Showing 333001 words to 336000 words out of 438336 words

Chapter 112 - Tsutsar Nama Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

2228

Uncle Abdullahi bai damu ba ya cigaba da yin maganarsa. “Ina son kamar yanda kayi kawaici ƙin nuna kasan nine a da yanzu ma ka cigaba da tafiya a hakan kawai na baka san ni ɗin waye ba. Dan tunda na fara aikin nan sai fa na kaisa in sha ALLAHU”.
“Uncle Amma....”
“Chapter is closed Awwab”.
Uncle Abdullahi ya faɗa cikin katseshi. Numfashi Maash ya furzar da faɗin, “Shi ke nan. Yanzu wane taimako kake buƙata. Dan duk yanda kake tunanin abun ya wuce hakan”.
“Nasani Awwab. Dan laifukan da masu laifukan sun kasance rassa daban-daban. In dai akwai wasu imformetion a wajenka ka bani su kawai zakaga yanda aikin zai cigaba da tafiya. Na kuma maka alƙawarin komai gareka zai zama a buɗe. Hatta da shawara zamu iya nema ta wajenka dan na fahimci kai bana wasa bane”.
Girgiza kai Maash yayi kawai batare da yace komai ba. Sai daya ja kusan minti ɗaya kafin ya ɗago. “Baka da matsala ina sha ALLAHU. Sai dai ina son ka bama Baba damar ganin Commondo dan hakan nada matuƙar amfani. Musamman ga ita matar nan dan akwai abinda take ƙoƙarin shiryawa kenan da ya kamata muyi saurin ganota”.
“Okay na fahimceka. Wato shiyyasa taje ta shirya ma Baba wancan ƙazon kuregen kenan na cewar Commondo ne yay kidnapping Yaya? Duk da ni inama zargin kamar tasan komai”.
Ɗan wani luuu da idanu Maash yayi sai kuma ya buɗe akan Uncle Abdullahi. “Tare da ita sukai komai”.
“What! Kana nufin harda ita akai kidnapping Yayan? Kenan itama tana da alaƙa da Commondo ɗin?”.
Ƙaramar dariya data bama Uncle Abdullahi mamaki Maash ya saki. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa. Kansa tsaye ya ce, “Uncle wannan zaren tsayinsa yafi na igiyar wutar lantarki. Idan nace zan maka bayani yanzu akan komai, bama zaka iya fahimta ba. Amma ka bani lokaci”.
Ya ƙare maganar yana miƙewa. Cikin girmamawa yay masa sallama ya fice abinsa yana wani makirin murmushi. Dan kuwa shi kaɗai yasan mi yake shiryama ransa. Zuwansa nan kuwa nada dalili da nasaba da son sanin ainahin abinda ke a ran Uncle ɗin nasa da kuma son tantance a wane matsaya yake yanzu...

Da sauri Jaga da Hayatu dake zaman jiransa duk suka miƙe. Gaba yay suka take masa baya. A waje ma su Shu'aibu na jiransa. Nan ma TJ ne ya buɗe masa mota. Jaga da anan suka haɗu da shi dama Maash ya ce ya shiga gaba. Shi kuma Hayatu ya dawo kusa da shi.. guards ɗin kuma duk suka shiga motocin su suma....

💢🌟💢🌟💢

Kamar yanda Baba prof ke a hargitse haka Hajiya ƙarama ke a harmutse. Dan ita koma wankan bata nema yi ba tana isowa gidan ta shige ɗaki ta kulle kanta. Bige-bigen wata ta fara. Ana ɗagawa ta ce, “Please ina son mu haɗu”.
Ban san amsar da aka bata daga can ba ta dai jinjina kan ta yanke kiran. A gurguje ta canja kaya dan yanda take jinta bata jin zata iya wani zaman yin wanka. Cike da fatan ALLAH yasa kada ta samu kowa a falon ƙasa kamar yanda ta shigo bataga kowa ba tayi. An koyi Sa'a babu kowan, dan akwai sauran safiya duk basu tashi barci ba masu gidan. Mota ta shiga ta fita a gidan duk da yanda take jin jikinta babu daɗi. Yanda take ɗibar motar yasa ta isa inda take harin zuwan da wuri. Can gefen gari ne wani ɗan ƙauye ko kuma ma mu kirashi club kawai dan mahaɗace ta gawurtattun ƴan iskan criminals ɗin Lagos ɓoyayyu da wasu manya suka ɗaurema ƙugu. Mata ne da maza a wajen ana ashararanci. Sai cinikayyar mugayen abubuwa na maye dana ta'addacin da ake gudanarwa. Mafi yawan waɗanda suka san wannan waje ƴan ɓadda sawune. Kasancewar safiya ce tsirarun mutane ta samu dan ansha shagalin dare duk sun zube barci wasu kuma sun kama gabansu. Sai masu kula da wajen ne keta aikin tsaftacesa sai kuma irin ogan da sunci dubu sai ceto kansu na iya ɗaukar kowane kalar kayan maye yanzu batare da sun jigata ba. Kamar yanda ƙa'idar take sai da aka binciketa tsaf sanan aka nema mata iso wajen boss ɗin. Mintina kusan ashirin aka shiga da ita ciki. Ƙaton falone da yaji kayan more rayuwa dan an shirya liyafar duniya a cikinsa. Gini ne to iya gini aka zuba a cikin jejin nan. Sai kuma aka bisa da iccen bamboo aka rufe ta yanda zaka ɗauka da shi aka yi san. Tana nan zaune kusan mintuna biyar ma sannan ya fito. Fari ne tass ƙarfaffan gaske jiki duk ya buɗe ya kuma sha zanen tattoo. Rantalelen kansa sai ƙyalli yake saboda yanda aka ƙwalƙwale gashin tsaf. Sam fuskarsa babu walwala amma yana ganin Hajiya ƙarama ya ɗan saki murmushi yana kaiwa zaune da faɗin, “Manyan ƙasa yau dai aƙalla an tuna da ni kenan?”. Cikin harshen turanci
Murmushin yaƙe ta saki da faɗin, “Hummm Marcel dama ban manta da kai ba. Kawai dai abubuwa ne suka min yawa. Ya naka?”.
“Komai normal muna nan muna zubawa? Da alama ta ƙwaɓe dan naga an kama mutuminki. Sai dai abinda ya ɗauran kai kamar wanda kike zaune a wajensa yanzu naga ance yayi kidnapping ko har yanzu dai yana sonki?”.
“Hakane Marcel. Sai dai duk abinda ya faru tare mukayisa. Abinda yasa na nemoka saboda Jannifer itama dai yarinyarka ce. Nasan kuna harkar bussines sosai batun yanzu ba. Na kuma san a tsarinka duk wanda ke tare da kai in har ya faɗa hannun jami'an tsaro kasheshi kake sawa ayi. Shiyyasa nazo neman alfarmar shima Commondo a kawar da shi kawai a lokacin kawai da Jannifer”.
Wata shaƙiyyyar dariya Marcel ɗin ya saki, sai da yay mai isarsa sannan ya tsagaita da faɗin, “Ada Jannifer ke yarinyata. Amma tuni na saidata ga Bancy. Shiyyasa bani da wata alaƙa da abinda ya sameta yanzu”.
Da mamaki Hajiya ƙarama ta ce, “Amma bata taɓa faɗa min ba”.
“To wannan tsakaninku ne kuma. Yanzu dai idan kina son aiki akan Commondo sai muyi ciniki kenan. Sannan batun Jannifer ki samu Bancy ɗin dan tabbas bazai barta a hannun jami'an tsaro ba. Daga nan kuma zuwa dare zai iya sakawa a saketa dan shi kinsan ba irin tsarinmu yake ba.....”
Sosai hankalin Hajiya ƙarama ya tashi, dan tsakaninta da Bancy fa sam babu jituwa. Idan kuma har yasan akan yimata aiki Jannifer ta shiga hannun kwalawa tabbas ya samu makamin yaƙarta kenan. Ina bazata faɗi ƙasa haka wanwar a tsakkiyar ƴan iska ba. Dan haka kai tsaye ta fito fili ta ce, “Akwai matsala kenan Marcel. Dan kasan bama shan inuwa ɗaya da Bancy yanzu. Idan har ban kawar da Jannifer ba zai yi amfani da wannan damar domin fallasa ni.”
“Eh kema kince wani abu. Sai dai gaskiya zan gaya miki dan kin san ni bana ɓoye-ɓoye a aiki. Ni da Bancy akwai yarjejeniyar da ta hana mana yin aiki a tsakanin mutanenmu. Dan haka banda lasisin kashe miki Jannifer sai dai Commondo kawai. Dan haka kije ki sake sabon tunani akan Jannifer saboda kin santa bakinta reza ne.”
Sosai hankalin Hajiya ƙarama ke'a tashe. Amma sai ta danne ta amsa masa da “Babu damuwa. Ka faɗi ko nawa kake buƙata akan Commondo, sannan yaya maganar poison ɗin nan na wajen doctor Khunal?”.
“Ki nemesa kuyi magana. Tunda kema kin san laifinki ne. Tun 3 to 4years ya haɗa abunnan amma kina jan jiki. Ki dai yi fatan bai saidama wani ba kawai. Dan kin sanshi dai akan kuɗi baya wasa mugun ba indiyen mam”.
“Ba damuwa zan nemesa. Lokacin amfani da abunne bai taso ba sai yanzu. Miye kuɗin aiki na? Dan bayan an gama da shi akwai wasu har huɗu. Idan kuma su haɗuwarsu zai zama wahala ko a rarrabe a ƙaddamar dan bana son a wuce kwanaki uku nan to a sakama gidan duka wuta. Sai dai kafin hakan ina buƙatar Maash, Mu'azz & Ummu-Hidaya a raye”.
Dariya sosai Marcel yayi da faɗin, “Fantastic. Wai har yanzu kina wahala akan wannan project ɗin? Koda yake bakiyi jiran banza ba, tunda ta ƙara mai kam. A bazan ji tausayinki ba kawai naji babban alert. Ta shi kije kawai daren yau labarin mutuwar Commondo zata zo gareki. Sauran aikin kuma ma ƙarasa zancensa a waya”.
Murmushi kawai Hajiya ƙarama tayi tana miƙewa. Sai kuma ta miƙa masa hannu sukai musabaha sannan ta fice..........✍️

🤔Matar nan ko?..



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_


.......Kasancewar yau ma sharkaf na tashi har sai zuwa ƙarfe ɗaya saura na samu zazzaɓin jikina ya sauka yasa ni bansan wainar da ake toyawa ba a gidan. Cikin ƙarfin hali na taƙarƙara nayi wanka nayo alwala. Koda na idar da sallar ban wani damu kaina ba na saka doguwar riga mara nauyi na ɗan saka turare. Ina ƙoƙarin fitowa wayata ta hau tsuwwa. Ɗauka nayi na duba sai naga shine. Zaune nakai kafin na ɗaga. Saukar sassanyar muryarsa cikin kunnena ya sani sauke ajiyar zuciya. Sallamar tashi na amsa masa tare da gaisheshi. Shima cike da kulawa ya tambayan yaya jikin?.
“Alhamdullahi, Yaya shine ka fita ban sani ba”.
A hankali Maash ya lumshe idanunsa dan shagwaɓar tata ya jita har tsakar kansa. Cikin sake sauke murya shima ya ce, “Am sorry. Uzirin fitar ne ya taso min dole My Tiger. Ina fatan dai yanzu babu zazzaɓin?”.
“Ya sauka, har nayi wanka zanje wajen su Ummie yanzu ma”.
“Masha ALLAH, ki daure kici abinci to, nima anjima kaɗan zan dawo.”
Cikin sake narke murya da shagwaɓeta na ce, “Karfa ka daɗe”.
Ina jin saukar sautin murmushinsa cikin kunnena, sai kuma ya ce, “Okay bye” ya yanke kiran. Ajiyar zuciya na sauke tare da kafe wayar da kallo, sai kuma na ɗan sumbaceta. Duddubawa nai naga miss call nashi ritutu, sai na Gwaggo Gudidi da Abba. Ya Musaddiq ma yamun ɗaya. Sai Fahad da Hafizzullah da Aunty Falaq. Ajiyar zuciya na sauke nayi kiran Abba muka gaisa harda amaryarsa. Ya sake tabbatar min da yana nan tafe in sha ALLAHU shi da Kawu Musa. Nayi murna sosai ya bama Auta shima muka gaisa yau baije school ba wai babu lafiya. Gwaggo na kira itama muka gaisa, mun ta hira da ita har na sauka ƙasa. Acan mukai sallama. Babu kowa a falon dan haka na shiga ɗakin aunty Falaq mai jegon ƴan gayu. Yo jegon ƴan gayu mana tunda sabgoginta taketa zubawa ba kamar yanda naga masu jego na nutsuwa waje ɗaya ba ko ɗan suna ayi sannan. Amma ita yau kwana shida ko ina ƙafarta zuwa take a gidan nan. Na samu tana barci. Dan haka banyi magana ba na fito. Ina son shiga na gaida Ummie amma na kasa saboda yanzu ba ita kaɗai bace a ɗakin. Har na nufi kitchen dai na daure na koma ƙofar ɗakin. Knocking nayi kamar mai jin tsoro sannan nayi sallama. Bammayi zaton za'a jini ba sai naji an buɗe ƙofar. Hajiya Mama ce, tana ganina ta saki murmushi da faɗin, “A'a Masha ALLAH daughter ce? Jiki yayi sauƙi kenan”.
Murmushin nima na sakar mata kaina a ƙasa na rissina na gaisheta. Ta amsa min da kulawa tana jan hannuna ciki. Paah na zaune ya jingina da fuskar gadon Ummie a kusa da shi tana bashi magani a baki. Jinai nutsuwa ta ƙara ratsani ganin Ummie jiki dai nata ƙara sauƙi, gashi itama har tana jiyyar wani. Har ƙasa na durƙusa na gaishe da Paah ɗin tare da tambayarsa jikinsa. Ya amsa min a hankali dan muryar tasa bata fita sosai. A mamakina nima sai ya tambayen yaya nawa jikin? Sake ƙasa nayi da kaina kawai ban iya na amsa ba. Dan haka kawai naji kunyar amsawar. Ƙaramar dariya Ummie da Hajiya Mama sukayi. Sai kuma Ummie ta ce, “Zo nan Babyna”.
Babu musu na tashi zuwa gareta, zan durƙusa ƙasa ta kamoni ta zaunar kusa da ita. Duk sai naji na daburce. Amma ta hanani saukar da nake son yi. A haka na gaisheta da tambayarta jikinta dana Paah. Ta ce duk Alhamdullah yaya nawa nima. Itama kasa amsa mata nayi sai tai murmushi kawai. Cikin basar da zancen tace, “Ai munje dubaki ni da Mashi'a amma kinata barci.
Kaina a ƙasa na ce, “ALLAH Ummie bamma san kunje ba”.
Cikin murmushi ta amsa ni da faɗin, “Shiyyasa dama bamu tadaki ba. ALLAH dai ya ƙara afuwa. Mi kike son ci yanzu?”.
“Ummie bana jin yunwa”.
“No bazai yiwu ba. Rabonki da abinci tun daren jiya. Faɗa min mikike son ci?”.
Kafin na bada amsa akai knocking ɗin ƙofar, ba kuma a jira anyi magana ba ko anyi sallama kawai aka shigo. Hajiya Mammah ce. Sai da ta gama kallemu sannan cikin harzuƙa ta ce, “Eh lallai. Mu an hanamu zuwa amma Mashi'a na nan. Wai ko dai zancen Fahad ɗin gaskiya ne mune ake zargin mun haukata kin Ummu-Hidaya?”.
Murmushi kawai Ummie tayi batare da tace mata komai ba. Sai Hajiya Mama ce ta ce, “Kai Adda wane zancene haka kuma?”.
“K! saurara min da'alla auta. Wai shin gaskiya a buɗe sai muƙi faɗa saboda muna tsoron wa? Yo inba da gaske mune dai ake ganin mun haukatatan kamar yanda ɗan ta ya faɗa ba wane take-take ne wannan? To idan ance ke kada mu dubaki ai ya kamata ma musan shi ɗan uwanmu yana gidan muzo mu gansa muji daɗi ko. Ni narasa wannan al'amari haka komai a munafunce. Yaranki sun rainamu a gida, kowanne sai ya gasa mana magana. Ƙarshen raini ma da nuna mu ba'a bakin komai muke ba aure Awwab yaje yayi a ɓoye saboda gamu mayu kada mu sani mu cinye matar ko? Ko miye abin ɓoyewa ga ƴar drivern gida? To fa gaskiya ni ina son gidan nan ayi zama, dan bazan bar waɗan nan abubuwan da suka faffaru su wuce a banza ba nan gaba a sake samun hanyar wulaƙantamu ehe. Dan haka ALLAH ya baka lafiya Mu'azz sai anyi zama wlhy. Shima Abdullahi naga ashe ya fara zama almunafunfun, yo inba munafunci ba dan ya zama ɗan sanda sai ya wani ɓoye fisabilillahi. Gida dai gaba ɗaya babu saiti kamar an koro mu da ga dawa kowa ruɓaɓɓe”.
Babu wanda yace da ita komai. Ita Ummie ma ta maida hankalinta kaina ne kamar bata san tanai ba. Sai na fahimci itama fa tana da irin shariyar Yaya Awwab. Sai Paah ne ya kalleta cikin mamaki ya ce, “Abdullahi kuma Addah?”.
“Ƙwarai kuwa Mu'azz Abdullahi dai daka sani. Ni ba zamansa ɗan sandan bane ya ɓatan rai ba, yanda ya ɓoye mana sai kace abun wani mugun abu. Ko miye a cikin ɗan sanda kuma mtsoww!!”.
A mamakin kowa sai Paah ya saki murmushi. Bai kuma sake cewa komai ba ya zame ya kwanta abinsa. Nima kama hannuna Ummie tayi muka fita a ɗakin muka barsu.......


💦💦💦💦💦

Kai tsaye gidan Baba prof ta wuce. Dan ta gama tsara dole ta sake neman kusanci da shi in har tana son aikinta ya tafi yanda ta tsara shi. Tako yi sa'adar samun farkawarsa a barcin da giya ta sakashi kenan. Zuwanta yasa aka isar masa da saƙo. Ya jima baice komai ba dan mamaki, sai da ga baya kawai ya jinjina kansa da yin alamar ta shigo.
Tunda ta shigo cikin takun ƙasaita da izza yake kallonta kamar yanda itama shi take kallo. Sai da ta kai zaune ta saki wani murmushi da faɗin, “Barka da rana”.
Maimakon amsa mata gaisuwar sai ya ce, “Miya kawoki nan?”.
Murmushi ta sake saki tana langaɓar da kai gefe sai kuma ta daidaitashi. “Da gani har kai ka sani na sani muna buƙatar juna a wannan gaɓar”.
“Haka tunaninki ya baki”.
“Kaima haka naka tunanin yake yallaɓai. Kada kai wasa da wannan damar. Daga ni har kai muna yaƙi akan abu guda ne, sannan maƙiyanmu guda ne. Idan munce yaƙin ne bazamu iya tare ba lallai munyi kuskure. Kafin kuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login