Showing 435001 words to 438000 words out of 438336 words
ke zama farin ciki”.
“Hakane Yaya Awwab. Dukiya kam ta zame mana fitina a wannan ƙarnin, ga Mom nan ta jefa rayuwar Baby a masifa da har abada tabonta bazai gogu ba. Haka kuma zatai ta kallon al'amarin da ita ta jefata saboda itace ta kawo mata mijin. Sannan suka tausheta da asiri harta yarda da shi itama. Yaya Awwab ni dai inaga zan fita da Baby zuwa waje ko za'a dace, dan ba'a yankema bawa hukunci da rayuwa”.
Numfashi ya sauke a hankali, tare da janye jikinsa a nawa ya matsa jikin gadon ya gyarama Awwab dake neman zuwa gaɓa kwanciya. Itama Heedaya ya sake matsar da ita sannan ya dawo ta inda nake ya zauna tare da kamo hannuna ya zaunar a cinyarsa. Cike da kulawa yana wasa da yatsun hannuna masu lallen biki raɗam ya ce, “Sweetheart kiyi haƙuri, batun fita da Baby bazai canja komai ba, dan yarinyar ta kamu da ciwuka masu haɗarin gaske da suka riga sukaci jikinta matuƙa. A yanzu haka su kansu doctors ɗin sun tabbatar mana bazasu iya mata komai ba sai dai jiran lokaci. Shiyayasa nai magana da wani ƙwarren likita akan irin wannan fannoni na ɗauka hoton Babyn na tura masa amma ya tabbatar min da gaskiya samuwarta dai yanda ake buƙata abune mai wahala. Sai dai ba'a yankema ALLAH hukunci akan rayuwa ko mutuwar bawa. Baga mahaifiyarta nan ba, shekara nawa tana ciwon zuciya tama ƙi yarda a mata aiki amma har yanzu. Akwai dai magunguna da zai turo zasu iso gobe insha ALLAHU sai a dinga mata amfani da su a samu su wannan tsutsan ya daina fita a jikinta.”
“ALLAH ya bata lafiya to, amma gaskiya Mom ta cutar da rayuwar yaranta. ALLAH ya sa mu zama iyaye na kwarai akan ƴaƴanmu. ALLAH ya hanamu fifita ƴaƴanmu akan wasu ƴaƴa dan kawai bamu muka haifesu ba”.
“Amin ya rabbi.” ya faɗa a hankali yana kissing lips ɗina. Yana neman sakin layi na shige jikinsa da faɗin, “My Hot yara fa”. Ajiyar zuciya kawai ya saki da shafo kansa. Sai kuma ya miƙe yana faɗin, “Muje wanka na gaji”. Hakan ya sakani sakin murmushi, shi babu ruwansa ɓacin rai bai hanashi biyan buƙatarsa. Wani lokacin ma idan yana cikin damuwar yafi ta'azzara min. Ɗakinsa muka koma acan mukai wanka ko nace ma ya taimaka min dan bani da wani ƙarfi sam. Tea ya haɗa mana da kansa muka ɗan sha da cake muka kwanta.
Washe gari ganin Hafiz lafiya ya saka ni samun ƴar nutsuwa. Haka mukai shiri muka wuce asibiti da abincin da muka haɗa. Mun samu jikin Abba da sauƙi sosai, sai dai ya kasa daina hawaye da neman gafararmu dan yace hakkinmu ne ke bibiyar zuri'arsa. Mudai munta lallashinsa. Da yamma aka sallesa. Itama dai Baby an bamu ita za'a koma da ita gida dan magungunanta sun iso. Shansu kuma yafi zaman asibitin. Itama Mom ta matsa sai an sallameta duk da tana a cikin wani hali. Haka dai muka ɗunguma zuwa gida. Amma mi sai Abba ya ce ai Mom bazata sake shiga masa gida ba ya saketa saki uku. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Iya haƙuri an bama Abba ya barta taje tai jiyyar ƴarta ya ce ina ai ya gama kuma, shi zai yi jiyyar Baby da kansa. Ansha matukar koke-koke. Haka Mom ta tafi gidansu tana kuka da aman jini. Sai dai can ɗin ma Ummanta tace bazata zauna mata a gida ba. Sai yanzu ne tasan da ita a duniya kenan. Taje ma duk inda zataje ita ba damuwarta bace. Mutane sunta bata haƙuri ta rantse tace bata buƙatar Jalilah a rayuwarta har abada. Ko mutuwa tayi ma kar a bari ta zo kan gawarta. Wannan magana tata yasa Mom dinga zaginta tana tsine mata da faɗin ai koma mi ta zama ma sanadinta ne, dan itace ta ɗorata a layin son abin duniyar da har takaita da danne hakkin marayu. Aiko sai suka fara tsinema juna da zagi kamar ba ƴa da uwa ba. Mudai muna gida labari ya same mu.
A gurguje Please 🥺
🤍🤍🤍🤍
Satin Baby ɗaya jikinta har ya fara ƙyau dan tsutsan da kurajen jikinta sunata lafawa sai kuma mai afkuwa ta afku. A wani daren talata ALLAH ya amshi kayarsa. Duk wannan bidiri da akeyi ko sau ɗaya Bibaa bata taɓa zuwa dubata ba sai yau data rasu ta shigo tana wani kukan iskanci. Ai tuni Abba ya korata da tabbatar mata baya buƙatar ganinta a gidansa. Ta koma can inda ta fito. Hakama Mom ya hanata shigowa sam ita duk danginta. Ashe yanzu tana a wani kango ne zaune tana jiyyar kanta. Ta sake lallacewa da fita hayyacinta. Sanadin wannan hanata shiga ta yanke jiki ta faɗi, sai ɗaukarta mutane sukai suka maida kangon jiki ya shanye. To koma dai yayane ALLAH ya gafartama Baby. Ita dai tata kuma ta zama labari. Addu'a kawai take buƙata. Naso taimakon Mom dan koba komai ita ɗin uwace a garemu, amma koda mukaje kangon sai tace bata buƙata. Ganinmu ma bata son yi sam a rayuwarta. Dan mune muka zame mata sanadin komai. Da iyayenmu basu mutu mun shigo rayuwarta ba da bata aikata abinda ta aikata ba har ake ganin laifinta. Hankalinmu ya tashi da kalamanta. Amma Hafizzullah da Fahad suka gaggaya mata magana sukasa muka baro wajen. Anayin addu'ar bakwai ɗin Baby ma duk muka kama gaban mu.
A wannan komawar ne kuma na fahimci inada shigar ciki. ALLAH ya taimakan Heedaya ba wani damuwa tai ma da mama ba. Sai kawai nace masa zan yayeta tunda dai wata biyu ya rage ta cika shekara biyun da yake buƙata. Zai fara min tujara na sanar masa ina hasashen kamar cikine da ni. Ai tuni ya ajiye fushi gefe ya rungumeni cike da farin ciki. Haka ya kwasheni mukai asibiti. Tun a gwajin farko ma aka tabbatar mana da shi sai dai ƙaramine sosai. Munyi farin ciki sosai, Ummie tazo ta ɗauke Heedaya zata yayeta a can. Bai so hakan ba amma babu yanda zai yi, nasan kuma abinda yake tsoro kar Ummie ta riƙeta, saboda Awwab ɗin Yaya Hayatu tuni ta ƙwace. Ni nasan sai dai haƙuri, dan bana jin Ummie zata barmu da Heedaya kam daman. Alhamdullah haka naita rainon cikina cike da kulawarsa, inada wata na biyar muka wuce Nigeria bikin Hafizzullah da Fatimansa. Bikine na ƴan gata da akaima shiri tako wanne fanni. Dan duka ɓangarorin biyu mun shirya tsaff. Yayinda ango keta rawar kai da abokinsa kuma yayansa Fahad. Munsha biki kam Alhmdllh, dan mun haɗa taro na nunama tsara. Ummie da Mama balki ne iyayen ango kuma na amarya. Yayinda mu ko muke amsa sunan manyan yayye. Ana gama biki washe gari ba mutunci Hafizzullah ya ɗauke matarsa suka baro Nigeria, wannan kam duk shirin Fahad ne. Sai neman amarya da ango mukai muka rasa. Yaya Awwab ya turnuƙe Fahad da faɗa kuwa. Aiko yayta soshe-soshen kai wai wannan ta faru kam sai haƙuri.......✍️
*🤣🤣 ALLAH dai ya shirya yayan angon nan gaskiya. Har shima dai angon yana buƙatar addu'a 😂.*
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒉𝒖𝒏𝒅𝒓𝒆𝒅 & 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒇𝒆_
*_Nagode sosai ƴan uwa da ƙoƙarin following ɗina da kukai. ALLAH ya bar zuminci. A ringayi ana sayen kaya kuma to karku hanani zama Ɗangote 😂, Makka ina son zuwa. Sannan na zagaye kasashen duniya duk da wannan sana'ar 😂😂😂. Ina godiya love you all 😘😘😘✨._
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JJkSofA4Hto57YwEu2Z8Xq
*_Wai ni Balki ina duk masoyan Bilyn Abdull ɗin nan dake a manhajar Instagram da TikTok ne?🤔? Kai jama'a gaskiya da kunya ace account na Bilyn Abdull a Instagram da TikTok iya kar fallowers ɗin kenan🥲😣. Ina masoyan facebook ɗin nan dana WhatsApp, Please a fito mana ai fallowing ɗina. Accounts ne na Bussines ko bazaki/zaka saya ba zakaga abinda ya burgeka ko kalarka ka nema a inda kake. Maza ku garzayo BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING kodan kashe kwarkwatar idanunku ku more kallo iya kallonku da kaya ƴan yayi cikin farashi mai sauƙi da rahusa. Muna bada sari, muna adashen gata, muna sai da ɗai-ɗai. Ka gani su burgeka, ka saka ka birge mai kallonka sai Bilyn Abdull online shopping. Bari muga akwai ƙaunar kodai-kodai....😉🫣. Ga link nan naga accounts ɗin nan biyu kamar zasu fashe da fallowers 😘😘😘😍😍👍🏻👇🏻_*.
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buɗe ido ƙasar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauƙi ta sama muku sauƙin tafiya cikin ƙa'ida da bin dokar ƙasa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buƙata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂😍👍🏻._
.......Ango da amarya sun fece mu miya rage mana. Sai mu haɗa kayanmu mu kama gabanmu muma yan biki. Dan haka Yaya Awwab yace sai mu wuce. Sai dai kafin hakan ya ɗaukeni zuwa Alheri tv. Inda aka sake faɗaɗawa da ƙawatawa aka zuba masa kayan aiki da samunsu kam bako ina ba. Sai da muka gama zagayawa mu duka dan har su Ummie muka je sannan ya kamo hannuna ya saka min takardu a ciki. Duk da na taɓa gani tun a sanda ya sayesan sai naji jikina yama kama rawa. Bamma san na faɗa jikinsa ba ina hawaye. Aiko su Ummie suka hau mun dariya da su MD. Yayinda Mansoor yay ƙasa da kansa kawai yana mai danne abinda ke cimasa zuciya daya gagara ajiyewa. ALLAH ya sani yana son Samraah har yanzu. Amma yana ƙoƙarin mancewa da bama matarsa kulawa da yaronsu. Fatansa kuma ALLAH ya cigaba da saka masa haƙuri da juriyar hakan. Dole dai tafiya ta ruguje dan Ummie tace sai anyi walimar buɗe wajen. Aiko walima aka shirya gagaruma ta nunama tsara. Aka gayyaci ƴan media sosai a wajen. Yau dai mutumina ya daure ya magantu, sai dai yace ni kaɗai zan masa tambayoyi. Hakan kuwa akayi, na tattauna da shi kamar yanda nima akai hira da ni da gaba ɗaya ma tawagar tamu. An gama samar da ma'aikata dama. Ni da Ruƙayya kuma zamu cigaba da aikinmu sai dai daga can ƙasashen da muke dan boss yace bazai taɓa yarda yana wani waje ba ni ina wani, hakama Yaya Musaddiq.
Washe gari duk muka wuce. Ta tabbata dai Ummie ta kwace Heedaya da Awwab. Dole kuma mun bar mata. Garama su Yaya Hayatu su akwai wani a gabansu. Muko fa sai fatan ALLAH ya saukeni lafiya kawai. Mun koma gidan daga mu sai Auta, shima a mafi yawan lokuta yana makaranta. Sai kaɗaici ya fara damuna. Dan Fateema nan zasu dawo idan sun gama honeymoon ɗin saboda makarantar ta. Dole nasa Ummie ta samo min ƴammata guda biyu, duk da Gwaggo Gudidi bata so haka ta shiryo ta dawo nan dan takanas Maash yaje har Nigeria ɗin ya ɗakkota. Ita ta cigaba da kula da ni har ALLAH ya saukeni lafiya. Wannan karon ma anan na haihu. Na samu Baby Boy. Yaro yaci suna Abdul-wahab. Rikicewa nayi dan ban taɓa zaton hakan ba, nayi zaton sunan Paah za'a saka ko Abie. Rasama mi zancema Yaya Awwab nayi sai kawai na rungumesa ina hawaye. Shima dai wannan sunan anyi shagali, dan kamar da gayya ma Yaya Awwab ɗin ke komai. Yanda yake kashe kuɗi har tsoro abin yake bani. Kowa kuma ya fahimci murtani ya sake maidawa akan taron sunan Heedaya daya haɗa cece kuce. To koma dai miye ALLAH ya raya mana yaranmu ta albarkaci rayuwarsu. Itama dai Fateeman Hafizzullah da alama an gamu, dan sai zubda kananun yawu akeyi. A haka muka je Nigeria bikin Malika itama da aka kai Niger. Ta koma kusa da ƴan uwanta su Azizat da suma zuwa yanzu duk sun haihu.
*_YEARS LATER_*
Rayuwa makaranta, daga wannan aji zuwa wancan. Sam-G ta da yanzu ta koma Samraah uwa. Uwar yara biyar ciff dan Yaya Awwab ba ruwansa da wani ƙa'ida. Idan son samunsa ne ma na ƙara. Amma dai nace masa in sha ALLAHU nayi kenan. Bayan Abdul-wahab, nayi Ibrahim, Abie, nayi Paah Mu'azz. Sai Auta Hayatu. Heedaya ce kawai mace. Yaso da fatan na ƙara mace saboda na lura yana matuƙar son ƴaƴa mata, amma sai ALLAH bai ƙaddara hakan ba. Dan haka tuni ya rakito yarinyar Fahad da taci sunana da ta Hafizzullah suma first born nasu mai sunan Mamanmu. Sai ta Yaya Musaddiq itama mai sunana. Ni kaina naji daɗin hakan, dan Heedaya na hannun Ummie ita da Awwab ɗin su Aunty Falaq. Idan ka ganta wajenmu sai idan hutu sukazo. Shiko Hayatu ma basu da ƴa macen ko ɗaya yaransu biyar suma duk maza ne. Kasancewar yanzu suma suna nan kusa damu. To a hankali ma sai gidana ya zama matattarar yaran, dan da anyi hutu duk nan suke tattarowa su taho har Yaran Fahad huɗu, na yaya Musaddiq shima huɗu, Hafizzullah keda uku. Gida ya cika dam sai ranar tafiya aita kewa. Daga ni har shi hakan na sakamu farin ciki sosai.
Kamar dai yanzu ma haka duk suna nan tare damu hutu suke yi. Hayaniyarsu tasa na haye can sama na rufe kaina da security dan akwai aikin da nake mai muhimmanci. Inba haka nayi ba bazasu barni nayi cikin salama ba musamman ƙananun. Jin ana taɓa ƙofar na ɗago da sauri ina jiran naga waye zai shigo, nama manta na saka security, ubangayyar ne kawai zai iya buɗewa. Sai da ya shigo na sauke ajiyar zuciya. Dariya yayi da faɗin, “Lafiya irin wannan sauke ajiyar zuciya haka?”.
“Humm ALLAH bazaka ganeba my Hot. Yaran nan gaba ɗaya sun hanani aiki, shiyya na gudo nan ina ganin na tsira. Da farko na zata sune shiyyasa da naga kaine nai ajiyar zuciya.”
Zaune ya kai kusa da ni yana murmushi, sai kuma ya zame ya kwanta a saman cinyata bayan ya ture lap-top ɗin gabana da takardun. Dama zaune nake a carpet na gaban gadon. Hannu ya kai ya shafi fuskata muna kallon juna cikin ido, fuskarsa da murmushin nan da nake matuƙar so a hankali ya furta, “To da'
anan suke dindindin fa?”.
Idanu na waro da ƙyau na ce, “A da wataran sai dai ku wayi gari kai da su na gudu wajen Ummie na kawai.”
Sosai dariya ta kamashi, ya dungure min kai yana faɗin, “Matsoraciya kawai. Nima barci suka hanani su Auta kawo ƙara kawai shiyayasa na gudo nan dan nasan nan ne wajen ɓuyanki”.
“Oh ashe muna da yawa matsoratan”.
Dariya mukayi mu duka. Ya ce “Cigaba da aikinki bari nayi barcina”.
“A hakan?”.
Kansa ya jinjina min kawai yana lumshe idanun. Ganin haka sai nima nayi shiru dan na fahimci barcin yake sonyi da gaske. Idanunsa har sun nuna hakan. Wasa na fara masa da gashinsa, tare da fara masa labarin aikin da nake yi zan tura Alheri tv. Murmushi kawai yake yi idanunsa a lumshen har naji ya fara sauke numfashi. Sai kawai gasu auta a guje ana kiran Dadaa! Dadaa! Ammie!. Da sauri na dafe kaina. Suna zuwa ƙofa nai saurin zaro musu idanu da saka hannuna a saman lips nace “Shiiii!!!”. Duk cak suka tsaya suna kallona. Na sake musu nunin su koma Dadaa na barci. Saɗaf-saɗaf suka juya suka koma. Kaina na dafe ina faɗin, “Oh ya rabba, ALLAH ya shirya yaran nan sai da kuka gano mu”.
Idanunsa ya ɗan buɗe ya kallan, sai kuma ya maida ya lumshe batare da yace komai ba. A haka ya ɗauka remote ɗin ƙofar dake a kusa da ni ya saka mata security. Zanyi magana ya juyo gaba ɗayansa ya manne lips ɗinmu waje guda. Daga haka labarin ya canja aka maida aiki gefe.✍️
To nima dai ya kamata na koma gefe ƴan uwa😂🤣. Dan magana ta ALLAH na gaji🥱.
ALHAMDULLAHI
ALHAMDULLAHI
ALHAMDULLAHI.
Godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) da ya rayani har zuwa yau na kammala wannan littafi. Ina roƙonsa kuskuren dake ciki ya yafe min badan halina ba🙏. Abinda nayi dai-dai ALLAH ya haɗamu a ladan baki ɗaya.
Masoya! Masoya! Masoya!!. Ina godiya ta haƙiƙa a gareku da haƙuri da juriyar da kukai na bibiyata. Ina muku fatan alkairi a duk inda kuke. ALLAH ya kareku ya baibayeku da RAHAMARSA ku da zuri'arku baki ɗaya. Ni kaina ina muku so da ban san iyaka ba, musamman ƴan DANDALIN TSUTSAR NAMA kun sakani nishaɗi bana wasa ba❤️❤️😋😋🙏
Ya rabbi