Showing 237001 words to 240000 words out of 438336 words
Kawu Musa ya masa ƙyautarki. Yace bazai iya watsama tsohon kasa a ido ba saboda sun bashi tausayi, koba komai shine ya saka auren rugujewa, idan bai amsa ba ai ya sake raunanasu kema kuma an cutar dake shiyyasa kawai ya amince. Sai kuma gashi auren shima ya zame masa alkairi, dan ya ce mana yanzu kin tallafi rayuwar mahaifiyarsa dake fama da jiyya shekara da shekaru. Nagode Samraah, Nagode matuƙa da kikayi haƙuri kika amshi ƙaddararki da hannu biyu, Nagode da kika kasance ɗiya ta ƙwarai, Nagode da kika cigaba da riƙe tarbiyyar ki. Dan tabbas naga tsagwaron jin daɗi a fuskar Maash game da ƙyautatama Mahaifiyarsa. Na tabbatar da koda a baya ba soyayya ce ta haɗaku ba yanzu kam yana sonki. Yana ƙaunarki, dan wannan alkairin naki ne muma ya jawo mana alkairin. Yanzu na fahimci dama Maash yaje garejinmu kai tsaye ne domin kawai ya ɗaukeni aiki, dan sai yanzu nake sake tariyo yanda aka ɗaukeni aikin cikin sauƙi ake kuma mutuntani da girmamani sama da ma'aikata da yawa. Gashi har an turani karatu wata ƙasa. Samraah tabbas ke ɗin alkairi ce. Gaba ɗaya halayen iyayenmu kin kwashesu. Dama ance TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. tabbas na yarda da wannan batu na malam bahaushe”. Ya ƙare maganar yana share hawaye.
Da gani har Hafiz muma kukan muke. Dan labarin ya matuƙar girgizani. Ashe haka abubuwa suka faru ni ban sani ba. Ashe mahaifiyar Mansoor ce tasa akai kidnapping ɗin a da farko. To amma tayaya akai hakan? Da sanin Mansoor ɗin kokuma? Idan bada saninsa ba taya akai tasan da videon nan? Shiyyasa ba'a son zargi, na daɗe ina zargin Maash akan ɓata min aure dan shi ya aureni ya cutar dani ya amshi video ashe abin duk ba haka bane ba. Kai jama'a, lallai masu iya magana sunyi gaskiya da sukace zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya. Nagodema ALLAH da ban taɓa masa tambaya akan auren ba duk da nasha son yin hakan kwarjininsa da shakka na hanani. Sosai nake jin kimarsa na sake ƙaruwa a cikin zuciyata. Ashe shine ma ya kubutar da ni daga hannun mahaifiyar Mansoor. Kai ban taɓa zaton matar nan zata iya aikata irin wannan al'amarin ba. Wato mutum kai dai kawai gansa ka barsa yanda ALLAH yayisa, akan kuɗi baka iya banbance mutumin banza dana ƙwarai da wuri, dan sanin zuciya sai UBANGIJIN kawai........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒘𝒐_
......Sai ƙarfe kusan uku mijin Baby ya iso gidan cikin ƙatuwar motar da ta sake haukace imanin su Mom. Sam ita bama damuwarta rabuwa da ɗiyar ba. Sai santin motar suke da sake kambama irin dukiyar mijin Babyn. Faɗa ma ta yarda akai baby iyayenta na Gwarzo su mata batayi ba. Sai sake shiryata da akai ciki wata alƙyabba mai ɗan karan ƙyau. Itako ido ƙemaƙayau ba ko ɗigon hawaye. Hasalima inda kwalliyarta batayi ba gyara abinta take ko tace a sake mata kaza bata son kaza. Su dai su Gwaggo Gudidi sunyi sororo suna kallon ikon ALLAH.
Abba baya nan ya fita, dan baiyi zaton mijin Babyn zai iso a lokacin ba kasancewar yasha jira kafin azhar amma shiru. Sai Alhaji Jafaru babban ɗan Gwaggo Gudidi ya jashi suka tafi wata gaisuwa a gyaɗi-gyaɗi. Su Gwaggo Gudidi suna tunanin ai za'a jira Abban su dawo. Amma mi sai gani sukai an fito da amarya baby tana taku ɗai-ɗai ko irin rufe fuskar nan ta amare batai ba. Sai ma hirarsu suke da kakarta Umma suna dariya. Babu wanda aka kalla a cikinsu aka wuce da Baby ƙofar gida aka sakata a narƙeƙiyar motar da angon nata yazo a ciki. Abu mafi ban mamaki mijin ko kallonsu baiyi ba. Sai Mom ɗin da Umma ne suka gaisheshi yana amsawa cike da shan ƙamshi. Baki a washe Umma tace, “ALLAH ya tsare to Alhaji. ALLAH kuma yasa ku dawo lafiya da babbar tsaraba ta tattaɓa kunnena. Alhaji mu ya maganar tafiyarmu saudia ne?”.
Duk maganar da Umma take harararta Baby keyi, miye na wani tabbayar zuwa makka dan zubar da mutunci. Badai shine da kansa yace ya biya musu ba ai sai tayi hakuri taga lokacin yayi baice suje ba ko. Shikam ma ɗan mannin rainin wayon hannu kawai ya ɗaga musu a taƙaice ya ce, “A jira lokaci”. Daga haka ya ɗauke kansa tare da bama drivern sa umarni ko kallon amaryar tasa baiyi ba. Driver kam umarnin ogansa ya cika. Ya tada mota abinsa yay reverse har yana neman taka su Mom dake tsaitsaye. Ai tuni mutane suka shiga faman jinjina kawunan mamaki. Ƴan anguwa suka guntsa kowa da abinda ya fassara al'amarin. Dan kuwa dai sunga sabon salon ɗaukar amarya ganin idonsu.
Duk abinda ake Halime batama sani ba. Tana can tunda ta idar da sallar azhar ta kira Abba tace ya saya mata rake da gyaɗa tai kwanciyarta. Har aka tafi da Babyn kuma bata sani ba. Sai da hayaniya ta fara tashi ta ƴan gwarzo sannan ta farka...
💦🌟💦🌟💦
Duk yanda Hayatu ke ƙoƙarin danne abinda ke cimasa zuciya ya kasa. Sai satar kallonsa yake ta cikin mirror har suka iso babban companyn da Ummie ta fara ginawa da hannunta tun mahaifinta na da rai wanda Paah ne ke riƙe da ragamar komai na companyn. Ƙatone bana wasa ba, sannan akwai ma'aikata jingim a cikinsa. A farkon ginashi ana sarrafa kayan suturu ne, bayan abubuwa sun kwaɓe akan ciwon Ummie companyn ya durƙushe harma ya daina aiki na tsawon shekaru. Sai daga baya Maash ɗin ya farfaɗo da shi tare da sake faɗaɗashi aka maida shi wajen sarrafa kayan abinci. Kusan kowane nau'i na kayan abinci har su mai magi duk companyn na fitarwa. Suga, gishiri, harsu omo da sabulai sannan kayan abinci tun daga kan shinkafa, taliya, fulawa, garin alkama, da ire-irensu, da dangoginsu. A yanzu dai a Africa babu companyn dake fidda kayan masarufi irinsa gaskiya. Dan tako ina suna kai abinci kuma sunada wasu reshika a wasu kasashen da dama.
Duk ta inda suka gitta gaisuwar girmamawa ake bama Maash. Shi ko yana mai amsa musu a daƙilen nan nasa dan motsin lips ɗinsa kawai suke gani sai kuma hannu da yake ɗaga musu. Duk wanda yayma Maash farin sani a rayuwa yasan wannan halin nasa ba wulaƙanci bane yanayinsa ne kawai a haka. Dan magana inba ta zamar masa dole ba, da wahala kaga yana yinta. Idan ma yayin bazaka taɓa jin sautin muryarsa sama ba. Sai fa idan an ɓata masa rai yayi matuƙar iya hargagin da ke gigita mutum.
Kai tsaye office ɗinsa ya nufa Hayatu biye da shi dan shima yana da office a companyn. Har yanzu suna kan bincike game da case ɗin nan na samun yara a containers ɗin sa na kaya da suka tura Ghana. Monday ɗin nan zasu shiga court yau kuma zai sake zaman meeting da lawyers ɗin su da Paah, duk da dai kwata-kwata an nuna case ɗin bai shafesa ba duk da kasancewarsa shugaban companyn shiyyasa ma yake tsula tsiyarsa da matan da ake ɗauka aiki a ciki har Maash ɗin ya gano sa ranar yake tujara. Sun samu Paah ɗin baya nan, lawyers ɗin kuma basu kai ga ƙarasowa ba. Sai hakan ya bama Hayatu damar fidda abinda ke ransa.
Kallon Maash dake zaune cikin kujerarsa ta office ɗin yana daƙilar keyboard ɗin computer ɗin saman desk ɗinsa yayi. Sai kuma yayi ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Yaya kamin afuwa, zan sake maimaita maganar nan dai ta kwanaki dana taɓa maka kaƙi cewa komai”.
Shiru kamar maash ɗin bazai amsa ba. Sai kuma can yace, “Uhumm ina jinka”.
Kai hayatu ya ɗan sosa yana sake ƙasa da kansa ya ce, “Nifa ALLAH yaya yau saina sake ganin kamanin Yayan Aunty sosai da Baba Abdull sun sake fitowa. Shi kuma ƙanin nan nasu Hafizzullah banbancinsa da Falaq kawai ita mace shi namiji. ALLAH tun ɗazu a ruɗe nake dauriya kawai nake yi. Ita kanta Auntyn yau sai naga suna fisgar kama da Falaq ɗin, kawai dan ita farace ita kuma aunty bata kaita has......”
Ruff bakin Hayatu ya rufe batare daya ƙarasa faɗa ba saboda kallon da Maash ɗin yay masa. Sai ya wayance da faɗin, “Yaya ALLAH ka duba lamarin nan iya gaskiyata nake faɗa”. Ya ƙare maganar cikin shagwaɓa kamar ba Hayatu PA ba. (Wato na lura akwai lokacin da Maash matsayin oga yake a wajensa. Akwai kuma lokacin da yaya yake😀).
Hararsa kawai Maash ɗin yayi ya ɗauke kansa ya maida ga aikinsa....
🩸🩸🩸🩸
“Ban gane mi kike son faɗa ba? Kin san dai bana son rainin wayo ko”.
“Wlhy yallaɓai babu rainin wayo a maganata. Kai ma kasan bazan yi hakan a gareka ba. Naje na samu nima ta sallameta. Kuma shi Awwab ɗin ne yaje ya sakata yin hakan”.
Wata shegen ashariya Yallaɓai ya kutuntuma. Sai kuma ya miƙe zaram yana kaima Centre table duka har sai da Hajiya ƙarama ta zabura tana ƙanƙame jikinta. Sai kuma ya juyi a fusace yana nunata da yatsa. “Idan har na samu matsala a aikina saboda ke na rantse da ALLAH sai na koya miki hankali”.
Sosai hankalinta ya tashi, dan tasan mugun nan komai zai iya aikatawa akan buƙatarsa. Amma ba komai lokacinsa ne. Zata bisa yanda yake so gaba kaɗan zatayi maganinsa ai itama. Dan ta gama shirinta a kansa tun shekarun baya. Murya ta sauke cikin nuna tsorata ta furta, “Kayi haƙuri nayi kuskure, amma na samo hanyar gyara kuskuren nawa. Na tabbatar bazai kaita ko'ina ba sai gida. Koda yake nama bincika an tabbatar min suna gidan. A wannan karon zan nuna abinda ya faru ina jin tausayinta na dawo da ita sashena. Kokuma na nuna zan share mata kukanta akan abinda ya faru ta hanyar nema mata makaranta ta cigaba. Da ganan sai musan abinda ya dace, kaga munma samu sauƙi”.
Shiru ya ɗan yi alamar nazarin maganarta. Sai kuma ya kai zaune yana mai jinjina kai. “Hakan ma yayi, sai dai ina mai gargaɗarki ki kiyaye. Dan bana buƙatar wata matsala kuma.”
“In sha ALLAHU babu abinda zai faru, shi mai bincike a kantan ya dawo ne?”.
“Zuwa jibi ne ƙarshen kwanakin daya ɗiba min. Dan ko jiya munyi waya da shi ya kuma tabbatar min da aikin na tafiya yanda zanyi farin ciki”.
Itama murmushin ta saki duk da ba haka taso ba. Dan a nata ɓangaren tasa itama a bincika mata wacece Samraah ɗin?.
✨✨✨✨
Gaba ɗaya ganin ƴan uwana ya wanke min duk wata damuwata. Hirarmu muke cike da farin ciki suna bani labarin cakwakiyar gidan Abba ta yanzu da amaryarsa, tare da yanda auren Baby ya kasance, sun dai baro ana jiran miji yazo ya ɗauke ta. Matsama Yaya Musaddiq nai ya kiramun aunty Zakiyya. Daga nan fa mukaita gaisawa da mutane harda amaryar Abba da kawai naji matuƙar ƙaunarta. Daga ƙarshe jikina yayi sanyi jin batun zuwan mijin Baby yanzu babu jimawa da yanda tafiyar ta kasance. Mun cigaba da jimanta abun bayan katse wayar. A haka lokacin sallar la'asar ya riskemu. Ina tunanin yanda zasu fita salla sai ga guard ɗinsa yazo yace suzo boss yace ya kaisu suyi salla. Kafin su dawo nima nayi tawa, na sake gyara sashen naje kuma na gano Ummie. Alokacin nake cema Mama Balki tazo su gaisa da bakin da yace. Ta ce tana zuwa idan ta kammala abinda take yi. Harta bani abinci na kai musu. Duk da sunci sun ƙoshi dan acan inda aka fara saukesu sunce sunci abinci, nan ma kuma da Hayatu ya rakosu da kayayyakin ciye-ciye suma mukaita ci muna hira sai da na ɗauka musu abincin. Sake zaman hirar mukayi, dan ji nake kamar mu dawwama a haka. Koda suɓutar baki ban sanar musu komai daya shafi gidan nan ba. Hirar abinda ya shafemu kawai mukeyi hankalinmu kwance. Hatta zancen alaƙar Mama Balki da nake zargi da baba ban gaya musu ba, shiyyasa ma na matsu tazo su gaisa. Dan duk wanda yasan mahaifinmu ya kallai Yaya Musaddiq yasan suna matuƙar kama, musamman yanzu da yake sake girma kamanin na sake fitowa sosai. Wajen ƙarfe biyar ina shirin zuwa na sake ganin Ummie da ga nan nayi kiran Mama sai gashi ya dawo. Sannu da zuwa su Yaya suka shiga yimasa da gaidashi. Ganin haka yasa nima na gaisheshi batare dana yarda na kallesa ba. Sai dai shi ina jin idanunsa na yawo a jikina, dan haka ma naƙi kallon nasa. Ciki ya shige yana faɗa musu bari ya ɗan watsa ruwa. Sukai masa fatan fitowa lafiya. Na gyara zama zan cigaba da hirata Yaya Musaddiq ya hararen, tare da mun nuni da ƙofar da ya bi.
Baki na tura cikin shagwaɓa nace, “Kai yaya mi kuma zanyi”.
Sosai yake kallona fuska a tsuke, “Oh kice karatun Mom kema kin ɗauka kenan?”.
Da sauri na shiga girgiza masa kaina. “Wlhy Yaya a'a”.
“Inafa a'a tunda gashi na gani da idona. Abba yakan dawo gida bai ishi Mom kallo ba. Kema ga mijinki ya dawo ko kallon inda yake bakiyi ba. Abba yakan dawo gida Mom bata bashi ruwa ba, ya shige yay hidimarsa. Kema kuma gashi mijinki ya dawo babu ruwa babu abinci, maimakon ki bishi kiji yaya ya dawo, miye matsalarsa kin gyara zama ke ga mai ƴan uwa sunzo ko. Haka kike so muma idan munyi aure matanmu suna mana?”.
Da sauri na sake girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla. Ya ce, “Okay to aya maza tashi, haba Kandalata ina islamiyyan ya tafi? Mu kin bamu munci mun ƙoshi yan uwanki shi dake wahalar nema ko oho. Ko kina so Hafiz ya rainaki”.
Da sauri na sake girgiza kaina ina Hararan Hafiz ɗin dake kumshe dariya. Tashi nayi na nufi ƙaton freight ɗin dining room. Ruwa na ɗauka da lemo na sa a tray dana ɗakko a kitchen sai glass cup mai ƙyau. Ni sai ma naji abun banbara ƙwai wai namiji da suna Hajara. Haka dai na daure dan bazan taɓa iya bijirema Yaya Musaddiq ba.......✍️
🥱A fito lahiya matar yayanmu
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
-------------
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
=========
.......A hankali nake tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki, koda na isa ƙofar bedroom ɗin na yi kusan minti ɗaya kafin nayi knocking a hankali. Banji motsin komai ba balle na saka ran za'a buɗe min. Hannu na kai zan sake knocking ɗin aka buɗe ƙofar. Da sauri na janye hannun nawa na riƙe tray ɗin da ƙyau kaina a ƙasa. Jin shiru ya sani ɗagowa a tunanina juyawa yay ya koma. Amma sai na gansa tsaye kawai ya zuba min cat eyes ɗin nan nasa. Sosai tsigar jikina ta tashi, dan wani irin kallo yake min mai wahalar fassara gashi da ga shi sai guntun towel iya gwiwa. Kaina nai ƙoƙarin sake saukewa cikin ɗan rawar harshe na furta, “D... dama ruwa ne...”
Bai bari na ƙarasa ba ya matsa min hanya alamar na shiga. Raɓawa nayi na wuce, kai tsaye na ajiye tray ɗin saman Centre table na buɗe ruwan na tsiyaya a cup tare da ƙoƙarin ɗagowa. Ido muka haɗa da shi, yana tsaye jikin mirror ƙafafunsa a harɗe yay folding hannayensa a ƙirji ya zuba min ido kawai. Ƙasa nayi da nawa, tare da takawa a hankali inda yake, batare dana kallesa ba na miƙa masa kofin ruwan. Shiru babu alamar zai amsa, dan haka na ɗago cikin yanayin kamar mai shakku na kallesa, har lokacin idanunsa a kaina suke, samun kaina nayi da marairaice face ɗina kamar zanyi kuka na ce, “Pleaseeee!”.
Ɗan luuuu yayi da idanunsa