Showing 288001 words to 291000 words out of 438336 words
da faɗin, “Zo ka zauna dan ALLAH. Yau fa favorite ɗinka nayi a gidan nan. Haba autan Ummie ƙanin Yaya Hayat ɗan Mama da Paah. Sannan Yayana ni kaɗai”
Sai da yaja mintuna kafin ya juyo yana kallona kamar zai yi kuka. Nima sai na marairaice masa fuska kamar zanyi kukan na ce, “Dan ALLAH ”. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi, tare da tahowa yaja kujera shima ya zauna kusa da Hafiz yana jan sirrin tsaki. Ɗagowa Maash ɗin yayi idanunsa har sun sauya kamanni. Da sauri na dafe masa hannu ina girgiza masa kai, ƙasa-ƙasa na ce, “Please”.
Cin abincin ya cigaba da yi bai sake magana ba. Dan haka dining ɗin yay shiru sai motsin cokula dana filet. Munyi nisa da cin abincin kawai mukaji ana knocking. Hafiz ne ya miƙe ya nufi ƙofar ya buɗe. Da ga inda muke muna jin yanda ya gaishe da mai knocking ɗin amma babu alamar an amsa masa. Kamar ma babu motsi. Juyowa Hafiz ɗin yay yana kallonmu. Kansa tsaye ya ce, “Yaya Baba ne”.
Ɗan jimmm yay kamar mai tunanin wane Baba, sai kuma ya ɗan kallan, ganin ya sake ɗauke kansa na fahimci so yake yaga koda mayafi jikina. ALLAH ya soni akwai. Cema Hafiz ɗin yay ya shigo, ya sake maida kansa ga abincin. Hafiz dai ya isar da saƙo, amma har ya dawo ya zauna ba'a shigo ba sai da Fahad ya miƙe yaje.
“Oh ALLAH Grandpa wai kaine da ma?.” yay maganar da kamo hannunsa suka shigo. Kallo ɗaya naima tsohon na fahimci a cikin shock yake. Sai kawai abin ma yaso bani dariya. A take kaina ya kawo wuta. Kaina tsaye nace ma Fahad, “Fahad kuzo nan Baba yaci abinci”. Murmushi ɗauke a fuskar Fahad kuwa yazo da shi har dining. Gogan kam tunda ya maida kansa ya duƙan bai sake kallon kowa ba abincinsa yake ci kamar baya so. Gaishe da Baban nayi ina ƙoƙarin zuba abinci a plate. Yanda ya amsa min kamar wanda ke'a cikin shakku har yanzu ya sani sakin murmushi da faɗin, “Baba ga abinci a saka mana albarka”. Murmushin yaƙe yayi, tare da jinjina kansa alamar to, daga haka kowa ya cigaba da cin abincinsa. Sai zuwa can a bazata mukaji ya ce, “Good morning ”. Mu dukanmu sai da muka kallesa, musamman ma Baba prof ɗin. Murmushi ya saki mai nuna tsantsar taɓuwar zuciyarsa. Kafin ya ce, “Ai na zata baka ganni bane.”
A mamakin mu sai Maash ɗin ya saki wani makirin murmushi. Kamar bazai ce komai ba sai kuma a hankali ya furta, “Wani abu ya faru a gidan ne na ganka da sassafe?”. Ba baba prof da yay ma tambayar ba hatta ni dake saurarensu sai da na shiga shock. Dan bai zama lallai Hafiz da Fahad su jisu ba sun ɗan yi nesa da mu, sannan hankalinsu nakan waya ne alamar akwai abinda suke kallo........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_
.......A mamakina murmushin Baba prof ɗin ya ƙara saki, sai kuma ya kai hannu saman kan Maash ɗin ya wani ɗan birkita sumar da yau bai ɗaure ba. Cike da son danne komai da fuskarsa ke son bayyanawa ya ce, “Ja'iri, dama sai wani abu ya faru nake zuwa da sassafe?. Kwana biyu ban zo naga daughter ɗina bace. Nayi busy da yawa shiyyasa yau dana samu chance nace bari na shigo”.
“Hummm”.
Kawai Maash ɗin yace.
Bakin Baba prof ɗin ne ya motsa kamar zai yi magana sai kuma yay shiru sakamakon shigowar Hajiya Mammah. Mu duka kallonta mukai banda gogan. Harara ta zuba mana ta ɗauke kanta. Niko sai na fuske nace mata “Mammah ina kwana”.
“Daban kwana ba zaki ganni ƴar tsirku. K! K! Ki kiyayeni ki fita idona. Wlhy idan kika bari na waiwayo kanki tofa kin shiga dubu bama uku ba. Idan su waɗan nan sihirinki ya cisu to ni bai cina. Dan nafi ƙarfin iyawarki nima shegiyar kaina ce nan da kike gani. Haba wace irin masiface wannan yarinya kin zame mana ƙadagangaren bakin tulu. Ƙiri-ƙiri kin mallake uwa da ƴaƴanta ke ga ƙwalluwar tantiriya. To wlhy yau sai kin bar gidan nan da ƙafafunki”.
“Ko kuma ke ki bar mata ba. Wai ke Mammah minene matsalarki? Masifa dai masifa dai kamar grandma. Ita mun samu ta mutu mun huta da nata jaraban ashe ta bar mana gadon ki. Can kin ishi mijinki ya koroki kin zo nan kin dame mu. Ina ruwanki, ba mallakewa ba tama haɗa wuta tayi farfesunmu ta cinye a cikinta ai dai ƴar uwarmu ce. To bari na baki labari wannan tana da matsayi mai girma a wajen mu. Dan har abada bazamu taɓa wulaƙanta zuri'ar Uncle Abdul-wahab ba. Ke kwanan nan ma zaku ganta matsayin matar aure a gidan nan kin ishe mu”. Ya wani ture plate ɗinsa ya bar wajen yana jan hannun Hafiz. Mu dukanmu da kallo muka bisa, a raina tausayinsa na kamani, dan na fahimci shi Fahad sona yake.
A mamakina sai naga gogan da tun da aka fara ihun yake ma latsa waya ya wani saki murmushi. Yayinda Hajiya Mammah ta kira sunan Fahad da ihu sosai. Amma tsabar wulaƙanci sai da yaje ƙofa ya juyo ya harareta da faɗin, “Kin je kin kira Grandpa to shima sai dai ya sake share musu waje dan yasan muhimmanci Uncle Abdul-wahab idan ke baki sani ba. Amebo woman a canja hali.” ya mata gwalo ya fice.
Haukacewa ne kawai Hajiya Mammah batai ba saboda azabar masifa. Dan har sai da takai Paah da Uncle Abdullahi sun zo sashen, can sai ga Maman Malika da Hajiya ƙarama. Kuka sosai Hajiya Mammah keyi wai Fahad ya zageta ta uwa ta uba kuma nice na sakashi. Sannan Awwab na zaune baice masa komai ba. Ita wlhy yau bazata yarda ba sai ta bar gidan nan. Har kamar ita Fahad zai wulaƙanta saboda tana zaune a gidan uwarsa. Ta ma fahimci Paah ne ke sakasu musu rashin mutunci.
Rai a ɓace Paah ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Point of correction Addah, nifa ki daina sakani a sabgarki da yaran nan yanzu. Dan kin fimu sanin mike tsakaninku. Bafa rami babu abinda zai kawo rami. Dan haka a can da kuka ƙulla ku warware kanku.”
“Ni kake gayama haka Mu'azz? Ni kake gayawa magana akan ƴaƴanka?”.
“An gaya miki Adda, wai yaya kike son nayi ne nikam. Dan ALLAH ku barni da abinda ya dameni. Nifa gaskiya nama fara gajiya da zaman kowa a gidan nan. Idan akwai matsala ne kowa ya koma inda ya fito mana. Ai nan ɗin su gidan mahaifiyarsu ne. Bamu da wani dalilin kuma zuwa mu tare a cikinsa. Koni da nake auren Ummu-Hidaya idan bata yarda na zauna mata gida ba bani da wani ƙarfin ikon yin hakan. Idan ance Awwab nada taurin kai kowa yasan Fahad a gidan nan na kowa ne. Amma gashi nan shima kuna neman kangarar min da shi bai shakkar kowa bai kunyar kowa a yanzu. Baba ya kamata kayi wani abu a wannan karon, idan ba hakaba magana ta ALLAH ka cigaba da shiru ana cigaba da aibanta min yara tofa ni da kaina zan ɗau mataki wlhy, dan ina sonsu fiye da komai, zan kuma tsaya na kare musu mutuncinsu kamar yanda kowa ke kare mutuncin nasa ɗansa. Da ɗin ma ina muku kawaici ne kawai amma na fahimci Adda bata san kawaici ba. Kai kuma a matsayinka na babba baka taɓa ganin laifinta balle ka tsawatar mata. Sai kace wai a barta da halinta ta gado Mama ne. Mama ai uwace a garemu zamu iya haƙuri da ita amma ita ɗin fa. To na gaji kowa ya koma inda ya fito kawai a barsu a gidan mahaifiyarsu su huta suma”. Yana gama faɗa ya fice fuuuu harda bugo ƙofa da masifar ƙarfi.
Yanda falon yay tsitt zai baka tabbacin kowa yayi sumar wucin gadi ne. Idan ka cire mai gayya da aiki da har yanzu yake faman latse-latsensa a waya daɗa duniya baya a wajen ne. Fuskokin kowa na fara bi da kallo. A mamakina Uncle Abdullahi murmushi yake yi. Hakama matarsa. Amma Hajiya Mammah, Hajiya ƙarama, baba prof ba'a magana. Hajiya Mammah dai hawaye take sharewa (gaskiya sai anyi shari'a, taya za'a saka gimbiya mandiya Hajiya Nafisatu bint Adams kuka😂😝). Hajiya ƙarama kam kamar jikinta rawa yake, ga wata irin zufa ta jiƙeta kamar ba ac a falon. Haka ma Baba prof zufa kawai yake har jikin hularsa ta nuna shatin laima, kansa dai a ƙasa baka ganin idanunsa da fuskarsa da ƙyau. A hankali na zare jikina daga wajen na shige ɗakin Ummie, a laɓe na samu Mama da alama itama show ɗin take kallo. Murmushi ta sakar min dan haka nima na maida mata murtani. Sai tamun jinjina. Dariya abin ya bani na ce, “Kai Mama. Ai ɗanki ne abin jinjina. Jibafa yanda yake zaune kamar baima san ana komai ba ya bama banza ajiyar kowa. Ga kuma Auta ya tunzura ya gudu. Ashe shima haka yake?”.
Ƙaramar dariya tayi da faɗin, “Ai hakan shine dai-dai. Dama shi Alhaji Ƙarami haka yake musu ya manna musu hauka ya watsar da su musamman a tsakanin nan na rasa miyasa. Fahad kuwa ai da zafinsa ya dawo da alama addu'armu na karɓuwa. Alhaji Mu'azz bai taɓa birgeni a rayuwa irin yau ba. Bawan ALLAH ashe shima yana ƙaunar ƴaƴansa. Ni kam zargina ya fara barin kansa. Amma bakiga murmushin da Alhaji Abdullahi da Maman Malika suke ba”.
“Na gani sarai, amma abinda zai baki mamaki su kamar babu wata damuwar komai tare da su sai ma daɗi da suke ji”.
“Tabbas naga hakan. Amma mutum ne baka yarda da shi sai yazo ya maka kwaf ɗaya. Shi kansa Paah ɗin sai fa naga ƙuru-ƙuru baida laifi zan yarda”.
“Haka ne kuma gaskiya Mama, ALLAH dai ya daidaita Yaya da Fahad a fara aikin Maja”.
“Amin ya rabbi ƴar albarka. Ai kece ginshiƙin komai”
Hannu nasa na rufe fuskata ina murmushi.
Jin shiru alamar sun bar falon yasa na fita. Har yanzu gogan na wajen zaune. Tattare kayan na shigayi. Batare dana ce masa komai ba nima. Ina kitchen ina wanke kwanikan da muka ɓata ɗin sai gashi ya shigo. Ni tsoro ma naji da farko. Dan yazo gab dani ne ya tsaya. Koda na juyo har karo muka ci. Da ga ni har shi sai da kowa ya dafe inda ya bugu. A ɗan shagwaɓe na ce, “Yaya ALLAH ka bani tsoro. Mi kake so?”.
Cikin tsareni da idanun nan nasa ya nuna min lips ɗina. Sosai na waro nawa idanun, sai ya ɗaga min gira. Kunya ce ya kamani. Nai ƙoƙarin juyawa amma ya hana hakan. Mun ja kusan minti uku a wajen dan sai da yay yanda yaso sannan ya janye lips ɗin nasa daga nawa. Hakan ya sani faɗawa jikinsa na rungumesa dan ƙafafuna ma ji nake sun gagara ɗaukata. Nan ma munja kusan minti biyu kafin na ɗago a hankali. Ina ƙoƙarin juyawa ya dakatar dani. Muryarsa a shaƙe ya ce, “Inaga zamu wuce yanzu”.
Da mamaki na kallesa na ce, “Ina?”.
“Nema mana”.
Sosai naji gabana ya faɗi, ni har ina murna ya ɗan rage tafiye-tafiyen tsiyar tashi ashe ba haka bane ba. Kuma tsabar manni irin na mutumin nan ace zakai tafiya amma sai yanzu kake sanarma matarka. Jinai raina ya sosu. Amma sai na daure na danne na masa murmushi. Dan na fahimci nice zan canjasa, amma yanzu ban isa cewa ga yanda nake so ba tunda a haka ya tashi komai sai a hankali. Addu'a na shiga masa da fatan nasara. Yanda yake lumshe idanunsa nasan addu'ar ta masa daɗi. Sake rungumeni yay kusan na mintuna biyu kafin ya kamo hannuna muka fito. A falo muka samu Hayatu da Mama na magana. Dan haka nai ƙoƙarin zame hannuna a cikin nasan amma ya hana hakan. Gaba ɗaya naji kamar na nutse, da ƙyar na iya gaida Hayatu da tun kallo ɗaya da yay mana ya ɗauke kansa. Mama ko bama ta nuna taga mi muke ciki ba, sai addu'a take kwarara masa. A hankali ya amsa mata da amin tare da godiya. Sannan ya ɗora da faɗin, “Mama Falaq zata dawo gida ta haihu. Inaga sai a saka a gyara mata bedroom ɗin nan na kusa da Ummie. Sannan za'a kawo sabbin masu aiki nan sashen.”
Murmushi Mama tayi da satar kallon Hayatu da ya ɓata fuska yana kallon Maash ɗin. Kamar zai fasa ihu ya ce, “Yaya nace maka a camma fa babu wata matsala”.
Hararsa yayi da faɗin, “Na gama magana. Idan ta haihu ka ɗauketa kuma tafi bangon duniya, yanzu dai zata dawo gida ta haihu”.
Dariya abin nasu ya bani, nai ƙasa da kaina ina murmushi. Mama ma ina ganin tana murmushin, yayinda Hayatu ya cika yay fam.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒇𝒕𝒚_
.......Hannuna yaja muka shiga wajen Ummie, tana zaune shiru abinta ta zubama television da ake karatun Alkur'ani ido dan yanzu haka muke yini da kwana da karatu. Har gabanta mukaje muka durƙusa, ya kamo hannunta ya riƙe cikin nashi. Juyowa tayi ta kallemu, sai kuma ta kalla hannunsu ta kuma maida ta kalla nawa da nashi dake a haɗe. Ta jima tana kallon hannayen namu kafin ta ɗauke kanta. Yanda yake mata magana da roƙon ta masa addu'a sai da naji hawaye sun cika min ido. Haka dai muka fito batare da tace masan komai ba. Sai dai har cikin raina naji daɗi da banji yayi complain kansa na ciwo ba yau. Alhamdullahi hakan na nuna ALLAH na amsar addu'armu...
Har waje haka ya fita hannuna a cikin nashi. An gama shirya motoci harda ƙyamishashshiyar baturiyar nan. Ashe har lokacin Baba prof na gidan. Dan muna fitowa shima yana fitowa tare da Uncle Abdullahi da Hajiya Mammah. Ko kallon inda suke baiyi ba, sai ma jinginani da yay jikin motar ba kunya ya sunkuya ya sumbaci goshina da lips ɗina. Inaga tunda nake a rayuwata ban taɓa shiga cikin kunya irin yau ba. Tabbas na yarda mutumin nan bai san kunya ba. Compound ɗin da mutanene sosai. Masu aiki, su baba prof, su Hayatu kai jama'a ina cikin jalala ni dai.
“Hafiz zai biyomu zuwa jibi in sha ALLAHU. Dan na canja masa school. Barinsa a Nigeria yanzu akwai haɗari saboda za'a iya amfani da shi domin cin dundumiyar mu. Ta ko ina bana san ya cutu akan laifin da ba nasa ba. UBANGIJI ne bangona. Ke kuma kece Hope ɗina Samrh. Dan zan barki ne matsayin tarko. Ga Ummie nan, ga Fa.. ha ..d nan”. Ya fadi sunan a rarrabe da ƙyar. “Dan ALLAH motsin kowannensu na dinga sani, suma tarko ne. Duk abinda kike buƙata ga TJ nan ga Shu'aibu. Ki faɗama Fahad zai samesu. A yanzu tako ina a sashen nan akwai camara da securitys, da ɗin ma dan bana zama ne babu kowa shiyyasa. Yanzu ko nasan ina da Tiger a gida na ko?”.
Yanda ya ƙare maganar ne ya sa nayi dariya. Shima sai ya murmusa. Ba ƙaramin shock na gani a fuskokin wasu da murmushin nasa ba. Koda ya shiga mota da aka buɗe mosa sai naji kuma duk babu daɗi, kaina a ƙasa na sake jera masa addu'a. Lips ɗinsa ne kawai ke motsawa alamar Amin. Kafin a hankali yace, “Wuce kije ciki”. Banyi masa musu ba na juya na tafi, sai da naje zan shiga na juyo, a kan iska na rubuta masa (I miss you) na shige abina ina murmushi idanuna cike da ƙwalla. Tabbas na yarda sabo ake ma kuka ba mutuwa ba. Cak na tsaya ina kallon Ummie dake jikin window ɗin falon tana leƙen komai. Harga ALLAH sai da naji shock. Amma sai na dake na nufeta ina share hawayen nawa. A mamakina ina zuwa gab da ita ta buɗe