Showing 405001 words to 408000 words out of 438336 words

Chapter 136 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2230

musu. Falaq da Hayatu da Jaga Hafizzullah suma ba'a barsu a baya ba. Waje dai kam sai sambarka kawai.
Duk fa wannan al'amari dake faruwa a idanun su Mom ne da tun ɗazun da suka iso taci karo da Mansion illahirin jikinta ya dakata da aiki. Sai hawaye, wani abu daya dinga yunƙuro mata a ƙirji yasa babu shiri ta bukaci shiga toilet. Toilet ɗin kusan neman gigita mata lissafi yayi, ta hau tari sai ga jini. Kuka sosai taci a bayin tana kallon jinin data tara a cikin hannunta. Ita kaɗai tasan abinda take ji a zuciyarta. Wannan wane irin al'amarine haka mai ban ruɗani. Shiyaysa tacema Ummanta bazata zo ba. Amma ta takura akan su zo kodan suga tsiyar da za'ayi. Damunta da Umma tai da knocking yasa dole ta buɗe bayan ta wanke fuskarta ta fita. Data fito ɗin ma ta samu an baje musu tarin abinci na alfarma da sai a gidan girma. Sai abinda kake so zaka ɗiba kaci, ga Halime sai dai zuba santi take ta kasa zuane ta kasa tsaye. Ashe ba'a nan abun ya tsaya ba, aka kwaso su kuma zuwa wajen nan daya ida gigita tunaninta. Harda matar shugaban ƙasa fa. Bama wannan ba, yanda aka ɗaukaki al'amari Samraah na bata mamaki da tsoro, koyaya ta motsa Maash na ankare da ita. Hakama mahaifiyarsa. Yaya Musaddiq kam duk abinda sukema ɗan su Fahad basu babbanta shi ba. Suna ɗaya ake kiransu da shi, ƙannen Maash. Ana cikin taron mahaifiyar Maash taje har inda su Samraah suke ta kamo hannunta ta dinga zagayawa da ita wajen manyan matan dake wajen suna gaisawa. Tsabar wulaƙanci tana ata gefen wata matar Minister amma ko kallonta Samraah batai ba kamar ma bata ganta ba, alhalin har haɗa ido sukai. Sai kuma can ta hangosu inda Halime take har Ummie na ɗaukar yaro ɗaya a cikin yaran suna dariya cike da nishaɗi. Akazo wajen liƙa kuɗi, Samraah da Maash fa daloli suka liƙa su. Akazo kuma aka lulluɓesu suma da liƙin. Ga kalaman da Maash ya dinga zubawa akan Samraah ɗin kansa tsaye cikin tsananin kulawa da tattali. Itama kuma ta zuba a kansa. Jitai ma gaba ɗaya idan ta cigaba da lissafin zuciyarta zata buga. Sai kawai ta tashi ta fice a hall ɗin idanunta har kamar ma basa ganin hanya da ƙyau...

Ba Mom kawai ba, acan asibiti jikin Baba prof da Hajiya ƙarama rikicewa yayi. Dan shi jijjiga ya fara kamar irin na mace mai naƙuda ya dinga taune lips suna jini kumfa na fita ta bakinsa ta hanci. Ga idanunsa ƙyam akan television. Itako Hajiya ƙarama kuka take iya ƙarfinta tana jama mahaifin nata ALLAH ya isa. Itama dai daga ƙarshe sai da doctors ɗin suka mata allurar barci.......✍️

Kuce dani ina Paah🏃🏃🏃?.


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒏𝒊𝒏𝒆_


*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.

*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._



......Paah na gida yana kallon komai shima. Dan tunda suka dawo ɗaurin aure can gidan Prof Uncle Abdullahi ya kaishi inda Hajiya Mammah take zaune kasancewar an sallamesa asibitin. Babu yanda Uncle Abdullahi baiyi da shi yaje dinner ɗin ba amma yace bazai iya ba. Wlhy bazai iya haɗa ido da Ummie ba, balle Muhammad da Fahad kuma. Dama ɗaurin auren da ƙyar ya iya dake zuciyarsa ya je. Dan kawai yana son ya halarta ne tunda bai samu zuwa na Maash ba a wancan lokacin. Haka dole Uncle Abdullahi ya barsa. Amma sai yace masa ya kalla to ko'a tv ne. Shine yay zaman kallo shima. Gaba ɗaya murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Ga hawaye sun gagara tsayawa. Ji yake inama ya dawo da baya ya goge dukkan abinda ya aikata ya zama kamar ba'ayi ba. Yasan ya tafka kurakurai masu yawa a rayuwarsa da shi kansa baya jin zai iya yafema kansa balle Ummu-Hidaya. Ya mata abubuwa da yawa a rayuwa da ya kamata ace ta yanke alaƙa da shi tuni amma ta jure ta cigaba da zama da shi har zuwa gaɓar da mahaifinsa ya aikata mata abinda bai taba sani ba, bai taɓa zato ko tsammani ba. Tabbas bama ita ba su kansu mahaifinsu ya zalincesu, ya cutar da su da rayuwarsu. Ko'a mafarki bai taɓa tunanin zai iya kwatanta abinda ya aikata ga mutum irin Abie ba. Wannan wace irin cin amana ce mai saka ruɗani da barazanar keta zuciya. Kuka mai ƙarfi ya sarƙeshi. A cikin wannan halin Uncle Abdullahi ya shigo a rikice yake sanar masa ya tashi suje asibiti jikin baba ya rikice. Ji yay tamkar yace bazai je ba. Amma dai ya daure dan yana son yin tambayoyi ga mahaifin nasu kafin shi ko shi wani ya bar duniya. A wannan gaɓar har cikin zuciyarsa yana fatan barin wannan duniyar ne....


🌿🌿🌿🌿


Alhamdullah taro ya tashi lafiya, anguna da amare sun kasance tare da juna. Washe gari baƙi da yawa suka kama gabansu. Ƴan Kano ne kawai suka rage. Sukam sai sunga wucewar Yaya Musaddiq da matarsa shiyyasa. Zuwa yamma manya suka yima anguna da amare nasiha da addu'a. Musamman ma Yaya Musaddiq da zasu wuce a ƴau China. Bayan sun kammala Yaya Awwab ya zauna da mu. Yaya Musaddiq, Aunty Falaq, ni sai Hafizzullah. Ya fara da mana nasihar riƙe junanmu da gaskiya. Tare da ɗaukar nauyin mu ya danƙa ga Yaya Musaddiq a matsayinsa na babba garemu a yanzu kuma uba. Ya nuna masa tarbiyyar daya bamu itace zamu haɗu mu gina family da har ƴaƴanmu zasuyi alfahari damu anan gaba kodan ƙoƙarin mahaifinmu. Daga ƙarshe yay maganar company da Abie ya bamu. Ya bamu shawarar za'a raba companyn bisa tsarin shari'a garemu matsayin gado. Sai kuma mu dunƙuleshi waje guda mu ginashi da ƙarfin ikon ALLAH. Abinda dai yake so mu gane anan ya kasance kowa yasan hakkinsa da kuma abinda zai dinga shigo masa koda anan gaba ALLAH ya ɗauke wani a cikinmu bazai zame mana rikici ba ko ya zame wa ƴaƴanmu.
Mu duka mun gamsu da shawararsa. Mun kuma masa godiya. Daga haka kuma kamar yanda ya faɗa aka ɗunguma tare da manyan iyayenmu zuwa wannan company. Ashe ma ana abubuwa cikinsa. Sai dai ba wani ƙato bane amma watarana in sha ALLAHU idan mun jajirce ALLAH ya kuma amsa zai kai ma inda ba'ai zato ba. Sheikh Muhammad ibn Khalipha Al-Hussain ya mana rabo na adalci, kowa yasan tsaginsa, ya kuma mana nasiha shima dan yau zai wuce...

Muna dawowa gida su Yaya Musaddiq sukai shiri. Rakkiya mukai musu airport. Bayan zaman mintuna kusan talatin jirginsu ya ɗaga shi da amaryarsa Ruƙayya. Baiwar ALLAH tanata kukan rabuwa da iyayenta. Haka dai suka tafi kowa na musu fatan alheri. Yayinda na koma sukuku ni kuma. Dan mun bar Mom a gida tanata aman jini. Su Hayatu dai suna shirin tafiya da ita asibiti. Daga nan asibitin muka wuce muma. Mun samu Alhamdullah jinin ya tsaya har sun sakata barci. Nan dai akai mata addu'ar samun lafiya muka wuce gida.
Banyi mamakin samunsa a gidan ba harma ya kwanta wai kansa ke masa ciwo. Nasan harda wannan hayaniyar. Wanka na farayi sannan na haɗo masa shayi. Da ƙyar na samu ya tashi ya sha. Magani kuma yace bafa zai sha ba. Iya lallaɓa yaƙi, dole ba haƙura na masa addu'a kawai muka kwanta dan nima takaina nake.
Washe gari mutanen Kano suka wuce suma da Mom a haka. Aunty Halime ta tafi ta barmu da dariyarta. Gidan ya koma shiru da ga mu sai mu. Sai masu aiki da keta ƙoƙarin saita komai. Ango da Amarya dai ko ƙeyarsu bama gani. Suna sashensu ana shan amarci. Sai dai a aika musu abinci a koma a ɗako kwano (Da gaskiyarka Fahad🤣😂).
Labarin rikicewar jikin Prof ta samemu a bakin Hajiya Mama da bata koma ba. Da farko dai babu wanda ya tanka. Sai daga baya Ummie tace mu shirya zamuje asibiti. Babu wanda baiyi mamakin jin batunba. Dan ko Maash da baya nan yaje Abuja yana dawowa dana faɗa masa kasa yin magana yay, sai idanu kawai daya zuba min. Sai kuma can ya miƙe ya fita. Ban san miya faru ba naga ya dawo dai ransa a ɓace. Bai gaya min ba ban tambayesa ba. Bayan sallar isha'i muka fita bisa umarnin Ummie. A asibiti mun samu duka yaransa tare da shi. Numfashi ma yanzu sai da abin shaƙar numfashi.
Tunda muka shiga ɗakin jikin Paah har rawa yake. Sam ya kasa haɗa ido da kowa a cikinmu. Ko gaisuwa da akayi da tambayar yaya mai jiki shi kam bai iya amsawa ba. Ni sai ma duk ya bani tausayi, ga ac a ɗakin amma shi zufa yake yi. Prof ma idanunsa a kammu ya ƙura ma Ummie su, da Yaya Awwab da tunda muka shigo yay tsaye a bakin ƙofa abinsa yana danna waya kawai. Bana jin ko gaisuwar da akai ma shi yayi. Baima kalla kowa ba. Miƙewa mukai da shirin tafiya prof ya shiga jujjuya kansa da shi kaɗai ne ke aiki. Uncle Abdullahi ne yay ƙoƙarin dakatar da mu, tare da matsawa gaban gadon ya cire masa oxgyen ɗin. Wani irin jan numfashi yay da ƙarfi har sai da muka tsorata, dan da sauri Bahijja ta shige jikin Fahad da ke kusa da ita. Cikin wani ƙarfin ya sauke numfashin idanunsa akan Ummie. Rawa lips ɗinsa suke alamar sonyin magana, sai da ƙyar ya iya tattaro abin faɗar muryar ma sam babu daɗi.
“Ummu-Hidaya kina gani kinci nasa ko?”.
Murmushi Ummie tai masa da gyara tsaiwa, batare data yarda ta kalla kowa ba ta ce, “So kake na tisa maka da bakina naci NASARAR ne? Dan nasan kai a karan kan ka kasan naci nasarar”.
Hawaye ne suka zubo masa, ya shiga jinjina kansa yana murmushi dake tabbatar da tsantsar takaicinsa da yanda zuciyarsa ke ƙuna. “Hakane Ummu-Hidaya. Na yarda kinci nasara, amma bazan taɓa karɓar FAƊUWA ba ni kuma. Domin kema baki ci nasarar ba sai da ƙarfin ikon ƊANKI”.
“Humm in dai har ka yarda naci nasarar ai Alhamdullah, domin idan ma ɗan nawane yaci ai kai da kaya duk mallakar wuyane. Saboda kaima yanzu daka tashi kiransa ƊANA kace.”
“Ɗanki kam, amma da jinin nawa ɗan nima. Shiyyasa ma ya iya irin NAWA salon. Domin TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE. Jinin ubanki bashi da ƙarfin da zaki samu wannan ZUMMAR ko shi ɗan naki ya samu”.
“Oh ashe akwai jinin ɗanka a jikinsa. To ai ban sani ba saboda ni kaina kawai nake kallo a matsayin mahaifiyar waɗan nan BARADEN. Idan kana tantama gasu nan ka tambayesu. Shin suna da wani ne bayan ni a matsayin wadda ta haifesu....”
Kafin ma ta rufe baki a kausashe Fahad ya amshe da, “Babu Ummie. Ke kaɗai muka sani, ke kaɗai kuma muke kallo. Kece DUNIYAR mu. Bayan ke daga ni har ɗan uwana ko DANGIN UBA bamu da su balle UBA. Kai ko tsohon BANZA ashe bazaka risina ba har sai kaji kanka a KABARI kenan? Ai kaima kasan dama itace mai nasara a kanka tun kafin yanzu. Kamar yanda Abie yake mai nasara a kanka dun kafin ita. Bakaji dama mita faɗa maka ba a wancan lokaci, kamar yanda ka ƙare rayuwarka a ƙarƙashin ƙafafun Abie. Haka zuri'aka zasu ƙare a ƙarƙashin ƙafafunta. Shin tsohon najadu baka fahimci wannan ayar bane ba a yanzu? Ko dai an maka filla-filla ne?. Gasu nan ka tambayesu. Su dukansu a ƙarƙashin ALFARMAR wa suke a da da yanzu. Ko kana tunanin badan ALLAH da MAZANTAKAR ɗan uwana ba da tuni kana bara a titi, su kuma suna can gidajen karuwai da ƴan maɗigo. Wlhy da ace akwai inda zanje a zuƙe jinin ɗanka a jikina da tuni na jima da tafiya. Ka iya bakinka kodan ka mutu a hannun ƴaƴanka, dan wlhy ina ɗaga maka ƙafa ne saboda Aunty Mama da Uncle Abdullahi. Amma ka sani wannan da kake gani tafi ƙarfinka. Shari'ar duniya kuma bata da lokacin yi da kai shiyyasa koda akace za'a kai ku kotu tace bata ra'ayi, muma kuma muna goyon bayanta. Wannan halin da ƴar shegen da kaje kayo ta saka ka ciki ya isheka. Ummie kumuje, ni banga amfanin ma ɓata lokacin yin magana da wannan wawan tsohon alakwan-kwan ɗin ba.” yaja hannun Ummie da Bahijja yana faɗin, “Aunty kumuje Please”.
Gaba ɗayan mu kamar an sagar mana gwiyawu. Sai dai ganin Yaya Awwab bai motsa ba duk muka kallesa. A mamakin mu Paah ya ƙure da idanu shi. Tsahon sakanni kafin ya sauke ƙafarsa daya dogara jikin bango, murya a dake ya furta, “Idan akwai igiyar auren Ummie a kanka, ina son ka yanke ta ta hanyar shaidar hakan. Idan kuma kaƙi zamu haɗu a court”. Daga haka ya kama hannun Ummie shima ya fice.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒆𝒏_


.......Mun iso gida babu mai iya cewa ko uffan. Ni dai harga ALLAH banji daɗin abinda sukai ma Paah ɗin ba. Koba komai mahaifinsu ne. Anji yayi kurkure, babban kuskure kuwa da magana ta ALLAH yafe masa ga ɗan da yasan zafin mahaifiya abune mai wahala. Sai dai kuma idan duk aka tattara akai haƙuri sai komai ya wuce. Koda muka kasance daga ni sai shi naso na masa maganar su ɗan sautama Paah ɗin, su kuma bashi damar neman afuwar Ummie, idan ta yafe masa suma suyi haƙuri su yafe masa. Tunda dai babu hannunsa a cikin manyan laifukan. Koda yake shima nashin babban laifi ne. Amma sai naji tsoron hakan. Dan kallo ɗaya kaima fuskarsa ta isa sakaka ka shiga hankalinka.

★★

A asibiti sun wuce sun bar cakwakiya. Dan Prof dai bakinsa yaƙi rufuwa sai tsinema su Fahad yake. A fusace Paah ya furta, “Ƴaƴana ba tsinannu bane ba baba. Kuma in sha ALLAHU bazasu kasance hakan ba. In dai kai baka kasance da tsinuwar ALLAH a kanka ba su mi sukai maka da kake aibanta min su?. Baba ka cutar da mu. Ka wulaƙanta rayuwarmu ta hanyar kasa godema ni'imar da UBANGIJI yay maka. Abie ya maka dukkan gata na rayuwa batare da kun haɗa komai ba. Ya tallafeka ya tallafi mahaifiyarka, ya tallafi matarka damu ƴaƴanka. Amma ka zaɓi sakashi a rana kai ka maye gurbin inuwarsa. Shin baba kai wane irin mutum ne? Bakaji komai ba a yayin salwantar da rayuka har shida saboda buƙatar DUNIYA mai yankewa? Bakayi tunanin kaima wataran zakaje inda suka tafi ba? Bakayi tunanin sune da nasara ba kai ne mai faɗuwa koda ace ka mallaki kuɗin daka salwantar da rayukansu a kansu. Kaicon mahaifi irinka, kaicon jini irin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login