta juya ta kalla Mama Balki. “Dama bake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login