Showing 417001 words to 420000 words out of 438336 words

Chapter 140 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2243

Mammi, shima dai namijin ya manyanta sosai. Rungumeta kawai Ummie tayi ta fashe da kuka tana faɗin, “Tabbas koda ba'ace min kuna da alaƙa da Mamina ba da grandma ni nasan ku jininsu ne. Miyasa kuka ɓoye min? Miyasa?”.
Hannu tsohuwa takai saman kan Ummie tana shafawa tana hawayen itama da faɗin, “An sanar mana Adda ta jima da rasuwa tun kwana biyu da barin Kano, hakama Rabi'ah dan haɗarin mota akace mana sunyi, kuma anje har inda haɗarin ya faru motar ta ƙone, an bincika tasha dan a tabbatar motar dai suka shiga aka sake tabbatar da hakan. Amma taya kika san Addata bayan ke ɗin baturiya ce..” kuka ya sake sarƙeta. Paah ne ya matsa garesu cikin lallashi shi da Dad sukace suje ciki tsaiwa a hakan babu daɗi. Haka kuwa akayi muka shiga ciki. Kasancewar falon babba ne sai duk ya kwashe mu batare da wani ya matsu wani ba sam. Har lokacin dai su Ummie kuka suke yi. Mammi kuma na riƙe da hannun Ummie ɗin kamar za'a ƙwace mata ita, yayinda ɗayan hannunta ke riƙe da hoton su Mama Rabi'ah. Gefenta dattijon nan ne da shima dai hawaye take ta faman sharewa yana ta kallon Ummie.......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏_



........“ALLAH sarki Adda ALLAH ya gafarta miki. Shiyayasa mahaifinmu har yabar duniya yana maimaita shi yana ji a jikinsa kina raye keda Rabi'ah. Ni kaina a lokuta da dama sai naita jin hakan a cikin raina. Har nakanji fata da ɗokantuwar inama ace zamu sake haɗuwa. Tabbas Marka ta cucemu, ta zalunci rayuwarmu. Mun barta ga ALLAH kuma shine zai miki sakayya da mu ahalinki. Uwarmu ɗaya ubammu ɗaya da Adda Maimoonatu. Ita iyayenmu suka fara haifa, sai kuma haihuwar ta tsaya musu cak tsahon shekaru basu sake samu ba. Harma sun fidda rai da hakan duk da matsin lamba da mahaifiyarmu ke samu wajen dangin mahaifinmu Babanmu bai taɓa kwatanta ƙara wani auren ba. A haka Adda ta kai shekaru goma sha uku. A tsari dai ta isa aure na wancan lokacin, dan haka wani abokin baba mai suna Kabiru na fitowa baba ya bashi. Duk da anata surutu akan hakan baba bai kula ba. Dan kuwa shima baba Kabiru shekararsa goma sha shida matarsa bata taɓa ko ɓatan wata ba. Haka dai akai biki aka kai amarya, sai me ba'a ƙulla wata biyu ba sai ga mahaifiyarmu da ciki itama Adda da ciki. Ikon ALLAH kenan, wannan al'amari ya matuƙar girgiza mutane. Yayinda Marka matar Baba Kabiru tai matuƙar tasar hankalinta. Kullum fitina ita da miji, ta kuma dinga gallabar Adda kenan amma ita bata kula mata. Da ga ƙarshe ma da akaga fitinar na neman yawa, wataran zata iya salwantar mata da ciki sai Adda ta dawo gida kusa da mahaifiyarmu suka ƙarasa rainon ciki tare. Mahaifiyarmu ita ta fara haifarmu ƴan biyu ni da mahaifiyar Abubakar” ta nuna Dad. Itace Hassana nice Usaina. Murna da farin cikin duk wani masoyan iyayenmu bai ɓoyu ba, dan sosai akai shagali na nuna tsara. Bayan suna Adda ta cigaba da rainon ciki mahaifiyarmu na wankan jegonmu. Sai da tai arba'in biyu kamar yanda akeyi da sannan Adda ta haihu mace itama. Itama anyi farin ciki, yayinda Baba Kabiru ya rikice dan daɗi, shima haka ya dinga ɓarin kuɗi a ranar sunan yarinya da taci Rabi'ah. Bayan suna anan gida ta cigaba da zama har tai arba'in.
Baba Kabiru ya matsa Adda ta koma ɗakinta, sai dai halin Marka na saka iyayenmu tsoro. Dan a hakanma da take gida ba ƙyaleta tayi ba. Shi kansa Baba Kabirun ba daɗin zama yake ji da ita ba. Dan kullum cikin tashin hankali suke. Shi kuma ya kasa sakinta saboda mahaifinsa ne ya aura masa ita cousin ɗinsa ce. Ya kuma cemasa idan ya rabu da ita bai yafe masa ba. Ga mahaifin nasa ya rasu yanzu. Haka dai badan mahaifiyarmu naso ba aka maida Adda gidan Baba Kabiru. Adda nada matuƙar haƙuri, shiyyasa ta iya jure halayen Marka na tsawon lokaci batare da ta taɓa zuwa gida ta faɗa ba. A haka Rabi'ah ta isa yaye aka kawota nan gidanmu, sai kuma ga Adda da wani cikin. Bamma san yanda zan musalta muku bala'i da masifar da Marka tai a wannan gaɓar ba, ta kuma ci alwashin sai Adda bata isa sake haihuwa a gidan ba, Rabi'ah ma data haifa sai ta koma. Zancenta ya tada hankalin mahaifiyarmu, har tace ita dai Baba Kabiru yay hakuri kawai ya rabu da Adda. Amma sai babanmu ya hana. Haka aka cigaba da rayuwar kullum Rabi'ah na nan gidanmu, sai dalili mai ƙarfi kesa a kaita gidansu. A haka ALLAH ya sauki Adda lafiya, sai dai ɗan baizo da rai ba. Tsabar jahilci na Marka ta dinga dariya wai alhakinta ne. Babu dai wanda ya kulata Adda ta sake zuwa tai wanka, dan lokacin sai mace tai haihuwa uku tana zuwa gidansu wanka. In dai takaice muku sai da Adda tayi haihuwa uku bayan Rabi'ah amma yara na zuwa babu rai. Kai tsaye kowa ya dinga faɗin Marka ce. Shi kansa Baba Kabirun ya sakama ransa ita ɗince, cikin rufewar ido yay mata saki uku. Abinda bata taɓa tunani bane, aiko ta gigice matuƙa ta kuma dawo tana bashi haƙuri da tabbatar masa zataje ta karya asirin da tayi ƴaƴan Adda ke mutuwar. Tashi hankalinsa ya sake yi, kenan dai gaskiya ne itace ke kashe masa ƴaƴa. Aiko sai ya sake harzuƙa ya lakaɗa mata uban duka. Haka aka kwasheta zuwa ƙauyensu. Wannan abu shine ta saka Marka ɗaukar alwashin sai ta ɗau fansa akan Adda. Babu wanda yabi takan batunta aka cigaba da sabgogin rayuwa. ALLAH bai sake bama Adda wani cikin ba sai da muka kai shekaru goma sha uku ana ma batun mana aure mu harda Rabi'ah ƴarta. Kwatsam sai ga ciki. Tayi rainonsa cikin aminci da salama dan yanzu hankalinta a kwance yake ita da mijinta da ƴarsu. Har dai ALLAH ya sauketa lafiya ta samu ɗa namiji, ranar suna aka saka masa Sulaiman”. Ta nuna dattijon ɗaya kamota ɗazun mai kama da grandma. Dukanmu babu wanda bai kallesa ba cikin maɗaukakin mamaki, kenan dai shi ɗin ƙanin mahaifiyar Ummie ne uwa ɗaya uba ɗaya. Mammi ta cigaba da faɗin,
“Ranar sunan Sulaiman komai ya canja daga yanda yake, domin kuwa da yamma a wajen taron suna aka nema jariri aka rasa. Hankalin kowa ya tashi Adda harda sumanta, sai dai ko sama ko ƙasar babu jinjiri babu alamarsa. Ana cikin wannan taraddadi kuma itama Adda da Rabi'ah aka nemesu aka rasa. Ai sai ma hankali ya koma kansu aka manta da batun jariri. An bazama nemansu tako ina. Nema iya nema babu ta inda aka dace, anata yawo da hotonsu har cikin tashoshi. Sai a kwana na biyu a wata tasha ake tabbatar mana lallai sunzo nan sun shiga motar zuwa Lagos, amma kuma ana raɗe raɗin motar tayi haɗari ma a jiya da dare mutanen ciki sun ƙone ƙurmus. Sake tashi hankali yayi, baba Kabiru da baban mu suka tafi garin da motar tai haɗin. Tabbas sun samu anyi haɗarin, kuma an tabbatar musu babu wanda ya tsira a motar. Suma kuma da idonsu sunga wajen sai kufan wuta da gwangwanin ƙarfen motar. Ko yaro akacema mutum zai rayu a ciki bazai amince ba. Haka suka dawo mana da wannan tashin hankalin da damuwa. Baba kabiru kuwa ya yanke jiki ma ya faɗi, tun daga nan bai sake tashi ba har ya rasu. An yima Adda da Rabi'ah sadakar uku data bakwai, a ranar ne shima Baba Kabiru ya rasu. Hankali ya koma akan al'amarin Sulaiman da shima ba'a da tabbacin yana raye, sai kuma hukuncin ALLAH wata ƴar uwar Marka tazo mana da labarin Sulaiman a binciki Marka, itace ta saka aka sace shi, kuma itace sanadin salwantar su Adda. Dan kurciya ta musu. Ɓacin rai ya saka Baba aika ƴan doka suka kamo Marka har ƙauyensu, sai gashi da taga wuya ta faɗi kamar yanda ƴar uwarta ta faɗa. Ta kuma faɗi inda ta kai Sulaiman ta yarda. Haka aka sake bazama nema cikin amincin UBANGIJI sai gashi an samo Sulaiman a gidan mai garin ƙauyen, wani ne ya tsinta Sulaiman a gonarsa shine yaje ya kai gidan mai garin. Matarsa kuwa ta kama ta riƙe ta adana. Dan da ƙyar ma ta yarda ta bada Sulaiman ɗin. Mahaifiyarmu ce ta cigaba da kula da shi, yayinda dangin baba Kabiru suma ke iya ƙoƙarin su na ɗawainiya da shi. A haka akai bikinmu ni da Hassana ta. Itama bata tsallake wata ukun farko ba ALLAH ya bata ciki. Sai dai ni ALLAH bai kawo ba harta haihu ɗanta Namiji. Shine Abubakar”. Ta nuna Dad ɗin su Mansoor. Bai shekara biyu ba sai ga wani cikin ta sake samu. Na fara shiga damuwa, dan ni mutum ce mai son yara sosai. Dan haka innarmu ta kwantar min da hankali da Hassanata. Na kwantar da hankalina sai dai na roƙi a bani Sulaiman na cigaba da riƙesa. Babu musu Baba yace hakanma yayi, dan suna ganin riƙon Sukaiman ɗin zai bani nutsuwa. Ya kuwa bani, dan tuni na manta da damuwar rashin haihuwa. Hassana ma ta sauka lafiya mace, aka saka mata Maimoonatu. Bayan haihuwarta babu jimawa ALLAH yay ma Baba rasuwa. Mun shiga matuƙar ruɗani, daga baya dai zukata suka haƙura akan dole. Shima bai shekara ba Innarmu ta bisa. Shike nan muka koma babu uwa babu uba kuma. Sai ni sai ƴar uwata da ƴan ƴaƴanmu. Bayan Maimoonatu da muke kira Adda Hassana ma bata sake haihuwa ba sai bayan kusan shekaru goma sha, sai ga ciki. Na tayata murna sosai, da mata fatan sauka lafiya, dan yanzu kam ni zuciyata ta dake. Abubakar ma kusan a hannuna yake shima. Wannan ciki ashe shine sanadin ajalin Hassana, dan kuwa a wajen haihuwarsa itama ALLAH yay mata rasuwa ita da abinda ke cikinta. Bamma san yaya zan fasalta muku halin dana tsinta kaina a wannan lokacin ba. Amma dai lallai na jigatu, kowa ya tafi ta barni kamar labari. Dole na tattare duka ƴaƴan ni da mijina muka cigaba da riƙewa, duk da dai dangin mahaifinsu Abubakar sun so tayar min da hankali akan amsarsu nafaƙi aminta sam. Dole suka haƙura suka barni da kayana. Rana ɗaya na aurar da su su duka ukun. Adda ta auri Sulaiman, Abubakar ya auri ɗiyar ƙanin mijina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Daga baya shima mijin nawa ALLAH yay masa rasuwa, muka koma daga ni sai su gasu nan. Sun riƙeni uwa mahaifiya, koda wasa basu taɓa gazawa wajen min hidima irin ta ɗa da mahaifi ba. Nima kuma ban ƙara kukan rashin haihuwa ba, dan duk abinda mai haihuwa zai buƙata na samu fiye ma da hakan a wajensu. Dan haka ina son sanin tayaya aka faɗi a ragaya? Bayan dukkan alamomi sun tabbatar mana Adda da Rabi'ah mun rasa su”..........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒔𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏_


......Paah ne cikin girmama al'amarin UBANGIJI ya shiga jinjina kai. Tare da faɗin, “Wannan hikima ce ta UBANGIJI Mama, mai rayawa a sanda yaso, ya kuma ɗauki rai a lokacin da yaso. Mu dukanmu anan babu wanda zai iya amsa wannan tambayar taki ta yaya akai su Mamie suka tsira har suka kasance a Lagos. Sun shiga motar, basu shiga bane, tsira sukai ALLAH shi kaɗai ya barwa kansa sani sai kuma su. Dan duk waɗanda zamu iya sanin ainahin zancen daga bakinsu ALLAH yay musu rasuwa babu ko ɗaya yanzu a raye. Kaɗan daga abinda muka sani dai ita Grandma Maimoonatu taje da Mamie Lagos ne suke abinci anan kusa da companyn mahaifin Ummu-Hidaya. Sai sabo ya shiga tsakani har ake zuminci. Daga baya kuma ya auri Mamie Rabi'ah kenan shi Abie mahaifin Ummu-Hidaya. Shine suka haifeta, ALLAH ma ya ƙara bada wani cikin wajen haihuwarsa ne ALLAH yay mata rasuwa. Itama kuma Grandma ɗin saita rasu a dalilin haɗarin mota da aka.....”
Saurin riƙe hannunsa Ummie tayi dan ta fahimci ɓaranɓaramar da yake shirin yi. Ta share hawayenta da cigaba da faɗin, “Haɗarin mota tayi kafin ma rasuwar Mamie na. Amma a tsakaninsu babu wani nisa sosai. Tabbas mahaifina ya taɓa sanar min Mamiena har ta bar duniya tana naci da ƙishirwar son sanin ina ahalinta suke, dan kamar dukansu an juyar musu da tunani ne sun manta komai musamman ma ita Mamie ɗin. Amma ita Grandma bata son faɗa mata. Idan ma ta dage da tambayarta sai ta nuna mata ɓacin rai. Sai dai tana yawan ɗaukar wannan hoton taita kallo tana kuka”. Ta miƙama Mammi hoton data ciro a handbag ɗinta. Amsar hoton Mammi tayi, aiko ta saki kuka mai ban tausayi. Iyayensu ne a jiki, sai ita Adda ɗin da cikinta da su a ranar suna su. Ta share hawayenta da faɗin, “Wannan mune da iyayenmu aranar bikin sunanmu ni da Hassana ta. Sannan tana da tsohon cikin mahaifiyarki. ALLAH ya jiƙan Adda da Rabi'ah. Ashe sallamar kenan mukayi. ALLAH ya saka mana, in sha ALLAHU Marka sai kin girbe abinda kika shuka tun a duniya. Amma ina son naje daku har wajen Marka ta tabbatar da UBANGIJI ya fita. Idan tana ganin ta salwantar da rayuwar Adda da Rabi'ah to ga baya nan sun bari”.
“Tabbas Mammi zamuje. Kinga wannan shine babban ɗan Ummu-Hidaya, sunansa Muhammad Awwab, ga matarsa nan da ciki. Sai wannan ƙaninsa ne Fahad, ga tashi matar nan satin daya gabata akai bikin nasu.”
Kuka Mammi ta sake fashewa da miƙa mana hannu tana faɗin, “Duk kuzo gareni ƴan albarka, kuzo naji ɗuminku kunji”. Garetan duk mukaje, ta kamamu ta rungume tana kuka.
Matuƙar farin ciki yau muna a ciki, Ummie taje kusa da kawunta Sulaiman ta zauna. Kuka yake sosai tun ɗazun, hannunsa ta riƙe cikin nata itama tanayi. Abin tausayi. Babu ɓata lokaci akai kiran su Mami a waya ta taho da ƙannen su Mansoor. Itama Adda matar Uncle Sulaiman akace ta taho da tawagarta. Cikin abinda bai gaza awa ɗaya ba gida ya gama hallara. Duk da Mami yanzu tasan babu matsala tsakaninta da Maash sai ta kasa haɗa idanu da shi har jikinta na rawa. Ta dinga satar kallon Samraah. Sai da aka musu kuma bayanin abinda ya faru sai ta sake firgicewa. Nan fa sabon kuka ya tashi. An sake gabatar da su Awwab matsayin yaƴan Ummie da mu matansu, sannan ƴaƴan Dad su huɗu suma da matarsa. Sai Uncle Sulaiman da Adda da nasu ƴaƴan shida ALLAH yay ma ɗaya rasuwa. Baza uku mata uku. Ashe a cikinsu ne ma Attahir zai auri ɗaya..

A gurguje Please 🥺

💢🌟💢🌟💢

Batun dai komawa Lagos ranar bata yiwu mana ba. Dole zuwa dare muka wuce can gidan gashi ma'aikatan gidan basu san da zuwanmu ba. Sai da muka isa aka hau gyarawa, sauƙin ma bawani dattine yayi ba tunda bamu daɗe da barin garin ba. Ummie dai can gidan Mammi muka barta. Dan tana nane da kakarta. A falo muka baje munata tattauna wannan iko na ALLAH mai ban al'ajabi da mamaki. Duk rashin son magana ta Yaya Awwab sai da ya saka mana baki. Ballema da nake basu labarin ni tun randa naga hoto a office ɗinsa nake laluben inda nasan mai kamannin. Sai dai da yake nima sau ɗaya na taɓa ganin Mammi ɗin na kasa tunawa. Shi kuma Maash yace a jikin Dad yaga kamannin, ashe ƙarfin jinine kawai. Ashe shiyyasa ma yace su shigo dan suga hotunan itama Ummie taga Dad ɗin. Mun jima muna hirar har Paah da Baban Hayatu kafin kowa ya nema makwanci. Kamar yanda tsohuwa Mammi ta faɗa washe gari suka kwashemu sai ƙauyen su Marka. Ni dai wannan tafiya bata min daɗi ba dan naci ƙaniyata gwargwadon iko. Saboda hanyar bata da ƙyau, sauƙina ma daga ni sai shine a motar, ina kuma jikinsa koyaya nace wash zai ce minene. Bama ni kaɗai ba kowa ya jigatan ashe. Haka dai muka fito yara da manya sun zagaye motocinmu suna kallo. A ƙofar wani ruɓaɓɓen gida da duk katangar ta cinye ana hango komai na cikinsa, ɗakin kansa wasu ɓangarori sun rushe an saka langa-langa ne da tsummuna harma da itace. Haka muka bi bayan Mammi kowa na yamutse fuska. Sai da muka shiga sosai mukaga yamushshiyar tsohuwar da tafi gidan gajalewa zaune acan ɗan lungu ta zuba tagumi tana kallon waje ɗaya. Sallamarmu ce ta sakata dawowa firgigit ta juyo tana kallonmu. Da alama ganin Mammi ya saka jikinta fara ɓari. Mammi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login