Showing 261001 words to 264000 words out of 438336 words
yin barci. Kasa jurewa nayi, na rissinar da nawa idanun a hankali ina maida fuskata ƙasa. Sai kuma na ɗaura bayan hannuna akan hannunsa da har yanzu ke akan haɓata. “Yaya jikinka fa zafi, baka da lafiya ne?”.
Shiru kamar bazai amsa ni ba, sai kuma ya jawoni jikinsa a hankali ya rungume. Da ƙarfi na sauke ajiyar zuciya, dan wani ratsani zafin jikin nasa yayi har cikin ƙashi. Cikin kasa daurewa na sake faɗin, “ALLAH baka da lafiya. Please muje kasha magani”.
“Nooh!”.
Ya faɗa da ɗan kaushin murya yana sake ƙanƙameni. Tuno maganar Mama nayi da tace baya ƙaunar magani. Sai naji abin ya bani dariya ma. Namiji da shi babba amma yake tsoron magani. Mun jima tsaye a haka kafin na ɗago dan ƙafafuna sun fara gajiya. Cikin raunin murya kamar zanyi kuka nace, “ALLAH yaya ƙafafuna sun gaji ni dai”.
Baice komai ba, baima da alamar motsawa. Sai da ya mula dan kansa kafin ya ɗagoni. Ajiyar zuciya na sauke. A saman sofa ya kawoni ya zaunar, shi kuma ya wuce closet. Da kallo kawai na bisa ina mai sauke ajiyar zuciya. Sosai tausayinsu ya kamani shi da ɗan uwan nasa. Dan a kallo ɗaya zaka iya fahimtar tsantsar ƙiyayyar da sukema juna a bayyane take. Nayi nisa sosai a tunani har ya dawo ban sani ba. Sai da ya kama min hannu na dawo firgigit tare da ɗagowa na kallesa. Da sauri na kauda kaina, dan bathrobe ce a jikinsa blue black bai ko ɗaure igiyoyin ba, hakkan ya bama boxer ɗinsa damar bayyana da murɗaɗɗen jikinsa. Magana na buɗe baki zanyi yay min alamar zipping akan lips. Dole na haɗiye sai dai zuciyata sai faman dukan uku-uku take. Tsorona kar yace wanka zan masa. Wani wawan ajiyar zuciya na sauke ganin saɓanin hakan. Dan ƙofa ya buɗe muka fito, sai kuma na shiga wasi-wasin ina zamuje haka. Bamu fita ba a ta wajen bedroom ɗin nasa ya buɗe ƙofar da na daɗe ina tunanin ta bedroom ce itama, ashe ba haka bane. Dan gani nai kawai mun fito ta wani ƙyaƙyƙyawan waje da ƙaton swimming pool ne kawai a cikinsa. A yanayin kamar a ɗaki, sai dai ta saman ginin kana iya hango sararin samaniya, hakama ta jikin bango zallar gilashi ne da kake iya hango cikin garden ɗin nan. Ata ƙasa an matuƙar ƙawatashi da green carpet tamkar koriyar ciyawa farkon toho. Sai hakan ya bada wani irin ƙawa musamman da yanayin ruwan shi kuma ya kasance blue yana wani walƙiya da ƙyalli kamar kaci da haƙori. Sosai dogayen fararen kujerun da kallo ɗaya zakama tausasan katifun samansu kasan zasuyi laushi suka sake ɗaukar hankalina. Na shagala matuƙa da kallon wajen har ban san ma ya zame bathrobe ɗin jikin nasa ba. Sai da ya rungumeni ta baya sannan na ja ajiyar zuciya. Yanda yake mun numfashi ata bayan kunne yay matuƙar saka tsigar jikina ta shi. Bamma san na ƙanƙame hannunsa dake saman cikina ba ina ƙara manne bayana da jikinsa idanuna a rufe. Cikin soft and silent voice ɗin shin nan yana wani irin mun salo a cikin kunne ya furta, “Za kiyi wanka a ciki?”.
Sosai na ƙara ƙanƙame jikina ina jujjuya masa kaina dake a saman ƙirjinsa.
“Why?”.
Ya faɗa yanayi kamar zai ciza kunnena. Jinai jikina yana neman fara rawa. Lips ɗina na rawa na ce, “Yaya wlhy tsoro nake ji. Ban taɓa shiga ruwa ba irin haka”.
Komai baice min ba, sai ɗan kwalina daya zame yana ƙoƙarin cusa hannunsa cikin gashin. Tanan kuma ɗayan hannunsa na yawo a jikina. Cikin ɗan ƙarfin da ya rage mun da sauri na janye jikin nawa dake ƙoƙarin fara rawa ina sauke numfashi da sauri-sauri. Komai baice da ni ba, bai kuma kallan ba, sai ƙarasa sakimmin hannun da yay a hankali. Idanuna na runtse, kusan minti ɗaya na buɗe su da sauri saboda jin ƙarar faɗawarsa cikin ruwan. Waro idanuwan nayi sosai ganin yanda ya wani nutse can ƙasa gaba ɗayansa sai motsin ruwan kawai kake gani ta sama.......✍️
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒇𝒊𝒗𝒆_
......Gaba ɗaya na shagala nayi da kallon yanda yake action a cikin ruwan da style kala-kala tamkar wani kifi. Yafi minti biyar kafin ya miƙe tsaye ta jikin bango ya wani furzar da ruwan dake bin fuskarsa da gaba ɗaya kwantaccen gashin dake kumatunsa da na saman kansa suka kwanta luff kamar ka zauna kaita kallonsu. Idanunsa kam sun ɗan kaɗa tare da kanƙancewa. Da hannu yay min nuni wai na zauna a ta bakin ruwan. Kafaɗa na maƙe masa. Sai ya ɗan tsuke fuska. Hannu na kai na ɗan shafa gefen wuyana, sai kuma na shiga takawa a hankali har zuwa inda ya nuna ɗin na zauna. Nuni yay min da ƙasan rigata. Nan ma sai da na marairaice fuska amma yay kamar bai gani ba. Dole na nannaɗe rigar idanuna a lumshe na saka ƙafafuna a cikin ruwan. A tunanina zan jisa da sanyi sosai sai naji ɗumi. Bamma san na saki ajiyar zuciya mai ƙarfi ba da sakin ƙafafun gaba ɗaya a ciki har iya kusan gwiwata ruwan ya kawo. Daga sama kuma ina zaune ne na naɗe rigata da ƙyau. Murmushi na saki tare da ɗan kallonsa na ce, “Ashe ruwan akwai ɗumi Yaya”.
Fuska ya ɗan yamutse kawai batare da yace min komai ba ya ɗauke kansa. Nima sai na murguɗa baki dan yanda yay ɗin ya bani haushi. Cikin ruwan ya koma ya nutse, ban farga ba kawai na gansa ya fito ta gabana har sai da na tsorata ina neman cire ƙafafuna zanja baya ya riƙeni. Kallonsa nai ina ɓata fuska kamar zan yi kuka. Fuska ya ɗan ɓata shima, ƙananun pinkish lips ɗinsa ya ɗan taɓe da yarfa min ruwan hannunsa a kan fuska.
Baki na tura ina kai hannu na ɗiba ruwan nima da faɗin, “Ni sai na rama”. Karon farko ya saki wani makirin murmushi tare da riƙe hannun nawa ya jawoni gaba ɗayana cikin ruwan. Tsabar tsorata bamma san na fasa ƙara ba. Ruff kuwa ya rufe min baki da nasa. Sosai na ƙanƙamesa dan illahirin jikin nawa na cikin ruwan har kusan saman kafaɗa ta. Badan yama riƙeni ba duka zan nutse a ciki. Ya jima yana yanda yaso da ni kafin ya ɗago ya zubama fuskata ido. Koda wasa ban yarda na buɗe idona ba, dan wata irin matsananciyar kunyarsa nake ji matuƙa. Jin hannunsa a bayana yana sauke zip ɗin rigata da sake nutsani a cikin ruwan ya sani buɗe idanuna da sauri. A cikin nasa da sukai wani irin mugun canja launi zuwa na gawurtaccen zaki ya sani jin firgici na shiga jujjuya masa kaina. Da idanunsa yay mun nunin na rufe nawa idanun, da gudu kuwa nabi umarninsa ina sake shigewa jikinsa. Tsaff ya zame rigar gaba ɗaya, tare janye ɗan kwalina shima tsefaffen gashina ya bayyana. Ribbon ɗin dana kamashi da shi ya zare gaba ɗaya. Kunya tsoro gaba ɗaya sun sakani manne masa, wace irin rayuwace wannan da ranar ALLAH a maka tsirara a bainar nasi. Yo tsirara mana tunda da ga ni sai b&p kawai. Inaji ina gani ya shige dani cikin ruwan bayan ya maƙalamin gilashin shiga ruwa. Da ƙyar nake iya riƙe numfashina, sai nayi kamar sakan biyar sai ƴa ɗagoni sama. A gigice nake furzar da ruwa ina girgiza kaina, ina gama dai-daita zai sake maidani. Haka ya dinga yawo dani a cikin ruwan ina a jikinsa da salo kala-kala. Har sai da yaga ina neman jigata sannan ya ɗagani cak ya ɗaura saman dakalin wajen, ya yinda shi kuma ke jingine a jikina daga tsaye a cikin ruwan. Kunya ta isheni ga wahalar ruwa, na rasa yanda zanyi dole na haƙura na zauna a haka yana ƙare min kallon nan nasa na ƙasan ido....
✨✨✨✨
Tun shashsharewar ƴan biki Halime ta sake jangwaɓema Abba. Dan da gaske cikin na wahalar da ita. Da ga ƙarshe dai dole Gwaggo Gudidi tazo ta ɗauketa ta maida gidanta. Dan yarinyar na bata tausayi matuƙa. Komawar Halime gidan Gwaggo Gudidi tai matuƙar janye hankalin Abba zuwa can. Dan barci kawai ke kawoshi gidan nasa saboda har yanzu basu shirya da Mom ba. Sai dai ya maida aurensu batare daya sanar mata ba. Gwaggo Gudidi da Alhaji Sadisu da Alhaji Jafaru ne kawai suka sam hakan. Gwaggon taso ya faɗa mata, amma yace tayi haƙuri ba yanzu ba sai Jalilian ta sake ladabtuwa. Dan ya fahimci auren nan na Baby ma kamar sake tunzurata yake tana ɗaukar kanta wata tsiya.
To a ɓangaren Mom ɗin ma dai ta tattara Abban ta watsar. Dan gaba ɗaya hankalinta yanzu nakan ta yanda zata biya basikan mutane da taci a bikin nan. Sai kuma fatan itama Bibaa ALLAH ya kawo mata irin mijin ƴar uwarta. A gefe kuma sunata shirin tafiya saudia da jiran mijin Baby. Itama dai Babyn jiran nata suke dan gaba ɗaya maganar biyan bashin nan ta ta'allaka ne da ita. Amma sai sukaji shiru har kusan sati kenan babu wayarta babu saƙo. Ko message ɗin sun sauka lafiya bata tura musu ba. Sam basu kawo komai a ransu ba. Sai tunanin ai amarcine ya riƙe ta, dan sun san magungunan da suka ɗika mata bazasu taɓa tafiya a banza ba ai.
Wannan hope ɗin ya sasu tattara batun Baby gefe ɗan sauran kuɗin hannunsu suka shiga karkaɗar da su a neman hanyar da cikin jikin Halime zai salwanta da kuma yanda batun tafiyar Musaddiq China zai canja daga ƙaro karatu zuwa wani bala'i daban. Kai hatta ita kanta Samraah a wannan gaɓar bata tsira ba. Dan sunanta ya sake komawa wajen teachers akan sunaso a ƙuntata rayuwarta a gidan aurenta ta yanda bazata taɓa ta samu wani jin daɗi ba sam. Ta rasa ina zata dafa taji daɗi. Dan suna son duk randa Samraah zatazo gida tazo wujiga-wujiga da ita kamar korarrar ƙauyen cikin sahara a wulaƙance kuma dan su sami abin yin dariya da maidama dangin Abba murtani....
💞💞💞💞
Duk yanda yake ƙoƙarin hiding abubuwa game da ahalinsa al'amarin ya kasa yiyuwa. Dan tun barinsa gida bai yada zango ko ina ba sai ƙasar Niger. Kusan watansa ɗaya ya shirya ya sake wucewa Dubai wajen wani abokinsa. Damuwar da yake a ciki da halin fushi ya bama abokin nasa damar fara masa huɗubar shaiɗan da sake bin hanyoyin busar masa da zuciya. Jan ra'ayin Mansoor ɗin yake sosai akan fara safarar cocaine da miyagun ƙwayoyi har ma da wiwi. Tun Mansoor na dojewa har dai zuciya ta fara ingiza shi akan yayi abinsa. Miya rage masa a wannan duniyar banda ta neman arziƙi kawai tunda ya rasa masoyiyarsa ahalinsa basa ƙaunarsa.
A ranar farko daya amsa zaiyi ya kasa barcin dare sam. Sai zuciyace ke faman masa kai kawo. Tunani da rashin barcin suka haddasa masa tashi da matsanancin ciwon kai. Tun yana ƙoƙarin dannewa har al'amarin ya fito fili ranar dai abokin nasa bai samu damar kaisa wajen ogansa da yay alƙawari ba. Kwana biyu yana kwance kafin ya warke. Ya sake yunƙurin shiryawa abokin nasa ya kaisa wajen boss abokin nasa ya faɗi a bayi yaji ciwo. Nan ma aka shafe wasu kwanaki yana jiyya kafin ya samu sauƙi. Kuɗin hannun Mansoor sun fara janyewa, kasancewar kashewa kawai ake ba wasu ke shigowa ba. A karo na uku da za'a sake kaisa. Sukai accident ALLAH dai ya taƙaita basu ji ciwo sosai ba. Sai ma shine ya ɗan ƙuje a gefen fuska. Nan ma bai yiwu sunje ba. Daga nan fa Mansoor ya fara shan jinin jikinsa. Zuciyarsa ta fara buɗewa ya fara fahimtar al'amarin nan fa ba alkairin bane garesa shiyyasa aketa fuskantar ƙalubale. A karo na huɗu da abokin nasa yace suje sai ya doje. Nan fa ya shiga masa naci, sai kawai ya fito masa a mutum yace ya fasa.
Ran abokin nasa ya ɓaci, dan babu ɓoye-boye ya tabbatar masa da bazai yiwu yasan sirrinsu ba ya kuma kware musu baya. Dole ne cikin biyu ɗaya ta faru, kodai ya shigan kamar yanda sukai magana tun farko, ko kuma ya shirya amsar hukunci. Mansoor akwai zuciya, aiko take ya yayyaɓama abokin nasa baƙaƙen magana suka rabu walle-walle ya canja wajen zama. Shiru kamar abokin nan ya barsa, dan har ya samu aiki a wani companyn saida kayan yara yana ɗan samun kudaɗensa na shiga dan har ma ya manta abinda ya faru da abokin nasa sai kwatsam rana tsaka police suka zo kamashi har cikin companyn da yake aiki. Da farko dai ogan companyn da yake aikin yaso tsayawa a fito da shi, sai da yaji abinda ake tuhumar Mansoor ɗin da shi wai safarar cocaine, a yanzu haka ma an kama wata yarinya ne da ita cikin kaya tace shine oganta, shine dalilin da yasa aka kamashin ma.
Da farko Mansoor ya ɗauka zai iya kare kansa saboda yana da hujjoji da kuma ƙwarin gwiwar abokinsa ne ya masa sharri. Sai daga baya ya fuskanci al'amarin fa ba wasan yara bane ba. Dan ƙulline shiryayye mai kuma zaman kansa. A hakan ma yayi ƙoƙarin ganin bai tada hankalinsa ba, sai dai kuma ina da alama awannan gaɓar ƙarfin zuciya ko jarumta bata da wani tasiri. Dan ba jami'an Nigeria bane ba ƙasar sa ta gado da wasunsu kan juya baƙi ya koma fari in har aljihunka da nauyinsa taf.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚-𝒔𝒊𝒙_
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
......Tunda muka dawo ɗaki na fahimci yanata faman dafe kansa. Ga jikinsa akwai matuƙar zafi har yanzu dan ya matsa sai da na shafa masa mai. Black tea ya buƙaci na bashi. Hakan ya sani fita zuwa kitchen ɗinsa a karo na farko na dafa abinda ya umarceni, sai kuma na haɗa da ɗan spaghetti ko zai ci dan inaga kamar harda yunwa a al'amarinsa. Koda na dawo kwance na samesa yama ja bargo jikinsa. Har cikin rai sai da naji gabana ya faɗi. Tray ɗin na ajiye a side drawer na hau saman gadon. A hankali na ɗaga bargon ta saitin kansa. Hannnuna na ɗaura a saman goshinsa. Zafi sosai da har sai da tsigar jikina ta tashi. Jinai gaba ɗaya na daburce. Cikin damuwa na shiga faɗin, “Yaya Awwab baka da lafiya sosai. Dan ALLAH ka tashi muje asibiti. Ko kuma na kira maka Yaya Hayatu yazo kuje”. Na ƙare maganar ina ƙoƙarin sauka a gadon.
Cak na dakata jin an riƙo hannuna. Juyowa nayi na kallesa zafin hannun nasa ma na ratsa jikina. Idanuna na tara ƙwalla na ce, “Please Yaya ka barni naje na kira su. Wlhy bazan iya ganin ka a halin ciwo haka ba na barka.”
“Samrh”.
Ya kirayi sunana a wani irin can ƙasan maƙoshi. Muryata na rawa na amsa. Bai sake magana ba sai jawoni da yay a hankali na faɗo jikinsa. Duk da akan bargon dake lulluɓe jikinsa nake ina jin zafin zazzaɓin duk da kaurin duvet ɗin. Fuskata ya shafa a hankali yana wani lumshe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya gama canjawa. “Bana son kowa ya sani bani black tea ɗin na sha”.
“Amma Yaya.....”
“Shiii!!!”.
Ya faɗa yana mai lumshe idanun nasa da sake riƙoni jikin nasa da ƙyau. Bani da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan haka na miƙe jiki a sanyaye na zuba masa black tea ɗin a kofi. Hannu ya miƙo min alamar na kamashi ya tashi. Badan zan iya ba na miƙa masa nawa. Sai dai koda na kama shin sai ya zam nice ma na faɗa jikinsa alamar ya rinjayeni.
“My Tiger ashe babu ƙarfi”.
Ya faɗa cikin kunnena kamar mai raɗa. Tashi da tsigar jikina tayi ya sani mikewa zumbur ina tura baki. Shima sai bai sake magana ba ya tashi zaunen. Nuni yay min da filo, dan haka na ɗauka na sanya masa a baya jikin fuskar gadon ya zauna tare da jingina ƙafafunsa na a cikin duvet ɗin. Zama nai daga bakin gadon a kusa da shi ina facing ɗinsa. Na ɗauka mug ɗin na miƙa masa. Cat eyes ɗin sa masu tsananin tasiri a gareni na kaina ya amsa. Koda ya fara sha ɗin ma bai janye ba sai nice na duƙar da kai kawai ina tunane-tunane. Tas ya shanye dan irin mitsitsin kofin nan ne na rowa. Cewar da yay a ƙara ya sani ɗagowa